Showing 72001 words to 75000 words out of 135404 words

Chapter 25 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46372

bayani”
“Ah ai Mallam kam baya nan, sai dai ke Shalele kuje ku ƙira shi mana”
Tare da su Ayrah suka fita sai zuba take musu tana nuna musu wurare tare da tuna memories ɗin ta a wurin. Dariya su dai suke yi tare da tabbatar da labarin da ta basu a baya. Duk inda suka wuce kallonsu ake manya da yara kowa sai gaida Ƴar Iya ake ana mata maraba da zuwa. Mutauniyar kuwa sai wani shan ƙamshi take ita ƴar birni.

Bayan sun dawo daga ƙiran Baffi ne kuma suka tarar da Damammiyar fura da nono ƙwarya-ƙwarya wanda suma a nan suka baje suna sha ana ta zance kamar an daɗe da sanin juna. Ita dai Khairy mamaki take yada suke shan furar hankalinsu kwance ba tare da nuna ƙyamarsu ba. Nan ƙima da darajarsu ta ƙaru a idonta.

Bayan Baffi yazo ne aka sake gaisawa, nan yake ta sauƙe musu damin godiya da irin sauyin da jikartasa ta samu. Daga gaishe-gaishe Daddy yace '“Khairy ki ja ƴan uwanki kuje ku yawata gari ko?”
Ai tunkan ya gama tace “To Daddy sai anjima, kai ku tashi muje cikin gari”.

Nan suka nausa cikin Gallara sai kewayawa suke. Dai-dai wajen Bala mai kifi ta tsaya tace “Ku zo mu gaisa da Bala ”
Suna ƙarasawa suka yi sallama, bala sai kallonsu yake yana ƙarawa ganin zuƙa-zuƙan ƴan mata kamar daga aljanna ya washe baki. Gaisawa suka yi yayinda hakima ke zaune akan benci. Cike da yatsina tace “Bala baka gane Ni bane?”
“A'ah Hajiya ku da ba ƴan gari ba kuma taya zan sanku?”
Dariya ta sheƙe da ita su kuma suka zuba mata ido don iya zamansu da Khairy basu taɓa ganin tayi irin wannan dariya ba. Tsagaitawa tayi tace “Bala ka manta Ni kake nufi, idan na kwashe kifin naka zaka gane Ƴar Iya ce kenan” ta ƙarasa tana kai dubanta ga kifin dake tashi da ƙamshi.
Ƙwalalo ido Bala yayi yace “Ai ban ganeki bane Ƴar Iya, ina ni ina mantawa dake?, Yaushe a garin”
Murmushi tayi tace “Bamu daɗe da isowa ba, waɗannan ƴan uwa na ne”
“To sannu da gajiyar hanya, bari a saka muku kifin”
Ayra tace “A'ah ka bar abunka in mun koma zamu fito da kuɗi sai mu siya”
Hararar ta Khairy tayi tace “Kaga Bala zuba mana” jiki na rawa kuwa ya zuba musu ya miƙa musu ledar. Khairy ce ta amsa daganan suka yi masa sallama suka yi gaba.

Ganin gidan Halima yasa tace “kuzo mu shiga gidan ƙawa ta Halima mu gaisa sai mu koma gida ko?”
Halima tayi mamaki ganin ƴan gayu a gidanta don ita bata ma gane Ƴar Iya ba sai da tace mata “Ƴar Iyace” salallami Halima ta fara tana faɗin “Ikon Allah, Ƴar Iya ke kika zama haka”
Murmushi tayi mata tace “Ƙwarai kuwa Halima, nice dai wannan rigimammiyar”
Dariya suka kwashe da ita Halima tace “Gaskiya kin canza sosai don ban gane ku ba, wallahi kamar wata ɗiyar Indiyawa kin ganki kuwa? Sauran kuma su waye halan”
“Waɗannan sune ƴan uwa na na can birni, Ayrah, yesmeen sai kuma Fauzah”
Halima tace “Sannunku da zuwa, bari na dafa muku taliya nasan dai da kina son ƴar murji”
“Ai kuwa har yanzu ina so, ammah zamu koma gida yanzu, ma dawo wataƙila kafin mu tafi”
Halima tace “Haba ƴar iya, to zan aiko muku can gidan Iyar”
Daga nan suka koma gida.

