Showing 12001 words to 15000 words out of 135404 words
Ƙawa ta, kawai zanyi kewar ki ne kuma kinga da kin tafi la'alla Inna ta tace aure zata min tunda kinga su Dijen Iyayye duk an bada su”
“Kar ki wani damu, ba daɗewa zanyi ba musamman naji garin babu daɗi dawowa zanyi”
Daga haka A'i ta wuce gida saboda yadda zuciyar ta ke mata.
Shirye-shiryen tafiya kuwa tuni an gama ranar Lahadi za'a wuce da ita zuwa makarantar kwana dake Sakwa.
Ranar Asabat Baffi yace zasu je suyi wa Baban ta sallama, ba don ta so ba sai kawai don Baffi yace in Bata je ba to za'a fasa tafiyar.
Tunda suka isa gidan Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya ta ƙasan Ido yayin da zuciyar ta tayi wani irin bugawa. Ba tare da ta bari sun fahimci komai ba ta kawo ruwa a kofin silver bayan sun sha Baffi ya buƙaci tayi wa Baban Ƴar Iya magana, a nan Baffi ya sanar da shi zasu wuce.
Cike da farin ciki ya amince haka Inna Zaliha har da bata kyautar kuɗi wai ta sha ruwa a hanya. Daga haka suka fito basu tsaya ko ina ba sai gida, Nan aka ƙara haɗa kayan Ƴar Iya wanda mafi yawanci sabi ne aka yi mata sai kuma ƙanzo da mai da yaji da Iya ta haɗo mata guzurin shi.
Cikin gari tuni anji labarin tafiyar Ƴar Iya birni, kowa farin ciki kamar anyi mishi albashir da gidan Aljanna, wasu har kyautar abubuwa suke kawowa saboda zasu rabu da Annobar su, maƙwabta da aka ɓata da su suma sun shigo suna taya Ƴar Iya murna.
Da daddare Ƴar Iya ta niƙi hanya sai gidan Arɗo. Ta samu tarba ta musamman saboda duk su ma murnar tafiyar ta suke, Innani ma ba'a bar ta a baya ba har da kyautar kuɗaɗe ga Ƴar Iya, Saratu Matar Arɗo ma ta bata ɗan kunne da jan baki.
Arɗo kuwa kuɗi ya bata tare da sanar da ita goben in zata tafi ta biyo zai sa a gasa mata zabi, daga nan ta wuce ba tare da tayi wa kowa godiya ba.
TOH ƳAR IYA FANS MASOYIYAR KU FA ZA'A TAFI BIRNI!
MEH KUKE TUNANIN ZAI FARU?, ƳAR IYA ZATA SAUYA KAMAR YADDA SUKE FATA?
YA KUKE TUNANIN RAYUWAR TA A MAKARANTAR KWANA?
IN KUNYI COMMENTS ZAN ƘARA MUKU LUNCH, KUMA ZAKU SAMU DINNER.
COMMENT& SHARE FISABILILLAH
[4/29, 7:48 AM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘13&14’’’’’
*ALEE POV*
Bayan yayi lunch nashi ne ya samu ya ɗan kwanta saboda irin gajiyar da yake ji.
Bai tashi ba sai around 4:00pm, ganin time na Asr prayer na shirin wucewa yasa ya yi saurin nufar Toilet.
A waje na jira shi ina ƙarema wani frame da ke ɗakin wanda ya tafi da imani na. Ƙarar buɗe ƙofar Toilet da naji yasa na ja gefe ina lafewa kada Yaya Zaki ya gan Ni.
Cikin nutsuwa ya gabatar da sallar shi. Bayan ya idar ma ya jika bisa praying mat ɗin kafin ya miƙe tsaye yana nufar parlourn. Ruwa masu sanyi ya ɗauko a fridge ɗin da ke dining area daga nan ya dawo.
Yana dawowa ya sanya bathrobe sannan ya nufi toilet. Sai da ya shafe 40minutes wannan karan tukun ya fito hannun shi riƙe da ƙaramin white towel da yake ta famar goge sumar shi da shi.
Bayan ya shafa mayukan sa ya buɗe closet tare da ciro wasu kaya.
