Showing 96001 words to 99000 words out of 135404 words
ta gama shiri yasa ta jawo ta suka nufi part ɗin Granny.
Bayan sun jera abincin Khairy ta kwaso wasu flowers wai zasu ƙara armashi da danƙon ƙauna, nan ta jera su Suma. Sun gama jerawa kuwa watarta tayi ringing, ganin habibinta yasa ta ɗaga, ce mata yayi ya iso saboda haka ta rikice sai da Khairy ta tsayar da ita, “Wai ke a rikicen Zaki je masa ne, ko so kike ya Raina ki?, Kinga tsaya madam ki daidaita kanki kafin ki fita kin gane, ki bar abincin sai kin kaishi garden ɗin sai kizo ki ɗiba kinji, Allah bada saa ya nuna mana randa zamu kaiki dai”
Murmushi kawai Ayrah tayi ta wuce. Bayan ta raka shi garden ɗin tace bari ta kawo masa abun sha, Tray ɗin tazo ta ɗauka daga nan ta wuce.
Tunda ta gama wannan aiki Kuma damuwarta ta dawo sabuwa, Hakan yasa ta ɗauro Alwala tana ta jera sallali tana addu'ah. Har Ayrah ta dawo bata Daina sallar ba, tun tana Jira har ta gaji tayi magana. “Wai ke Khairy lafiya kike kuwa?, ko so kike gabas ɗin ta koɗe ne?, Kinga ni idar muyi magana sai ki ci gaba”.
Bayan tayi sallama ta idar ta juyo tana kallon Ayrah ɗin Alamar tana Jira taji daga gareta.
“Ke Khairy Allah Hamma Hammad yana so na sosai, kiga fa zoben da ya kawo min?, kin san shopping ɗin da muka je kwanaki naga wasu couples sun saya wallahi da kunne na naji ana ce musu 500k” zaro idon Khairy tayi tana faɗin “Gaskiya Kam yaci kuɗinsa, Allah ya Sanya alkhairi ya tabbatar da alkhairi ”
“Yauwa Khairy ga naku inji Hamma Hammad, yace in an saka Rana zai zo saboda ku saba nasan kema baki San shi ba”
Buɗe ledar ta fara tana murmushi “Ah wallahi bajau da mu, dole mu bashi ke ko bakya so iri wannan kyauta haka, ki yi mana godiya don Allah, tashi muje sauran wuraren” daga haka suka nufi ɓangaren Mom sai suka tare a part ɗin Nenne.
Bayan gurminsu da suka sha har zasu watse Khairy ta marairaice fuska tace “Babes, rabonku da Kuga Hamma Zaki tun yaushe don Allah?”
Kallon kallo suka aikawa juna suna sakin dariya. Fauzah tace “Lallai Yaya na ya kama zuciyar ƴar uwata” dariya suka yi gabaɗayansu Banda Khairy da ta ƙara marairaice fuska kamar Mai shirin kuka.
“Don Allah ni tambayarku nayi fa”
Fauzah tace “Yo ni tun yaushe ma, jiya ya shigo wurin Mom bayan dawowarmu kafin mu wuce gidanshi”
Ayrah tace “Eh na ganshi a part ɗinmu ma” Yesmeen ma tace “Har Masa naga Nenne ta zuba mishi”
Kai kawai ta jijjiga daga haka tace “Babes zan kwanta nikam sai da safe” dukkansu basu ji daɗin yanayinta ba Amma sun San halin. Khairy ba faɗa musu zata yi ba ko sun takura ta sai tace kaza ke mata ciwo. Cikin sanyin jiki ta koma bedroom ɗinta tana faɗin “Allah ka sa dai lafiya ”.
Wayarta ta ɗauko ta ƙara trying number sai dai baya shiga har lokacin. Ganin Haka yasa ta wuce ɗakin Granny wai tsoro ɗakin ta yau ke bata. Kamar jiya bata yi bacci ba hakan yasa ta miƙe ta fara jera nafilfilu tana roƙon ubangiji. Ta Kuma yi alwashin in dai zargin da take yiwa wannan shegiyar Mamin Prettyn ya zama gaskiya wallahi duk sai ta koya musu darasi, mutum bai ci ba bai sha ba kawai su saka rayuwarsa a haɗari?, ba zata tona musu asiri a yanzu ba saboda baby Humairah, Amma akwai ranar da zasu yi bayani. Bari dai gobe tayi sa gani ai.