Can gida kuma bayan fitar su ne Daddy yayi wa Baffi bayanin dalilin zuwan su, ammah kafin nan ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, saboda haka Sheikh Imam yayi masa bayanin komai da komai.
Baffi har da hawayensa yace “Kai amma Allah ya saka muku da alkhairi, wallahi yau naji daɗin da rabona da jinsa tun haihuwar shi uban yarinyar! Mun gode sosai, yanzu dai bari naje na sanar da Arɗo zuwanku sai a buɗe masauƙin ku tunda sai zuwa gobe ko jibi zaku wuce.”

Bayan Baffi ya sanar da Arɗo, tuni aka buɗe musu gidan bakin wanda yake ɗauke da ɗakuna biyar ginin block. Sai da aka gyara tsaf tukun suka wuce Fada, sai wajen takwas na dare mazajen suka wuce. Abinci kuwa daga gidan Arɗo aka kawo musu, kuma sunci suna ta yaba karamci iri. Na mutanen ƙauyen.

Washegari da sassafe aka aiko da abinci daga gidan Arɗo, Shinkafa ce da miya sai kuma gasassun kaji da kuma Damammiyar fura da nono. Bayan sun karya suka yi wanka daga nan akace su Ayrah su tafi can gidan Iya su kaiwa Khairy abinci, daga nan kuma su sanar da Baffi cewa suna jiransu a gidan.

Yaron da suka gani a waje suka tambaya ya raka su gidansu Ƴar Iya yace “Tab, ku kuwa me zai kai ku gidan nan bayan Ƴar Iya ta dawo, to Aradu nidai duk abunda ta muku kada kuce Sa'idu ne ya raka ku”
Dariya suka yi kamar ba gobe, suka ce masa “Eh ya raka su mana babu damuwa ai ba zasu ce shi ya raka su ba.

Nan Sa'idu ya raka su yana ta basu labarin ƴar Iya har da labarin ranar da ta ganshi da kaji zai je ya sayar ta ƙwace ta yanka da ta yanka kuma sai ta bashi wai yaje gida a dafa, ta san duk su ma na gidan kwanɗayin naman suke yi. Yace “Ai kuwa ranar naci duka duk da ba laifi na bane, kawai da dare sai ga ƴar Iya wai a bata rabonta, daga nan aka ce babu nan masifa ta tashi wai ya za'a yi tayi musu sanadin dadi kuma suci su kaɗai?, Sai da Baffan mu ya bata kaza ɗaya ta tafi”
Me su Fauzah zasu yi in banda dariya. Da suka iso ne suka ce masa ai tare suka zo da Ƴar Iya, daga nan suka shiga. Bayan sun gaisa da iya suka miƙa mata abincin don sun san ba lallai Khairy ta tashi ba. Fauzah tace “Iya ina ne ɗakinta, don na san ba lallai ta tashi ba”
“Ina kuwa zan tashi tunda Fauzah bata zo ta tashe ni ba” ta faɗa tana cillawa Fauzah harara. Dariya suka kwashe da ita suna faɗin
“Kinga abinci muka kawo miki ba komai ba, in Baki ci sai mu koma da shi”
Da sauri tace “Yi haƙuri Ƴar uwata mai hanjin lagwani, bani abincin”
Iya ce ta miƙa mata tana murmurshi, sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba.

Ayrah ce tace “Au Iya, wai a sanar da Baffi su haɗu dasu Daddy tare da Ƴar Iya”
Harara ta banka mata tace “In zaki ƙira Ni da Khairy na to, kar ki ƙara ce min Ƴar Iya”
Dariya suka yi ita dai iya cewa tayi “Ke Shalele ai ba'a manta da, maza kici ku wuce Kinga baffin ki ya riga da ya shirya tun ɗazu”
Da “To ta amsa tana cin abincin, tas ta cinye daga nan kuma tayiwa Baffi magana cewa ta shirya.

