Showing 3001 words to 6000 words out of 135404 words

Chapter 2 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46352

ta ga Saratu tayi tana yamutsa fuska tace
“Ke kuma gobe in na zo ki ƙara min rashin kunya ki gani, bari na ƙira dogari ɗaya ya sanar da sarki matar sa ta karye” ta faɗa tana kashewa da dariya sannan ta fita.

A bakin ƙafa ta sanar da dogarin cewa Saratu matar sarki na neman sa daga nan ta cika bujen ta da iska.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan su A'i Aminiyar ta wacce take take mata bayar kamar bafadiya. A'i ma ba baya ba a rashin ji shiyasa duk ƙauyen babu wacce Ƴar Iya ta zaɓa matsayin abokiyar ta irin A'i, tare suke tsula tsiyar su, su tsokali wannan su zagi wannan in sun ganshi su duka wannan aikin su kenan cikin gari ini suke suna yawo kamar ƙudaje daga nan sai can.

Tun daga baƙin soron gidan su A'i Ƴar Iya ke ƙwala ƙiran ta.
“A'i A'ilo kan kaza Amadu ya siyo mata kaza taci” wannan shine kirarin da Ƴar kewa Aminiyar ta tuni zaki ga ta fito da yake ita ma duk ta ishi gidan su har Allah Allah suke ta fita. Yau da bata fita ba tsiyar da ta tsula musu ba'a magana.

A'i na fitowa daga gida ta dubi ƙawar ta tace
“Kutt Ƴar Iya dama kina cikin Gallara yau ko kallon ki banyi ba, ko dai kin samu kaso ne shiyasa”
“Dallah ni ba magana nace ki min ba ki zo muje gida yau na samo babban rabo”
Nan ta bata labarin kifin Bala da ta kwaso da kuma Naman Iya Uwa Maman sarki. Suka yi ta dariya suna shaƙiyyancin su.

Har sun kama hanyar gidan su Ƴar Iya A'i tace ”ah Ƴar Iya wallahi mu bi ta dandali ta wurin Bayero mai balangu nasan zamu dara. Tafa hannu suka yi suna dariya Ƴar Iya tace
“Ke A'i yau kam dai sai cikin mu ya cire don ciwo mu dai wuce.

Tafiya suke suna taɗe-taɗen su har suka iso dandali, duk da cewa dare bai yi ba lokacin ne ma ake kiran sallar Ishã ammah yara da manya, ƴan mata da samari sun cika maƙil ga kuma ɓangaren Bayero da yake sayar da balangu sai kai kawo ake a wurin.

Ganin kowa hidimar shi yake yasa Ƴar Iya ƙwallah ihu ita da A'i Suna faɗin,
“Wallahi Sakse ya biyo ta hanyar nan, kowa ya gudu ya tsira da kansa don kuwa har da wuƙa a hannun sa” Nan wasu suka fara gudu yayin da Ƴar Iya da A'i suka ci gaba da ihun
“Wallahi dagaske ga nan Sakse....mun shiga ukuuuu”

Waɗanda suka ɗan ja gefe tuni sun fara neman wurin ɓuya, Bayero kuwa da Mai Salisu mai shayi duk sun watse sun shige kiosk ɗin Baaba Mai trader, tuni wurin yayi tsit babu almaun motsi kowa yayi shiru don tsira da ransa shi, hakan yasa Ƴar Iya da A'i nausawa kai tsaye tsaye wurin bakangun Bayero. Tas suka kwashe shi cikin ledodin da ke ajiye bisa teburin balangun, har sun lallaɓo zasu tafi Ƴar Iya ta hango wasu ɓula-ɓulan breads kan teburin Salisu, tuni ta wuwuro biyu ta riƙe.

Juyawar su da niyyar tafiya suka ji motsi a bayan su, waye kuwa in ba Sakse ba ai tuni suka arta a na kare Sakse na biye da su. Dama bread ɗin a hannun Ƴar Iya suke , sai da suka ja Sakse ta lungun ƙarashi kukan ka Ƴar Iya ta faki ido ta damƙo ƙasa ta watso masa sai ciki idon sa, ta ƙara damƙa ta watsa sai da ta tabbatar ƙasar ta masa illa ba zai iya gani ba ta tsokalo karen Baushe....tuni suka yi siɗaf-siɗaf suka gudu suka bar Sakse da kare ga kuma ido car ƙasa.