Few minutes ya kammala sanya White Armani T-SHIRT nashi mai ɗauke da rubutu ta gaban _STRUGGLE_ sai kuma wani Navy blue jeans da ya saka wanda yayi matuƙar amsar jikin shi, tuni kyakkyawar surar shi ta ƙara bayyana yayin da ya fara feshi jikin shi da wasu turaruka nan da nan ƙamshi ya cike ɗakin kamar kogin turare. Wani expensive wristwatch ɗin shi ƙirar _Magsonic Sonnerie_ ya sanya tare da ɗauko phones ɗin shi yana ficewa daga bedroom ɗin.
Cikin takun shi irin na cikakkun maza masu izza da kuma jarumta ya fito, suna ganin fitowar shi suka matso kusa da shi suna sara mishi. Bai bi ta kan su ba ya fito yana zaga gidan.
Yayi tafiya kaɗan can ya iso garden ɗin dake ta ɗan gefen apartment ɗin nashi. Wuri ne wanda yaji shuke-shuke masu ɗaukar ido kama daga flowers izuwa green grass carpet da ya malale garden ɗin. Dai-dai wani ɗan cool down dake wurin ya nufa tare da zama ɗauke da ambaton Allah a bakin shi.
Phone nashi da yayi ringing har ya kusa katsewa yayi picking da sauri ganin sunan *DADDY* make kan screen ɗin wayar.
A kunnen shi ya kara ta tare da sakin nauyayyiyar ajiyar zuciya at the same time fuskar shi ta sake kamar ba shi ba.
“Assalamu Alaikum sweet daddy”
Murmushi Mai sauti Daddy ya sake jin Muryar gudan jinin sa kuma abun alfaharin shi Shareef.
“Son, kana lafiya”
“Lafiya Lou Daddy nake, ya su Mom da su granny?”
“Lafiya ƙalau suke son, ɗazu muna magana da Mom ɗin ka take sanar da Ni ka dawo irin shigowa haka babu sallama”
Murmushi Hamma Zaki yayi yana ƙara sauƙe Muryar shi wacce ke fita kamar an saka shi dole.
“Ayya Daddy I just wanna make u surprise, gobe zan ƙaraso In Sha Allah”
Daddy yace
“Toh son sai ka dawo, i love u”
“I love U too sweetheart”
Daga haka kiran ya katse.
Wayar tashi ya ajiye tare da kwantar da kanshi jikin kujerar da yake kai yayin da ya lumshe idanuwan shi, iskar da ke kaɗawa ne ke kaɗa sumar shi ta baya, hakan ba ƙaramin ƙara mishi kyau yayi ba.
Ya jima a zaune kafin ya miƙe yana komawa apartment ɗin shi.
★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Tun kafin Asubahi ta tashi tana zagaya gida zuciyar ta fal murna yau zata koma birni. Bayan Baffi ya dawo daga masallaci ya je har ƙofar gidan Malam Salihu ya sanar da ɗan sa Shayibu wanda shi kaɗai ne ya mallaki babur cikin ƙauyen.
Misalin ƙarfe 5:50am Ƴar Iya ta nufi gidan Arɗo ai kuwa zabin da yayi mata alƙawari an riga an gasa mata, tana amsa ta wuce.
A tare da Baffi suka hau mashin ɗin, bayan ta hau Baffi ya hau sannan aka haɗa musu kayan a gaban Shayibu, Iya kuwa kuka take kamar ranta zai fita saboda za'a rabata da shalelen ta. Da ƙyar ta koma bayan tada babur ɗin da Shayibu yayi ɗiiiiiiiiiii....
(Ni DIAMOND LADY nace safe trip Ƴar Iya Allah ya bada abun da aka je nema....Team Ƴar Iya ma duk sun yi mata fatan alkhairi, su Ummu Basmat, Maman Usman, Ayeesh, Ameran Mama, Hindatu Hassan, Faty Shareef, har da su Maman Hakeem da sauran Fans na ƳAR IYA READER'S HUB duk suka bi bayan babur ɗin suna murna yau zasu birni😀).
