Showing 111001 words to 114000 words out of 135404 words
bacci. Ba komai yake ba sai tunanin irin zaman da zai yi da amaryar da ko sunanta bai sani ba, all he knows is ɗiyar abokin Daddy ne. Whatever the case might be in dai irin halin pretty gare ta to babu shakka zai koya musu zama don ba zasu tayar masa da hankali ba.
Duk yadda suka so ya biyo su su wuce abun ya faskara sanin hali irin nasa sai suka haƙura suka barshi. Amman sun tabbatar masa zasu yi masa Rakiya zuwa ɗakin amarya.
************
Tun kafin a ɗaura auren suka riga suka fara kuka musamman Khairy da ba ta da wata madogara sai Allah. Ko da gida ya ɗauki labarin aure ya ɗauru sai guɗa, tuni amaren suka ƙara fashewa da wani irin kuka, tun Aunty Baraka na lallashi har abun ya ishe ta ta fara musu faɗa, da ƙyar aka samu suka tsaya da kukan.
Da misalin ƙarfe 3:00 na rana Aunty Baraka ta saka amaren gaba don suyi wanka, da suka fito ta basu kayayyakin da Granny ta yi musu, basuyi kwalliya ba suka shirya cikin kayan tare da ɗaura alkyabba a kai. Part ɗin Granny da ke ɗauke da ita kanta Granny, Daddy, Uncle Suraj, uncle Bello, Mom, Nenne da Kuma Mommah aka kai su. A kan lallausan carpet ɗin suka yada zango kansu ƙasa sai sharar ƙwalla suke.
Granny ce ta buɗe taron da addu'a daga nan tayi musu ƴar nasiha game da zaman aure, hanyoyin da zasu bi don yin ingantacciyar rayuwa a gidajen aurensu a gurguje, daga nan ta yi addu'ar Allah ya basu zaman lafiya. Su Mom suka amsa da Ameen.
Nan Daddy ya ɗaura nasa nasihar a kai tare ɗan jan hankaulansu da kuma nusar da su ga haƙuri cikin zaman auren nasu, uncle Suraj ma yayi haka Uncle Bello. Iyaye matan da su ma kukan suke na rabuwa da ƴaƴayen nasu basu ce komai ba. Nan daddy ya rufe da addu'a tare da fatan zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba ga ƴaƴan nasa.
Daga nan ya umarce su da su fito iya su don shi da kan shi zai kai su, ƴan rakiya sa je daga baya. Yesmeen aka fara kaiwa, ko da suka je tare da daddy suka fita, sai da ya ƙara jan hankalinta suka fito suka barta tana kukan rabuwa da iyaye da ƴan uwanta da take matuƙar ji da su.
Daga nan aka wuce da Ayrah wacce itama daddy ya ƙara mata nasiha Sannan suka baro ta ita ma dai tana kukan rabuwar. Fauzah ce ta gaba ita ma da Daddy ya ajiye ta sai da yayi mata nasiha sosai kafin suka taho.
Khairy ce ƙarshe saboda haka zuciyarta bugawa kawai take yi don bata san irin mijin da zata tarar ba, mai tausayi ne ko mugu Allah kaɗai ya sani.
GRA aka nufa da ita direct, dai-dai wani babban gida Daddy yayi horn, ko da aka buɗe ya shiga tare da parking motar sannan ya umarce ta da ta fito. Ba musu ta fito kanta ƙasa ba tare da ta duba ko ya gidan yake ba. Daddy ne ke gaba ita kuma na biye da shi har suka isa dai-dai wani madaidaicin apartment, da bismillah ta shiga tare da fara sanya ƙafarta ta dama yayin da wani tsoro da fargaba suka lulluɓe ta.
A haɗaɗɗen parlourn da aka kashewa Naira Daddy ya tsaya, kamar dai yadda yayiwa sauran ƴan uwanta itama yayi mata nasiha mai ratsa jiki, tare da ƙar jan hankalinta sosai akan tayi wa mijinta biyayya kums ta ƙara da haƙuri. Daga nan ya juya. Nan ta ƙara sakin wani kuka mai tsuma zuciya. Mintuna ashirin da zuwants ƴan uwa da abokan arziki suka fara zuwa don ganin gida.
