Showing 42001 words to 45000 words out of 135404 words

Chapter 15 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46369

“Ki bar zancen ku da Sulaiman ya wuce mana Pretty, na san shine har yanzu a ranki” daga haka ta kalli Mom dake mamakin Pretty tace “Kiyi haƙuri Mom kada kiyi tunanin dake take, tana da rashin lafiyar maimaita abu idan ya faru da ita, ga bata iya mantuwa”
Murmushi Mom tayi tace “babu komai”

Ganin shiru babu wacce ta ɗago waya ta ƙira Hamma Zaki yasa Mom tace “Ku ƙira shi manah, ni zan wuce ciki”
Cike da duniyanci Ishy ta kaɗa yatsar ta “Wayyo Mom, Kinga saboda saurin da muke na har mun mace wayoyin mu a gida”
“Shikenan bari na wuce, zan ƙira shi”.

Bedroom ɗin ta ta koma tana mai juya maganganun baƙin Hamma Zaki. Bayan ta sanar da shi ta hanyar kiran shi a waya ta faɗa tunanin su waye waɗannan, ko suwaye da gani babu alkhairi a tattare da su, yara sam babu ɗaa bare girmama babba.....
“Hmm to Allah ya kyauta, amma tabbas tana son sanin abu game da su.

Kwance yake yana latsa wayar sa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aikin shi ba. Ya miƙa wayar zai ajiye gefe yaji ringing na wayar. Kamar ba zai yi picking ba ya na tsani tare da ɗagowa, ganin Mom yasa ga zare idanuwa tare da picking.
“Sweetheart...” ba tare da ta barshi ya faɗi me zai ce ba ta katse shi da faɗin
“Kana da baƙi a waje, suna jiran ka a parlour”
“Parlour?” ya faɗa cikin sigar tambaya coz Basu yi da Dr. Faruq zai shigo ba ko wani friend nashi.
“Who Are they Mom?”
“Get down and see” daga haka ta katse ƙiran.

Kamar baya so ya buɗe ƙofa tare da fitowa, shi ba mutum bane mai son gulma ba hakan yasa bai dubo daga can ba. Black jallabiya be jikin shi, kamar koyaushe ƙamshin daddaɗan turaren shi ke tashi. Sam ko kaɗan bai sa a ranshi matan nan ne baƙin shi ba hakan yasa ya miƙe zai je Bedroom ɗin Mom. Cak ya tsaya jin an riƙe hannun shi. A hanzarce ya waiwayo don ganin waye wannan. Dum! Ƙirjin shi ya buga, shi bai yi magana ba sai wani kallo da yake aika mata cikin ranshi kuma yana faɗin (This girl again?”.

Ganin hankalin shi na kanta yasa ta marairaice fuska “Please Sweetheart, no sau ɗaya ka bani damar nan, wallahi ina son ka shi yasa na baro Abuja takanas saboda kai, Please ko sau ɗaya ka bani lokaci”.
Ba tare da yace mata komai ba ya janye hannunsa ya wuce zuwa bedroom ɗin Mom wondering why yarinyar nan ta ƙara dawowa gare shi. Tun shigowar shi Mom ta tare shi “Kun gaisa da baƙin ne?”
Kai ya gyaɗa yace “Mom, why are they here, ban san su ba” Mom tace “Ban gane ba, baka sansu ba fa kace?”
Cike da ƙosawa yace “Is ok”
Daga haka ya fito, fitowar shi yayi dai-dai da shigowar Sarah daga bedroom ɗin ta.
“Good Evening bro”
“Evening” daga haka ya wuce zai haye stairs ɗin.

Ganin zai wuce yasa Pretty miƙewa da sassarfa tabi bayan shi, babu tsammani taji an riƙe ƙugunta ta baya. Juyawa tayi don ganin waye ke shirin yi mata shamaki da abun son ta.