_Naga alama Fans so kuke na rage post, ko dai labarin ya daina burge ku ne😔😣, gaskiya da sakel, in bazaku ke yin comments ba zan ajiye alƙalami na._
_Na gode_

_Ku biyo ni don jin ya za'a kaya a gidan Inna Zaliha tare da Sheikh Imam_
_Comment and share Please_
_Diamond Bhatool ce_
[8/25, 10:15 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: https://whatsapp.com/channel/0029VamEf2Y4dTnFmjl4Dv1Z


🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*










SHAFI NA “““75&76”””

A can suka haɗu tare da su Daddy, bayan ta gaidasu ne suka nufi can gidan mahaifin khairy wato Mallam Umaru Gallara. Suna tafe suna hira yayin da Khairy tayi tsam bata cewa uffan har suka iso.
Baffi yace “Shalelen Iya ki shiga ki mana iso ko”
“To” tace tana gyaɗa kai. Daga nan ta kutsa kanta cikin gidan da akewa laƙabi da na mahaifinta bayan ko kwana ɗaya bata taɓa ɓatawa cikin gidanba. Da sallama a bakinta ta shiga yayinda ta tarar da Inna Zaliha tana wanke kwanukan da suka ci tuwo.

Inna Zaliha da taga kyakkyawar yarinya ƴar birni yasa ta ajiye wanke-wanken tana washe baki
“Lale maraba da zuwa ƴan mata, bari a shimfiɗa miki tabarma” bata dakatar da ita ba sai ma makewa da tayi tana jiranta. Inna Zaliha ta fito da sabuwar tambarmarta tana shimfiɗawa “Sannu da zuwa sannu sannu”
Sai da ta zauna kafin ta dubi Inna Zalihar a wulaƙance tace, da baƙi muke a waje idan mai gidan yana nan ki masa magana”
Washe baki tayi tace “Babu komai bari nayi masa magana”

Can ta fito daga ɗakin nata tana murmurshi tace “Gaahi nan zuwa ki sanar musu”
Miƙewa tayi ta sanar da su Baffi, don a cikin shirin ya Sheikh babu barin inna Zaliha tasan me yake faruwa shi yasa suka jira a waje.
Ta juya zata koma suka ci karo da Baba yana fitowa, kanta ta kawar saboda irin kallon da yake mata tace “Ina wuni”
“Lafiya ƙalau”
Daga haka ya shige waje ita kuma tayi ciki. Ƙara ajiye wanke-wanken nata tayi tana dawowa kan tabarmar sai surutu take zuba mata, ita dai Khairy ji take kamar ta kamata da duka don tun da ta tsani wannan matar.

A can waje kuma bayan sun gaisa ne cike da girmamawa Baffi yace “Waɗannan baƙi ne daga birni, kuma Arɗo ne yace a rako su saboda akwai wani abu da suka harbo daga can birni kuma nan ya faɗo a dai-dai bayin gidan, saboda haka sun zo tonewa ne su tafi”
“To Baba ai ba komai sai su iso ko?, Ku shigo mana, muje bari na ɗauko magirbi”.
Sallama suka yi suna kutsawa gidan yayinda Inna Zaliha ta gansu sai da gabanta ya faɗi amma ta dake tare da bin bayan Baba wajen kayan nomarsa.
“Mallam su waye waɗannan ɗin”
Bayani yayi muta kamar yadda suka yi mata. Cike da firgici tace “Allah yasa ba abun mutuwa suka Wullo mana ba” cikin ranta kuma tana tuna ajiyarta da tayi a wurin, tsoronta ɗaya kar a tono wannan abun don in bata manta sharaɗin boka ba cewa yayi idan har aikin nan ya ware to itama zata yi mutuwar wulaƙanci ne kamar yadda Barira ta mutu ammah ita sai ta tozarta.

Tsoro da firgici ne lokaci ɗaya suka yanyameta, daga ƙarshe dai ganin zaman nan ba zai fisshe ta ba yasa ta fito tare da ƙarasa wanke-wankenta. Tana gamawa wata dattijuwar mata ta shigo wacce da gani kasan uwar manya ce. Granny kenan. Bayan sun gaisa ta koma gefen baƙuwar da bata san wacece ba, ita dai nata ido ne don yau kam ita kaɗai tasan me take ji ga kuma zuciyarta dake bugu kamar wanda ake harzuƙa ta.

Ɓangaren su Sheikh Imam, Baba ƙin barinsu yayi suyi tono a cewarsa ba zasu iya ba ga kuma baƙi ne da mahaifinsa yayi musu iso. Nan ya fara tono yana tono sai dai basu ga komai ba. Har wajajen sha ɗaya basu tarar da komai ba.

