Showing 54001 words to 57000 words out of 135404 words

Chapter 19 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46348

zama a baki gadon bunun dake ɗakin.
“Shalele lafiya na ganki a nan?” ta tambaye ta cikin Muryar dake nuna tsantsar damuwa.
“Iya ai birni zan tafi nikam, tuni Arɗo ya sake ni”
Cikin ƙwalalo ido waje Iya tace
“Ya sakeki kuma? Jiya fa kika tare?”
Cikin sigar kwantar da hankali tace
“Eh Iya ni na saka shi, birni nake son tafiya, nima ina so na zama Ƴar gayu, na zama abun alfahari gare ku.”
Duban ta Iya tayi kafin tace
“Duk da haka ban ji daɗin kashe auren ki da kika yi ba”

Hawaye ne suka zilalo daga idanuwan yayin da suke sauƙa akan kyakkyawan kumatun ta. Duban Iyar tayi cikin ido tace
“Iya na gaji, tunda nake kullum jefa ku cikin damuwa nake saboda wannan”
Ta faɗa tana nuna hannun ta
“Hannu na shine dalilin komai, Iya zan koma birni nima na gina rayuwa ta kamar yadda Aunty Jiram ke faɗa min”
Cikin karyewar zuciya Iya ta dubi shalelen tata sannan ta saki murmushi
“Duk da haka muna buƙatar ki Shalele, ƙaddarar ki ce haka, mu bamu gaji da ke ba kuma bazamu gaji da ke ba koda kuwa kece zakiyi silar ajalin mu”

Murmushi itama tayi tace
“Iya ta kenan, banajin zan cigaba da zama da ku, Ni ɗin annoba ce ƙwarai, amma duk dare kwanan nan sai an ƙira Ni zuwa birni....dole naje birni iya a can ne zan zama mutum kamar kowa...gaskiya ne Ni ba cikakkiyar mutum baceeeeeeeee”
Ta ƙarasa cikin murya mai fidda wani razanannen amo.

Jikin Iya har rawa yake ta rasa ya zata yi, bayan wasu daƙiƙu kuma ta koma kamar ba ita tayi ihun ba. Duban Iya tayi tace
“Ki amince da tafiya ta saboda hankali na duk ya tafi can, zan dawo gare ki a matsayin cikakkiyar mutum Iya ta, ina ƙaunar ki. Sannan idan Baffi ya dawo ki sanar da shi, duk wanda ya tambayi ina nake kuce na tafi birni....zanyi kewar ku Iya”

Iya ta goge hawayen ta tace
“Shikenan Shalele na amince ki je birni, kije birni Shalele na! Ina so ki zama abar alfahari a gare ni, zan so kiyi rayuwa mai kyau”
Murmushi tayi tare da rungume Iyar kamar zata mayar da ita ciki, sun ɗau tsawon mintuna kafin ta saki iyar tana miƙewa tsaye.

Daga haka ta nufi bukkar ta....duk kuɗaɗen ta da ta tara na maganin mata ta ƙwaƙulo su tare da fara jera su. Sai da ta jera sannan ta Ƙirga taga dubu 20 cif, haɗa su tayi da kuɗin da Arɗo ya bata ₦2000 sannan ta ƙulle su cikin wani tsumma, daga haka ta miƙe tare da komawa ɗakin Iya.

Jakar Ghana Must go da aka saka kayan auren ta ciki ta janyo tare da saka kuɗin ciki, iya kuma duban ta kawai take cikin karyayyiyar zuciya da kuma tausayi.

“Tabbas ta cancanci rayuwa mai kyau, tun daga kan iyayen ta take fuskantar hukunci, hukunci maras daɗi, an mayar da yarinya rabi mutum, ya Ubangiji!” a zahiri kuma tace “Ka kula da Shalele na”

Bayan ta tabbatar ta haɗa komai nata ta ajiye gaban ta, hawaye na tsiyayowa daga idanuwan ta ta ƙarasa tana rungumar Iya
“Zsn wuce Iya, Baba na ma ki sanar da shi in ya buƙaci hakan, zanyi kewar kuuuuu”
Daga haka ta saki jikin iya tana ɗaukar Bagco nata ta ɗaura a ka.

A haka ta fice daga gida ta nufi hanyar bayan gari, duk da cewa bata san ina zata je ba haka take tafiya ba tare da waiwayowa ba.

