Showing 15001 words to 18000 words out of 135404 words
meyeh wannan. Bayan sun shirya aka tafi classroom.
Assembly aka yi daga nan kowa aka ce ya wuce aji. JSS one shine ajin da aka kai Ƴar Iya, tana shiga ta fara baza ido, ganin kowa yana neman waje ya zauna yasa ita ma ta nemi waje ta zauna kamar mutuniyar kirki.
Malamin su na English ya shigo, kowa ya miƙe ya gaida shi banda Ƴar Iya wacce gabaɗaya hankalin ta na kan jakar da Ajiram ta kawo mata wai Principal yace a bata, cikin zuciyar ta tace ke kika san miye Principal ɗin ma ai.
Mr. Bello kenan, mugun gaske ne kuma baya sake ma ɗalibai fuska, in ya bada assignment baka yi ba to kashin ka zai bushe ne. Ba tare da ya kalle ta ba ya fara magana cikin harshen turanci.
“Ke wannan da baki tashi ba jira kike na gaishe ki?”
Tuni idanuwan Ƴan aji suka dawo kanta ita kuwa da ake maganar akan ta bata ma san me ake ba, yoh ita da Hausan ma ya aka ƙare bare Yaren da tunda Innar ta haife ta bata taɓa ji ba.
Idanuwan da suka zubo mata ne yasa ranta fara ɓaci ta fara hararar su. Mr. Bello kuma duk tunanin shi shi take harara saboda haka ya hasala ya tunzura daga nan yayi waje.
(Ko meh zai yi ohoo)
Ganin Baturen nan ya fita yasa ta miƙe tsaye tana bin Ƴan ajin da mugun kallo.
“Ku kuma masu idanuwan mayi uban me naci muku zaku zubo min ido, duk ku juya ko naci Bura Ubanku”
Wasu da suka sha jinin jikin su duk suka juya yayin da tsagerun da ke ganin suna dai-dai da ita suke Binta da kallon raini don daga gani wannan baƙauyiya ce.
Ganin sun ƙi daina kallon ta ga kuma wani irin kallo da suke mata yasa ta ƙara harzuƙa....kan mai uwa jawabi tayi duk wanda ta yo kanshi in ta buga mishi duka sai tayi gaba, haka take taka saman desk ɗin kamar biri tana ta tsalle tare da bugun jama'a. Tuni wasu suka fara gudawa waje suna ƙwalla ihu don kuwa bugun da take musu ba na wasa bane.
Su kuwa tsagerun nan basu bar ajin ba ai kuwa ita ma bata daina bugun Ƴan Iska ba don kuwa duk yawan su haka take gabzar su.
Ana cikin gumurzun yaƙin ne sai ga Mr. Bello ya dawo hannun shi riƙe da wata sharɓeɓiyar bulala. Ba tare da yace komai ba duk da yaga wasu students a waje bai ko tambaye su dalili ba tunda ranshi a ɓace yake ga hankalin shi da ya tafi ga hukunta wanan yarinyar da ta ƙi gaida shi.
Ganin yadda yarinyar ke tsalle tana bugun mutane yasa ranshi ƙara ɓaci babu ɓata lokaci kuwa yayi kanta ta bulalar.
Murna ce ta kama su ganin Mr. Bello yayi kanta, ita kuma Ƴar Iya bata san da shigowar shi ba sai jin bulala tayi a gadon bayan ta nan da nan ƴan aji suka saka shewa. Bata kai ga waiwayo ba ta ƙara jin bulala a bayan ta wanda taji matuƙar zafin ta.
Wani kukan kura Ƴar Iya tayi tana juyawa saman desk ɗin ta ƙara sakin wani tsallen tare da hayewa saman malamin, a dai-dai kafaɗar shi tayi masauƙi yayin da ta naɗe ƙafafuwan ta a wuyan sa.
Ƙoƙarin wurgo ta yake tana hanawa har sai da ta tabbatar wannan fah ɗan banza ne. Bulalar hannun shi ta fuzge duk da haka bata bar kan kafaɗun sa ba, nan da nan ta fara zabga masa bulalar babu ƙaƙƙautawa.
Mamaki ne ya cika shi jin irin zafin bulalar gashi ya kasa ƙwatar kan shi, ƴan aji kuwa jiki yayi sanyi ganin yadda newcomer ɗin ke bugun Mr. Bello.