Cikin sanyin murya Sarah tace “You again?, What brought u here?” ta faɗa tana pointing Pretty. Cikin son danne fushin ta don ita kanta ta fara tabbatar wa cewa Sarah matar Sweetheart ɗin ta ne ko da ganin mahaifiyar Sweetheart ɗin nata tace “Rabu da Ni ba rigima nazo yi ba”
“Then me ya kawo ki?” jin tayi shiru yasa tace “Idan ma saboda shi ne ki sani baki kai ya soki ba, mata masu daraja kaɗai ke samun matsuguni a zuciyar shi, hope I'm clear!”
Cikin jin haushi Pretty ta janye jikin tare da nufi bedroom ɗin da taga Mom ta shiga ɗazu, babu sallama tace
“Mom!” mamaki ya hana Mom ko da amsawa ne sai jin Muryar Pretty tayi tana faɗin
“Mom na zo ne don furta soyayya ta ga ɗan ki Captain, da farko i thought zai yi sauƙi kamar ke but ashe kawai hasashe ne iri nawa, don Allah Mom let him Know that Ina son shi. Gobe zan wuce gida Abuja, amma zan ƙara dawowa”
Daga haka ta fice tare da yiwa su Ishy da ke cikin mamaki da ɗimuwa alamar su fito. Babu shiri suka miƙe suna makawa Sarah harara tare da ficewa.

★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Sana'a Ƴar iya ke yi babu kama hannun yaro, ciniki kuwa sosai baa magana, da zarar kayan sana'ar ya ƙare zata ɗebo ta ƙara busarwa taje gidan Arɗo ta daka abun ta.

Samun da take yi bai hanata yin halin da ta saba ba, gashi bikin A'i sati mai zuwa ne, hakan yasa Ƴar Iya bada himma wurin sana'ar ta, kullum tayi ciniki zata kawowa Halima ta ajiye mata.

Safiyar yau tunda Ƴar Iya ta tashi take jin shiga hancin mutane, hakan yasa ko karyawa batayi ba ta fice sai gidan Inna Zaliha. Inna Zaliha da aka ce wai ciki gare ta abun yayi wa Ƴar Iya daɗi don yadda ta san wannan kwaɗayayyiyar to dole zata ji daɗi musamman da ta tuna duk zuwa gidan da zata yi sai ta tarar da abun daɗi.

Tana isa lokacin Inna Zaliha ta shiga bayi ga kuma tukunya bisa murhu ƙamshi na tashi. A hankali cikin sanɗa ta ƙarasa wajen murhun tana lashe baki.
“Wayyo Ni Ƴar nan, yau akwai burauba, bari na samu na fice kafin mayyar nan ta fito.”
A haka ta ɗaga tukunyar daga kan murhun tare da lallaɓawa ta fice abun ta. Tana kaiwa hanyar waje ta ajiye don ganin menene a ciki. Ido ta zaro tana faɗin
“Shegu ai yau kam mun haɗu, Aradu kun daina ci ku kaɗai”.
Dahuwa ce ta kaza wacce daddawa taji a ciki, ga romon jajir da shi kamar me.
Bata tsaya ɓata lokaci ba ta arta a guje sai gidan Iyar ta.

COMMENT PLEASE


🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*







__Fictional story of life with full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA “““43&44”””

_ina Taya ki murna sosai Ameeran Mama (amarya), Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya ya sa gidan ki Kenan. Ina godiya da ƙaunar ki sannan ina ƙaunar ki da yawa_
_Shafin nan na baki shi ke kaɗai duk da cewa littafin na Nazari Writers ne amma Ni da kaina nayi kyautar shi😀😏

Inna Zaliha na fitowa daga bayi ta ƙyalla idon ta ga murhun da ta ɗaura dahuwar ta. Ƙwalalo idanuwa waje tayi tare da rufe bakinta da hannu.
“Subhanallahi” ta furta tana juya wa tare da fara ƴan dube dube. Ta shafe kusan mintuna 30 tana dube-duben da take yi gashi fitowarta daga wanka kenan.

Zuciyar ta na wani irin bugu ta shiga bukkar ta tare da ajiye soson buhu da kuma garin omo da tayi wanka da shi. Zanin ta iya ƙirji ta fito tana mai ci gaba da dube-duben nata sai dai babu tukunya babu kuma alamar ta. Hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba musamman da bata ji ko ganin alamar shigowar wani ko wata ba. Ganin dube-duben ba zai fisshe ta ba yasa ta koma bukkar ta tare da zama a bakin gadon karan ta tana jajantawa kanta.