A lokacin ne kuma ya iso kan wani makeken dutse baƙi ƙirin, haka ƙasar wurin itama kamar gawayi. Basu tsinke da mamaki ba sai da ya kafa magirbinsa kan wannan dutse, nan wurin ya fara jijjiga ga kuma wani gurnani da yake fita. Ba kowa bane sai Khairy da ta baje akan tabarmar da take zaune ita da Granny.

Kuzo kuga idon Inna Zaliha Tuni ya Raina fata nan jikinta ya fara ɓari da jin gurnanin da ke fita daga bakin baƙuwar tata. Da sauri Sheikh Imam ya juyo daga bakin bayin da yake dama shi bai shiga ba iya Baffi ne, Daddy sai kuma Baba.

Yana zuwa yayiwa granny Alana da ta fito da jakar da suka bar mata ta taho da ita. Wata bottle ɗin ya buɗe yana kallon da ruwan tare da ɓare zamzam yana zubawa a ciki. Gaurayawa yayi daga nan ya watsa mata ruwan. Wani mahaukacin ihu ta saka wanda a daidai lokacin ne Baba dake tono ya kammala sare baƙin dutsen nan. Baki buɗe yake kallon abunda ke ciki. Da sauri Baffi ya ƙaraso yana kai dubansa ga ramin, shima Daddy ƙarasowa yayi ganin duk sun kasa magana.
Mamaki ne ya kama gabaɗayansu yayin da Baffi yayi bismillah cikin ransa sannan ya sa hannunsa zuwa ga ramin. Da ƙyar da taimakon Daddy suka ciro da baƙin ƙullin da ya kai kaya kala 20. Basu bata lokaci ba suka fito waje tare da nufar wurin da Sheikh Imam yake.

Ina innna Zaliha?, A dai-dai lokacin da Baba ya fara sare dutsen bugun zuciyarta ya ƙaru, yayinda numfashinta ke fita da sauri da sauri. Gagara tsayawa tayi akan yarinyar da akewa karatu hakan yasa ta jingina da bangon ɗakin nata tana kallonsu.


Fitowar su daga bayin akan idonta ne, ai ganin abinda ke hannunsu, abunda ta ajiyeshi tsawon shekaru goma sha shida ba tare da sanin kowa ba yau an haƙo shi yasa ta miƙe tana nufarsu da gudu.
“Yau naga ta kaina ni zalihatu, me nake gani haka, wacce irin rana ce wannan?” ta faɗa tana zubewa ƙasa a gabansu tana kuka.
“Kuyiwa Allah da ma'aiki ku bani ajiyata”
Da mamaki Baba ke kallonta yayinda furucinta ya matukar bashi mamaki cikin ransa yana nanata “Ajiyarta”.

Daddy kuwa amshe ƙullin yayi yana zamewa gefe tare da nufar Sheikh Imam gani matar tana son kawo musu wargi.
Ai da hanzari ta miƙe zata bishi Baba ya riƙe ta
“Ina zaki je haka ne Zaliha?”
Cikin fitar hayyaci tace “Kaima kana gani zai tafi da ajiyata, rabu da ni naje na amso abuna”

Bai sake ta ba yaja ta zuwa ɗakinsu sai lallaminta yake don shi gabaɗaya hankalinsa bai kai ga Sheikh Imam da yake ta rera karatu a yarinyar ba.

Bayan shafe wasu awanni yana karatunne suka fara magana.
Sallama yayi musu don in bai manta ba sun karɓi shahada a wancan karen .
A tare suka amsa kamar haɗin baki. Shi dai Sheikh Imam kamar ko yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi.
“To ƴan uwa na yau gamu mun ƙara haɗuwa, ina muku fatan alkhairi, Annabi tsira da aminci yace “Almuslimuna ala shuruɗihim, saboda haka yau zamu kammala sadaukarwar da kuka yi alƙawarin zaku yi, gamu ga ƙarshen aikin amma kafinnan bari a ƙirawo mahaifin yaron”.

Baffi ne ya leƙa yana ƙwalla ƙiransa, tare da Innna Zaliha suka fito idonta ya raina fata kamar wacce ta shekara ɗari tana jinya jikinta kuwa sai ɓari yake. Sai da suka zauna tukun Sheikh Imam ya umarce Aljanun da suyi bayani kamar yadda suka mishi a kwanakin baya.

Baki buɗe suka fara bayani tamkar dai yadda suka yi a wancan lokacin. Murmushi Sheikh Imam yayi yana duban su gabaɗaya sannan yace “To yanzu dai Mallam Umaru kaga abinda ya kawo mu, duk da cewa kaima a yanzu ba dai-dai kake ba muna so muji ta bakinka”.