Bayan sun isa dai-dai bakin hanya wata mota irin Tanker ɗin nan tazo wucewa...saura kaɗan Ƴar Iya ta hantsilar da mashin ɗin don wani tsalle ta buga kamar biri sai da Baffi ya riƙe ƙafafuwan ta.
“Ƙundun Jakar uban can.... Baffi wallahi ƙarfe me ciki ke tafiya kaga hala ya kusa haihuwa Aradu Baffi ka sauƙar da Ni na bi shi”
Haka tayi ta musu ƙauyanci tun Shayibu na ɗan jin haushi har ya fara dariya.
(Ni dai ban ga laifin ta ba saboda wannan ita ce first tafiyar ta).
Tafiya suka yi mai tsayi a babur ɗin yayin da Ƴar Iya ke zuba ƙauyanci son ranta.
Ganin yadda suke wuce bishiyoyi yasa ta calla ihun murna tana faɗin.
“Baffi Aradu suma tafiya suke yi....kai jakar uba Baffi su ma raka Ni suke yi....woooohuhuuuu Ni Jikar Iya ina da masoya”
Haka tayi ta zubar ta har suka iso Azare. Wani babban gida ta gani upstairs can kuma ta hango kamar mutum daga gidan Ai anan ne kallo ya koma sama don Ƴar Iya sabuwar rigima ta ɓarke da shi.
“Baffi ka dakatar da shi don Allah Ina son hawa kan wancan abun...wayyoh Baffi Allah zan dirƙa in Baku tsaya ba”
Baffi da ya rasa me yake masa daɗi da wannan hali na Jikar tasa ya fara lallashin ta .
“Yi haƙuri shalelen Iyan ta, ke da zaki zauna a nan kuma ai ba sai kin hau yanzu ba, kullum in kina so kawai zuwa zaki yi ki hau”
Da haka ta haƙura suka ci gaba da tafiya.
Suna isowa cikin garin Sakwa suka ce karo da wani mai amalanke zai fita, tsayar da mashin ɗin Baffi yayi ya fara mishi magana cikin harshen fulatanci
“Don Allah ina ne hanyar makarantar kwana?”
Kwatanta wa Shayibu yayi saboda haka suka miƙe sai Gov'nt Girls College Sakwa.
Tun daga bakin gate Ƴar Iya ta fara sakin murmushi, gani yara Sa'annin ta da check na pink yard wasu na tuƙa ruwa wasu kuma sun tsugunna gaban wata mai Blue Check hakan ya bata dariya tace.
“Kutumar Uba....Aradu akwai kallo”
Baffi ne yaja hannun ta zuwa wajen wasu matasa da suke zaune kan wasu kujeru bakin bishiya.
Gaishe su Baffi yayi Ƴar Iya kuwa ko a jikin ta. Bayan Baffi ya faɗa musu cewa Ƴar shi ya kawo makarantar suka nuna mishi hanyar ofishin Principal.
Sun miƙe zasu wuce ne wani Ƙatoton malami mai ƙaton ciki, gashi gunt, baƙi ƙirin yake ga kuma kanshi ɗan ƙarami kamar an san mishi. Ai kuwa da gudu Ƴar Iya ta fizge hannun ta tana nufar inda yake. Sai da tazo dai-dai da shi ta ƙara rage tsayi tana mishi kallon ƙwaƙwaf... Bai ma lura da ita ba sai da yaji ta kwashe da dariya
“Hhh.....hhhhhhh..hhhhhhh wayyoh ciki na, A'i na baro ki da nace kizo kiga mai kama da Bijimin Baffi hhhhhhh....Kutumar Uba Aradu banbanci shi da Bijimin Baffi ƙaho ne sai jela”
Haka ta ƙara kashewa da wata mahaukaciyar dariyar. A lokacin ne malamin yayi noticing nata ya kuma ji abun da ta faɗa, kunya da ɓacin rai suka sauƙa mishi lokaci ɗaya. Gashi yarinyar da yake so Sahiba Bashir sun zo wucewa ita da abokan ta kuma ya tabbatar taji.
Tuni yayi kan Ƴar Iya yana ayyana ko ƴar uban waye yau sai taci uban ta.