Gudu suka ƙara har sai da suka iso gidan Iya tukun suka tsaya suna haki suna mayar da numfashi. Tun daga lungun da zai sada ka da cikin gidan suka jiyo Muryar Baffi...Ɓata fuska Ƴar Iya tayi saboda ta san halin ɗan tsohon sam baya ɗaga mata kuma duk iya shegen ta bata isa tayi masa musu ba in yace abu.

Da yake su Ƴan duniya ne sai suka haɗa plan, Ƴar Iya ta shiga da gudu zuwa Bukkar ta kamar an biyo ta sai A'i ta biyo bayan matsayin wacce ta tsokalo. Hakan kuwa suka yi tuni Ƴar Iya ta arta A'i na biye da ita basu ko kalli Iya da Baffi basuka shige, dariya suka ƙyalƙyala suna tafa hannaye.

Baffi da ya lura da su kuma ya gane shiri ne irin nasu bai bi ta kan su ba kawai yayi musu addu'a ya miƙe zuwa tashi bukkar. Har Iya zata bi bayan shi ta tsinki Muryar Ƴar Iya
”Ina kuma zaki je Iya baki bani aikin da nayi miki ba?” ta tambaya tana wani yamutsa fuska. Iya da dam tuntuni take jiran dawowar jikar tata saboda ta bata ita ma ko ta maida ƴaƴan yasa tayi murmushi ta nufi ɗakin ajiya ta ɗauko naman kajin da ta soya, ba tare da ta ɗauki ko ƙafa ba ta miƙa mata.
“Gashi nan Ƴar Iyan ta”
Cinya da fuka-,fukai ta zaro da miƙa wa Iya tuni ta amshe kamar sabuwar mayya sai wani wage Baki take ita ala dole zata ci nama.

Wani abun mamaki tas suka cinye kajin da zasu kai huɗu kuma ba ƙanana ba sannan suka ƙara da balangun Bayero na yi tunanin zasu bar bread ɗin zuwa safiya ai kuwa sai Ƴar Iya taja ɗaya ta buɗe A'i taja ɗaya ta buɗe tuni suka lamushe su tasss....

Suna gama cinye wa suka ƙara fita waje ammah wannan fitar ta satar mangwaro ne kuma bishiya zasu hau.

(Nace sai kun je aljanu sun wurɗo ku ai😀 ehmana)

Gonar da ke kusa da gida suka nufa. Bayan sun tsinko mangwaro suka dawo.

Duk da cewa dare ya tsala hakan bai hana su yawata cikin ƙauyen ba don farauto wani abun su ƙara a cikin su kafin kowa ta wuce gida don huce gajiya.

*WACE CE ƳAR IYA*?

Mu haɗu gobe don jin wacece ƴar iya, tabbas akwai ɓoyayyen al'amari a tattare da ita....ku ci gaba da bibiyar alƙalami na don jin ya zata kaya.

COMMENT PLEASE!!!

[4/26, 8:45 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*








__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __



SHAFI NA ‘‘‘‘‘5&6’’’’’

*WACECE ƳAR IYA?*

Malam Umaru Gallara haifaffen ƙauyen Gallara ne da ke cikin ƙaramar hukumar Shira da ke jahar Bauchi. Mahaifiyar sa AISHATU wacce aka fi sani da Iya sunyi auren zumunci ne da Baban sa Mallam Musa wanda ake ƙira da Baffi.

Tunda suka yi auren nan Allah bai basu haihuwa ba har suka share shekaru goma sha biyu cikakku, hakan ne ya tada hankalin Iya saboda dangi sun yi caaa akanta suna faɗin juya ce, Musa ya ƙara aure.

Wannan tashin hankali yayi wa Iya illa sosai, don kuwa haukacewa ne kawai bata yi ba, ana cikin wannan yanayin ne wani al'amari ya faru wanda shine mafarin komai cikin rayuwar wannan ahali na Malam Musa.

Wata guda da fara wannan hatsaniya Iya ta samu ciki, kada ku so ku ga murna wurin Baffi don kuwa a ranar sai da ya raba buhun gero fiye da ashirin saboda farin ciki. Dangi murna kowa yake yi da wannan cikin yayin da kowa ya ƙwallafa ranshi akan yaron da masu so da kuma marasa so.

