Showing 36001 words to 39000 words out of 135404 words
ta iska.
Tana komawa gida ta fara ƙulla abun da nimah kaina ban san me take nufi da shi ba. Tana murmurshi har ta kammala ƙullawa. Lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen Ishã saboda haka ta adana abun ta. Daga nan ta fice dandali ba tare da bi takan A'i ba.
Ba ita ta dawo ba sai da taga dare ta ɗan yi nisa, a hanyar ta ta dawowa ta tsinci wuƙa. Kar kuso kuga murna a gun Ƴar Iya kamar wacce ta samu abun arziƙi. Rungume wuƙar tayi a ƙirjin ta sannan tace
“Kai yau dai da shegiyar Sa'a na tashi Aradu, wuƙa sabuwa haka” ta faɗa tana ƙarema wuƙar kallo “Kai daga gani wuƙar nan zata yi kaifi aradu” dariya mai sauti tayi sannan tace “Da gaske mutanen ƙauyen nan so suke na fara samun halaliya ta!!! Toh ai shikenan nikam bani da wata matsala zan yi sana'a da ita” daga haka ta caka wuƙar a kunkumin ta tana tafiya tana ƙwambo irin dai yadda masu yawo da. Wuƙar nan suke yi cike da taƙama.
Cike da farin ciki ta wuce abunta har ta isa gida. Tana shiga ta ƙara jawo daron ta ta buɗe tare da irgawa don kada taje fitar ta Iya ta sace Mata. Tas ta lissafa tare da yankewa kayan sana'ar ta kuɗi. Daga nan ta ɗale gadon ta mai ɗauke da katifar yayi Nan ta faɗa duniyar bacci. Babu jimawa sautin gwartin ta ya karaɗe ɗakin.
(Nace Allah hokku sa'a Ƴar Iya”)
Ba ita ta tashi ba sai wuraren ƙarfe goma na agogo. Hankali kwance tayi miƙa tare da tashi, yawun baccin da ya bushe a fuskar tata ta ɗan ɗebi guntun ruwan dake ƙasan buta ta goge sannan ta cika bujen ta da iska.
Ba ita ta dawo ba sai wuraren sha ɗaya na rana, ɗumamen da iya tayi taci sannan taci caccanga da miya da iya tayi da rana. Sai da tayi hani'an ta miƙe tayi wanka. Tana fitowa ta ɗauko murtar da Iya ke ajiye Vaseline nata, shafawa tayi abunta duk da cewa wani wurin yayi yawa wani wurin kuwa bai san wani zance ake ciki ba don babu alamar maiƙo a tattare da shi. Tana shafawa ta ɗauko kwandon kwalliyar ta ɗauko ledar powder irin mai ƙasar nan tare da ɗauko madubi tana kallon fuskar ta. Murmushi tayi kafin ta fara shafa powder ɗin tace “Nimah dai kyakkyawa ce, idan nayi ado ai sai naci gasar kyau ta duniya” dariyar da tayi kumatun ta suka lotsa, abun da ban taɓa tunanin akwai shi fuskar ta ba.
Ganin in ta tsaya kallon madubin zata ɓata lokaci yasa ta fara shafa powder ɗin. Yadda take laftawa kai kasan za'a kwashi kyau a wurin. Kamar dai yadda shafin manta ya kasance haka shafin powder ɗin ma, duk tayi damɓare damɓare ga powder Allah ya zuba mata ja kamar masifa. Tuni fuskar nan ta sauya kama daga ta mutum zuwa ta aljana Ƴar Iya.
Murmushi tayi tana ci gaba da kallon madubin ta “Ni ƴar nan da yanzu na zama ƴar gayu fah a birni” tayi murmushi lokacin ɗaya kuma ta kwaɓe fuska “Toh ƴan birnin mugaye ne shi yasa amma ina son sukul ɗin” kamar zata yi kuka ta ƙara cewa “Zan koma watarana lokacin na ɗan ƙara wayo....ko dan sai nayi aure tukun” haka ƴar Iya ta saka madubin a gaba tana ƴan zantukan ta.
