Showing 99001 words to 102000 words out of 135404 words
ya faru?” gyaran murya tayi tare da miƙa masa wayarta, “ka san wannane?”
Super yace “Ummulkhairy wannan ai yayan nan naku ne Ina wani babban soja?” Kai ta gyaɗa cike da gamsuwa tace “Yauwah anzo wajen, shi ne fah, to ka san meye?”
“A'ah sai kin faɗa”
“Kwana biyu ne da suka wuce aka yi kidnapping ɗinsa” zaro Ido super yayi yace “Innalillahi”
“To ni nasan wadda suka sace shi gaskiya” nan ta labarta masa abunda taji ranar Mamin Prettyn na faɗi.
Hannunsa a kumatu yace “To yanzu ya kike so ayi?”
Tace “So nake idan dare yayi yau, kazo gidan nan Amma ka rufe fuskar ka, dukkanmu ka fito da mu, ka tsawatar musu akan ka san suna da hannu akan sace Mai gidan, idan suka Musa kace musu akwai video da ka ɗauka daga CCTV camera lokacin da suke maganar, na tabbata zasu tsorata.”
“haka ne” super ya faɗa.
“To sai kace musu ka basu kwana ɗaya idan bai dawo ba zaka Kai su ga hukuma daga nan sun San sauran.”
Tafi yayi yana faɗin “Good! Ai kuwa baki da matsala zan yi yadda ya kamata”
Daga nan yayi mata sallama ya wuce.
Can ɓangaren Naira Family House an gama haɗa kuɗi Kam, sai dai suna tsumayin Ji daga kidnappers ɗin akan a Ina za'a Kai musu Kuma yaushe and yaushe zasu saki yaron a Kuma Ina. Kowa ka gani yanayinsa zai tabbatar maka ba lafiya ba.
*DARE*
*1:00am*
Cikin baƙaƙen ƙaya mutanen suka nufo katafaren gidan Hamma Zaki, ta zaman Katanga suka haura tare da shigewa da yake akwai haske basu sha wahala ba suka shiga cikin katafaren Parlourn.
Sanda ce riƙe a hannun kowa, duk ɗakunan Dake Parlourn sai da suka buɗe sai a na ƙarshen suka tarar da mutum, side drawer ɗaya daga cikinsu ya buga, nan ta miƙe a tsorace. “Fito waje” ya faɗa cikin kaushin murya, a razane ta fito zuwa wajen yana biye da ita. Haka ya hau sama nan ma sai gashi tafe da Pretty, Mami sai Kuma Ishy Wanda suke kuka, daidai wurin da Khairy take durƙushe suka nuna musu, da sauri suka ƙarasa Suma suka yi kneel down.
Ogan cikinsu Wanda ke riƙe da ƙatuwar sanda yace “Ku mutanen gidan nan Ashe ƴan ta'adda ne bamu sani ba?, ke!” ya faɗa a tsawace yana nuna Khairy “Cikinku waye ya sace captain?”
Kuka ta fara tana faɗin “Wallahi ranka ya daɗe ban sani ba, kidnapping ɗinsa aka yi Kuma kuɗaɗe masu yawa ake buƙata, ka yadda da ni ni ƴar uwarsa ce”
“Yi min shiru, an duka ki ne?”
“a'aah” ta faɗa tana ƙara kama jikinta.
Kallonsa ya mayar kan su pretty “Ku su waye a gidan nan?” Mami da jikinta ke mazari tace “Uwar matarsa ce ni, matar ce ta haihu sai nazo, wannan Kuma aminiyarta ne” “Ke dallah ya isa haka, anya ba ku kuka sace shi ba?” ƙyƙƙyafta Ido Mami take yayinda jikinta ke ɓari tace “A'ah mu Kuma mata da sata yallaɓai ”
Shiru mutumin yayi yace “A cikin ku huɗun nan ne Ina da ɗaukan video na maganar waɗanda suke da baki wurin sace shi, ko Kuna so na kunna”
Mami da pretty har da faɗuwa ƙasa “A'a yallaɓai wallahi ba sai ka kunna ba, kayi haƙuri kaji?”
“ke nan ku kuka sace shi?”
Sharaf sun manta da Khairy Dake wurin suka ce “Aah yallaɓai Amma Amma...”
Tsawa ya daka musu yace “Amma me?”
