Showing 114001 words to 117000 words out of 135404 words

Chapter 39 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46366

ya ɗauka, bayan ya sha ya koma bedroom nasa tare da faɗawa toilet, sai da yayi wanka ya tsaftace jikinsa tukun ya sanya kayan bacci. Daga nan ya kwanta yana addu'ar Allah yasa bacci ya zo masa.

A ɓangaren amarya tana kwance ne lulluɓe amma ba bacci take yi ba, ta yaya ma zata iya bacci bayan ta ga irin take-taken mijin nata, she's in deep pain, shawara kawai take da zuciyarta, jin alamar buɗe ɗakin yasa ta ƙara lafewa don kuwa tana da tabbacin shi din ne, ba ma wannan ba, abunda ya matukar tafa hankalinta shin ƙamshin da taji irin na Rouhy ɗinta, sai kawai zuciyarta ta gargade ta kan cewa he must not be the one kawai tunaninsa da ta saka a ranta ne.

Har ya fita guzirin ƙamshin na nan hakan yasa ta miƙe ta zauna, ganin dai haiƙan baccin ba zuwa zai yi ba yasa ta nufi toilet tare da ɗauro Alwala nan ta gabatar da nafilfilu tana faɗawa Ubangiji damuwarta.


*********************

Washegari da ƙyar ta tashi tayi sallar subh, tana idarwa ta watsa ruwa sai kawai ta tsinci kanta da jin sha'awar ganin gidan ko ya yake, a hankali ta fito har ta iso parlourn. Masha Allah kawai take furtawa, gaskiya dole ta yi ƙoƙarin cire Rouhy a ranta duba da irin yadda su Daddy suka yi ɗawainiya da ita but the question is how?. Haka dai ta gama kalle-kallenta daga nan kuma ta wuce main kitchen ɗin tana mai kalle-kallenta, tunawa da kazar jiya yasa ta fito da ita tayi warning, duk da akwai komai na buƙata kawai sai ta ɗauki ɗaya a plate, ɗayan kuma ta ajiye masa a. Dining if he likes eat, in ya so Kuma kada ya ci.

Ko da ta ci wankanta tayi ta sanya wani haɗaɗɗen lace ɗinkin Riga da zani Wanda yayi matuƙar yi mata kyau. A bedroom ɗinta ta zauna saboda bata wani son damuwa. Around 10:00am sai ga mutanen Gallara sun zo yi mata sallama.

A ɓangaren Hamma Zaki bayan ya dawo daga masjid kamar kullum yakan karanta Alqur'ani mai girma, bai koma bacci ba coz na jiyan ma sace shi yayi, yana daddana wayarsa can sai ga ƙiran Daddy, nan ya sanar masa da anjima ƴan uwan amarya zasu wuce ya tabbatar ya sallame su in sun zo. Da to ya amsa kawai sai yaji wayar ma ta ishe shi, ajiye ta yayi, ko gama ɗauke hannunsa bai yi ba ko me ya tuna sai ya ƙara saka hannu ya janyo ta. Gallery ya shiga a dai-dai hotonta ya tsaya yana kallo yayin da ya lula i zuwa duniyar tunani.

Tabbas bai san menene so ba, a bayan soyayyar iyaye da kuma ƴan uwa bai taɓa imani cewa akwai son wani kuma ba, bai taɓa tunanin zai so wani abu kamar haka har ya son abun ya hana shi sukuni ba, tabbas jarrabawa ce daga ubangiji, fatansa Allah yasa ya iya lashe ta.

Haka ya ci gaba da bin pictures ɗin yana kallo, wani yayi dariya wani kuma akasin shi, gajiya da zama ya sa ya fito don ya zaga gidan da ya gina musamman saboda masoyiyarsa ta hakika but God destined it to be na wannan so called amaryar.