Jambaki ta ɗauko tare da murɗa shi har sai da ya kai ƙarshe, ai kuwa a lokacin ya karye. Tsaki tayi tana kwaɓe fuska “Mtss kaima ai sai kayi, don ubanka yau duk sai ka ƙare” ta ƙarasa tare da damƙo jambakin da ya ɓalle daga stand nashi ya faɗo. Ba iya baki bane ya samu janbaki har kusan hancin ta ta sama ta ƙasa kuwa har haɓar ta. Ganin akwai saura yasa ta shafa akan cikakkiyar girar ta tare da shafa wani a saman fatar idon ta.
Har zata miƙe ta ƙara kallon madubin. Murmushi ta sake tace “Aradu zan ci kuɗin samari, dubi kyau kamar Ni nayi kai na!”
Ta faɗa tana miƙewa. Bagco nata ta ƙarasa tare da ɗauko atamfar ta leda mai kalar ja, blue, green, yellow sai orange. Blue gyalen ta ta ɗauko ta yafa tare da janyo daron kayan sana'ar ta.
Har ta ɗaura a kanta ta tuno da wuƙar ta, saurin ɗaga katifar ta tayi ta janyo ta sannan ta soka ta a kunkumin ta. Daga nan ta ɗaura daron kayan sana'a ta fice tana waƙar ta
_kai ku kama sana'a mata_
_kai ku kama sana'a mata_
_macen da bata sana'a aura ce_
Haka tayi ta waƙen ta wasun dai-dai wasun kuwa ta kwaɓa abinda taga dama. Gidan Arɗo ta fara shiga.
“Salamu Alekum, gafaran ku dai iyayen ƙauye, gafaran ku dai matan sarki, ga baƙuwa mai neman halaliyar ta nan”
Ta ƙarasa tare da shigewa cikin gidan.
Ƙofar Saratu ta shiga tana tafka sallama kamar wacce ta kawo abun arziƙi. Daga ɗaka Saratu ta fito jin Muryar Ƴar Iya tana amsa mata sallamar.
“Wa Alekumussalamu, maraba da Ƴar Iya shugabar kowa cikin ƙauyen Gallara, maraba da Ƴar Iya tamu mai hannun ɓarna”
Jin kirarin da Saratu ke zabga mata yasa tayi murmushi tare da ƙara sawa wajen ta. Sauƙe daron tayi “Wayyoh”
Saratu tace “Sannu da zuwa ga taburma nan” ta faɗa tana nuna mata taburmar roba da ta ɗauko daga ɗakin ta.
Zama suka yi tare a taburmar Saratu ta gaishe da Ƴar Iya ita kuma ta amsa. Daga nan ta miƙa hannu ta jawo daron kayan sana'ar ta........
COMMENT & SHARE PLEASE!
[5/18, 10:47 AM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘“36&37”””
Zama suka yi tare a taburmar Saratu ta gaishe da Ƴar Iya ita kuma ta amsa. Daga nan ta miƙa hannu ta jawo daron kayan sana'ar ta.
Da mamaki Saratu ke kallon Ƴar Iya ganin dai dagaske take. Murmusawa Ƴar Iya tayi tace
“To Saratu Amaryar Arɗo...ga ƴar iya tazo neman halalin ta, kuyi mata ciniki.”
Riƙe haɓa Saratu tayi tace
“Toh Hajiya Ƴar Iya ai dole ayi maki ciniki, meyeh wannan ɗin?” ta tambaya tare da ɗaukar ƙulli ɗaya tana ƙarewa abun kallo, ganin bata gane meyeh ba yasa ta kaiwa hanci.
Hannun ta Ƴar Iya ta buge tare da wafce ƙullin tana aika mata harara.
“Ungo wannan” ta miƙa mata ƙullin
“Maganin mata ne sadidan da kike gani, Aljanu ne suka bani sirrin wannan maganin da nace musu ina son fara samun halal ɗinah”
Tsurewa Saratu tayi jin an ce Aljanu tare da damƙe ƙullin a hannun ta.
Ganin yanayin da Saratu ta shiga yasa Ƴar Iya kwantar da murya ƙasa sannan tace:
“Kina ji na ko Amaryar Arɗo?” gyaɗa kai saratu tayi
“Kinga wannan ƙullin ba wa kowa zan sayarwa ba saboda tsadar sa, kinga ke na zaɓo har gida na aiko miki, saboda haka ki gwada amfanin sa kiga in baiyi ba a biya ki kuɗin ki. Ba tare da ta fahimci me Ƴar Iya ke cewa ba saboda tsananin mamakin taya ma za'a ce yarinyar nan har tasan wani abu aure, balle kuma gyaran shi....toh zai iya yiyuwa tunda Aljanu gareta ammah abun akwai ɗaure head ace yarinyar da yanzu ne ma ta fara fitar da ƙirgen dangi.