“Yallaɓai mu fa muna gida ba mu bane”
Sai da yayi dariya na tsawon lokaci yace “Bari kuji, idan har Baku sa an sake shi zuwa gobe ba, Kuma sai na sace ku sai ayi 1-1, Kuma bari kuji in ya dawo sai na sanar da shi that you guys are behind his dismissal, Kuma sai na kaiku gaban hukuma tunda ku miyagu ne”
Zaro Ido pretty tayi tace “Ka rufa min asiri yallaɓai, ai gobe goben nan ma za'a sake shi, don Allah kar ka faɗa masa cewa da hannu na, wallahi Ina son miji na”
“Hhh, kin san kina son sa aka haɗa baki Dake wurin sace shi?”
Ƙafarsa ta riƙe tana faɗin “Don Allah yallaɓai kar kayi haka, don Allah ”
Bata yi aune ba taji Mari akan fuskarta, ɗagowa gabaɗayansu suka yi don ganin waye, ba kowa bace sai Khairy. “Dama Ashe ba son Hamma kike yi ba, da haɗin bakin ki aka sace shi?, to wallahi yau ɗin nan ba sai gobe ba zan ƙira gida na sanar ku kuka sace shi, kin ma ci albarkacin jego wallahi da tsaf zan iya kashe ki da duka” ta ɗan dakata tana hararta, “Me kuma” ta nuna Mami “Allah ya shirya ki, saboda son abun duniya kika sa a sace sirikin ki!, tir da irin halinki, wallahi Hamma ya dawo sai kun gane kurenku”
Ɗaya daga cikin mutanen ne ya daka mata tsawa nan ta koma wurin zamanta “Ya isa! Yanzu akwai deal!, idan Kuna so asirinku ya rufu to kawai ku saki bawan Allah lami lafiya, in Kuma aa to hukuma zata yi aiki kanku, ke Kuma!” ya faɗa a zafafe yana nuna Khairy “Idan maganar su ne suka sace captain ta fito sai kin gane kurenki” Kai ta jijjiga daga nan yace kowa ya koma makwancinsa.
Hankalin pretty in yayi dubu ya tashi, suna shiga ɗakin ta hau Mami da faɗa “Kinga ai Mami sai da nace Miki kar ayi kika nace, gashi yanzu wannan aljanar yarinyar ma ta sani, ya kike so nayi idan Sweetheart ya rabu da ni?”
“Kinga daughter ba wannan ba, wai ta Yaya aka yi ma Hakan ta faru?, ni anya baki faɗawa wani sirrin nan ba?” harararta pretty tayi tace “Ni da nake gidan nan Ina zan fita, nidai ki San yadda Zaki yi kar a raba ni da sweetheart, don ba zan iya rayuwa Babu shi ba, shima Daddy ɗin duk kuɗin da yake da shi ai sun ishe shi”
Duka Mamin ta Kai mata “Ke fa baki da hankali, waye kuwa kuɗi zai ishe shi?”
Tura baki pretty tayi tace “Yanzu ni gaskiya ki ƙira Daddy tun yanzu su sake shi, in kuwa asirinmu ya Tonu Ina da tabbacin sweetheart ba zai raga mana ba, kawai a sake shi da wuri in ba haka ba wannan aljanar ƙanwar tasa ma ba barin mutane zata yi ba”
Ƙasa-ƙasa Mami tayi da murya tace “Ni fa anya ba ita bace ma ta San sirrin nan ba?” shiru pretty tayi can tace “a'ah bana Jin Hakan, ai kin san bata Hawa sama ma, Kuma lokacin da muka yi zancen har Fauzy sai da kika kora ta”
“Shikenan dai, ni fata na kada daddyn ki ma yace da ga gangan Hakan ta faru, Amma zan San yadda zanyi da shi”
Ita dai pretty shiru tayi wani ɓangare na zuciyarta na nuna mata gaskiya ɗayan Kuma na ingiza ta, ɗaya na nuna mata halin iyayen nata ba Mai ɓullewa bane ɗayan Kuma na nuna mata Hakan shine daidai. Tsaki ta ja tana juyawa abunta.
Shiru ne ya wanzu tsakanin su daga bisani bacci ɓarawo ya sace su.
Ɓangaren Khairy tana shiga ɗaki ta saki dariya irin wacce ta kwana biyu bata yi ta ba, tabbas ta shiga damuwar rashin Hamma Zaki, but now komai ya wuce, zata cigaba da rufawa pretty asiri saboda irin yadda take son Hamma, Amma tabbas sai ta hukunta ta.