_Share FISABILILLAH_

[20/09, 7:41 a.m.] Famanté 💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““113&114”””

Da abinda ke dining ya fara cin karo sai ya ɗan taɓe baki yana nufar wurin, kamar wanda baya so a san yana wurin ya buɗe yana ɗan zaro ido sai kuma ya yamutsa fuska yace “Damn it!” yana mai naushin iska. Tsintar kansa yayi da zama, sai da ya ci ya ƙoshi sannan yayi hamdala kafin ya fita don yin abinda y kawo shi.

Bayan ya zaga gidan ne ya koma ya gyara jikinsa tsaf y fito yana ƙamshin mayataccen turarensa, har ya fito ya koma ya ɗauko wata briefcase 💼 ya fito. A garden yayi zamansa specifically Kuma jiran ƴan uwan amaryar yake yi don ya sallame su kamar yadda Daddy ya faɗa.

*****************

Su Iya da kuma su saratu amaryar Arɗo da sauran ƴan uwa mata da abokan arziki da suka zo bikin tun daga Gallara sun matuƙar yaba da gidan Khairyn (yo ai Ni ƴar birni ma gidan ya tafi da imani na talkless of mazauna karkara).
Khairy tayi farin ciki sosai nan da nan ta sake suna ta hira hira abunsu.

Can dai suka yi mata sallama cewa zasu wuce, kamar zata yi kuka tace “Yanzu Iya kema tafiya zaki yi?, shikenan ai” sai kuma ta Turo baki gaba. Dariya dukkansu suka yi ganin dai tafiyar zasu yi yasa ta wuce bedroom ɗinta ta kwaso wasu kayayyaki da sabulai ta. Saka musu cikin wata babbar jaka daga nan ta kawo musu. Sun ji daɗi sosai ganin Khairy bata wulaƙanta su ba duk da cewa ita yanzu ta riga ta waye abunta, nan suka yi mata sallama suka wuce.

Daidai zasu fita Gate man ya tsayar da su yana faɗin “Hajiya ku ɗan tsaya mai gidan ya ce in zaku tafi ayi masa magana”
Iya tace “To to shikenan”
Garden ɗin mai gadi ya nufa ya sanar masa, babu ɓata lokaci ya fito kuwa. Mamaki ne ya kama shi ganin mutanen karkara a matsayin dangin matarsa sai kuma ya basar kawai ya ƙarasa, cike da girmamawa suka gaisa don har ga Allah shi bai ma gane Iya ba ita ma kuma a nata bangaren bata gane shi ba.

Wata file jacket ya miƙs musu sannan yace bari ya miƙa su tunda gida zasu koma, godiya sosai suka yi masa nan ya jawo mota ya kwashe su zuwa gida daga nan kuma ya dawo.

A yanzu dai Hamma Zaki ya yanke shawarar neman transfer zuwa Lagos don har ga Allah ba zai zauna mata su maida shi mahaukaci ba, idan yaso bayan watanni bibbiyu sai yazo yayi kwana ɗaɗɗaya gidan ko wacce. Hakan ya sa ya ƙira Major ya snag da shi. Abunka da jajirtaccen mutum tuni Major ya ce masa ya zo ya cike takardun daga nan ya koma. Yayi farin ciki sosai da hakan har ya gagara ɓoyuwa a fuskarsa sai murmushi yake yi.

A ɓangaren Khairy tunda suka yi mata sallama ta koma bedroom ɗinta, WhatsApp ta hau luckily ta tarar group nasu na babes duka suka active, kowaccen su na faɗin dama haka auren yake, kamar ba su ne masu rawar kan ayi ba. Ita dai nata dariya ne nan suka hau kanta wai don ta auri mai tausayi shine take musu dariya, to wallahi zasu rama ne.

