Showing 69001 words to 72000 words out of 135404 words

Chapter 24 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46336

ne, ina sonka Captain, ina sonka sosai Captain!”
Haka tayi ta bin frames ɗin dake ɗakin da kallo sai yaba irin kyan da mijinnata yayi, “Tabbas nayi sa'ar samun Captain matsayin mijina, tabbas zan tsaya da anyi sabon aikin nan na kula don cikin cousins ɗin nan nasa masu kama da aljanu zai iya ƙyasa wa”, fuska ta ɓata tana wucewa Toilet ɗin shi.

Bayan ta fito main parlourn ta dawo, da yake babu kowa duk sai taji zaman ya ishe ta saboda haka ta fara chat abunta.

Tun fitar Pretty granny ke sauƙe bala'i kamar tana gabanta.“Ho ni Shatu, wannan wace irin mata ce?, Yo ai nayi mamaki ma, in Banda iya shege tazo ɗaki na kuma tana buɗe min hanci kamar wando,mtsss marar tarbiyya ko ina ya shiga sai ya nuna. Ai dole na nemawa maza mata don baya zama da wannan mai zubin shaiɗanun”

Kamar daga sama taji Khairy na faɗin “Granny ruwa zan sha”
“Yi haƙuri ɗiyar arziƙi wannan shashar duk ta ɓata min rai, karɓi ki sha abunki”


_To ga Pretty a Adamawan Yola fa, Mami Kuma tace za'a sabunta aiki, ga kuma ƙudurin granny ma, uwa uba ya kuke tunanin tashin Khairy?, Kasance da alƙalamina don jin yadda zata kaya._
_Comment and share please_


[8/24, 9:35 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*










SHAFI NA “““71&72”””

Kwana biyu suka shafe a gidan, Pretty dai damuwa tayi mata yawa sosai, gabaɗaya bata samun kan mijinnata, saboda haka yasa ta fara tunanin aborting cikin don babu yadda za'a yi ma ta fara cewa cikin nasa ne saboda kwatakwata ma sau nawa ne suka tara?. Dole ta samawa kanta mafita don ba zatai sakacin rasa kyakkyawan mijinta ba.

Khairy ma dai har yanzu babu wani kyakkyawan cigaba da za'a yi magana sai dai takan bi duk wanda yazo dubata ne da ido, babu wanda aka bari a baya wurin bata kulawa.

Yau Litinin, a kuma safiyar nan ne Pretty ta shirya zuwa asibiti don aborting cikin da wanda ake tunanin nasane bai sani ba. Sassafe ta tashi ko jira ya tashe ta bata yi ba ta nufi toilet. Wanka tayi ta shirya cikin wasu English wears sannan ta feshe jikinta da turare tana jiran zuwansa don tashinta kamar kullum. Around 5:58am ya shigo ɗakin da niyyar tashinta, ganinta zaune yasa yayi yunƙurin juyawa sai dai da sauri ta isa gare shi, cikin wata yaudararriyar murya tace “Good morning sweetheart”
Bata yi zaton zai amsa mata ba yasa ta buɗe baki don sanar da shi zata hospital sai taji yace “Morning” hakan ma ya faɗa ne cike da mugun jin haushinta.
“Sweetheart dama ina son zuwa hospital ne bana jin daɗi”
Sai da ya kusa fita ya juyo yace “I'll call the family doctor, zai zo ya duba ki”.
Cike da jin haushinsa tace “Wallahi sai naje, sai dai ka kashe ni, shegen baƙin rai, mami zata yi mana maganinka ne”

Ko da suna breakfast da yake tare da su Mom ne, da wuri ya miƙe saboda kallon da take aika masa. Fitowarsa cikin uniform ɗin da suka matuƙar dace da shi yasa Pretty jin daɗi. Sai da ya fita bayan Daddy ma ya miƙe, Fauzah ma ta fita ɗauko school bag nata ta kalli Mom cikin ladabin ƙarya tace “Mom, dama ina son zuwa shopping ne don siyo abunda bani da shi a nan”
Kawar da mamakinta Mom tayi tace “Kin sanar da shi mijin naki?”
“Eh ah dama na faɗa masa sai yace wai driver zai kaini”
Mom tace “Shikenan, zuwa 10:00am sai ya miƙa ki”
Bata iya ɓoye farin cikinta ba har godiya tayiwa Mom wadda ya matuƙar ɗaure kanta.