Washegari da misalin huɗu Mami ta ƙira daddyn Pretty a waya, bayan ya ɗaga tace “Alhaji an samu matsala fa”
“Matsala ta me kenan?” ya tambaye ta.
“To fa jiya an shigo gidan shalele da dare Kuma mutanen sun tabbatar mana da cewa muna da hannu wurin ɓatan mijin nata, da farko mun Musa Amma sun tabbatar da Hakan da video Dake wurinsu”
“What!” daddy ya faɗa a zafafe
“E fa, yanzu haka abunda nake faɗa maka sunce ko a sake shi ko Kuma su miƙa mu hannun hukuma, kaga tun Abu bai yi zafi ba mu haƙura, ma hukunta su ta wata hanyar”
Zufa ce ketowa Daddy yace “Amma anyi ƴan Abu ta kazar uba, kuɗi sun Riga da sun kusa shiga kawai suyi mana haka, ai kuwa motarsa ba zata dawo ba,”
Mami tace “Shikenan, ma sake Sabon tsari kawai, Amma an mana shigar sauri gaskiya, ni dai ka saka a sake shi don ga shalele ma ta saka damuwa wai zai sake ta idan ya fahimci Hakan, ko don farin cikinta ALHAJI ka saka su sake shi ya dawo.”
“Shikenan Hajiya ta, zuwa ƙarfe Takwas ma zasu shaƙa masa hodar ibilis sai su fita da shi, in sun kawo shi bakin wani wuri sa ajiye shi sai a ƙira iyayen a faɗa musu Amma fa sai na amshi wasu kuɗaɗen duk da haka”
Dariya Mami tayi tace “Wani kayan sai amale, miji na ba zaka canza ba Kai Kam, ka kwasa Kam yanzu a neme su.”
[10/09, 7:53 p.m.] Famanté 💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““101&102”””
Yana kashe wayar ya saki tsaki, wayar Hamma Zaki ya jawo wacce take wajensa a palace ɗin nasa Dake cikin jejin, bugun fari aka ɗauka, a kausashe yace “Mun rage kuɗin fansar, zaku bada million ɗari zuwa ƙarfe biyar na safe, ku zo daidai junction ɗin kaza ku ajiye sai kuyi ciki zaku ga yaron ku ku ɗauka” daga haka ya katse ƙiran.
Ƙiran yaransa yayi yace suje wajen junction ɗin su laɓe, da zarar sun ajiye kuɗin su Kuma su ɗauke su yi gaba.
Hakan kuwa aka yi, tun 4:55 su daddy suka isa wurin da aka ce suje, suna ajiye kuɗin suka wuce ciki ai kuwa a yashe suka ga Hamma Zaki kamar gawa, da sauri suka yi kansa su ukun.
Uncle Suraj ne ya ɗaga shi kamar wani jariri nan suka ƙarasa motarsu suka yi gaba.
Asibitin da ke cikin estate ɗinsu aka Kai shi, nan likitoci suka hau kansa suka fara aiki.
Ɓangaren Khairy gari na wayewa tayi breakfast, tana ci ta hau sama ko knocking ƙofar ɗakin bata yi ba ta shiga. Tana shiga ta tsaya kansu tace “Ga can breakfast nayi ni zan fita, Mami ko?, eh Mami kiyi haƙuri ki sauƙa ki kwaso muku Kuma ki tabbatar yau kin Lula zuwa gidan mijinki ki bar ƴarki tayi zaman aure, ke kuma” ta nuna pretty “Bazan tona Miki asiri ba ko dan albarkacin Baby Humairah Dake hannunki, sai anjima” daga haka ta fara waving hanunta tare da juyawa har ta fita.
Wanka tayi ta shirya, daga nan ta ɗauki wayarta ta nufi waje, driver ne ya miƙa ta gida.
A lokacin da ta isa ta tarar da kowa fuskar nan Babu yabo Babu fallasa. Nan su Ayrah suke ce mata an sake shi, ta nuna murnarta sosai duk da cewa ita ta Riga ta San yau ɗin zai dawo.