___________________________________________________________

*A WEEK LATER*

Tsawon sati guda kenan daga ango Hamma Zaki zuwa kan amaryarsa Khairy babu wanda ya san wanene partner ɗinsa, ita kuwa pretty duk ta bi ta tsige kamar wsta aljana dama yaya jikin yake bare kuma an saka damuwa, gwani mijin mata biyu kuma ana shirin tafiya lagos a barsu a Adamawa. Ita kuwa Khairy tana jin daɗi kaɗan ko dan saboda Amrah da take zuwa mata sosai da sosai

Yau Lahadi ne wanda yayi daidai da ragowar kwana biyar da tafiyarsa zuwa Lagos. Kwance yake akan makeken gadonsa yana aikin na tunani, ƙarar da wayarsa tayi yasa ya miƙa hannunsa ya janyo ta. Ganin unknown number ya sa ya mayar, ƙara ƙira aka yi amma bai yi picking ba, mai ƙiran dai da alamun yana buƙatar yin wayar sosai sai ya ƙara ƙira, ɗan tsaki yayi yana mai ɗagawa tare da kara wayar a kunnensa.
Shiru yayi ta ɗaya bangaren aka yi sallama, a hankali ya amsa yana lumshe idanunsa. Tsawon mintuna shida aka ɗauka ana magana a ɗaya ɓangaren can kuma da na lura da Hamma Zaki sai naga fararen idanunsa sun koma tamkar gauta haka nan kuma farar fatarsa ma tayi ja. Sauƙe wayar yayi yana ajiye ta tare da ƙara jingina da pillow ɗin. Lumshe idanunsa yayi ya kuma sauƙe ajiyar zuciya.

A wannan yanayin ya ɗauko wayarsa ya ƙira numbern Dr faruq, cike da mamaki Dr ya ɗaga don tsawon rayuwarsa da Hamma Zaki, hardly ka ga ya ƙira wani amma yau sai ga shi ya ƙira shi. Sallama yayi masa amma Hamma Zaki cikin ransa ya amsa. Jin shiru yasa Dr faɗin “Lafiya Captain?” shiru nan ma, “Please kayi magana kana lafiya kuwa?” jin shirin yayi yawa yasa ya katse ƙiran tare da shiga Google maps yayi tracing location, ganin yana gidan pretty yasa yayi saurin fitowa ya nufi motarsa daga nan sai gidan Prettyn.

A firgice ya fito daga motarsa ya nufi entrance door na gidan, ganin a buɗe yasa yayi sallama yana shiga, da yake babu kowa ma a parlourn kawai ya haye sama, bedroom ɗinsa ya nufa ganinsa cikin wani iri yanayi numfashinsa si fizgewa yake yasa yayi kansa da sauri.

Da ƙyar ya tallafo shi suka fito don yadda ya firgice ba ma zai iya treating abokin nasa ba. Hospital ɗinshi ya nufa da shi, ganin patient ɗin ogansu yasa suka rufi kansa don ceto rayuwarsa. Tsawon wani lokaci tukun aka ci nasarar ceto rayuwarsa.

Sai a lokacin hankalin Dr ya ɗan kwanta amma cikin ransa yana tunanin ko me ya sami abokin nasa. Numbern Mom ya ƙira ya sanar da ita cewa Ga hamma zaki da a hospital nashi, nan ta ruɗe ta nufi Granny ta sanar mata, babu shiru kuwa suka taho, sai a lokacin Granny ta tuna da Khairy, miƙawa Mom wayar tayi tace ta duba mata number Khairy, bayan tayi dialling ta miƙa mata.


Suna zaune da Amrah a parlourn ƙasa sun kallon maimaicin series film ɗin أمينتي و أن تحققت wayarta tayi ƙara, gani Granny yasa tayi murmushi tana faɗin Allah sarki grannny am, picking tayi sannan tayi sallama. Granny ta amsa tana tambayarta lafiya?, lafiya lafiya ta amsa mata. Granny tace “Khairy g fa mijinki nan bashi da lafiya kwance a asibitin Faruqu” dum gabanta ya buga sai tayi ƙoƙarin saita kanta tace “Inna lillahi, gani nan zuwa nima”. Ta faɗi hakan ne saboda kawai kar a fahimci wani abu, babu wanda ya san har yau bata san waye mijin ba har yau, hatta babes babu wanda ya san da hakan, su tunanin su ma ta sani tunda dama sun san ita da Hamma soyayya suke ko da labarin cewa da shi aka ɗaura yazo babu wacce ta kawo mata zancen.