Tun Mr Bello na ƙoƙarin ƙwace kan sa har dai ƙarfin shi ya soma ƙarewa, ita kuwa duka kawai take kai mishi tana sakin wani irin huci. Class monitor ce tayi tunanin zuwa staff room ta sanar da su cewa ana yaƙi a class ɗin su.
(Kaji ta fa wai yaƙi😂).
Babu ɓata lokaci staffs suka taho Jss one, ganin students ɗin a waje ga kuma gurnanin da suke ji yasa cikin hanzari suka nausa don ganin me ke faruwa haka. Arba suka yi da Mr. Bello, mutumin da ko su staffs baya yi musu da sauƙi saboda irin yadda ya tsani raini. Gashi yashe a ƙasa sai kuma Newcomer ɗin jiya wacce ta azabtar da Mr. Small tana jibgar sa.
Ƙoƙarin janye ta suke ai kuwa ta dawo kan su ta fara jibga, ihun malaman ne ya jawo hankalin students da sauran teachers dake sauran classes, tuni aka fito ana tambayar JSS one students dake a waje nan suka fara bada labari.
Wannan abu da yake faruwa Principal dai na office ɗin shi, Ajiram lokacin da ta riski labarin sai ta tsinci kanta da kutsawa cikin ajin duk da riƙe ta da ake yi haka ta shige, nan fa tana shiga tace mata
“Zo mu tafi sister”
Abun mamaki babu musu suka ga Newcomer ta ajiye bulala a gefe ta nufi wurin Ajiram tana rungume ta.
Cikin lallami Ajiram ta ja ta suka wuce hostel ai kamar jira ake ta tafi kuwa masu aljanu suka fara zubewa, ihu kawai ke tashi cikin makarantar, wannan in ta yanki jeji da gudu sai kiga an bita, cikin waɗanda suka bita suma sai kiji wata ta sake ihu tana kama tata hanyar.
Lokaci ɗaya students duk suka ɓararrake, wanda basu da aljanu kuwa sai zare idanuwa suke ko ajajjaɓin abun basa yi.
Bayan jibgar da staffs ɗin nan suka sha a haka suka ɗaga Mr. Bello suka nufi da shi clinic, nan aka ce kawai su wuce Hospital, da ƙyar aka amshi Mr. Bello don kuwa doctors ɗin cewa suka yi sai an zo da police. kuka wasu daga cikin malama suke yi ganin haka yasa doctor ɗin amsar shi nan aka fara bashi agajin gaggawa.
Ɓangaren Ƴar Iya kuwa kuka kawai take zabgawa yayi da Ajiram ke aikin rarrashin ta. A haka suka isa hostel ta cire mata uniform ɗin tare da sanya mata check ɗin su na zaman hostel.
Da ƙyar Ƴar Iya ta daina kukan saboda yadda Ajiram ke ta rarrashin ta.
Bayan kukan ya tsagaita basu koma class ba har lokacin lunch, dining Ajiram ta Kama hannun Ƴar Iya suka tafi kafin su dawo ta gama wartsakewa.
Abun da baku sani ba duk wannan alaƙa da ta ƙullu tsakanin Ƴar Iya da Ajiram babu wanda yasan sunan ɗan uwan shi.
Sai da suka dawo Ajiram ke tambayar Ƴar Iya sunan ta ɗauke da murmushi a fuskar ta.
“Kinga Ni ko sunan ki ban sani ba, yaya sunan ki”
Sai da ta ɗaga kanta sama tukun ta tuna sunan tace.
“Aishatu Umar Gallara”
Murmushi Ajiram tayi tana faɗin
“Sunan ki yana da daɗi sosai Ni kuma zaki iya ƙira na da Aunty Ajiram”
Ƴar Iya ta maimaita
“Antijiram”
Dariya Ajiram tayi tace
“A'ah kice Aunty”
“Aunty”
“Ajiram”
“Ajiram”
“Toh kice Aunty Ajiram"
“Aunty Jiram”
Ganin dai ba zata iya faɗa ba yasa ta ƙyale ta tace ta ƙira ta yadda take so.
Haka Ƴar Iya ta saki jiki suna hira da Ajiram har ta fara bata labarin ƙauyen su, haka suka yi ta hirar su kamar ba Ƴar Iya tamu ba (There must be reason behind this fah).