Haka Iya ta raini cikin nan tare da taimakon Baffi da kuma Mahaifiyar sa Baba Maunde. Baffi da Baba Maunde sun matuƙar bawa cikin Iya kulawa ta musamman har ta kai watanni tara ta haifi ɗan ta namiji, kyakkyawa son kowa.

Bayan sati guda da haihuwar yaro Baffi yayi masa laƙabi da Umaru. A ranar Iya ta samu goma sha tara na arziƙi daga kowanne fanni, dangin ta da kuma dangin Baffi.

Haka dai yaro ya ci gaba da girma har ya kai shekarun fara zuwa ɗaukar karatu, da yake Allah yayi mishi baiwa ta musamman yana da shekaru goma sha shida ya kammala haddar sa ta Alqur'ani. Bayan ya dawo Baffi yasa aka shiryawa Umaru Ƴar wata ƙwarya-kwarya yadda aka ci aka ƙoshi.

Tun bayan dawowarsa Baffi ya ke zuwa da shi gona har ya kai shekarun Aure. A lokacin ne kuma fitina ta ɓarke, Iya ta kawo zaɓi Baffi ya kawo zaɓi. Da ƙyar aka samu Baffi ya janye nashi zaɓin akan sharaɗin bayan shekara da auren Umaru zai auri Zaliha ɗiyar Abokin sa wacce ita tace tana son Umaru.

Sannu sannu babu wuya inji hausawa, haka aka sanya ranar auren Umaru da Barira ƴar yar Iya. Barira mutum ce ba mai ƙaunar tashin hankali ba hakan yasa suka yi zaman su lafiya da mijin ta Umaru wanda shima lokaci guda yaji ba zai iya ƙara auren wata matar ba bayan Barira.

Shekara guda da auren Allah ya albarkace su da samun ƙaruwar ƴa mace sai dai yarinyar tazo da salo na musamman. Ranar suna yarinya taci suna Aishatu...an yiwa Iya takwara kenan.

Tun daga wannan lokaci Zaliha ta fara ƙoƙarin shiga gidan Mallam Umaru tare da ƙudurruka masu ɗumbin yawan gaske, da farko ta fara ne da salon ta na ƴa mace ganin ba zata ci riba yasa ta fara biye-biyen ƴan duba wanda suka tabbatar mata da cewa in dai Barira na raye to gidan Umaru bata da matsuguni.

Wannan abu shi ya ƙara tunzura Zaliha saboda haka ta nemi Aminiyar ta Larai suka nufi gurin boka don cimma manufar su ko ta yaya ne. Abu mafi muni bayan boka ya maimaita mata irin abun da ƴan duba suka faɗa mata sannan yace matsawar tana son auren nan to sai an kashe Barira, Ba tare da ta damu ba kuwa ta sanar da BOKA shawarar da ta yanke.

Bayan Boka ya sallame su suka nufi gida zuciyar su cike da ɗumbin farin ciki.

Sati guda da faruwar wannan al'amari kwatsam Barira ta fara jinya, lokaci ƙanƙani jinya tayi tsanani bata iya gane komai sai dai a tayar a kwantar, ana cikin wannan yanayi kuma Mallam Umaru yazo da al'amarin son auren Zaliha. Kowa abun ya bashi mamaki sai dai babu yadda suka iya saboda haka kowa ya kawar da kanshi ya zubawa sarautar Ubangiji ido.

Iya tayi matuƙar baƙin ciki da hakan, saboda irin halin ko in kula da Mallam Umaru ke nunawa akan jinyar Barira yasa Iya ɗauke ta ita da ɗiyar ta ta kawo su gaban ta tana jinyarta.

Rayuwa kenan, kullu nafsin za'iƙatul maut...wata rana Allah ya karɓi ran Barira. Iya tayi kuka kamar ba gobe haka dangi sun ji mutuwar ta kasancewar ta mace mai sanyin hali da ƙaunar jama'a.

Sati guda cif da rasuwar Barira Mallam Umaru ya auro Zahiha wacce yake jin ta kamar sarauniya a birnin zuciyarsa. Daga nan komai ya fara sauyawa.