Amrah ce ta dube ta tace “Ya dai, wani abu ya faru ne?” kamar kar ta faɗa Mata kuma sai tace “Wai mai gidan ne babu lafiya yana asibiti amma ba zuwa zanyi ba”.
Kallon baki da wayo Amrah tayi mata tace “Ban gane ba” sai kawai ta basar tace “Wasa nake zan je fa”
“Ko ke fa, yanzu dai ki tashi mu haɗa abinci mai rai da lafiya sai mu je tare ko?” babu yadda ta iya haka suka shiga kitchen, tunanin me zasu yi kawai sai ta tuna da favourite ɗin Rouhy ɗinta kawai ta yanke shawarar yi masa ko da baya so.

Bayan sun gama suka suka yi wanka sannan su ka kwashi abincin suka fita, da yake Amrah na driving motar ta ta ɗauko suka tafi da ita.
A daidai parking lot na asibiti suka yi parking, Khairy da ke riƙe da abincin ta fito sannan Amrah ta biyo bayanta, a nutse har suka iso reception, a nan suka tarar da Granny da Nenne, cike da girmamawa suka gaisa su nan suka tambayi yaya jikin nasa, Alhamdulillah yaji sauƙi ma sosai.

A lokacin ne kuma Dr ɗin ya ce zasu iya shiga duba sa yanzu za'a kai shi ward. A tare suka tashi kowa na rige-rigen bin Dr ɗin. Duk irin yadda gabanta ke faɗuwa a haka ta bi bayansu riƙe da abincin.

Amenity ward room 3 a nan aka ajiye shi, Granny da Nenne ne suka fara shiga duba shi yayin da khairy ke tsaye ita da Amrah, ba komai ne ya hana ta shiga ba sai fargabar abinda zata tarar in ta shiga. Gajiya da tsayuwar da suka yi yasa suka nemi kujera suka zauna.

Can sai ga Granny ta fito tana faɗin “Ummul khairy” Nenne ma a lokacin ta fito. Da sauri khairy ta amsa da “Na'am granny” tare da ƙarasawa gabanta ta ce “Gani”. Sai da Granny ta ƙanƙance Ido kafin tace “Mu zamu koma gida ki zauna ki kula da mijinki in ya so idan abokiyar zaman naki ta iso zuwa yamma sai ki koma tunda ya ce la'alla zuwa dare ma zaa sallame shi”. Kai kawai khairy ta gyaɗa nan su Granny suka kama hanya.

Gaban ta ne ya bada wani mummunan sauti jin abokiyar zama, kenan ma har mata ne da shi shiyasa bai neme ta ko sau ɗaya ba?, lallai namiji sai shi, da ba don bata son kowa ya san alaƙa da muamalarsu ba ai da babu anunda zai kawo ta jinyarsa. Cike da ƙarfin hali ta juyo tana kallon Amrah, alama tayi mata da ta zo su shiga. Tare suka jera har zuwa cikin ɗakin.

Lulluɓe yake da farin blanket na asibitin yana kallon bango hakan ne yasa mai shigowa ba zai iya ganin fuskarsa ba. Dumm ƙirjinta ya buga, in ba gizo Rouhy yake mata ba to tabbas irin ƙirar jikinsa ne so giant. Kau da kai tayi ta nufi drawer Dake bedside ta ajiye basket ɗin hannunta sannan ta jawo kujeru biyu da ke ɗakin, zama tayi ta nuna wa Amrah ma da ta zauna. Bayan sun zauna kuwa wayarta ta kunna tana chat don in tace zata yi surutu tabbas zai iya tashi and bata so ya ganta ma gabaɗaya.

Ko me Amrah ta tuna sai ta ce mata zata je gida ta dawo, ba dan ta so ba tace mata “To shikenan, thanks Amrah” “Welcome” daga haka tayi waving mata hannu tare da ficewa.