Bata kawo cewa Ƴar masu gidan ce ta ɗauke ba duk tunanin ta Almajirai ne, bayan dawowar Baba da ta sanar masa ya lallashe ta tare da bata haƙuri.

*ƳAR IYA POV*

Tana Isa gida iya ta shige da gudu, bayan ta ajiye tukunyar ta fara ƙwallawa Iyar ƙira kamar wuyan ta zai faɗo
“Iya! Iya!”
Jin shiru yasa ta shiga bukkar ta. Kwance ta sameta tana sharara bacci har abun haushi, ga wani yawun baccin ta a wurin. Tsinke ta zara daga tsintsiyar kwakwa dake gurin, sai da ta saita cinyar iya ta caka mata tsinken tana cije baki.

“Inna lillahi” iya ta faɗa tana miƙewa a zabure, “Na shiga uku meyeh wannan ɗin”
Ƴar dariya Ƴar Iya ta sake tare da faɗin “Aiki na kawo miki, kizo ki ƙarasa dafa mana muci daɗi”
Bayan ta Iya ta bi suka fita, a dai-dai wurin tukunyar ta tsaya tare da nuna mata “Ki juye ki bani na mayar musu”
“Toh” iya ta faɗa tana juyewa cikin wata tukunyar.

Bayan ta juye Ƴar Iya ta ɗauki tukunyar tare da wucewa gidan Inna Zaliha, tana shiga kamar dai ɗazu haka ta lallaɓa ta ajiye tukunyar. Ta juya zata fice murfin tukunyar ya karkace tare da bata sautin ƙarr...ƙurrr.

Da gudu Inna Zaliha ta fito daga cikin bukkar ta don ganin ko an maido mata da dahuwar ta ne. Bata ga kowa ba sai wulgawar mutum, hakan yasa ta ƙaraso da gudu tana buɗe tukunyar sai dai ga mamakin ta babu komai a ciki.
Ihu ta tsala tana faɗin “Na shiga uku ni Zaliha ƴar dahuwar tawa aka sace min!”

Ta share mintuna tana kukan ganin dai babu sarki sai Ubangiji yasa ta janyo tukunyar ta wulla ta wurin wanke-wanke.

*ƳAR IYA POV*

Wankan ta tayi tare da sheƙa kwalliya abun ta, atamfar ta ɗinkin riga da zani ta sanya tare da wani yanƙwanannen mayafin ta irin na ƴan ƙauye ta saka. Bayan tayi wa Iya sallama kai tsaye ta wuce gidan su A'i.

Matsayin ta na Aminiyar amarya yasa tana shiga suka wuce dandali coz dama ita suke jira ta iso.

Wasanni iri-iri aka yi a dandali ciki kuwa har da wani wasa da ya ƙayatar. Amarya da angon na zaune a kan benci ne dama tare da ƙawayen su dake kewaye da su.

Ƴar Iya da kanta ta iso gaban su ɗauke da faranti a hannun ta, haka shima Sama'ila abokin Basiru shima da nasa.

Cikin farantin Ƴar Iya jar hoda ce, turare ɗan feshi sai kuma hula, ledar dake hannun ta kuma tsire ne ciki. Farantin Sama'ila kuma turare ne ɗan feshi da kuma kwalin kayan dake jikin amarya A'i sai kuma leda dake hannun shi.

Ƴar Iya a gaban ango ta tsugunna shi kuma Sama'ila gaban amarya. Sai da aka tabbatar kowa ya shirya tukun aka fara.

Ƴar Iya tace: yanzu ango zai nuna mana yadda zai tafiyar da matar sa, zamu ga ko zai iya kula da ita ko a'a”. Sauran ƴan mata da samar suka saka shewa.

Basiru ne ya ɗauki hodar dake kan farantin Ƴar Iya, ya buɗe tare da zazzaga hodar jikin soson hoda.

Bai tsaya ɓata lokaci ba ya kamo fuskar A'i tare da fara shafa mata hodar. Nan fili ya kacame da ihun ƴan mata da samari, kowa sai dariya yake don wasan ya burge su.