Babu tsammani tace “Yanzu yana Ina Hamman?” sai da suka dara gabaɗayansu Fauzah tace “Omo see love bird” Yesmeen tace “Hmm to yana nan asibiti ki bari sai ya farfaɗo sai muje, naji Abba na faɗin wai cocaine aka sheƙa masa Amma zai iya farfaɗowa zuwa zuhr”
Ajiyar zuciya Khairy ta sauƙe tace “Ok, Allah ya Kai mu”
Nan suka fara tsokanarta wai masoyi zai dawo.
Da yamma suka shirya suka nufi asibitin Dake cikin estate ɗin, ko da suka je basu wani sha wahala ba nurse ɗin tayi leading nasu zuwa room ɗin da yake. Idonsa rufe lokacin da suka isa Hakan ya tabbatar musu da cewa bacci yake yi.
Zama suka yi yayinda Khairy ke kallonsa cike da tausayawa, ƙasa ƙasa suka fara tsokanarta wannan yace kaza wannan yace kaza ita dai bata ce musu uffan ba. Sai da suka gaji da zama ganin ba zai tashi ba Khairy tace “Babes ku tashi mu wuce ko?” miƙewa suka yi har sun Kai baikin ƙofa suka ji muryarsa “Kun gama gulmarku shine zaku tafi Babu gaisuwa”. Zare idanuwa suka fara ba tare da sun juyo ba. Ita kuwa Khairy taji daɗi da yaji su, addu'ah take Allah yasa yayi maganinsu.
Juyawa suka yi kowa kansa ƙasa sai famar zare idanuwansu suke, a kunyace suka haɗa baki wurin faɗin
“Ina yini Hamma” basu sa ran zai amsa ba hakan yasa suka ƙara haɗa baki wurin faɗin “ya jikin, Allah ya ƙara kiyaye gaba” “Amen” ya furta. Tsaye suka yi ba tare da sun ɗago ba sai dai lokaci zuwa lokaci Khairy kan sci kallonsa yayin da shima hakan ke faruwa a ɓangarensa sai dai da suka haɗa ido sai kowa ya kauda kai.
Mintuna shida suka shuɗe hakan yasa Khairy zungurar Fauzah dake gefenta, sai dai abun da bata sani ba Hamma Zaki ya ganta. Batare da sun ɗago ba Fauzah tace “Hamma zamu wuce Allah ya kiyaye gaba” amsawa yayi da “Ameen” daga haka kuma suka nufi ƙofa, Fauzah gaba sai Ayrah biye da ita sai kuma Yesmeen, Khairy ce karshe, tana shirin fita ta tsinkayi muryarsa “Zo nan” kamar ba zata juyo ba ko me ta tuna sai ta juya kanta ƙasa don har yanzu kunyarsa take ji, ai sai yayi tunanin ita ke musu ƙaryarr suna soyayya ma.
Kamar zata yi kuka ta ƙarasa, da yatsa ya nuna mata kujerar da ke gefen gadon, babu musu ta zauna tana duƙar da kai kamar wata munafuka. Muryarsa taji yace “Ina kuma zaki je ba zaki yi jinya ta ba?” tayi matuƙar mamakin jin hakan har sai da mamakin ya bayyana ƙarara akan kyakkyawar fuskarta.
Samun kanta tayi da faɗin “Kayi haƙuri” daga haka babu wanda ya kuma cewa komai tsawon mintuna talatin, ganin lokaci ya fara ja yasa tayi ƙarfin halin faɗin “Hamma zan tafi ” don kuwa ba ƙaramin nauyin zama kusa da shi ɗin take yi ba musamman yadda zuciyarta ke wani irin mahaukacin bugu yayin hakan. Shima hakan take a ɓangarensa sai dai ba zaka iya fahimtar hakan ba saboda kasancewar sa namijin duniya, “Ok” kawai yace daga haka ta miƙe tana faɗin “Allah ya ƙara maka lafiya ya kuma kiyaye gaba” yaji daɗin addu'ar tata hakan yasa ya amsa da “Ameen” a bayyane.
Fitar ta bata tarar da su Ayrah ba hakan ya ƙara tabbatar mata cewa sun wuce, ɗan ƙaramin tsaki ta saki tana mai wucewa da ɗan sauri zuwa gida. Ko da ta isa a Parlourn granny ta tarar da su, suna ganin shigowar ta suka saka ihu. Fauzah tace “Yau naga wani salon love” Yesmeen tayi caraf tace “Ashe Hamma ma sharukhan ne!” Harara ta watsa musu tana wucewa zuwa ɗakinta don zuwa yanzu ta fara gajiya da tsokanar tasu. Su kuwa dariya suka yi suna faɗin “a gama guje_gujen dai in tayi wari zamu ji.”