“Baki tambaya nawa ake saidawa ba kuma kin riƙe a hannun ki”
“Yi haƙuri duk farin ciki ya mantar da ni” Ƴar Iya cikin ranta tace “Ke kika sani ai nidai kuɗi kawai nike so” a fili kuma tace “Babu tsada ₦500 ce. Gwalo ido Saratu tayi tace “Ɗaribiyar fa kika ce Ƴar Iya?”
“Eh haka nace in baki siya ne ai sai ki faɗa bana son rainin wayo” ta faɗa a ɗan hasale .
Marairaice fuska Saratu tayi sannan tace
“Kinga kuɗin ne ba'a samu sosai ina ma laifin jaka ɗaya?”
Kallon baki da wayo Ƴar Iya tayi wa Saratu kafin tace
“Bani abu na in Baki siya a haka, ƴar rainin wayo naga idan maganin yayi amfani ko million Kika tambayi Arɗo ba haka ki zai yi ba”
Ɗan tunani kaɗan Saratu tayi ta gyaɗa kanta “Shikenan yanzu yaushe ne ranar biya?”
Ƴar Iya tace “Da an kawo sabon kaya ko gobe ne to zaki bani kuɗi na”
“Shikenan”
Daga haka Ƴar Iya ta miƙe tare da ɗaura daron ta aka ta fice.
Ɓangaren Salamatu ta shige tana roɗa sallama
“Salamu Alekum, ina mutan gidan ne kam?”
Salamatu dake madafa ta kammala kwashe tuwo cikin ƙwarya ta amsa sallamar tana washe baki.
“Wa Alekumussalamu, maraba da Ƴar Iya tamu, yau ke ce a gidan nan”
“Eh nice amma neman halal ya kawoni, kinga miƙo min taburma In Zauna”
Taburmar kaba salamatu ta shimfiɗa wa Ƴar Iya ita ma ta zauna. Hakan ya sa Ƴar Iya sauƙe daron ta tare da zama gefen salamatu.
“To salamatu tallan maganin mata na kawo wanda na gaji sirrin daga wurin Aljanun soyayya, sabila da haka ban san ko zaki saya ba”
“Toh maganin mata kuma Ƴar Iya, meyeh shi?” ta faɗa tana zare idanuwa.
Harara ta wullo mata tana aika mata kallon baki da wayo
“Wallahi sai kin siya salamatu na riga na faɗa miki, sarai kin sani Ni zaki yiwa tsiya?, To bari kiji nimah nan na san kina buƙatar maganin, kaji shegiya burgujejiya kamar shanuwa.” ta ƙarasa tana aika mata kallon raini. Cikin kiɗima Salamatu tace
“Yi haƙuti Ƴar Iya ai ban ce ba zan saya ba, dole na siya kam.”
“Ah to karma ki siya nikam bani da hurobulom ai, kece zaki neme Ni da kaina tunda kishiyar ki ma ta saya, idan Arɗo ya koraki gida nan zaki zo har bukka ta a gidan iya”
“Shikenan dai Ƴar Iya, nawa ce kuɗin?”
“₦500 ce babu yawa!”
“Ɗari biyar!”
“Eh a haka kishiyar ki ma ta siya ai, in baki siya ba ma kece a ruwa, a to”
“Na ma siya ai, bari na ɗauko kuɗin ko cikin na abincin gobe ne”
Murmushi Ƴar Iya tayi kafin tace “To yi sauri ina son shiga cikin garin ne”
Fitowa tayi riƙe da ₦500 sannan ta miƙawa Ƴar Iya, daga nan ta ja daron ta ta fice.
Gida uku ta ƙara shiga ganin sun bata kuɗi a hannu yasa ta dawo gida abun ta tana murna ita ma yanzu zata yi kuɗi daga nan kuma zata koma birni.