Alhamdulillah, yau tun safiya Khairy ta tashi kuma Alhamdulillah da warginta ta tashi. Murna wurin granny kamar tayi rawa. Darun da ta tasa wai zata je school yasa granny yin fushi, bata so hakan ba saboda haka tace ta haƙura.

Ko da Pretty taga motar da za'a kaita sai da ta saki baki, cikin ranta tace “Bazanyi sakaci na bar wannan daular ba, dole ka dawo nawa Captain” umarni ta bawa drivern ya kaita wani private hospital Mai kyau. Bayan sun isa ta shiga, card ta yanka daga nan ta zauna a reception tana jiran layi yazo kanta. Ba'a jima ba kuwa aka kira sunanta “Nabila Ali Naira” da sauri ta shiga don ganin likitan. Bayani tayi masa a kan abinda take so, da farko cewa yayi it's illegal Kuma basu yi a nan, daga baya ya amince tare da tambayar ta cikin wata nawa ne?, “3months” tace masa, Magungunan yayi prescribing daga nan ta fita pharmacy ta siya. Tana kammalawa tace ya kaita shopping mall. Pads ta kwasa sai wasu abubuwan saboda rufe baki da cewa shopping taje.

Can gida Hamma Zaki ya kira family Dr nasu in person of Dr. Faruq abokinshi. Ko da yazo suka gaisa da Mom ya sanar da ita yazo duba matar Captain ne tayi mamaki. Bata iya ɓoyewa ba tace “Bata jin daɗi ne?”
“Eh Mom haka ya faɗa min yace Please I should come and see her”
Haɓa ta riƙe tace “Ai kuwa ta fita shopping ma, ikon Allah”
“Kar ki damu Mom, inaga taji sauƙi ne”
Daga haka ya wuce abunsa, ko da Hamma Zaki ya tambaye shi yaje ce masa yayi Madam ta ɗan fita shopping amma zai koma in ta dawo.

Cikin sanɗa take taka steps ɗin yayin da takalmanta ke riƙe a hannunta. Tana isa last step kuwa tayi wuff ta shige ɗakinta ta zauna tana mayar da numfashi. Ba tare da bata lokaci ba tasha drugs ɗin kamar yadda Dr ya faɗa mata sannan ta haɗa da pain relief.

Few minutes ta fara jin mild ciwon ciki, a hankali kuma ya fara tsananta. Tun tana jurewa har ta fara fita daga hayyacin ta. Daga nan bata ƙara sanin yadda take ba sai wuraren ƙarfe 5:00 na yamma. Ganinta a ɗakin asibiti yasa ta fara maimaita innalillahi wa inna ilayhi rajiuun cikin ranta. Ganin mom ce yasa ta ɗan ji sanyi a ranta. “Kin farka, sannu tashi maza kici abinci” Mom da kanta tayi feeding ɗinta, bayan ta gwma Dr ya shigo ya ƙara duba ta, daga nan ya buƙaci ganin mijinta, an ci Sa'a kuwa lokacin Hamma zaki ya shigo room ɗin.

Bayan Dr yabi yadda yayi masa bayani kan cewa “Eh Yallaɓai matarka tasha maganin zubar da ciki ne and munyi ƙoƙarin ceto cikin sai dai ya riga ya zube. Yanzu tana buƙatar kulawa sosai, za'a yi discharging ɗinta sai aci gaba da kulawa da ita a gida”
Ba zaka iya banbance irin yanayin da yake ciki ba, Bayan anyi discharging nasu suka koma gida kai tsaye.

Bai ce da kowa komai ba ya fice daga motar bayan daidaita parking da yayi. Yana shiga Bedroom ɗinsa ya zube bisa faffaɗan gadonsa, shi kaɗai yasan azabar ciwon da kansa yake yi.
Bawan Allah jiniyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu ga wani ɓacin rai da yake ji kamar yayi hauka.
How comes ace matarsa nada ciki and unknowingly to him har tayi aborting cikin?, Nazari ya fara tare da lissafa zaman su, 8-9months kenan amma yana iya tuna last tarawar da suka yi about 6-7months back. To wane irin ciki ne wannan da drugs ya zubar da shi, tabbas baa daɗe da samun wannan ciki ba kenan, then how?. Da ƙarfi ya furta “Noooooo!, That's impossible” barazanar da zuciyarsa ke masa yasa ya runtse idonsa yana maimaita Innalillahi wa inna ilayhi rajiuun.