Cikin waɗanda suka zo mafi akasarinsu mutanen Gallara ne, har da su saratu amaryar Arɗo da su A'i Aminiya mai hanjin lagwani. Isowarsu ne suka ja ta zuwa ɗaya daga cikin bedrooms da ke ɗakin. Basu wani daɗe ba suka koma can Naira family House.
Ita kaɗai suka bari hakan ne ya bata damar janye alkyabbar tana ƙarewa bedroom ɗin kallo, Masha Allah ta furta tana yaba tsaruwar ɗakin da kuma dukiyar da aka narka masa. Da yake bata ja door na bedroom ɗin hakan zai bata damar jiyo wa idan wasu baƙin sun zo. Komawa tayi ta zauna tare da fashewa da wani kukan da ta tuna da Granny da Kuma sisters ɗinta, yanzu shikenan ta bar Granny sai dai kawai kai ziyara?, Allah sarki duniya.
Tana cikin tunanin irin rayuwar da zata shimfiɗa a gidan auren nata ne ta jiyo motsi kamar an shigo parlourn, zamanta ta ƙars gyarawa tare da gyara zaman alkyabbar da ke jikinta.
Wata matashiyar budurwa ce fara kyakkyawa da ita ta shigo, Masha Allah ta furta ganin irin dream parlour ɗinta da Kuma kuɗin da ya ci. Sai da ta gama kalle-kallenta kafin ta sa kanta ga bedroom na farko. Cikin Sa'a kuwa nan ɗin ne amaryar take.
Sallama tayi Khairy ta amsa ƙasa-ƙasa. Ƙarasowa budurwar tayi tare da zama a gefen Khairyn, cikin ranta kuma mamakin ganin amaryar ita kaɗai take yi. Ɗan murmushi tayi tace “Amarya sannun ki da zuwa, suna na Amrah, gidanmu na opposite da nan, Ammy na tace na shigo na ganki saboda Gen. Abokin Abie na ne.
Ɗan sanyi Khairy ta ji jin ta samu wata kawar kusa da ita, ajiyar zuciya ta sauƙe tana faɗin “Na gode, Ni kuma suna na khairy” “Nice name” Amrah ta furta. Cikin ƙanƙanin lokaci suka saba da juna har Amrah na faɗa mata ita ma next month ne bikinta.
Kiraye-kirayen sallar maghriba yasa Dukansu suka yi alwala suka yi sallar, nan Amrah tace “Bari naje gida na ɗauko make-up kit na sai na dawo ” har Khairy zata ce a'a sai kuma ta fasa da ta tuna da irin yadda kowa ke musu nasiha akan riƙe Sirrin gidan aure, ko ba komai ba zata bari wani ya fahimci zaman da take yi ba ko da kuma sisters ɗinta ne.
Daƙiƙu kaɗan sai ga Amrah ta dawo hannunta ɗauke da make-up kit ɗinta.
“Khairy in ƙawayenki ne kin san fa idan an rako ango ana yin wasu programs ɗin ko?”
Langwaɓar da kai gefe Khairy tayi cikin ranta tana faɗin “Wannan angon kam ba zuwa zai yi ba tunda ko sau ɗaya bai taɓa zuwa ya ganni ba tunda aka saka mana rana”.
“Kinyi shiru” Amrah ta dakatar da ita. Murmushin da ake cewa ka fi kuka ciwo tayi sannan ta ce “Ayyah kinsan friends ɗinah uku ne kuma sisters na ne and tare aka aurar da mu” ɗan zaro ido Amrah tayi tace “Ok, zan cike gurbinsu gare ki in sha Allah ”
Bata ɓata lokaci ba ta saka Khairy gaba tayi sabon wanka ta sauya kaya sannan ta tsaka mata kwalliya mai kyan gaske. Shiru shiru babu miji babu alamunsa hakan yasa ranta ya ɗan ƙara ɓaci, zuciyarta na ingiza ta akan cika alwashin da ta ɗaularwa kanta.