★★★★★★★★★★★
*SHAREEF POV*
Bisa grass carpet dake a garden ɗin ya zauna saboda ɓacin rai. Da ya rufe ido babu abunda yake gani sai wannan ƙazamar halittar da ta taɓa hannun sa. Tuno da koɗaɗdiyar fuskar ta mai ibi da a Aljanu yayi, ga kuma wani attachment da tayi kitso tuni zuciyar shi ta fara tashi amai ya taso mishi, da ƙyar Hamma Zaki ya miƙe ya wuce sink ɗin dake cikin garden ɗin, amai yayi sosai kafin ya wanke bakin sa ya fito saboda lokacin sallah yayi. Daga cikin abinda ya tsana yaga mace ta sanya bai wuce attachment ba, ya tsani abun gabaɗaya ma shi ƙyama abun ke bashi.
A daddafe ya miƙe ya ƙarasa ciki, part ɗin Nenne ya wuce ba tare da kowa ya san yana can ɗin ba saboda duk suna can part ɗin Mom ana ajajjaɓin ko ina Hamma Zakin ya shiga. Da ƙyar yayi sallar a zaune ma saboda yadda kanshi ke ƙara juyawa.
Yana idarwa ya samu gado ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi. Yanayin gabaɗaya is not stable for him. He just wanna forget that devil creature and yayi alƙawarin wulaƙanta ta idan ya warware daga takaicin da ta ƙunzuga mishi a gaban ƙannen shi.
(Bata da ma hankali, bata san waye Hamma Zaki ba, mutumin da kyawawan mata waɗanda ba na ƙasar ba wasu ma ƴaƴan sarakuna suke nuna zalamar su kan shi baya damuwa da su, ko kallon arziƙi baya bari su amsa daga wurin shi. Ballantana ita...toh ai ko Sarah da take baindiya bai bawa fuska bare kuma nunar rana. Afwan Aunty pretty gaskiya mike faɗa miki)
Allah sarki Mom da ƙyar aka lallashe ta ta haƙura ta zauna. Gaba ɗaya hankalin ta duk ya fice daga jikin ta jin ance ya dawo ammah kuma gashi su sun rasa shi, tsoron ta ma kada ace ya illata kansa.
Hajiya Granny ma sai Nenne ke aikin rarrashin ta saboda kuka take bilhaƙƙi.
“Shikenan uban me rai suka yiwa ɗan jikan nawa, yo Ni dama can Shagalin bai kwanta a raina ba gashi wata tsinanniyar ta wargaza wa jika na farin ciki. Wallahi ko ɗiyar waye sai muyi Shari'a da ubanta akan jika na”
Cikin kwantar da kai Nenne tace “Kiyi haƙuri Granny, Ina da tabbacin duk inda Shareef yake yana cikin aminci, kin san Allah bazai cutar da wanda baya cutar kowa ba saboda haka kiyi haƙuri nasan zai dawo”
Cikin shessheƙan kuka Granny tace
“Toh Allah yasa”
A nan part ɗin Mom dukkan su suka yi sallar maghrib daga iyaye mata zuwa ƴaƴayen, iyaye mazan kuma sun fice don neman mafita.
Wani matsiyacin bacci ne ya ɗauke shi a kan gadon cikin wannan yanayi. Ƙiran sallar Ishã ya sa ya farka, miƙa yayi ɗauke da addu'ar bacci a bakin sa. Ganin duhu ya tabbatar masa da Ishã tayi. Tuna cewa babu wanda yasan yana nan yasa ya yi yunƙurin miƙewa don yasan iyayen shi na cikin tashin hankali.
Miƙewa yayi ya fara takawa a hankali, da ya fito parlourn yaga babu kowa ciki ya tabbatar ma kanshi suna can ana neman shi, da sauri ya fice daga part ɗin Nenne zuwa part ɗin Mom.
Kamar ance su juyo dukan su duka waiwayo ai kuwa ganin shi ɗin ke shigowa ya sa duk suka miƙe tare da nufar sa. Kukan Mom keyi tace “Son where have u been?, Duk nan ka sa mun shiga tashin hankali”
Murmushin yaƙe yayi yace
“Calm down everyone Ina can garden ne” daga haka kowa ya koma tare da miƙewa da niyyar yin sallar Ishã in sunyi sai suyi dinner daga nan kowa ya wuce part ɗin su.
Mom kuwa sai da ta ƙira su Daddy ta sanar da su cewa an samu son ɗin nasu tukun tayi sallah.