Sai da ya gama shafa mata hodar ya janyo kwali ya ɗaura mata tare da ɗaukar turaren yana feshe ta da shi. Bayan nan Sama'ila ma yayi gyaran murya yace “Yanzu zagayen na ango ne, Saboda haka zamu so muga yadda amarya zata shirya shi.

A hankali A'i ta jawo hula tare da sanya masa ita daga nan ta fara feshe shi da turaren. Nan da nan ƙamshi ya cike ko ina.

Bayan an yi shiru kuma aka juye tsiren dake cikin leda bisa farantin. Ango ya bawa amarya a baki haka amarya ma ta bawa ango. Daga nan aka watse kowa ya wuce gida abun sa.
Rana bata ƙarya in ji malam bahaushe yace sai dai uwar ɗiya taji kunya. Kamar haka ne yau Lahadi aka ɗaura auren A'i da mijin ta Basiru mai gyaɗa.

Murna da farin ciki sosai su Ƴar Iya suke musamman yadda suka yi haske abun su saboda gyaran da Halima ke musu.


A daren ranar ne kuma aka miƙa A'i gidan mijinta. Ginin jar ƙasa ce wanda aka laikaye shi da jar ƙasar, ɗakuna biyu gareta sai kuma madafar abinci sai bayi.
Ko ina zancen A'i ake yi ai yarinya tayi goshi, yarinya tayi goshi. Bayan an kai amarya Ƴar Iya ta dawo gida tare da adana kuɗaɗen ta da ta samu.

Washegari da sassafe Ƴar Iya ta daka kayan sana'ar ta ta fita talla, sai da ta sayar da shi tas sannan ta wuce gidan A'i. A can taci abincin rana da aka aiko daga gidan su Basiru sannan ta wuce zuwa gidan Iyar ta.


*ALEE POV*

Mom ba ƙaramin mamaki tayi ba jin batun su Pretty. Ganin zama bai kama ta ba yasa ta fice don dubo yaron nata.

Kwance yake bisa faffaɗan gadonshi dake laikaye da white bedsheet, idanuwan shi lumshe yayin da fuskar shi ke kallon sama. Zuciyar shi ke mishi ɗaci da zafi.
“Why this girl?, Me yasa suke son shiga rayuwar shi ne kam?”

Ganin babu mai bashi amsar yasa shi miƙewa tare da nufar Toilet ya watsa ruwa. Ƙarar ruwan da Mom taji yasa ta fahimci yana Toilet me but duk da haka da buƙatar ta jira taga a wani hali yake.

Ganin shiru bai fito ba ne yasa Mom sauƙa ƙasa ta jira shi.

Fuskar shi a ɗaure ya sauƙo, ganin babu kowa yasa ya fice tare da nufar motar shi, Joseph da ya zo hannu kawai Hamma Zaki ya ɗaga masa alamun bai buƙatar tafiya da shi, Wani pack dake kusa da su yaje ko zuciyar shi zata daina ƙuna da kuma zafi.

Sai around 11:00pm ya dawo, lokacin Daddy ma ya dawo. Mom da ta sanar da Daddy abun da ke faruwa yasa yake jiran dawowar Hamma Zakin.

Daddy ne ya miƙe tare da tunkaro Hamma Zaki dake shigowa, cike da sakin fuska ya iso dai-dai Hamma Zakin yana hugging nashi. Duk irin yadda yake ji sai yaji zuciyar shi tayi wasai.
“Good Evening Dad”
“Evening sweetheart, Ina ta jiran dawowar ka” Daddy ya faɗa yana sakin murmushi.
Shima Hamma Zakin murmushi yayi yana faɗin “Thatz my Dad, I'm back”
Ya faɗa tare da zaunar da Daddy a kan kujera sannan ya zauna kusa da shi.

Shafo sajen sa Daddy yayi yana murmushi kafin yace
“Sweetheart me yake damun ka?, It seems like you are not happy today” marairaice face Daddy yayi yace “Tell your Dad what's wrong with u?”
Cike da kulawa Hamma Zaki yace “Nothing Daddy, I'm ok”

Kallon ka raina min wayo Daddy yayi masa sannan yace
“Ok what about that young lady?, I mean wacce tazo ɗazu”
Ɓata fuska Hamma Zaki yayi yana yamutsa ta “Oh Dad, please don't like her at all”
Murmushi Mai ɗauke da ma'anoni daddy yayi sannan yace
“Alright tunda baka so, brothern ka ya kira ka and baka picking call ɗin, ya ce a faɗa maka he's coming back tare da Waheeda da kuma baby Fauzan.” daga haka Daddy ya fara shirin miƙewa, murmushi Hamma Zaki yayi yace “Ill call him in na shiga, good night sweetheart”

Waving hand ✋ Daddy yayi tare da wucewa.
Shima Hamma Zaki ya wuce bedroom ɗin shi.