Inna Zaliha kuwa ta ma kasa magana jin asirinta yau ya gama tonuwa, idonta sauƙe a ƙasa hawaye ne kawai ke zubo mata.

Kasa magana shima yayi hakan yasa Sheikh Imam yace “Malama Zaliha, muna so muji ta bakinki”
Cikin Muryar kuka ta fara magana “Tabbas ban taɓa nadama akan abinda na aikata ba sai yau ko don ina tunanin asiri na ba zai taɓa tonuwa bane” taja hanci sannan taci gaba “Bazance kada a since wannan asiri ba saboda nima na ɗana rayuwar, a yanzu bana fargabar mutuwar saboda nayi nadama akan abinda na aikata, na sa an kashe rai da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciya irin nawa da neman cikar buri, na sa an juyar da tunanin yarinyar da bata ji ba bata gani ba, na raba ɗa da iyayensa ba tare da wani ƙwaƙkwaran daliliba” jan hancin ta ƙara yi tace “Na cancanci duk wani hukunci, Mallam a since wannan asiri nima na girbi abinda na shuka”.

Ina granny? Granny sarauniyar tausayi kuka kawai take yi, haka Daddy Shima hawaye yake sharewa, Baffi ne ma kawai za'a ce idanunsa ne kaɗai suka sauya launi sai kuma Baba da shima yake sharan ƙwalla. Sheikh Imam yayi gyaran murya sannan yace “To, komai da zai faru da bawa a rubuce yake, Zaliha ki ji tsoron Allah ki tuba tuba Mai kyau duk da cewa mutuwa boka yace zaki yi bazamu yi imani mu yadda ba saboda ba shi ya baki ran ba, naji daɗi da kika gano kuskuren ki kuma kika amsa hannu bibbiyu, ki sani ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma hausawa suka ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, kamar haka ne ta faru, kin jima kina morar abinda kika yi yau ɗaya kuma waɗanda kika jima kina zalunta zasu fara more tasu rayuwar. Ubangiji Allah ya shirye mu”
“Amin” dukkaninsu suka amsa.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya fara since ƙullin yana karanta ayoyin karya sihiri. A hankali ya kammala buɗe komai dake cikin ƙullin wanda ba komai bane sai wasu mutunmutumi guda uku, sai kuma gashi, da kuma tsumman atamfa da yadi”

_Tabbas addinin musulunci haske ne kuma ni'ima ne, wane addini ne cikin addinai ke da irin wannan ni'ima?, Babu. Alqur'ani da kuke gani ƴan uwa abincin ruhinmu ne, wallahil adhim duk wanda ya riƙe Alqur'ani babu wata musiba da zata same shi sai dai abunda Allah ya riga ya rubuta zai same shi._
_Azkar, wato ambaton Ubangiji shima makami ne na mumini, Allah maɗaukakin sarki ya nuna mana muhimmanci ambatonsa a cikin Alqur'ani a wurare daban daban, haka hadisai ingantattu sun zo akan muhimmancin ambaton Allah_
_Akwai zikirorin safiya da maraice waɗanda suke da matuƙar muhimmanci. Imam Annawawi Allah yayi masa rahama yace “Madallah da masu ambaton Allah musamman zikirorin safiya da maraice, ida mutum bai yi su duka ba to ya daure da safe ya karanta ɗaya haka da yamma”. Saboda haka ƴan uwana, mu riƙe azkar ɗin nan da kyau wallahi zamu ga faidar hakan, babu wani da ya isa ya cutar da mu sai dai abunda Ubangiji ya riga ya rubuta zai same mu_
_Ƴan uwana mata ina ƙira gare mu da muji tsoron Allah kuma mu sani shirka itace mafi muni daga cikin kaba'ir. Idan muka dubi ayoyin da suka zo cikin Alqur'ani zamu tabbatar da hakan, mu tuna lokacin da Luƙmanul Hakeem yake yiwa dansa wasiyya, shirka itace abinda ya fara tsawar masa akai, ayar tana suratul luƙman. Akwai makamantan ayoyi da suka zo, saboda haka mu kiyaye, kada mu bari shaidan yayi galaba akanmu har ya kaimu ga halaka._
_Wasu matan suna cewa shirka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login