Ɓangaren Aishatu ɗiyar Barira Allah ya raya ta sai dai tun lokacin da ta fara zama ta soma addabar iya da ɓarna. Idan zanin shimfiɗa aka shimfiɗa a gado to in Sha Allah sai ta yaga shi fata-fata da hannun ta.

Basu ɗauki abun da muhimmanci ba kawai sun ɗauke shi ne matsayin ƙiriniya, ana haka yarinya ta fara rarrafe sai abu yaci gaba, idan girki aka ɗaura to zata je ta tunkuɗar da shi ba tare da jin wahalar hakan ba, babban abun mamaki kuwa shine yadda wuta bata kama yarinyar duk irin wasan da zata yi da ita.

A wasu lokuta kuwa ta kan rarrafa jikin buhuhunan hatsi da aka tanada don ci ta ɓula ƙasan su ba jimawa buhun zai yoye haka sai anyi sabo. Wannan abu ba ƙaramin mamaki yake bawa Baffi da Iya ba saboda ɓarnar ta wuce hankali da tunani amma basu taɓa sanar da wani na waje ba.

Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, Aishatu ta fara tafiya, tunda ta fara takawa kuma zaman gida ya zama ba nata ba, ɓangaren ɓarna kuwa sai abun da yayi gaba ammah tafi so ta fita gidan maƙota sam bata son zaman gida. Hakan kuma na da alaƙa da Baffi saboda bata iya yi mishi musu in yace abu.

Idan Aishatu ta fita maƙwabta babu abun da take sai ɓarna, tun suna shiru har abun ya fara isar su suka fara kai ƙarar ta. Iya da a lokacin ke daure mata gindi sai tace sharri akayi wa ɗiyar ta , hakan ne yasa jama'ar gari suka kafa ƙahon zuƙa kan Ƴar Iya bayan tattarawar sirri da suka yi. Sun riga sun yanke hukuncin hukunta Ƴar Iya a duk lokacin da ta musu ba dai-dai ba sai dai abun da basu sani ba tafi ƙarfin su baki ɗaya.

Wata rana lokacin Ƴar Iya bata wuce shekaru shida ba a haife, ta fita yawon ta da ta saba ne kwatsam ta bi ta layin wani marowacin mutumi. Dai-dai zuwan ta ƙofar gidan mutumin ya fito da langar sa cike da waina. Tunda taga wainar nan kuwa hankalin ta ya tashi, hakan yasa tabi bayan mutumin ko ɗaya ya bata.

Bayan ya zauna a shimfiɗar tabarma irin ta kaba ɗin nan ta iso, ido ta zuba mishi amma abun ka da marowaci bai gane ba. Ganin bashi da niyyar bata yasa ta faki idon sa ta jawo langar ai kuwa ta arta a na kare yayin da take cin Masar shi kuma mutumin bai daina bin ta ba.

Sai da ta cinye tsaf ta daina wanda mutumin gashi abun tausayi ya jigata, ganin hakan yasa ta wulla masa langar ai kuwa rasss sai a kanshi. Tuni ya fashe jini sai zuba yake.

Da ƙyar aka tsayar da jinin a chemist tukunna ya dawo. Wannan dalilin ne yasa mutumin harzuƙa har ya yanke hukuncin kai ƙara fadar Arɗo. Bayan ya faɗawa Arɗo abun da ya faru ne sai Arɗo ya aika a ƙira masa Baffi. Kamar ta sani kuwa lokacin suna zaune a tabarma ta tasa tukunyar ɗumamen safe a gaba sai ci take kamar jaka, ana sallama kuwa ta fita akace tace ana sallama da mai gidan a fada....

Tana isarwa Baffi saƙo ta shiga bukkar Iya, bata jima ba ta fito still hannun ta kwaɓe da ɓakar miyar kuka da ta shafe ko ina na jikin hannun.

Baffi na fita bai tsaya ko ina ba sai a fada, mutanen da ya gani maƙil a fadar ne yasa ya shiga tashin hankali na wani lokaci, lokaci guda da ya tuna da jikar sa Ƴar Iya nan ya gano hala ta aikata wani laifin ne.