(Nace lallai baka san Ƴar Iya ba ne)
Wata irin damƙa yayi mata kafin ta farga ai kuwa tuni tayi wani juyi tare da murɗe hannun da ya janyo ta da shi. Abun ka da ƙato dama muscles sun mishi yawa tuni jikin yayi tsami gashi ta ƙi sakin shi.
Mamaki ne ya kama shi ganin iri ƙarfi da yarinyar ke da shi gashi ya kasa ƙwacewa. Yanke shawarar ihu yayi ko za'a samu masu taimaka mishi.
“Wayyo Allah jama'a ku kawo ɗauki, innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir....”
Bai kai ga ƙarasa ihun ba Ƴar Iya ta buge bakin shi nan da nan jini ya fara zubowa.
Malaman da ke gindin bishiyar nan ne suka ji ihun ai kuwa suka taho don ganin MEH ya faru. Arba da yarinya ƙarama na riƙe da Mr. Small duk iri girman shi yasa suka shiga ɗimuwa.
Faɗa wasu suka fara mata kan ta sake shi ammah shiru....wanda yayi dai-dai da fitowar Baffi da office ɗin Principal nasu don ya ƙira ta ayi mata interview.
Ɗauke da mamaki a fuskar shi ya daka mata tsawa tuni tayi wulli da hannun Mr. Small Wanda yayi dai-dai da faɗuwar shi ƙasa.
Tana sake shi ta nufi wurin Baffi su kuma malaman suka je don bawa ɗan uwan su agaji.
Bayan sun shiga Principal ya fara mata interview ammah sai ya fahimci bata san komai ba....ABC common Bata sani ba tunawa da bayanin Baban ta yasa ya yanke shawarar kai ta aji ɗaya don kuwa ya san halin yarinyar tunda Baban nata yayi masa bayani.
Babu ɓata lokaci Principal ya ƙira wata Senior tare da nuna mata Ƴar Iya yace ta tafi da ita hostel a Bata room da gado. Ba musu ta miƙawa Ƴar Iya hannu a kan su tafi. Ganin Baffi zai tafi yasa ta arta da gudu wurin babur ɗin.
“Baffi ina zaka je?”
“Zan tafi manah, ba kince kina son birni ba?, toh ki zauna gobe ma zan zo kinji”
Kai ta gyaɗa kamar ta fahimta tare da komawa wurin kayan ta.
Ganin babu kayan ta babu alama yasa ta kwarma ihu tare da sakin ashar.
“Kutumar Buhun uban jakin nan, uban waye ya sace min kaya na?”
Rasa mai bata amsa aka yi da ƙyar Principal yace
“An kai miki shi makwancin ki”
Senior ɗin da ta kai kayan ne ta dawo saboda haka ta lallaɓa ta suka wuce room ɗin da aka bata.
_YAR IYA'S FIRST DAY AT SCHOOL_
Ganin makarantar cike da bishiyoyi yasa ta ɗan ji sauƙi a ranta shiyasa ta fito tana kewaya ko ina, kun san Sunday babu karatu mostly students sukan wanke uniform nasu ne suyi wanka.
Ƴar Iya na cikin tafiya zata hau bishiyar mangwaro da ke ɗan nesa da hostel ɗin nasu taji an dakatar da ita.
“Keeee! dan Bura Ubanki zo nan, uban me kike yi a wajen?” Senior ɗin ta faɗa cike da bada umarni da taƙama.
Cike da ɗumbin mamaki Ƴar Iya ta waiwayo ta kalle ta, cikin ranta tana ayyana wace tsagerar ce ta tare ta yau zata san ta zage ta. Juyawa yayi ta ɗale bishiyar abun ta, yadda take tsalle kuwa kai kace biri ne.
Senior da ta ƙulu da rashin kunyar da sabuwar ɗalibar ta ƙunsa mata wuri ta nema ta zauna tana jiran sauƙowar ta tare da tunani iri-iri akan uƙubar da zata bugawa yarinyar.
Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake.......