Khairy ce zaune a parlourn tana shan yankakken fruits da granny tasa a kawo mata. Shigowar sisters ɗin ta yasa ya miƙe da gudu tana hugging ɗin su.
“Khairy, sannu ya jikin?”
Suka haɗa baki suna tambayarta.
“Da sauƙi gobe ma zanje makaranta saboda na warke. Bana son a wuce ni”
Fauzah tace “Shikenan Allah ya ƙara miki sauƙi”
Ayrah ta dubi Khairy tace “Khairy Kinga Hamma Zaki da muke faɗa miki kuwa?”
Yamutsa fuska tayi tace “A'ah tukunna dai, kuka ce baya zuwa ina?”
Yesmeen tace “Ya fa zo, yanzu kam ya dawo nan da zama tare da muguwar matar tasa”
“Muguwa kuma Yesmeen?” Khairy ta tambaya.
“ke dai ki bari, ” nan suka kwashe labarin yada aka yi bikin suka faɗa mata fuskarsu ɗauke da damuwa. Cikin halin ko in kula Khairy tace “Amma dai zanso naga matar nan! Ni nan zanyi maganinta, kinsan nifa bani da mutunci?”
Dariya suka yi gabaɗayansu tace “Bari na baku labarin ni ɗin wacece”
Nan ta fara basu labarin rayuwarta ta ƙauye tare da Ai ƙawarta amma bata faɗa musu batun auren Arɗo da tayi ba. Sun ci dariya sosai kamar zasu yi kuka har sai da granny tazo tayi musu magana.


★★★★★★
*A GURGUJE*

Haka rayuwar Khairy ta cigaba da gudana cikin wannan ahali wanda suka zame mata komai na rayuwa. Kulawa da soyayya tana samu daga wurin kowa ina ka cire Boss ɗin gidan da matarsa. Wani abun mamaki da ya faru shine Khairy taci gaba da zuwa makaranta saboda Sheikh Imam ya samu ƙiran gaggawa kafin suje ƙauye, saboda haka ta bada himma kan karatunta, a term ɗinta na farko tayi ƙoƙari don hukumar makarantarsu da kanta tayi promoting ɗin ta zuwa JSS 3 instead of jss two.

Khairy ta ƙara kyau da kuma shiga ran mutane cikin sauƙi, tayi sabbin ƙawaye a school kuma babu laifi yanzu turanci kam ba'a magana. Tana kwatantawa don kuwa ko magana zata yi zaka ji ta jefa turanci a ciki. Ɓangaren karatun Alkur'ani ne dai babu cigaba sosai, amma karatun sallah kam ta koya kuma tana ƙoƙarin kiyaye sallah.

Wani sauyin kuma shine na halittar jikinta, Da yake tana cin mai kyau tasha mai kyau in ka ganta sai kace ta kai shekaru goma sha takwas amma shekarunsu 15 ne gabaɗaya.

A wannan lokacin ne kuma aka saka bikin Adda Salma da Adda Najmah. Adda Salma zata auri Dr Faruq ita kuma Adda Najma wani Captain ne abokin Hamma Zaki. Shirye-shirye ake yi babu kama hannun yaro. Kowa murna yake yi. Su Khairy sai shiri ake yi.

Yau Litinin suka je su kai ankon su ɗinki. A _Gorgeous tailoring service_ suka miƙa. Tunda suka shiga tailors ɗin dake wajen suka fara binsu da ido suna faɗin Masha Allah.

Khalifa shine Wanda yafi kowa iya ɗinki cikin wajen, so da suka isa Yesmeen ta tambaya “waye yafi iya ɗinki cikinku?”
Khalifa dake famar aikinsa ba tare da ya kalle su ba aka nuna. Cike da takunsu irin na yara masu tasowa suka ƙarasa.