Bayan gaisuwa irin ta mutunci da suka yi da Mai martaba kamar kullum.
Mai martaba yayi gyaran murya yace:
“Toh Mallam Musa tunda Allah yayi ka iso da wuri kai tsaye zamu fara abun da ya tara mu”
Cikin sanyin jiki Baffi ya kaɗa kai.
“Toh Malam Musa, kamar yadda kaga na aika a ƙira ka ba wani abu bane ya faru sai wannan abun da JIKAR ka ta wajen Iya ta aikata”
Yana kai nan ya tsaya tare da yiwa dogarai alamar su shigo da mutumin nan. Baki buɗe Baffi ke kallon sa don kuwa abokin sa ne Ishiyaku. Ganin kansa ɗaure da bandage da kuma plaster yasa Baffi maida hankali don jin me Arɗo zai ce.

“Toh Mallam Musa, kamar yadda kaga Mallam Ishiyaku kansa naɗe da kayan ciwo, ba komai ne ya faru da shi ba sai karon da suka yi da jikar ka wacce ta kusa hallaka shi bayan sace masa waina a daro da tayi”
Kasa magana ma Baffi yayi yayinda kunya tabi ta lulluɓe shi, tuni ya sunkuyar da kan sa ƙasa.
Mai martaba ya ƙara gyaran murya yace
“Mallam Musa muna sauraron ka, kayi shiru”
Cikin ƙarfin hali da takaici Baffi yace
“Don Allah Mai martaba ayi wa Ƴar Iya haƙuri in Sha Allah in na koma gida Zan hukunta ta, yaran yanzu ne ka haifa baka haifi halin su ba, don Allah ayi mata afuwa.

Tuni mutanen wurin suka kaure da hayaniya wani yana faɗin
“Wallahi ba zata saɓu ba, ko dai a ɗauko yarinyar nan a hukunta ta ko kuma wallahi mu bi har gida mu nakasa ta.” yayin da wasu ke ganin hakan ba dai-dai bane.
Wani Matashi ɗan azagwai ne ya miƙe yace:
“Wallahi ko yanzu a zo a hukunta ta ko mu mu hukunta ta, yarinya ƙarama duk ta addabi jama'a, Aradu Arɗo in ba'a hukunta taba toh mu zamu bi mu hukunta ta”

Tsawa Arɗo ya buga nan da nan aka yi shiru ana sauraron sa.
“Toh mun ji ƙorafi daga wurin mahaifin mai laifi, Mallam Ishiyaku ya kake ganin za'a yi? Ka haƙura ko kuma sai an ɗauko yarinyar?”
Na gefen shi ne ya zuga shi hakan yasa yace sai dai a ƙira yarinyar.

Arɗo yace “Shikenan ammah miye hukuncin yarinyar?”
Hayaniya ta kacame wasu na faɗin a biya kuɗin raunin da tayi kuma a bata aikin noma da yiwa matan Arɗo aike sannan kullum ayi mata bulala uku da safe. Wasu masu tausayin kuma cewa suke ayi mata haƙuri yarinya ce...cikin zafafan mutanen ne wani ya kalli mai cewa ayi haƙuri yarinya ce yace
“Kutumar uba, toh wallahi yarinyar nan tafi mahaukacin kare haɗari”

Ganin ba zasu yi shiru ba kuma sun tayar da rigima ne Arɗo ya daka tsawa kafin yai gyaran murya.
“Ya isa haka” ya faɗa yana mayar da kallon sa kan Baffi.
“Toh Mallam Musa, kai yanzu me kake ganin za'a yi?”

Bai kai ga bada amsa ba suka ji Muryar yarinya ƙarama wacce bakin ta ma bai gama fita ba tace
“Toh ai ba shi yayi laifin ba nice”

Shiru ne ya wanzu yayin da kowa kallon sa ya koma kan Ƴar Iya da ta tsaya a gaban su ƙyam ko tsoro babu a tattare da ita, nan da nan wasu suka sha jinin jikin su yayin da wasu kuma suke miƙewa tare da yunƙurin kamo ta....

Mu haɗu gobe don jin cigaban yarintar Ƴar Iya!
Ko kuna tunanin zata bari su hukunta ta kamar yadda suke ikirarin hakan?
Duk AMSOSHIN ku na jiran ku, sai mun haɗu.
Ku yi sharing sannan kuyi comments.🥰

*DIAMOND BHATOOL ce!*


[4/27, 5:57 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login