Allah sarki su pretty tana nan zuciyarta babu daɗi akan abinda iyayen nata suka aikata tsoron ta ɗaya ne kada zance ya bayyana don tana da tabbacin rabuwa da Hamma Zaki idan hakan ta faru. Ganin damuwa na shirin yi mata yawa yasa ta yiwa driver magana, can Naira Family House ya sauƙe ta zuciyarta babu daɗi. Yau a mutunce ta gaida Mom don har sai da mamakin ta ya kasa ɓoyuwa. Jiki mace haka ya zauna don Mom ƙin sake mata fuska tayi.
Shigowar su Khairy yasa ta ɗan ji sanyi ko ba komai zata san a wane mataki ake. Ajiye baby Humairah tayi kan kujerar ta ƙaraso da sauri tana riƙe kafaɗar Khairyn. A sanyaye kamar ba ita ba tace “Khairy don Allah sweetheart fa?” duk da ta fahimta sai ta waske tana ɗaga mata gira. Cikin ƙarfin hali pretty tace “Ina nufin yayan ku” tausayi ta bata shiyasa tace “Yana hospital da ke cikin estate ɗin nan” bata gama ji ba ta ƙarasa tana ɗaukar babu Humairah, driver ne ya kaita saboda yarinyar da ke hannunta. Ko da ta je duk yadda ta so taga ya sake mata bata samu ba, tunda ya karɓi baby Humairah yana mata wasa bai ƙara kallon ɓangaren da take ba.
Gajiya da shirun tayi ta ce “Zamu koma sweetheart, Allah ya sauwake ” cikin ransa ya amsa yana miƙa mata baby Humairah, Hakan Kuma yasa ta sha jinin jikinta, addu'ar ta Allah yasa ba asirinta ne ya Tonu ba. Bayan fitar ta bata koma ta can gidan ba tasa ya miƙa ta can gidan da take.
Kwana ukun da yayi a asibiti ya ji dama sosai don cocaine ɗin da suka shaƙa masa ya gama sakin sa, cikin kwanakin nan kullum sai sun zo sun gaida shi, Khairy kam ta rasa me yake damunta har additional zuwa take ba tare da sanin su Fauzah ba. Pretty kuwa tun ranar farko bata ƙara bi ta kan sa ba sai dai ta ɗan rame saboda yadda ta saka abun cikin ranta.
A kwana na huɗu aka sallami Hamma Zaki, jiki yayi kyau daga nan kuwa Mom ta ce ya zauna yayi kwanan yau gobe ya koma gidan nasa.
Hankalin kowa yanzu ya kwanta, safiyar yau suka zo gida Granny , bayan sun taɓa kunun gyaɗa ne Granny tayi gyaran murya tace “To Alhamdulillah, maza ya dawo dole mu ƙara gode wa Allah, fatan mu Allah ya kiyaye shi daga sharrin maƙiya, sannan tunda hankali ya kwanta yanzu ya kamata ace an tuntuɓi sirikan naku batun saka ranar, ya kuke gani?”.
“Eh Hajiya hakan ma yayi” daddy ya faɗa yana sunkuyar da kai. Sauran shiru suka yi saboda hukuncin da Daddy ya yanke basu taɓa ja da shi.
Hakan ce ta faru kuwa Daddy ya ƙira su ya sanar da su su yiwa iyayensu maza magana. Ranar da suka zo aka tsaida ranar biki watanni biyu masu zuwa da yardar Allah. Iyayen sunyi matuƙar farin ciki da hakan, tun daga nan aka fara shirye-shiryen bikin.
Hamma Zaki ya koma gidansa kuma an samu sauyi sosai don kuwa alaƙar su da pretty ta sauyi albarkacin baby Humairah wacce yake matuƙar ƙauna kamar ya haɗiye ta. Ranar kyakkyawan motsi baby Humairah tayi zaku ga tsantsan kulawar da zai bata. Wannan dama da pretty ta samu yasa cikin ranta yanke shawarar ƙin komawa gida kamar yadda Mami ta ƙira ta faɗa mata.
Washegari Daddy ya