Khairy ce ta fara isa tana mai sallama cikin sassanyar muryarta. Da sauri Khalifa ya ɗago yana kai dubansa gare su, cikin ransa yana faɗin “Tabarakallahu ahsanul kaliƙin”. Ɗauke da murmushi ya amsa Musa yana ajiye ɗinkin da yake yi.
“Ina yini” suka faɗa a tare. Washe baki Khalifa yayi yace “lafiya lou” Khairy tace “Don Allah kaine Khalifa?” “Eh” ya faɗa yana murmushi.
Yesmeen tace “Dama ɗinki muka kawo amma muna buƙatar shi ne da wuri, Allah yasa zamu samu”
“Ah babu komai zaku samu, kala nawa ne?”
“kala Uku uku ne, ya kama 12 kenan” Ayrah ta bashi amsa.
Zaro ido yayi yace “12?”
“Eh ba zamu samu bane?” Khairy ta jefa masa tambaya.
Murmushi yayi yace “A'a zaku samu, mu gani”
Fitowa da kayan Yesmeen wacce ke riƙe da su tayi “Gasu nan, ka faɗa mana kuɗin, sai ka bamu account numbern ka da mun koma a tura maka”
Murmushi yayi yace “Ku uku, da ke da ke” yana pointing Yesmeen, Ayrah da Fauzah “kuɗin naku 20K each, ita kuma wannan” ya nuna Khairy “Ba sai an biya ba”.
Ƙwalalo ido suka yi suna faɗin “Me?”
“Babu komai fa, dama haka nake aiki na, idan na mutane da yawa ne ina yiwa customers ɗina ragin na mutum ɗaya saboda su ƙara zuwa nan gaba”
Murmushi suka yi suna mishi godiya, sannan suka amshi account numbern shi suka wuce.

Tun a mota suke ta famar zolaya Khairy wai tayi goshi.
Ayrah tace “Amma fa babu laifi yana da kyau fa Khairy, mun samu wurin kai ɗinki yanzu kam” harara Khairy ta Banka mata caraf Yesmeen tace “Daina harararta mana Khairy ai gaskiya ne, Ni dai Allah yasa kar yayi mana rashin mutunci yayi naki yafi namu kyau” tafawa suka yi ita da Fauzah. Fauzah tace “Ai kuwa yayi haka ba zamu bashi ita ba”
Haka suka yi ta shirmen su har suka dawo.

_Comment and share Please_
[8/24, 9:35 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*










SHAFI NA “““73&74”””

A parlourn Granny suka yada zango sai mita suke yi. Granny na jinsu suna z ancen amma bata tanka musu ba.

@@@@@@@@@@@@@@@@@@@

Ina Hamma zaki ne da Pretty?, Sati guda suka yi Daddy ya basu umarnin su koma gidanshi su bar family house ɗin. Pretty tayi murna sosai ko ba komai zata samu damar yin yadda take so don yanzu yana ɗan sake mata kuma yana ƙoƙarin sauƙe mata haƙƙinta da ya rataya a wuyansa.

★★★★★★

Mom da kanta ta tura kuɗin ɗinkinnasu tana murmurshi saboda yadda suke ta zolayar Khairy. Kamar yadda yayi musu alƙawari kuwa ranar driver ya kaisu shagon su Khalifa. Tunda suka shiga yake ta kallon su, but kallon duk na Khairy ne.

Bayan sun gaisa ya basu ɗinkin Ayrah har da cewa a buɗe a gani idan yayi na Khairy yafi kyau sai dai su ma ya sake yi musu.
Ai kuwa su uku nasu yayi shige sai santi suke yi. Tunda suka ga na Khairy suka tada mishi rigima wai dan me zai banbanta su?. Shi dai Khalifa yaga ta kanshi ita kuwa Uwar gayya tayi musu banza kamar bata san suna yi ba. Ganin zasu ɓata musu lokaci gashi sai sunje saloon da sauran abubuwa yasa Khairy haɗe rai tace “Ku zo mu tafi Please”

Da ƙyar suka fito suna faɗin “Don naki yafi kyau shine kike wani kafsewa to wollah sai munyi magana”.
Murmushi tayi musu daga nan suka wuce.

Biki yayi biki inji Sarkin waƙa, tabbas duk wanda yaga bikin nan yasan anyi biki. Masha Allah an Kai kowacce gidanta wanda ya gaji da haɗuwa, ƴan rakiya suka dawo tare da barin kowacce da halinta.