IN ANYI COMMENTS ZAN ƘARA MUKU UPDATE ZUWA JIMAWA
INA GODIYA GARE KU MASOYAN LITTAFIN ƳAR IYA, MASU COMMENTS ƊIN NAN DA MASU TAYA NI INA MATUƘAR ALFAHARI DA KU, ALLAH YA BAR ƘAUNA. much Love my esteem fans.
DIAMOND LADY 💎 CE!
SHARE FISABILILLAH.
[4/29, 2:48 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘15&16’’’’’
Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake yayin da ta kife a ƙasa kamar kwaɗo.
Ba komai bane ya faɗo bayan senior sai Ƴar Iya wacce sai da ta saita bayan nata ta diro a kai.
Ganin tayi wa Senior ɗin illa yasa ta cika bujen ta da iska, bata tsaya ko ina ba sai ɗakin da aka bata. Lokacin kuwa har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar. Bata kula kowa ba ganin babu wanda ya kula ta, in fact kowa ma hidimar gaban sa yake sai dai abun da ta fahimta shine fita waje suke yi gabaɗayan su.
Wata senior da taji ana kira da Ajaram taso saitin Ƴar Iya tace
“Ke ba zaki je dining bane ko baki ga lokacin cin abinci yayi ba”
Da yake babu kowa a room ɗin yasa ta fahimci da ita take saboda haka ta zubo mata ƙwala-ƙwalan idanuwan ta alamun bata fahimta ba.
Da yake Ajiram na da sauƙin kai kuma bata cin zalin yara yasa ta ƙara maimaita mata. Ƴar Iya tace
“Meye kuma Dayin?, Ba dai wanda ake lalle ba, to ai ni bana yi Aradu ko a ƙauyen mu”
Mamaki ne ya cika Ajiram lokaci guda kuma ta fahimci yarinyar ƴar ƙauye ce saboda haka ta saki murmushi tace.
“Dining gurin da ake bamu abinci ne a nan, ki tashi muje kada ya ƙare baki samu ba”
Huhuhu! Su Ƴar Iya manya, wani zungureren mamaki ne ya maƙale ta, yau itace wani ke lallaɓa tazo taci abinci, ita da bata da aiki sai ƙwacen na wasu taci shine ake nunawa tausayi. Lokaci ɗaya taji tana ƙaunar matar.
Da niyyar ta shine ta ɗauko zabin ta na wurin Arɗo taci kawai sai taji bari ta ɗauko su ci da wannan matar. A hankali ta ɓaro buhun kayan ta ta janyo ledar zabin. Duk abun da take Ajiram na jiran ta don bata tafi ba, tunanin ta ko dai zata ɗauko wani abun ne.
Ledar ta ɗauko tare da buɗe ta, janyo zabuwa ɗaya tayi ta miƙawa Ajiram, mamaki ne ya cika ta lokaci ɗaya ganin gasasshiyar kaza....
“Gashi muci wannan sai muje Dayin ɗin”
Murmushi Ajiram tayi tana tsintar kanta da zama kusan Ƴar Iya, tare suka cinye ta farkon ita dai ta ƙoshi ammah mutuniyar ta saba saboda haka ta janyo ɗayar.
Tasss ta cinye ɗayar, ita kuwa Ajiram mamaki duk ya cika ta. Bayan ta cinye tace wa Ajiram ɗin ta raka ta Dayin suje suci wancan, a lokacin kuwa har ya kusa ƙarewa saboda haka aka ɗan zuba musu kaɗan kaɗan.
Bata wani damu ba tacinye sannan ta fara waigen inda zata ga wannan baiwar Allah ta ɗazu, tana hango ta ta wuce wurin ta guduuuuuu....
Tare suka dawo da yake room ɗaya suke Ajiram na jan Ƴar Iya da hira ita kuwa ta zage sai bata labari take.
Lokacin kwanciya yayi Ajiram ta taya Mutuniyar hawa nata gadon sannan tayi musu addu'a tare da shafawa Ƴar Iya a jikin ta. Nan da nan bacci ya kwashe su.
Washegari da safe da yake ba kullum ake wanka ba a school ɗin ɗalibai suka fara shiryawa cikin uniform ɗin su, Ajiram ita ta taya Ƴar Iya saka nata tana mitar kayan