Bayan farfaɗowar Mr. Bello Babu abinda yake faɗi sai “Kiyi haƙuri, nace ba mutum ba mutum bace ke wallahi ki ƙyale Ni haka, ah wash”
Jin irin sunbatun da Mr. Bello yake yi yasa suka sanar da likita, injection ɗin da aka mishi ne ya sa bacci ƙara ɗaukar sa.
Sai lokacin malaman suka samu damar zuwa duba student ɗin da jiya da daddare aka ji ihun ta wajen bishiyar mangwaro, ita ma dai sunbatun kawai take yi.
Lokacin da labari ya kai ga kunnen Principal ranshi ya ɓaci sosai, duk da cewa su ma malaman suna da laifi ammah ita wannan yarinyar gaskiya ba zai iya barin ta a school ɗin nan ba, dole baban ta yazo ya ɗauke ta in ba haka ba akwai matsala.
Da yake Baffi a ranar ya siya waya saboda yasan dole za'a samu matsala da shalelen Iya. Yana zaune kan taburmar shi sai wayar shi ta hau ruri....da sauri ya ɗaga tare da sallama.
Ko amsawa ba'a yi ba ya fara jin Muryar Malamin makarantar su Shalele nan ya maida hankalinsa don ji me yake faruwa..............
TOH FAH...
AKWAI ƘURA FAH.
KO PC ZAI BAR ƳAR IYA TA CI GABA DA ZAMA A MAKARANTAR KWANA BAYAN TSIYAR DA TA TSULA??????
MU HAƊU A DINNER IN KUNYI COMMENTS....MUCH LOVE MY ESTEEM FANS.
SHARE & COMMENTS FISABILILLAH!
[4/29, 7:57 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA ‘‘‘‘‘17&18’’’’’
Early morning ya tashi coz Flight ɗin 8:00am yayi booking. Sai da ya gama aikace-aikacen da ya saba cikin Laptop ɗin shi daga nan ya fara tattare kayayyakin sa, trolleyn da ya shigo da ita tun zuwan shi ya buɗe, ba tare da ya ɗauki komai ba ya zuge ya mayar. Sai da ya gyara mata zama tukun ya buɗe closet nashi tare da ɗauko wata Black Briefcase, a ciki ya jefa Laptop ɗin daga nan ya ajiye ta a bedside drawer.
Bathrobe ya Sanya daga nan ya nufi toilet, bai wani daɗe sosai ba ya fito yana goge sumar kan shi da ƙaramin towel dake hannun shi. Cike da karsashi yayi drying lallausar sumar shi wacce lokacin ɗaya ya gyara hairstyle nashi. Mayuka irin iri ya shafa daga bisani ya buɗe closet nashi.
Cikin mintuna ƙalilan ya kammala shirin nashi, so masha Allah, ƙaryar mace ta gan shi tace zata kauda ido, kyau kam ba'a magana ga kuma wani fayau da skin nashi yayi.
Turaruka ya fesa masu yawan gaske nan da nan ƙamshi ya buɗe ɗakin kamar kogin turare, har ya juya zai fita ya dawo ya buɗe closet nashi tare da ɗauko wani ɗan ƙaramin kwali.
Ya salaaam! Turaren nan mai suna _Majesté impériale_ wanda ni gaskiya ban taɓa arba da wani mai amfani da shi ba saboda tsananin tsadar shi, ko a ƙasashen Turai da wuya ka samu masu amfani da shi sai waɗanda suka jiƙe da ruwan Kuɗi.
Yana fitar da turaren wani mayetaccen ƙamshi ya bayyana wanda yayi sanadiyyar disashe ƙamshin turarukan da ya shafa. Kaɗan ya fesa daga nan ya jawo trolleyn shi ya jefa turaren.
Briefcase nashi ya ɗauka tare da trolleyn shi janye a ɗayan hannun ya sauƙa downstairs. A nutse yake takawa har ya fito daga parlour.
Kamar jira suke ya fito kuwa suka amshe both trolleyn da kuma Briefcase nashi suna sara mishi saying
“Good morning” in chorus.
Bai ko kalle su ba ya nufi motar da take tsakiyar convoy da suka shirya kamar dai yadda yazo, yana shiga suka figi motocin sai airport.
Suna isa aka fitar da trolleyn nashi, sojan nan da ya ɗauki Briefcase ranar zuwan shi still yanzu ma a hannun shi yake, hakan ya tabbatar min da cewa shi ɗin amintacce ne gare shi.