Ranar Sunday Sheikh Imam ya ƙira Daddy Kan su shirya Monday suje garin su wannan yarinya don ɗazu ya dawo. Daddy bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da granny. Murna wurin Khairy kamar ba gobe musamman da aka ce tare da su Ayrah za'a je. Ta kasa zama sai haɗa wannan take da wannan duk saboda za'a ga iya.

Washegari da sassafe suka shirya, motoci biyu ne, ɗaya yaran ne da driver sai kuma ɗayar Daddy ke driving sai granny da kuma Sheikh Imam dake gidan gaba. Nan motoci suka lila sai Bauchin Yakubu.

Wass-wasa tafiya ake yi amma taƙi ƙarewa, duk tunaninsu ba wani nisa daga nan zuwa can saboda sun saba flight suke be koyaushe. Isarsu Bauchi suka yada zango a wani restaurant, bayan sun ci abinci suka siya tsaraba a wani wuri Mafi kusa daga nan suka nausa bisa titi. Tafiyar awanni uku suka yi suka isa Azare, basu ƙara 1hour ba suka iso Shira, hanyar kam babu daɗi saboda ramukan gashi duk jikinsu yaji.

Ai tunda suka miƙi hanyar Gallara Khairy fa hankali ya tashi, sai uban zuba take musu tana basu labarin tana zuwa wurin nan ita da ƙawarta A'i. Hango gidajen zana da kuma shanu da suka gani suna kiwo yasa suka fahimci an iso, saboda haka suka yi parking motarsu a dai-dai bakin kasuwa.
Mutane sai kallonsu suke yi suna mamaki, yara kuwa sai ihu suke suna faɗin “Yeye yaye wallahi wannan sunanta mota, in kaje birni zaka gansu, ahayye mota a Gallara”.

Su dai murmushi kawai suke yi yayinda Khairy ke musu jagora sai dai duk wajen wanda suka wuce cikin ƴan kasuwar sai tayi musu magana yayinda basa gane ta har sai ta bar wurin. Ai kafin isarsu gidan iya tuni zance ya isa mata cewa Ƴar Iya tazo wallahi ita ce ta zama ƴar birni.

Dai-dai ƙofar gidan Iya taja birki yayinda take tunawa da asalinta, a zahiri kuma kallonsu Sheikh Imam take yi. Granny tace “Ummul-khairy nan ne?”
“Eh granny nan ne”
Granny tace “Wallahi har na tuna lokacin da muke kiwo, mu shiga yaran nan”.
Da sallama a bakinsu suka shiga, Lale maraba, sannunku da zuwa, baƙi daga birni”. Ta ƙarasa tana shimfiɗa musu sabuwar bujukurar tabarma. “Maraba ku zauna” abun mamaki ko kallon Khairy bata yi ba. Da gudu Khairy taje ta rungume Iyar tana faɗin “Haba Iya ta kina gani na shine ko ki ɗan rungume ni?”
Sai a lokacin Iya ta gane cewa shalelenta ce ai tuni ta fara sharar ƙwalla tana faɗin
“Shalelen Iya kece?” lokaci ɗaya kuma ta sake ta tana ja da baya tare da ƙare mata kallo. Kamar wadda aka tsikara ta ƙara rungume Khairyn tana sakin kuka.
“Yau Allah yayi Shalele na ta waiwaye ni, Allah na gode maka ni Shatu”.
Tunawa tayi da tare dasu granny suke ta saki Iyan tace “Iya ga baƙi nan baku ko gaisa ba”
“Ai, wallahi duk na Shafa'a tunda na ganki, kuyi haƙuri, sannunku da zuwa maraba lale”
Granny tace “Yauwa sannu”
“Ina wuni ina gajiya, ya hanya kuma”
“Alhamdulillahi” inji granny “Tare muke da baƙi muma”
“Kuma kuka barsu a waje, ke Shalelen Iya shigo da su mana”

Bayan sun shigo ne aka sake buɗe babin gaisuwa. Nan Khairy ta sanar da Iya waɗannan sune Sabbin iyayenta, ” abun har abun dariya sai da aka ƙara gaisawa sai godiya iya ke zuba musu. Gyaran murya Sheikh Imam yayi yace “To dama dai akwai abunda ya kawo mu, amma kafin nan idan mai gidan yana kusa to da shi sai muyi muku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login