_COMMENT & SHARE FISABILILLAH_.
[07/09, 2:23 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““97&98”””
Ko da gari ya waye ta cewa Granny zata amso kaya gidan Hamma, Amma da yiyuwar ta zauna saboda ta San ba zai samu abinci ba.”
Granny tace “Ni Kinga rabona da shi tun ranar shagalin nan naku, ko yana lafiya, Kinga ƙira min layinsa kafin ki tafi Ummul Khairy ” ta faɗa tana miƙo mara wayar tata. Gudun kar Granny ta kawo komai a ranta tayi dialling, still switched off Amma sai tace “Granny ta shiga Amma Ina ga ko yana aiki ne, zai biyo baya, bari nawuce”. “To Ummul Khairy a dawo lafiya” “Amin” Khairy ta amsa mata tare da ficewa, driver ta yiwa magana ya kaita har gidan Hamma Zakin.
*************************
Cikin ƙarfin Hali ya fara motsa jikinsa Wanda ko Ina ke masa ciwo. Tsawon mintuna goma kafin ya fara ƙoƙarin buɗe idanunsa Wanda sun Riga da sunyi masa wani mahaukacin nauyi ga Kuma kansa da ya Sara lokaci guda.
Kirif ya rufe idon nasa yana sakin jikinsa, can Kuma ya buɗe idon a hankali. Hannunsa ya miƙa gefe don kunna side lamp saboda matsanancin duhun da ɗakin yake da sai yaji hannun a ƙasa. Nan ya fara tariyo yammacin da mota ki bin bayan tasa, faɗan da suka fara da kume sheƙa masa Abu da suka yi Wanda daga nan bai ƙara tuna komai ba. Sunan Allah ya ambata yana faɗin “Ya Allah” sai Kuma yayi ƙoƙarin miƙewa Amma jikinsa yayi masa mugun nauyi ga wani irin ciwo da yake yi.
Ƙofar aka turo aka shigo, wani mutum ne saɓanin waɗanda suka ɗauko shi sanye yake da jallabiya sai facemask da ya Sanya. Hannunsa ɗauke da leda ya shigo cikin ɗakin. Sai a lokacin Hamma Zaki ya buɗe idonsa ganin haske yasa ya ƙara duba ɗakin. Babu komai a cikin ɗakin sai katifa wacce ko bedsheet baa shimfiɗa mata ba, tsakar ɗakin kuwa plaster ne aka yi, Babu wani wurin da iska zata shigo sai wani ɗan ƙararramin window da yake can saman ɗakin, ga Kuma wata ƙofa wacce bai San ta miye bace.
Ƙarasowa wajensa mutumin yayi tare da taimaka masa ya miƙe tsaye, ƙofar nan ya nufa da shi yace “Ga bayi nan, kayi wanka ga brush” ya faɗa yana miƙa masa sabon brushi ɗin da ya Ciro daga ledar “Kayi wanka idan kana so” ba tare da Hamma Zaki ya kula shi ba ya shiga bayin, Babu laifi a wanke yake Hakan yasa ya fara da wanke baki daga nan yayi Alwala don gaskiya ba zai iya wanka a wurin ba, idan yayi ma Babu yadda za'a yi ya Maida kayan jikinsa, fatansa Allah yasa su barshi ya koma abunsa.
Yana fitowa matashin ɗazu ya dawo, ko kallonsa bai yi ba ya ta-da sallah, bai San nawa ake binsa ba Amma dai yayi yadda yayi tunanin su suke gabace shi, sallolin kwana biyu kenan. Ko da ya idar mutumin ya miƙo masa plate Mai ɗauke da ƙwai soyayye sai Kuma bread, sai a lokacin yaji yunya, mutum na farko da ya tuna a wannan lokacin Ummul Khairy. Cikin ransa yace “Allah sarki, yanzu haka ta dafa tana Jiran nazo naci”. A hankali ya furta “Silly girl”
Babu yadda ya iya haka yaci abincin, sachet water ya miƙo masa. A ransa yace “Tunda Mom ta haife ni ban taɓa Shan wannan ruwan ba, Amma yau wai ni za'a kawowa shi, I must deal with the person accountable for keeping me here” daga haka ya amsa yana yamutsa fuska yasha.