(Safe trip Ƴar Iya.... Allah sada mu da alkairin shi)


*ALEE POV*


Bai wani jima ba ya dawo gidan, ko alokacin su Ishy basu bar gidan ba. Cikin takun shi na zaratan maza ya fito daga motar tare da nufar apartment ɗin su, fuskar nan tamau kamar dai Hamma Zaki yaron Mom 😒.

Ciki-ciki yayi sallamar yana sanya ƙafar shi ciki, ganin basa parlourn yasa ya haye sama zuwa bedroom nashi. Wanka yayi sannan ya kwanta kan lallausan gadon nashi. Bacci yayi niyyar yi amma kuma ya kasa, ya rufe idon amma ina, ganin baccin ba mai yiyuwa bane yasa ya janyo wayar shi ya fara latsawa don tunanin da yake addabar shi baya so ya samu matsuguni.

WhatsApp ya shiga Yana replying messages Wanda yawanci wishes ne ake masa, ɗaya ɓayan ɗaya yayi replying duka wishes ɗin sayin “Thanks”, “Thank You”, “I appreciated” “Thanks alot” amsoshin kenan.
Sai kuma messages ɗin Hamma Yusuf da su Dr. faruq wanda duk zolaya ce. Ba tare da yayi musu reply ba ya fice ya koma status, duk da cewa shi ba ma'abocin ganin status bane haka nan ya tsinci kanshi da sha'awar haka.

_Sarah_ ne farko, gaban shi ne ya faɗi ganin numbern ta a wayar, haka kawai ya tsinci hannunsa da shiga. Pictures nata ne da gani a bikin Hamma Zakin tayi. Sanye take cikin blue and pink sari wacce ta fidda ainihin kyau irin nata, doguwar sumar ta da ta jiƙa da gyara ga kuma wani mahaukacin hairstyle da akayi sai abun ya ƙara ƙayatarwa, pink 🎀 ribbon aka ɗan maƙala ta baya....nace Masha Allah.

Sai da yayi zooming gashin yana ƙara dubawa tare da lumshe idanuwan shi. Tunawa da kan Pretty da yayi wanda ya kasance kamar hamatar ɗan iska sai uban attachment da ta maka yasa yaja tsaki “Mtsss”. Bai tsaya ba yaci gaba da kallon Sara, fuskar Mom ɗin shi ne ta faɗo a ranshi nan ya ƙara tabbatar da cewa Sarah kyakkyawa ce.

Da ƙyar ya bar picture ɗin yayin da wani yayi appearing, wannan kuma ita da Captain Sulaiman ne, haka kawai yaji ranshi ya ɓaci daga nan ya fice yana viewing sauran statuses ɗin.

Sauƙa yayi daga WhatsApp ɗin ya koma Instagram nan ma dai karo yaci da pictures da kuma videos na dinner ɗin su, tsaki yaja tare da ajiye wayar gabaɗaya yana runtse idon shi tunawa da Pretty da yayi, ya kamata ya duba ta. Wata zuciyar tace
“Waɗannan bullshits ƙawayen nata na nan”
“To kai ina ruwan ka?” wata zuciyar ta faɗa mishi.
Miƙewa yayi yana nufar bedroom nata dake downstairs. Kamar kar ya Ƙarasa kawai yayi ƙarfin hali tare da danna kanshi zuwa hanyar, sai da yayi knocking jikin ƙofar sannan ya shiga. Su Ishy kuwa najin knocking suka wuce Toilet abunsu.

Da gudu tazo tayi hugging nashi tana sakin kukan shagwaɓa.
“Sweetheart ina ka shiga haka tun asuba ban ƙara ganin ka ba....”
“Sorry Nabees” abunda ya iya furtawa kenan sakamakon yanayin da ya tsinci ruhin shi da gangar jikin shi. Kissing nashi tayi sannan tace
“Ok shikenan kaga ko abinci fa ban ci ba”
“Baki ga abinci a dining bane?”
“uhm uhm Ni ban gani ba, ai baka ce min akwai ba”
“Sorie”
Hannun ta ta ɗaura a kafaɗar shi sannan tace “To muje ka raka Ni naci”
Kasa musa mata yayi sai ya bi bayan ta. Nan ma dai kukan shagwaɓa ta saka wai ita sai dai yayi feeding nata.

Haka ya zauna yana bata har ta ƙoshi daga haka tace yazo su gaisa da friends ɗin ta. Kamar ba shi ba ya haɗe fuska yace baya zuwa daga nan ya wuce sama ya barta a wuri tana kallon shi galala.