*************************
“Haba Dude, ai ba haka ake yi ba!, wani hanin fa ga Allah baiwa ce, baka san wace irin mata ce daddy ya zaɓar maka ba, baka tunanin saboda kyawawan halayenta Daddy ya haɗa auren ku? Gaskiya man ka tashi muje mu raka ka” Dr faruq ya faɗa yana mai dafa kafaɗarsa yayin da shi kuma yake zaune yana shaƙar sassanyar iskar da ke kaɗawa.
Captain Sulaiman ya ɗan haɗe rai yace “Ni na rasa gane. Captain wane irin mutum ne ma, kana gani ko wancan bikin yadda yake ta rawar ƙafa ka tuna?”.
Dariya Dr. Faruq yayi yace “Rabu da shi sai zaɓin daddy ne ake wa shan ƙamshi” Sai yanzu yaji babu daɗi, ko ba komai ya kamata ace ya karɓe t hannu bibbiyu ko da baya ƙaunarta, ita ɗin zaɓin iyayensa na ya kamata ta samu mutuntawa ko da kuwa kaɗan ne daga gare shi. Wani Gwauron numfashi ya saki cike da dakewa yace “Ni ku don Allah me yasa kuke son takura min, na faɗa muku ai zan je ko?”
“To ka tashi mu je mu raka ka, ka ga ko kazar amaryar ba'a saya ba” Dr. Faruq ya faɗa.
Sam shi ya manta ma da na kaiwa amarya wata kaza, sai da suka miƙe tukun ya miƙe kamar baya so.
A hankali ya bi bayansu zuwa parking space da ke garden ɗin, ganin yana nufar motarsa yasa Dr. Saurin faɗin “Man ka zo mu ajiye ka mana, ango guda da driving ”. Ya faɗa cike da tsokala. Bai ce musu komai ba ya nufi wurinsu, nan suka fice daga garden ɗin.
Tsayawa suka yi suka siya kaza da kuma Yoghurt sannan suka miƙi hanya zuwa gidan shi, horn suka yi nan da nan gate man ya buɗe gate ɗin, bayan sun daidaita parking Dr. Faruq da captain Sulaiman ne suka fara fita. Har suka fita yana zaune bashi da alamar fitowar, hakan yasa Dr. Faruq miƙawa Captain Leather ɗin shi kuma ya koma ba tare da ya ce da shi komai ba.
Hannunsa ya riƙo kawai ba musu Hamma Zaki ma ya miƙe tare da fitowa.
_To Hamma Zaki a gaida mana amaryar._
_Comment and Share FISABILILLAH_
[19/09, 8:50 a.m.] Famanté 💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““111&112”””
Cikin ransa ya furta “Bismillah” tare da shiga ƙatoton parlourn da yaji kayan ƙawa na more rayuwa yayin da wani dadddaɗan ƙamshi ke fita daga ciki. Lumshe idanunsa yayi tare da buɗe su, ganin babu kowa a parlourn yasa yayi hamdala cikin ransa amma kuma yana tunanin to ma a ina zai kwana ne?, wata zuciyar tace masa “Alee ka sallami waɗannan guys ɗin da sun tafi ka koma can gidan da ka saba da shi.” wannan shawarar a kanta ya daidaita, hakan yasa ya ɗan saki fuska yana faɗin “Men! Na gode sosai ku sami ku wuce gida kada matanku su neme ku”
Maganar ta matuƙar basu mamaki har suka ɗan samu Shakku a kansa, mutumin da yace bata zuwa kuma yanzu shi yake cewa su je. Yanayin da fuskarsu ya nuna na nuna rashin yadda yasa yace “Ku je mana, na gaji zan huta” idon ya ɗan kanne saboda har ga Allah shi so yake su bashi wuri ya samu shima ya wuce wurin da zai iya bacci ya huta.
Basu kai ga cewa komai ba suka jiyo takun takalma daga staircase ɗin, wata matashiyar budurwa fara ƴar kyakkyawa da ita. Idanuwansu ne duka ya koma ga kallon ta yayin da Hamma Zaki ya ɗan ƙara haɗe ransa, a ransa yana faɗin “Habibty na ta daban ce” ɗan yamutsa fuska yayi don duk tunaninsa ita ce amaryar, suma dai nasu ɓangaren haka suke tunani.