Few minutes da fitar mutumin sai ga wasu gunguma gunguman mutane baƙaƙe wulik gasu munana, idonsa ya Kai kansu nan yaga wayarsa a hannunsa ganin tasa ce yasa yaji damm, a ransa ya furta “Kidnappers!”.
Ko da suka ƙaraso miƙa masa suka yi ya buɗe musu, bai Musa ba ya buɗe musu, call logs suka shiga, ganin Daddy yasa suka danna ƙira. Bayan an ɗaga ɗayansu cikin muryarsa ta ƴan ta'adda yace “Haloo”
A ɗaya ɓangaren sai da zuciyar Daddy ta buga dumm, sai ya Dake yace “Son!” “Ba shi bane!, kaga bamu ƙira don ka ɓata mana lokaci ba kawai in kana son yaronka ka tanadi quadrillion Naira, bama son aiki da Ƴan sanda, In ka saka su cikin al'amarin mu Ina tabbatar maka da zamu kashe yaron mu bawa karnuka namansa su cinye” daga haka ƙitt ya kashe dukkansu suka kwashe da dariya.
Allah sarki daddy kaɗan ya rage bai faɗi ƙasa ba, a hankali ya sa driver ya dawo dashi gida. Ko da ya iso yana shiga Mom ta fuskanci akwai damuwa tattare da shi, ga taɓa son tambayarsa Hamma Zaki don kwana biyu kenan rabonta da shi Amma ta fasa. A bedroom ɗinsa suka yada zango Mom na tambayarsa damuwarsa Amma bai faɗa mata ba saboda tsoron tashin hankalin da zata shiga. Ce mata yayi abokinsa ne ya rasu Amma yanzu zai je. Ko bayan fitarsa a mota ya ƙira number Ƴan uwansa yace su haɗu a masallaci, da yake duk suna gari ma basu ɓata lokaci ba suka zo.
Bayan sun hallara ne ya buɗe baki cike da tsoro da firgici yace “Yanzu aka ƙira ni da number Mai sunan ALHAJI, kidnappers ne Kuma since yana tare da su”
Uncle Suraj yace “Kidnappers?? Innalillahi wa Inna ilaihy raji'un, yaushe kenan?”
Daddy yace “Yanzu suka ƙira wai kuɗin fansa 1quadrillion” a fusace Uncle Suraj yace “Basu da hankali, Babu abunda za'a basu”
Ƙasa da murya daddy yayi yace “Kaga Suraj,mu bi komai a sannu, sunce in dai ƴan sanda suka shiga zancen zasu yanka shi ne, I don't want to loose my only son so early, zan haɗa kuɗin. Zan siyar da gidan da yake zaune yanzu, ga ATM ɗinsa ba lallai ya fita da shi ba yaran nan sun San PIN ɗin sai muje a cira, nan ma za'a samu millions, sai a haɗa a basu”
Dukkansu jikinsu yayi sanyi, Daddy yace kar a gayawa matan gidan Amma uncle Suraj insisted that a faɗa musu ko da addu'ah zasu taimaka. Ko da aka sanar musu kuka har an rasa Mai rarrashin wani, Granny Kam kamar zata zauce, ai Babu shiri Uncle Bello yace mata “Gobe za'a Kai kuɗin a amsoshi”.
Majina ta fyace tace “Tsinannun mutane ba zasu gama da duniyar nan lafiya ba, yanzu su rasa wa zasu ɗauka sai mutumin da baya shiga rayuwar kowa?, Allah ya isar mana, Maza Allah ya kare min Kai, shiyasa kwana biyu naji shiru, yau da zan ga mutanen nan wallahi duk sai na murɗe musu wuya”.