Sai da ya wuce tayi ƙwafa tace “Zaka gane baka da wayo ne, bari nayi sati zamu koma sai ka dawo kamar bawa na Captain....sai na wahalar da kai kwatankwacin yadda ka wahalar da Ni, mami da Daddy ma ba zasu Barka ba”

Ganin babu amfanin tsayuwar yasa ta koma wurin su Ishy waɗanda suke ƙunshe a Toilet har lokacin. Tunda suka fito suka ci gaba da budurin su hankali kwance.

Hamma Zaki tunda ya koma Bedroom ɗin shi yake jin shi wani iri, why yake ma pretty abun da take so? Me yasa? Ganin tunani na shirin saka mishi ciwon kai yasa ya diro tare da nufar Toilet, Alwala ya ɗauro yazo ya gabatar da sallar walaha tare da yin addu'oi, nan yaji ƙirjin shi ya yi sauƙi kamar an cire mishi wani nauyi. Daga nan ya yi musu order na Lunch sannan ya kwanta.


*SALATUL-DHUHA (Sallar walaha*

_Ya inganta ayi sallar dhuha raka'ah biyu da kuma raka'ah hudu sannan qna yinta dai-dai rana ta daukako lokacin da take da zafi._

_Akwai hadisi masu yawa wa danda suka zo da bayaninta da kuma falalar ta, daga ciki akwai:_


*1. Hadisi daga Abu Dharrin Al-ghifariy (ra) daga manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama):*

_yana wayar Gari cewa akwai Sadaƙah bisa kowacce Gaba dake Jikin kowanne mutum guda cikinsu:_

_kowanne tasbeehi Sadaƙah ne kuma kowanne tahmeedi Sadaƙah ne kuma kowacce hailala ma Sadaƙah ce kuma kowacce kabbara ma Sadaƙah ce._

_yin Umurni da akin Alkhairy ma Sadaƙah ne kuma yin hani Daga mummunan aiki shima Sadaƙah ne_

_kuma raka o'i guda biyu wadanda daya daga cikin ku zai sallata to Da walaha sunyi dai dai da wannan imamu Ahmad da muslim da Abu dawud ne suka ruwaitoshi_.__

_Wato wannan hadisin yana faɗakar damu cewar ladan sallar walaha yana daidai da ladan yin Sadaƙah sau dari uku da sittin kenan domin gaɓoɓi ɗari uku da sittin ne ajikin dan adam.

*2. Ga wani hadisin wanda yake Ƙara fitowa fili da bayanin da nayi yanzu shine hadisin da Imamu Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito daga sayyiduna Abu buraudah (Radhiyallahu anhu) cewa manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama) yace.*

_Ajikim Dan adam akwai Gabobi guda dari uku da sittin lallai ne gareshi ya rika sadaqah bisa kowacce gaba_

_FALALARTA_

_Sallar walaha dai-dai take da sadaka 360. Sahihu,Abu dawud(5242)_
_Sallar walaha tana ɗaga darajar mutum har ta kaishi zuwa darajar auwabina. Sahihun muslim(748)_
_Duk wanda yayi sallar walaha toh yana cikin kariyar Allah a duk yininsa. Sahihun Abu dawud(1289)_
_Sallar walaha dai-dai take da ladar umrah. Hasanun Abu dawud(558)_
_Sallar walaha wasiyyar manzon Allah ce ga al'ummar sa. Buhari(1178) muslim(721)_
_Sallar walahs aikine kaɗan amma lada mai yawa. Hasanun Abu ya'alah(6424)

_Ƴan uwa masu albarka muyi ƙoƙarin kasancewa cikin masu sallatar dhuha ko dan saboda ɗumbun daraja da falalar da take da shi. Allah ya bamu iko._



COMMENT & SHARE FISABILILLAHI!

[8/17, 6:12 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*










SHAFI NA “““57&58”””

*ƳAR IYA POV*

Tunda ta fito ta miƙi hanyar da zata sada ta da bakin titi bata ƙara waiwayowa ba. Yayi tafiya sosai kafin ta iso bakin titin. A wata ƴar rumfa ta yada zango har wani lokaci babu alamun abun hawa balle har ta tafi.

Tun tana jiran tsammani har dai taga abun na shirin fon ƙarfin ta ga wata shegiyar yunwa da take ji kamar tayi yaya. Ganin dai zaman bashi da amfani yasa ta fara tafiya akan titin yayin da bagco na kayanta ke bisa kanta. Tayi tafiya sosai kafin ta hango wata mota na tahowa, murmushi tayi har sai da kumatun ta ya lotsa yayin da farin ciki ya mamaye zuciyar ta.