Sunayen da aka fara kira ne yasa ya nufi steps na Flight ɗin tare da shigewa, sojan ya bi bayan shi. Without much time wastage Flight ɗin ya ɗaga yayi landing a jahar Adamawa, Yola.
*ADAMAWA STATE*
*YOLA*
*SHAGARI ESTATE*
Tunda suka nufo cikin ESTATE ɗin kowa ya tabbatar da cewa yaron General ne ya iso saboda yadda ƙarar jiniya ke tashi.
Dai-dai wani ƙerarre kuma babban gida motocin suka yi horn, Babu arziƙi gate man ya wangale gate ɗin.
Dai-dai parking lot ɗin su da ke ɗauke da wasu zuƙa-zuƙan motoci suka yi parking, bai bi ta kan kowa ba ya fice don ko Briefcase nashi bai samu ta amsa ba.
Part na farko ya nufa, bai sha wahalar danna doorbell ba tunda ƙofar a buɗe take, kamar wani na bin shi haka ya shiga da sauri.
Kai jama'a, anya kuwa wasu na tunanin mutuwa?, Makeken parlourn da na shiga ɗauko report ne yasa na tuna da hakan.
Masha Allah kawai baki na ya furta, tsayawa bayani da kuma siffanta tsaruwar parlourn ma ɓata lokaci ne ku dai kwatanta shi cikin zukatan ku.
Wani babban frame da naga wanda ke ɗauke da picture na wata kyakkyawar mata cikin shigar indiyawa ya bani tabbacin Mom ce tare da Daddy. Sai wani frame ɗin mai ɗauke da hoton wasu kyawawan samari da kuma iyayen su, tashi ɗaya na gano gwarzon maza kuma soja marmari daga nesa wato _Hamma Zaki_ sai kuma ɗan uwan shi wato Hamma Saleem.
Ɗaya frame ɗin kuma dukkan su ne har da wata kyakkyawar yarinya wacce ta buɗe baki tana dariya sai kuma Mom, Daddy, Hamma Saleem sai kuma Hamma Zaki da auta Fauzah.
“Mom, Mom, First love” (nace dama wannan yana magana haka ne?). Jin shiru bata amsa ba ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka, cike da mamaki nace anya wannan kuwa HAMMA Zaki ne?.
Hanyar kitchen yayi yana ƙara ƙwala ƙiran
“First love, where are u?”
Kamar daga sama taji Muryar gudan jinin ta kuma mafi soyuwa cikin zuciyar ta. Ajiye cake ɗin da take baking tayi tana yiwa Laraba alamar ta ƙarasa, daga nan ta fice da sauri.
Arba suka yi a dai-dai dining area ai kuwa da sauri ta ƙarasa tayi hugging nashi ta baya.
“Oyoyo My Son, so you wanna surprise us shiyasa ka shiga da wuri, Daddyn ka yace zuwa yamma zaka shigo”
Murmushi yayi yana juyowa tare da facing Mom dake ta zuba murmushi kamar an mata kyautar Aljanna. Peck ya manna mata a cheek nata sannan yace
“Common first love, ai gashi na baku mamakin”
Maƙale da juna suka dawo parlourn ta zaunar da shi kan sofa tana kallon shi tana murmurshi. He can not afford to reject this saboda haka shima ya buɗe baki sai murmushi yake.
Sun shafe more than 5minutes kafin Mom tace
“Oya lemme get u some refreshments now” har ta fara tafiya ta juyo.
“Do You know what?”
Kai ya gyaɗa tare da zaro ido.
“Na yi baking favourite naka”
Ɗauke da tray ta fito, sai da ta tsiyaya mishi drink ɗin ta miƙa mishi, sai zuba take cikin Hausar ta da kana ji zaka ɗan ba cikakkiyar bahaushiya bace.
Yana gama sha ya miƙe saying
“Mom, lemme fresh up please”
Duk irin gayu na Mom tana mamakin son nata, duk uban ƙamshin da yake yi wai let him fresh up, mutum sai kace kifi. Ta faɗa a ranta.
Steps ɗin ya ɗale, yana isa bedroom nashi ya shiga.
Kai jama'a wannan guy fah he's addicted to white color, everything there is white ga kuma wani makeken frame Mai ɗauke da photon shi shi kaɗai cikin wasu jahilan English wears daga gani a wani beach yayi.. kyawun fuskar shi ba'a magana a picture ɗin.
