Showing 123001 words to 126000 words out of 135404 words

Chapter 42 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46357

da iyayenki saboda haka ina mai sanar da ke na datse igiyar aure da ke tsakani na da ke!” daga haka yasa hannunsa ɗaya a aljihu ya ciro takardar ya miƙa mata.

Idan hankalinta million ne to gabaɗaya sun gama tashi don bata yi tsammanin faruwar al'amarin nan a nan kusa ba, duk a nata tunanin zata ci albarkacin babynsu ya ci gaba da zama da ita ko da ya gano hakan daga baya, ashe yaudarar kanta take.

Ganin taƙi karɓa ya sa ya ce “Karɓi mana Nabila” babu musu ta karɓa sai kuma yayi wani murmushi irin na ƙarfin hali yace “Kuɗin da iyayenki suka amsa daga gare mu mun yafe, ke ma na yafe Miki duk wani cutarwa da kika yi min, ina fatan ke ma ki yafe Ni idan na cutar da ke, a ƙarshe ina roƙon Alfarmar ki tafi da Baby Humairah ki shayar da ita zuwa watanni biyu zan karɓi ɗiya ta, idan ba zaki iya Alfarmar ba kuma sai muyi yarjejeniya na biya ki”.

Ganin tayi shiru yasa ya miƙa mata baby Humairah yana faɗin “Zan tura Miki kuɗin Flight sai ki je kiyi booking” karɓarta tayi ta ajiye ta a kan cot ɗinta. Juyowar da zata yi taga yana ƙoƙarin fita. Da wani irin mahaukacin gudu ta iso gare shi tana riƙe ƙafarsa.
“Don Allah sweetheart Kada kayi min haka, wallahi ina sonka ba zan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake Ni ka mayar da auren mu albarkacin Babynmu” ta ƙarasa tana fashewa da wani kuka mai ban tausayi. Ganin yana janye ƙafar tasa tasa ta ƙara ƙanƙame shi tana faɗin
“Ka taimake Ni sweetheart Kada Ka datse auren nan, ka mayar da shi sweetheart na bi Ka na bi Allah da Manzonsa, kada ka datse shi da wurwuri haka, ka taimakaaa”

Ganin zata ɓata masa lokaci yasa ya fuzge jikinsa ya ja mata ƙofar, zubewa ƙasa tayi tana sakin kuka mai ban tausayi. Tabbas tayi sake da damarta amma duk da haka ita da shi mutu ka raba takalmin kaza, dole ya dawo gare ta. Cike da ƙwarin guiwa ta nufi wayarta tana share hawayen da suka zubo mata. Numbern Mami tayi dialling, tana ɗagawa ta fashe mata da kuka.
“Shalele me ya faru ne?” bata kula ta ba ta ci gaba da kukanta. Hankalin Mami ne ya tashi ta ce “Kinga Daughter me yake damunki ne?, yi shiru ki faɗa min.”
“Mami Sweetheart ya gano komai har cikin da na zubar kwanaki, yanzu haka ya sake ni”
A zabure Mami tace “What?, ya sake ki fa kika ce?”
“E Mami ”
“Shikenan yanzu share hawayen ki ki saurare Ni, saki nawa ne ma wai?”
“Ɗaya”
Dariya Mami tayi tace “Da sauƙi ma ai, kinga yanzu ki yi booking flight ki taho nan, in kin zo zamu san yadda. Za'a yi ki koma”
Nan ta yanke ƙiran ta fara haɗa kayanta da na baby Humairah, daga nan ta ɗauki key na motarta ta nufi airport. Allah ya so akwai Flight ɗin za zai tashi 3:00pm zuwa Abuja kuma baki cika ba, nan ta dawo ta ƙarasa haɗa kayan nasu. Sai da ta bi ta kan ƙawarta tukun suka taho, ita kuma ta dawo da motar zuwa gidansu.3:00pm jirgin su pretty ya ɗaga zuwa babban birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.
(Nace safe journey pretty, a gaida na gaba, na baya su samu lafiya).

A ɓangaren Hamma Zaki tunda ya fito daga gidan yaji ransa wasai kamar ya sauƙe wani nauyi, direct gida ya wuce, su Granny na ta tsokanarsa wai jarumi da kwanciya a asibiti. Murmushi kawai yake yi don kuwa yana cikin farin ciki kasancewar abun da yayi muradin mallaka ya mallake shi, addu'a kuma babu irin wacce bai yi wa iyayen nasa ba da suka haɗa wannan aure.

Sai wuraren 5:00pm ya baro gidan ya nufi gidan shi dake GRA, babu kowa a parlourn sai wani sassanyan ƙamshi da ke tashi, lumshe idanuwansa yayi yana faɗin “Everything about her is unique”, a haka ya tako har tsakiyar parlourn, idanuwansa ne suka sauƙa a kan flasks da ke jere, hakan ya sa yayi murmushi ya nufi wurin, duk da ya ci abinci amma ya rasa me yasa baya ƙoshi da girkinta ba kuma ya so yayi missing ko sau ɗaya, kamar bai ci komai ba haka cikinsa ya koma, da sauri ya zauna yayi serving kansa. Sai da ya ƙoshi yayi hamdala tukun ya tashi ya nufi bedroom nasa.

Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kaya wanda suka matuƙar amsar jikinsa, yayi kyau kamar ka sace ka gudu, daddaɗan ƙamshin da ke fita daga jikinsa ke fara isa duk wurin da ya nufa. Kai tsaye motarsa ya nufa daga nan ya wuce gida Dr. Faruq, sosai Aunty Rahima ta tarbe shi, nan yaron Dr wato Mahmud ya zo ya ɗale shi yana faɗin “Uncle! Uncle” fuska sake ya ɗaga yaron yana faɗin “Oyoyo yaron uncle ”.