Few minutes da fitar Khairy sai ga Dr. Faruq ya shigo don an ce masa an yi stabilizing na condition ɗin har an Kai shi amenity ward shiyasa ya ce Bara ya dawo yayi jinyarsa.
Turus ya tsaya ganin mace a ɗakin, can dai ya samu ƙarfin halin furta “Assalamu Alykum”, “Wa Alykumussalam” ta amsa ba tare da ta juyo ba. Hakan ya jefa shi cikin tunani to waye wannan, zuciyarsa ta bashi amsa da Nabila or amarya, one of them. Juyawa yayi zai fita sai kuma ya dawo tare da ƙarasowa yadda suke.

Cikin wani irin yanayi mai ɗauke da rashin yadda ya ce “Baiwar Allah”. Sam ita da aka yi sallamar bata ɗauki mai Muryar ba sai yanzu da ya shigo, ɗan sakin fuskarta tayi ba tare da ta juyo ba tace “Ina yini Hamma Faruq” shima dai sai yanzu ya gane Khairy ce, fuska sake yace “A'ah Ummul Khairy, ke ce kike jinyar yayan naku?” ba tare da fahimtar komai ba ta gyaɗa kai tana faɗin “Eh nice”, “Ok shilenan tunda kina nan, in ya tashi ki dubo likita Please ” bai jira amsar ba ya fita abunsa yana tunanin wani abun. Shi fa wallahi tun ba yanzu ba ya so Dude ɗinsa wannan yarinyar aka aura masa don lokacin da take a gidansa sai da ya ƙara wani haske tare da murjewa.
(Ni kuwa nace baka san ita ɗin aka aura masa bane ko me?).

_Comment Please_

[20/09, 2:45 p.m.] Famanté 💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““115&116”””

Tsawon awa guda ta share zaune tana danna wayarta, kamar daga sama ta ji ya fara mutsu-mutsu, ɗan yamutsa fuska tayi duk da cewa gabanta faɗuwa yake yi. Har za ta miƙe sai kuma ta fasa jin kamar yana magana. Kunnenta ta kashe sosai don tabbatarwa.
“Kin cuce Ni Nabila, oh Allah ”.

Dumm gabanta ya faɗin jin kamar Muryar Rouhy ɗinta, shiru tayi saboda ta ƙara tabbatarwa, gabanta ne ya ƙara faɗuwa jin ya ƙara magana. Tabbas shine, to me yake yi a nan?, “anya kuwa Granny ta san cewa Hamma Zaki ne baya da lafiya ta ƙira ni?” ta faɗa cike da ruɗu a fuskarta. “To idan ta sani what does that mean eh?” haka ta zauna tana karanta wasiƙar jaki don kuwa dai babu mai bata dukkan waɗannan amsoshin.

20 minutes later ya fara motsa ƙafafuwansa, a ɗan zabure ta miƙe tana zuba idanuwanta a kansa. A hankali ya fara buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyi yana mai yamutsa fuskarsa, hakan ya sa ta tabbatar yanzu ya farka ne, miƙewa tayi tare da ƙarasowa kusa kusa da shi ta ranƙwafar da kanta gare sa har tana iya jiyo hawa da sauƙar numfashinsa. A hankali ta furta “Sannu Hamma, bari na ƙira Dr.”

Da sauri ya ƙara buɗe idanuwansa da suke lumshe sakamakon jin Muryar ta, ganin dai ita ɗin ce ya sa ya yi mata alama da kansa akan Toh. Da sauri ta fita don ta ƙira Dr ɗin, tare suka shigo da Dr tana biye da shi har zuwa room ɗin, fuska sake Dr ya ce “Sannu Captain” kai ya daga masa hakan ya bawa Dr damar ƙara aika masa tambaya. “Ya jikin naka?” buɗe kyawawan idanunsa yayi yana ƙarewa ɗakin kallo, ganin dripstand yasa ya tabbatar asibiti ne, a lokacin kuma ya fara tunano ya aka yi yazo nan, ɗan dafe kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login