Irin wannan shi ake kira da *NAMIJIN NOVEL* (Littafi na na gaba kenan)
Da sauri yayi wanka ya sanya jallabiya tare da feshe jikin shi da turarukan shi masu daɗi.
Yana fitowa ya nufi ƙofa, part ɗin Uncle Suraj ya shiga, bayan sun gaisa da Nenne matar uncle take sanar da shi uncle Suraj baya nan.
Daga nan ya wuce part ɗin Uncle Bello, sun gaisa cike da girmamawa ya taho zai fita yaji Muryar Salma cikin shagwaɓa kamar wata ƙaramar yarinya
“Mommah don Allah yau kam ki barni naje shopping ɗin nan kinga su Rumah da su Ayra duk yau zasu je ko so....”
Bata kai ga ƙarasawa ba taci karo da Hamma Zaki da ya juyo ya zuba mata ido.
Haɗiye maganar tayi ta fara rarraba idanuwa tana ƙarasawa kusan shi. Cikin cracking voice tace
“Good morning Hamma Zaki”
Ba tare da ya amsa mata ba ya watsa mata tambayar
“Meh ya hana ki zuwa school?”
Cikin Muryar inda-inda tace
“Uhm...eh..aaaa...damah ba...bani..da...lafiya ne”
Da ƙyar ta kai ƙarshe saboda irin kallon da yake jifan ta da shi kuma sarai ta san ya gano ƙarya take.
“Shine kike tambayar fita shopping ko?”
“Eh...ah... I'm sorry Hamma Zaki....i”
“Shut ur mouth up”
Ya daka mata tsawa
“In na ƙara ganin baki je school ba ranki sai ya ɓaci, stupid girl”
Nan da nan jikin Salma ya fara rawa ganin hakan yasa ya wuce abun shi.
Mommah kuwa dariya tayi tana faɗin
“Alhamdulillahi, naji daɗin hakan, tunda dodon ku yazo ai zamu samu salama yanzu kam”
Bai zame ko ina ba sai part ɗin tsohuwa mai ran ƙarfe wato granny.
Tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo ɓaɓatun ta tana faɗin.
“Yo ni AISHATU ina ganin ikon Allah, bari anjima Salamatu ta zo ta saka min ƙiran wayar nan dai”
Sallamar shi ce ta dakatar da ita daga maganar.
“Ah soja marmari daga nesa, soja mazan fama an baro ƙasar nasara kenan?”
Dariya yayi sai a lokacin na ƙara gane cewa shi ƙarshe ne a kyau.
“Tsohuwa mai ran ƙarfe, nayi zaton ai in nazo zan tarar kin bunga ne”
Zaro ido Granny tayi tace
“Bakin ka ya sari guntun kashi ɗan baƙin ciki kawai, yo Ina dalili ni anya kai jinin Muhammadu ne ma?. Kai to bari kaji in gaya maka in ma mutuwa ne ubanka da uwar ka ne zasu fara mutuwa kafin ni, ja'iri kawai”
Dariyar sa yake babu ƙaƙƙautawa can yayi shiru
“Haba Uwar gidan Alee mazan fama kuma uwar Muhammadu, ai ba zaki mutu yanzu ba ko bakya son ganin matar jikan naki ne”.
Goron da ta gutsira ta cire tana murmurshi sannan tace
“Ba shakka kuwa ammah kai anya ma akwai wacce zata aure ka, abu kamar kututturen ice ga kuma fuska babu fara'a, wallahi duk wacce ta aure ka ma jaraba ta aura”
Hamma zaki yace
“Lallai ma tsohuwar nan, ni ne kututturen icen ko? To sai anjima”
Ya faɗa yana miƙewa zai wuce.
“A'ah haba Maigida duk kishi ne dai irin nawa kasan bana so kayi min kishiya ai”
Murmushi mai sauti Hamma Zaki yayi yana ficewa.
“Daga baya kenan, zan dawo Granny”.
Around 12:00pm wata babbar mota ta danno hanci cikin gidan, bayan tayi packing wasu ƴan yara suka fito su shida.
Fauzah da kuma Yesmeen kan su ɗaya, Najma da Ra'eesa kan su ɗaya sai Rumah da Ayrah suma kan su ɗaya.
Fauzah part ɗin su ta shige, Yesmeen da kuma Najma suka wuce nasu haka Ra'eesa da Ayra suma suka wuce nasu part ɗin.
Ɓangaren Baffi yana ɗaga wayar yayi sallama sai dai ko amsa sallamar Principal bai yi