Nasan readers sun Matsu su san wacece pretty!.

*Wacece pretty?*

Alhaji Saminu Hambali shine cikakken sunan mahaifin ta, matar shi ɗaya rak wato Hajiya Salima. Sunyi aure ne irin na soyayya sai dai sun shafe shekaru basu samu haihuwa ba sai akan Nabila (Pretty), Hajiya Salima (Mami) mace ce mai shegen biye-biyen malaman tsibbu da kuma bokaye, ko kaɗan bata ƙaunar wata ta shigo gidan mijinta da sunan mata, hakan yasa ta mallake Alhaji Saminu (Dad).
Dad a ɗaya ɓangaren Hamshaƙin ɗan siyasa ne wanda a yanzu haka yake riƙe da matsayin ministan walwala.

Pretty ta tashi cikin gata da sangarci, hakan yasa ta tashi da buɗaɗen ido tunda ita kanta mahaifiyar Tata bata samu isasshiyar tarbiyya ba talkless of ta bawa wani. Sam ko kaɗan Pretty Bata shakkar kowa, ko uban waye yayi mata bata ƙyale shi.

Bayan ta kammala secondary school ta fara karatun ta a Nile University dake birnin tarayya, a nan tarbiyyar ta ta ƙara taɓarɓarewa don kuwa maza ne ƙawayen ta, biye-biyen hotels da clubs baa magana, a nan suka haɗu da Ishy wacce ita ma mahaifin ta babu laifi yana da kuɗi. Sanadiyyar Ishy da ta kasance ƙawar Fauzy. Fauzy ma ta gagari iyayen ta duk da irin gatar da suke mata amma haka ta zaɓi rayuwar banzanci ta bar su, takan shafe watanni ba tare da ta ziyarce su ba. Sai kuma Sumy wacce itace baya bata a harƙar shaiɗanci, iyayen ta ba wasu masu hali bane compared to Iyayen sauran, sanadiyar Fauzy ta fara harƙar lesbian hakan kuma na da nasaba da yadda Fauzyn ke kashe mata kuɗi.

Waɗannan ƙawaye ka nemi tsarin Allah daga sheɗan sannan ka nema kan su, don sun san salon bariki da iskanci, Pretty kuwa in ta saka rai akan abu to babu makawa sai ta samu, hakan yasa bata damu ba ko da Hamma Zaki ya nuna baya yin ta, coz ta san da Mamin ta tasan batun shikenan zai shigo hannu.

Wannan kenan!

Kun jini shiru masoya Littafin Ƴar Iya?, To na dawo da zafi zafi na fatan ba zaku bari na huce ba😒😂 ah toh, in na huce sai kun neme ni.
Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, yanzu ne Littafin Ƴar Iya zai fara daɗi, wai hausawa suka ce wasa farin girki😄 to haka a nan ma fah, ku dai kuci gaba da bibiyar Littafin, Ga Ƴar Iya, ga Hamma Zaki, ga Pretty kuma? To ko yaya haɗuwar su duka zata kasance?. Ku ci gaba da bibiyar Alƙalamin DIAMOND LADY💎, Ina matuƙar ƙaunar ku.

Yanayin comments ɗinku yanayin tsayin page da yawan post.
Love U all.

[6/12, 11:40 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️:



🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*











SHAFI NA “““45&46”””

Tunda Pretty suka isa Abuja, ko dropping ƙawayen nata bata yi ba su ma basu buƙaci hakan ba coz da gani tana cikin tsantsar damuwa, ta kuma yi alwashin auren Hamma Zaki ko ta halin yaya.

Mamin ta na zaune a parlourn ta ƙaraso janye da trolleyn ta, da gudu ta saki trolleyn tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login