Sai da taso basu dariya da zancenta, haka dai gida ya koma kamar maƙabarta, Fauzah tace “Dama Khairy sai da ta faɗa mana tana Jin wani Abu zai faru da shi Amma bamu mayar da hankali ba, Allah ya bayyana mana shi”
Ayrah tace “Amin ya Allah, Fauzah kin san kwana biyu da suka wuce tun ranar speech na kasa gane kan Khairy, Ashe abunda zai faru da Hamma, idan taji na San sai ta fimu shiga tashin hankali duk da kusancin ƴan uwanta Dake tsakanin mu da shi”
Yesmeen tace “Ai dole, Khairy tana son Hamma Zaki wallahi, Allah dai ya dawo mana da shi”
Fauzah tace “Ameen, yanzu a faɗawa Khairyn ko?, Kinga sai ta faɗawa shegiyar Aunty Nabilar nan duk da nasan ba lallai ta damu ba don da gani kyau da kuɗi ta aura”
Ayrah tace “Mu bar batunta muyi masa addu'ah, a faɗawa Khairyn abunda ke faruwa.”
Nan suka ɗauki waya suka ƙira number tata sannan suka faɗa mata
*****************************
A fusace Hamma Zaki ya miƙe yayi kansu zai Kai musu bugu, cike da shaƙiyyanci ɗayansu yace “Eh lallai Kam, dole ka nuna mana Ashe fa soja jinin soja ne, yanzu mun San ka cika ai” sai Kuma yayi shiru. Ɗayan yace “Barshi, kaga yallaɓai idan a waje muka haɗu da uniform jikinka, Amma a nan mune yallɓais ɗin ka gane?, in kace zaka nuna mana halin to ƙill zamu je mu yanke kayuwan na GIDA kafin muzo kanka, ko ka samu Nasara kanmu kaga mun barka da mummunan tabo, yallaɓai a samu a fanshe ka mu samu kuɗaɗa” sai suka kwashe da dariya. Kamar zai yi hauka haka ya kaiwa iska naushi tare da komawa ya zauna.
Ɗaya daga cikinsu yace “Shegu kuɗi garesu fa dama, kaga Jikin baban nan fa kamar a taɓa jini ya zubo, da gani bai San wuya ba”.
“Ina kuwa zai sani, ƴan Abu ta kazar uba ni dai zanyi iyaka iyawa ta a kammala a bani kaso na nima na Gina tawa rayuwar, kowa yana son Jin daɗin nan fah, ah toh”
Haka suka ƙarashi zancensu suka fita ko uffan bai ƙara ce musu ba har suka fita suna rufe ƙofar ɗakin, nan duhun ya ƙara mamaye ɗaƙin kamar a Daren damina.
“Quadrillion” ya furta a hankali “Wai ma iya kuɗin fansarsa, lallai basu da hankali mutanen nan, kuɗin ce musu aka yi a ƙasa ake samu?, to wai me nayi musu da sai ni zasu kama?” Haka ya ƙarashi tunaninsa har ya gaji, can ya furta “Silly girl, she must be there waiting for my arrival, ya Rabb” ya faɗa yana dafe kansa “Have mercy on me, ka kare ni daga sharrin waɗannan mutane”
Nan ya fara karanta *Lā ilāha illā anta subhānaka innī kuntu mina-ddhālimina*.
_Masu karatu, ko kunsan irin tasirin wannan addu'ah ga Wanda ke a cikin damuwa?._
_Wannan itace addu'ar Annabi Yunus Alyhissalam a lokacin da yake cikin duhu iri uku, duhun cikin kifi, duhun cikin teku ga Kuma duhun duniyar ko da Annabi Yunus ya fara karanta wannan addu'ar ubangiji baigl gushe ba sai da ya samar masa mafita._
_Kema, Kaima, haka nima da kuma baki ɗaya idan kuka ɗauki addu'ar nan kuka samu yaƙini da Kuma Imani akanta Ina tabbatar muku zaku ga sauyi sosai, kuka ba shine maganin matsala ba, ku riƙe addu'ah kawai don ita ɗin makamin mumini Kuma garkuwar kowanne musulmi ne kamar yadda magabata suke faɗin الدعاء سيف المؤمن، الدعاء حصن كل مسلم._
_Ina mata masu azabtuwa gidan aure, Ina yaran da matan uba suke azabtar da rayuwarsu?, Ina kuke waɗanda kuke cikin damuwa, ku lazimci wannan addu'ah bi'iznirrahman zaku sha mamaki ƙwarai, ubangiji ya kare mu daga sharrin azzalumai, ya kare mu daga sharrin shaiɗanu daga cikin mutane da Kuma aljanu._
لإله الا أنت سبحانك اني كنت من الظالمين
_Wannan itace addu'ar Annabi Yunus, Lā ilāha illā anta subhānaka innī kuntu mina-ddhālimina._
*Ina tunanin zan ɗauke alƙalamina tunda bana ganin comments gaskiya😏, ya kamata ku gyara ku sani fa comments ɗin shine ƙwarin guiwar mu, munyi rubutu ya kamata ake motivating namu hilis, masoya Banda Sanya don Allah ana comments tare da sharing kunji mutanen kirki😉*
*Allah sarki team Hamma Zaki ana nan ana addu'ah Allah ya fito da shi, team pretty Kuma ana can ana murnar za'a samu kuɗi, team Khairy 😥😟.*