Bayan sunyi sallah duka suka hallara a dining area, a nutse aka fara ci yayin da baka jin sautin komai sai ƙarar cokala. Ana gama dinner kowa ya watse zuwa nashi ɓangaren.
Hajiya Sarah na gama cin abincin ta ta wuce bedroom nata tare da ɗauko wayar ta. Instagram ta fara hawa tare da posting pictures ɗin da suka yi ita da sauran family wurin taron, few seconds aka fara liking, COMMENTS kuwa ba'a magana. Wasu na tambayar mijin ta ne ko dai?. Wasu kuma har sun ajiye zancen mijin ta ne, hala shi yasa ma baya kula kowacce mace tunda ya samu wannan indian girl ɗin.
Cikin daren kuwa babu abinda ya kai pictures masu trending a Media, Instagram, Facebook, Twitter, YouTube, duk ta ko'ina zancen ake. Wasu na can suna publishing shati faɗin su kan Sarah da kuma Hamma Zaki, yayin da wasu ke ƙara santin haɗa jini da wannan kyawawan family masu nagarta.
Around 10:00pm wayar Sarah tayi ringing, picking tayi tana murmurshi tare da kara wayar a kunnen ta.
“Hello” aka faɗa daga ɗaya ɓangaren
“Hi” ta faɗa cikin sanyi murya.
“Princess how're u doing?, Kin koma gida lafiya?”
“Alhamdulillah”
“Masha Allah, kiyi saving digits na, we'll talk tomorrow”
“Ok bye”
Murmushi Mai sauti yayi sannan yace “Ok good night and sweet dreams”
Daga haka suka katse kiran.
Haka kawai Sarah ta tsinci kanta cikin tsananin farin ciki bayan kammala wayar da Captain Sulaiman wanda shima ɓangaren sa wani irin farin ciki ya shiga, burin sa ya kusa cika, ya samu choice nashi, ga kyau ga wayewa ga kuma ilimi. Uwa uba nasabar ta da abokin su wanda suke ji da shi.
Ɓangaren Hamma Zaki bayan sun ci abinci kiran Hamma Saleem ya shigo, sanin wane irin hali ɗan uwan shi zai shiga bayan jin bayanin abinda ya faru a wurin taro yasa yake ta banko masa ƙira tun lokacin sai dai shikam yana can garden ma, ko da ya dawo cikin gidan ma bai samu sukunin taɓa wayar ba.
Lallamin sa shima Hamma Saleem ɗin yayi nan da nan ya sauƙo har da ƴar dariyar shi, daga haka suka yi sallama yana ce masa zai shigo in Sha Allah.
Bayan sun kammala wayar ne kawai yaji sha'awar hawa online. A nan yaci karo da abubuwan dake trending, cike da mamaki ya shiga pictures ɗin yana dubawa wasu yayi tsaki wasu kuma yayi murmushi, kan picture nashi wanda aka yi musu da duka sisters ɗin shi ya tsaya. Ya jima yana dubawa yana murmushi. Ƙaunar su ce kawai ke yawo cikin zuciyar shi yayin da yake jin zai iya sadaukar da komai nadhi saboda su.
Daga nan comment section ya shiga, nan fa yayi ta jera tsaki ganin haukar mutane. Ya jima yana dubawa wani wurin kuma ya yi murmushi. Haka ya leƙa all media handles nashi daga nan ya kashe phone ɗin tare da ajiyewa.
Wanka yayi tare da ɗauro alwala ya saka Armani pyjamas tare da fesa turare, daga kashe light ya bar iya bedside dim light, nan ya haye bed ɗin sa tare da janyo blanket, addu'oin baccin sa yayi tare da kwanciya.
_Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace, duk wanda yayi alwala kafin yayi bacci, ya kaɗe shimfiɗar sa sannan ya kwanta ɓangaren dama tare da karanto addu'oin bacci, Ubangiji zai sanya Mala'iku su zama dakarun da zasu yi gadin sa har zuwa lokacin da zai tashi._
Hadisin ingantacce ne.
_Addu'oin bacci_
★Ayatul kursiyy
★Amanarrasul
★Suratul-ilhlas (qul huwallahu ahad)
★Suratul falaq (qul authu birabbil falaq)
★Suratul-Nas (qul authu birabbil nas)
★Bismikallahumma Amutu wa ahya.
COMMENT & SHARE FISABILILLAHI!
[5/18, 10:50 AM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_