Tsayawa tayi tun kafin motar ta iso tana ta kallon ta.
“Wai yau ni shalelen Iya zan shiga wannan abun, kai Aradu birni akwai daɗi, wayyo birni” Ta faɗa a zahiri ta kallon motar da ta tsaya gaban ta, cikin harshen Hausa drivern ya sauƙe glass ɗin tare da leƙowa yace “Hajiya ina zaki je?”
Shiru tayi tana tunanin ina zata ce, ita dai a rayuwar ta bata san wani gari ba in ka cire Gallara da kuma ƙauyukan da ke kewaye gashi ko sunan garin da tayi sukul bata sani ba.


Katse mata tunanin yayi da faɗin “Hajiya ko baki ji ne? Ina zaki je”
Can ƙasan maƙoshi tace “Birni zanje”
Daga cikin motar wani mutum yace “Wannan fa da gani bata da hankali, driver mu wuce tana ɓata mana lokaci”
Caraf maganar shi ta faɗa kunnen ta hakan yasa ta ɗago a zafafe tace
“Aradu nonon uwarka nasha shi yasa ban tashi da hankali ba”
Ƙoƙarin buɗe motar yake wai ta zage shi, driver ya katse shi da faɗin
“Haba malam kai ne fa ka fara zagin ta kuma yanzu kace zaka hukunta ta don ta rama”
Haka sauran ƴan motar suka yi mishi caaa wannan tace kaza wannan yace kaza. Ganin dai babu mai bin bayan shi yasa yayi shiru.

Driver ya ƙara kallon Ƴar Iya yace “Mu nan Bauchi muka nufa, Hajiya zamu wuce in Baki san yadda zaki ba”
Cikin rashin sanin madafar ta yasa tace
“Nima can zanje”
Daga haka driver yasa aka samar mata space ta shigo. Nan motar su ta miƙe sai Bauchi.

Awanni uku da abubuwa suka shafe suna tafiya kafin motar su tayi packing a Tasha, nan aka fara sauƙewa kowa kayan shi. Bayan Ƴar Iya ta sauƙa daga motar ta fara tunanin ina ɗaya zata nufa!.

Can ta hango wata mota a tashar ana ƙara ɗiban mutane, a hanzarce ta ƙarasa wurin. Ji tayi ana “Gombe, Adamawa”
Caraf tace “Gombo zani”
Dariya wani na gefen ta yayi yace “Gombe ake cewa” bata kula shi ba saboda kayanta da aka karɓa aka saka a Boot, ba'a daɗe ba motar ta cika bayan kowa ya biya kuɗin shi ta tashi sai Gombe.

Dai-dai roundabout ɗin dake ɗauke da signboard na Welcome to Gombe State ne wata gingimemiyar mota trailer da tayo loading shanu ta bugi motar su Ƴar Iya. Ƙiiiiiiii kake ji sai kuma na cikin motar suka fara ihu, wayyo Allah, mun shiga uku shikenan!. Ba tare da trailer ɗin ta tsaya ba ta ƙara ɓangare motar tasu nan da nan ta kifa itama trailer matuƙin ta da ya tsorata ya saki staring ɗin shi tuni tayi wani irin juyi. Mutane na ihu shanu na ihu har dai motocin suka tsaya lokaci guda kamar haɗin baki.

A lokacin ambulance ta iso tare da motar ƴan sanda. Da sauri suka nufi motar su Ƴar Iya tare da ɓanɓare ƙofar da ƙyar, innalillahi wa inna ilayhi rajiuun!!!! Mutanen ciki babu wanda ke motsi sai wani hijab baƙi dake tsakiyar su dake ɗan motsawa da gani kuma neman agaji yake.

Da sauri aka fitar da su ɗaya bayan ɗaya har aka gama sannan aka yi asibiti da su. Cikin ikon Allah ashe mutane uku ne kaɗai suka rasa ransu, sauran dai sun ji ciwo wasu da karaya wasun kuma gocewar ƙashi. Abun mamaki yarinyar dake ciki babu abunda ya same ta sai dai ta tsorata har ta shiga shock.

Mintuna kaɗan da faruwar hatsarin aka fara nunawa a gidajen talabijin da kuma rediyo. Ciki har da Ƴar Iya da ake magana akan abun mamaki babu abunda ya sami matashiyar dake cikin motar.