Ko da ta sauƙo sai ta nufo yadda suke tana ɗan murmushi, fuska sake ta ce “Haba ƙawayen ango, ya za'a yi ku riƙe ango har ya kai yanzu baku rako shi ba, gashi amarya har ta gaji da jira ta yi fushi.” ta ƙarasa tare da kwaɓe fuska. Ko kallon yadda take bai yi ba, ita kuwa sai da ta ƙare musu kallo tana tunanin waye ango cikin nasu cikin ranta kuma tana yaba kyau irin na wanda ke tsakiyarsu.
Ƴar dariya Captain yayi yace “Tuba muke amarya, yanzu dai mun kawo Miki shi ai” Hararar gefen ido Hamma Zaki ya aika mata jin yana son ya ba da su a wurin wannan so called amaryar. Wata irin dariya tayi kamar zata shiɗe yayin da Hamma Zaki ya cika fam wai an aura masa maras hankali. Lokaci ɗaya kuma tayi shiru tana maida hankalinta kwacakom gare su.
“Wai ku ƙawayen angon ma baku san wace ce amaryar ba?, kar ku ce min angon rowar ganinta ya yi muku?” “Oh” Hamma Zaki ya dafe kansa ɗan kuwa surutun yarinyar ya ishe shi gabaɗaya.
Captain ne yayi dariya da ya fahimci ba ita ce amaryar ba kuma alamar bata san wane irin aure bane gashi baya son a San sirrin abokin nasa sai yace mata “Sorry, kin san fa angon babu sauƙi, kawai kunyi kama da ita amaryar ne shiyasa” ya faɗa don tunaninsa ƙanwar amaryar ce ko yayarya.
Juya ido tayi tana buɗe baki tare da riƙe haɓarta alamar maganar don shock her.
“Rufa min asiri, ina Ni ina kama da amarya! Ai wannan amarya kyanta ya zarce misali” sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba. “Kuyi haƙuri na tsayar ku da surutu, bari na rako amaryar in an gama al'ada sai ango ya wuce da ita nima na wuce gida.
Murmushi Dr yayi da ya kasa cewa komai tun shigowarsu “Laa Kinga ai angon ma baya jin daɗi kawai bari mu wuce, ki fito muyi dropping naki”
Murmushi kawai budurwar tayi tana mai faɗin “To Allah ya sauwaƙe, nima fa sai yanzu na gano angon cikinku, kar ka damu ga gidanmu nan opposite da gidan nan, zan wuce.”
Daga haka ta juya tare da koma saman tana ƙara ayyana kyan angon nan, gaskiya amarya tayi dace ta faɗa cikin ranta.
Veil ɗin ta ta ɗauko ko da ta sauƙo ƙasa har lokacin suna tare su uku kamar yadda ta bar su. Murmushi tayi tace “To Ni na wuce” Dr faruq yace “Ok sai an gobe ko in ce sai wata rana” bata tsaya ba kawai tayi waving musu hannunta tare da wucewa. Su ma Captain sallama suka yi wa Hamma Zaki tare da wucewa suna barinsa tsaye ɗauke da Leather ɗin kamar gunki.
Ganin dai tsayuwar ba zata fisshe shi ba yasa ya nemi ɗaya daga cikin kujerun parlourn ya zauna yana dafe kansa da ke masa ciwo. Mintuna shida ya kwashe zaune, kamar wanda aka tsikara kuma sai ya miƙe yana yamutsa fuska. Shawarar zuciyarsa ya bi kawai ya nufi staircase ɗin zuciyarsa na bugu da sauri da sauri.
First bedroom ya tsaya, wani tunani yayi hakan yasa ya ɗaura hannunsa ɗaya akan handle na ƙofan yayinda ya ɗanyi knocking da ɗayan. Jin shiru yasa ya sauƙe ajiyar zuciya yana murna tayi bacci. Buɗewa yayi ya shige hankalinsa kwance, ganin babu kowa yasa ya nufi can ciki zuwa ƙofar toilet, gani ƙofar a buɗe kawai yasa ya ɗan yi knocking, kamar daga sama ya ji Muryar da ba zai taɓa matawa da mallakinta ba tana faɗin “Kai Amrah, yanzu zan fito don Allah ki ɗan jira Ni”
Ƙirjinsa ne ya bada sautin dumm! Yayin da wutar kansa gaba ɗaya ta ɗauke.