# Hamma Zaki
# Khairy (the great Ƴar Iya)
# Pretty
# kidnappers.
Let's see su waye da garin.
_Comment & share Fisabilillah_
[07/09, 10:00 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““99&100”””
“Innā lillāhi wainnā ilaihi raji'ūn” kawai ta furta daga haka ta kashe wayar ta ajiye gefe. Ɗakin ta fara zagayawa tana tunanin ta yadda zata ɓullowa wannan al'amarin. “Tabbas shi suke nufi, thank God naji hirar nan, dole zan San dabarar da zanyi su sake shi”.
Tunanin da wa zasu haɗa Kai wurin aikin take yi gashi Kuma ta rasa mafita. Kamar zata yi kuka tace “I know nobody here, yanzu zan fita na dawo.” veil kawai ta yafa dama yanzu ta yafe girki, wa iya kanta take yiwa ta shiga da shi ciki, majiya daɗin in sun ga dama suyi order in sun ga dama Kuma su fito su jagwalgwala.
Driver ne ya kaita har police station ɗin sai dai ko da ta shiga sai da tayi kyakkyawan tunani har zata isa wurinsu sai Kuma ta juyo, gida kawai ta koma tana huci.
Tana shiga ɗakinta ta ɗauko wayarta, group nasu n school ta shiga tana duba numbersa tare d fatan Allah yasa ta samu, ganin SUPER yasa tayi hamdala tana murmushi. Saving tayi ta koma contacts tare da searching number tana murmushi. Bugu biyu kuwa ya ɗaga.
“Ya halo”
“Ehm Hello super, Ummul Khairy ce ta ajin ku, ina yini ya gida”
Ko bi takan gaisuwar bai yi ba yace “Khairiyya iyayen kyau, ke ce yau Kuma d ƙira na?, Allah yasa dai lafiya”
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace “Lafiya b lafiya ba, don Allah kana gari ne?” “Eh” ya amsa mata. “Yauwa don Allah zan tura maka address ɗin yadda nake, in baka wani Abu kazo zamu yi magana”
Dariya kawai yayi yace “To Khairy iyayen kyau yanzu ma kuwa.”
Murmushi tayi ta sauƙe wayar tare da tura masa address ɗin, da sauri ta fita tayi masa warming pepper soup ɗin da tayi jiya Kuma bata ci ba, tana gamawa sai ga ƙira, da sauri ta ɗaga ganin super ne.
“Khairiyya gani na iso”
“Ok ka cewa gateman ya raka ka garden nima gani nan zuwa”
Daga haka ta gimtse ƙiran tare da ɗaukar tray ɗin tayi waje, veil ɗinta ta zara ta wuce garden ɗin Kai tsaye.
Gaisawa suka yi tana masa sannu da zuwa Amma shi ko a jikinsa kallonta kawai yake. Ɗauke Kai tayi tace. “Super don Allah akwai wani aiki da nake so ka taimaka min nayi, wallahi in yayi kyau zan baka har kuɗi in kana so, kafin nan dai ga abun sha ko?” ta miƙa masa cup bayan ya karɓa ta zuba mas pepper soup ɗin a plate.
Super ya sauƙe cup ɗin yana dariya“Khairiyya ai ke ce, ko wane irin aiki ne zan Miki, Amma me