Inspector Suraj da kanshi yayi handling issue ɗin, and alhamdulillah duk an ɗaura waɗanda suka karye, masu gojewar ƙashi suma an daidaita kuma kowa Ƴan uwan shi sun zo.

Abun mamaki yarinyar dake cikin shin kuma babu wani nata da ya bayyana. Shi kuma inspector Suraj Yana son wucdwa Adamawa ne sai dai babu hali saboda wannan yarinyar. Ƙarshe dai shawara ya yanke bayan ya cike waɗansu takardu ya wuce da yarinyar Adamawa kan in ta dawo hankalin ta sai aji ina ne gidan su sannan a miƙa ta.


Jiya iyau dai matashiyar yarinyar bata farka ba hakan yasa yaci gaba da jinyar ta da yake a asibitin dake cikin estate ɗin da yake rayuwa take. Tana samun kulawa ta musamman kuma kullum sai familyn shi sun zo dubata....tsawon sati shiru yarinya taƙi farkawa Gashi dai numfashin ta dai-dai yake tafiya, zuciyar ta ma na bugawa dai-dai haka bp nata ma bai yi ƙasa ko sama ba amma abun mamaki shiru.


*CAPTAIN ALEE POV*


Tun daga bakin ƙofar da zata sada ka da ɓangaren zaka san cewa gidan ya sauya. Ƙura ce a parlourn ga kuma wani irin smell dake fita daga ciki, in ka tsura idanuwan ka a ƙasan zaka ga datti kamar dai abinci ne ya bushe.

Wai a cikin gidan nan kuwa Hamma Zakin mu yake rayuwa?, Mutumin da ya tsani ƙazanta, datti komai ƙanƙantar sa baya so amma gidan shi ne wannan 🤔.


Tsawon sati guda kenan Hamma Zaki ana cin amarci, sai dai wani abun mamaki kullum ƙara ramewa yake yi kamar dai ba wannan giant Hamma Zakin ba, miskilanci kuwa ƙaruwa yayi don yanzu gabaɗaya baya sakarwa kowa, ita kanta amaryar ya mugun sauya mata cikin satin ga kuma wani rashin mutunci da ya ƙago na hana ƙawayenta shigo masa gida.

Haushin shi sosai Pretty ke ji hakan yasa ta shirya zuwa gida don tayi maganin shi. Ranar juma'a da safe, misalin ƙarfe bakwai kamar kullum Hamma Zaki ya sauƙo daga bedroom ɗin shi cikin shigar kakin sojoji wanda suka yi mugun amsar shi.

Babu laifi yayi Fayau amma da ka ganshi in har ka sanshi zaka gano ramar da yayi, fuskar nan kamar an aiko mishi da saƙon mutuwa har ya ida sauƙowa, ganin irin dattin dake kacame a parlourn yasa yaja tsaki tare da nufar bedroom ɗin ta.

Cikin baccin ta ta jiyo ƙamshin turaren shi hakan yasa tayi juyi alamun ko sallar asuba bata yi ba. Tsaki yayi yana mamakin irin hali na Pretty, mace kamar ba mace ba ace common gyaran gida da girki ba zata iya ba.

Tabbatar wa da tayi shine yasa ta miƙe zaune tana hamma.
“ahhhhhh lafiya Sweetheart”
Cike da mamaki yake kallon ta, don shi kullum sai ta ƙunsa mishi abun mamaki hakan ko shine tata gaisuwar?. Banza yayi mata ganin dai zata ɓata mishi lokaci yasa yace “Please Nabees a gyara gidan nan duk yayi datti babu daɗin gani”
Daga haka ya fice abun shi.

Da harara Pretty ta bishi tace “Sai kayi kuma, mutum da shegen tsafta sai kace shine tsaftar kanta....mtsss zanyi maganin ka ne”.

Sai da ta tabbatar Hamma Zaki ya fice itama tashiga toilet tayi wanka, kwalliya ta cancara kamar mai zuwa gasar kyau kafin ta ɗauko wasu English fitted gown ta saka tare da fesa turare sai ta fito sak dadar roba lol😂. Wani siririn mayafin ta kamar net ta ɗauko ta yafa sannan ta fito.

Tsaki taja da ta iso parlourn ganin dagaske yayi dattin sannan tace “Ka nemo ƴar aiki in ka gaji ai” daga nan tayi waje. Tana fitowa tayi dialling wata number Bayan anyi picking tace “Yea, na shirya, Please don't waste time”daga haka ta yada zango a ƙayatattun kujerun dake compound ɗin.

Baa fo mintuna biyar ba wayar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login