“Thi voice here! Ya Salam!” ya faɗa yana dafe kansa. Tsawon lokaci yana tsaye kamar ya tuna abu kawai sai ya ajiye Leather ɗin yana ficewa abunsa.
Ɗaya bedroom ɗin ya shiga, Masha Allah, komai white colour ne kamar dai bedroom ɗinshi na gida ga kuma ƙayoton Frame mai ɗauke da picture ɗinshi da ya taɓa yi cikin uniform nashi. “Oh Allah ” ya furta yana faɗawa kan makeken gadon. Mintuna uku ya miƙe ya nufi toilet tare da watsa ruwa ya kuma ɗauro Alwala.
*******************
*Khairy*
Ɗan gajiya tayi da kayan jikinta gashi sun mata nauyi uwa uba kuma fuskarta data ɗan takura mata saboda bata taɓa yin irin kwalliyar nan ba. “Amrah bari na shiga wanka, bana jin angon zai zo ma, kema ki samu ki wuce gida” bata jira amsar Amrah ɗin ba ta yi shirin wankan ta ta shige.
Tana fitowa kawai ta ci karo da Leather jingine da mirror nata, baki ta kama tana tunanin ko waye ya kawo sai ta ƙwala ƙiran “Amrah!” jin babu amsa ya sa ta tabbatar Amrah ma ta wuce gida, Turaruka kusan kala biyar ta mulke jikinta da su sannan ta sanya night wears. Har ta nufi bed ɗin sai Leather nan ta faɗo mata a rai, cikin ranta tace “Tabbas bani da muhimmancin da zaa kawo min kazar amarcin ma kamar kowa sai dai a ajiye min a fice” ɗan tsaki tayi tana faɗin, “Mu zuba mu gani my unknown husband, zan nuna maka irin darajar da mata ke da shi, matan ma kuma iri na Ummul khairy, Ƴar Iya wacce ta taso da Hannun ɓarna”.
Jan ledar tayi ta buɗe, ganin abinda ke ciki yasa ta ɗauki Yoghurt ɗaya ta buɗe ta sha don sai lokacin ma ta tuna da wani abu wai shi yunya. Sauran kuma ta saka hijabi ta sauƙa ƙasa ta ajiye a kitchen. Nan ta dawo ta baje a kan makeken gadonta.
A wannan dare mai tarihi ma'aurata ukun suka zama abu ɗaya yayin da na wannan gidan kam kowa yake lamarinsa yadda yake so.
Yunwar da ta fara damunsa ne yasa ya miƙe daga sallayar da yayi sallarsa ta shafa'i da kuma witri, tunawa da ya bar Leather ɗin a ɗakin so called amarya yasa yayi tsaki. Tsawon wani lokaci ganin ba zai iya jurewa ba yasa ya miƙe bayan shawarar da zuciyarsa ta bashi na ya koma ya ɗauko ko iya Yoghurt ne ciki don zuciyarsa ta tabbatar masa da so called amarya tayi bacci.
A hankali kamar wani ɓarawo ya murɗa handle na ƙofar, kamar wani ɓarawo ya ɗan leƙa ganin mutum kwance cikin blanket yasa ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya. Takawa ya fara yi har ya kai wurin da ya ajiye Leather ɗin but babu leather babu dalilin ta. Kamar ya saka hannu a ka ya kwaɗa ihu haka yaji saboda rabonsa da saka wani abun a bakinsa full three days kenan.
Haka ya juya ya fita jiki babu ƙwari sannan ya ja ƙofar ya rufe a hankali. Tunani ya fara akan yanzu yaya zai yi? Tunawa da fridge yayi hakan ya sa ya fara takawa da saddarfa har ya iso ya buɗe, hamdala yayi ganin fridge ɗin cike, Yoghurt kawai