Sauƙe shi yayi ya zaunar da shi shima ya zauna a gefensa, bayan sun gaisa Aunty Rahima ta kawo masa drinks, nan Mahmud ya fara zuba kamar gidan Radio 📻.
“Uncle wai da gaske ne kayi wani aure?” kai ya ɗaga masa yana faɗin “Eh boy”
“Daddy na ne ya faɗa min da nace ya kai Ni wurinka, amma ina zaka kai Ni wurin amaryar?”
“Zan kai ka boy, zan kawo ta ma ta ganka”
“Yeee Uncle zan ga amaryar uncle, Daddy yace....”
“Kai Mah friend, yi min shiru haka” Aunty Rahima ta katse shi.

Shi dai murmushi kawai yayi yana fatan shima wata rana gidansa ya kasance kwatankwacin haka. A nan suka yi sallar maghrib da Isha tukun yayi musu sallama. Kai tsaye gidansa ya nufa, bedroom nasa ya shige tare da buɗe closet, wata farar shadda ƙal da ke ƙyalƙyali ya janyo yana murmushi. Saurin faɗawa toilet yayi ya samu yayi wanka, a hanzarce ya shirya sannan ya shafa dadddaɗan turarensa na Império majesté. Tuni ɗakin ya ɗauki ƙamshi.

Duk wanda ya san Hamma Zaki ba zai ce yau ka rana ɗaya da ganshi cikin manyan kaya ba, yayi kyau sosai kamar me, babbar rigar da ya saka ita ta ƙara haskaka shi. Da sauri ya ɗauki key ɗin motar ya fice daga gidan. Kai tsaye suya spot ya nufa, bayan ya amshi kajin ya ƙarasa ya siya Yoghurt don yau ya ƙudirin faranta wa amaryar tasa, ya kuma yi aniyar buɗe mata Sirrin zuciyarsa la'alla ta tausaya masa ta kuma bashi damar nuna mata irin tarin don da yake mata, zai baje mata kolin soyayyarsa har sai ta karɓe shi.

Yana isa yayi horn, bayan gate man ya buɗe gate ya shiga, a parking lot ya daidaita tsayuwar motar daga nan ya fito hanunsa ɗauke da manyan ledodin guda biyu. Zuciyarsa ne ta fara bugawa da sauri sauri amma a haka ya nufi entrance na Parlourn, yana shiga ya rufe. Directly bedroom ɗin sa ya nufa, lumshe idanuwansa yayi yana zuba mata albarka, ya tabbatar yanzu ne yayi aure, gashi dai kullum cikin faranta masa take duk da irin tarin laifukansa gare ta, sai da ya ajiye ledodin ya dawo zuwa bedroom nata, a zaune a kan sallaya ya tarar da ita, bayan ta amsa sallamarsa ba tare da ya shigo ba ya ce mata “Ummul khairy ki same ni a bedroom ɗina”

Daga haka ya juya ya nufi bedroom ɗinsa, yana shiga ya cire babbar riga ya lanƙaye ta, sannan ya zauna bakin gadon. Da sallama a bakinta ta shigo, ya amsa mata fuska sake tare da miƙewa ya nufe ta, hannun ta ya riƙo ya zaunar da ita bakin gadon sannan ya ɗan ranƙwafo kanta yace “Yau na ke ango fah” yana wani kanne mata ido, kamar ta binne kanta haka ta ji don wata irin kunyarsa da ta dirar mata. Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Ita mamaki ma abun ya bata, mutum irin Hamma Zaki dama yakan rasa ta ido ne?, a duk tsawon lokacin auren su bai san lafiyarta ba sai cikin kwana biyu da ya gane zai fara mata rawar kai!.

Da kansa ya ɗauko jakar kajin, ya shimfiɗa wani lallausan abu kafin ya jiye, ita dai ido kawai take binsa da shi, ko da ya shimfiɗa kitchen ya nufa ya haɗo plates da kuma bowl ganinta zaune a yadda ya barta yasa yayi murmushi a ransa yace “Silly and classic girl”. Ajiyewa yayi sannan ya nufi toilet har zai shige ya juyo yace “Ki yo Alwala, I'll be waiting for you ”
Kamar wata wawuya ko maras fahimta ta koma, it's after some seconds ta fara comprehending abunda ta ji ɗin, miƙewa tayi ta wuce zuwa bedroom nata, tana shiga ta tura ƙofar tana Turo bakinta gaba. “Oh lallai maza ba su da kunya, na San dai Hamma ba so na yake ba, kawai ya karbi auren na ganin Ni ce zaɓin da aka masa, amma ina fan ya so ni ɗin kamar yadda nake addu'a, ganin zata ɓata ɓ masa lokaci kan zancen zuci ya ta nufi toilet, sai da ta watsa ruwa sannan ta ƙara shafa different perfumes sai suka bada wani daddaɗan ƙamshi. Kaya ta sauya zuwa nighties ta zumbula ƙatoton Hijaɓ ɗinta sannan ta nufi bedroom nasa tana mai fargaba duk da ta san me hakan ke nufi, ta karanta sosai bugu da ƙaro groups ɗin da su Ayrah suka saka ta yasa ta san abubuwa da dama. A hankali ta tura ƙofar da sallama a bakinta.

_kwana biyu kun jini shiru, I'm sorry wallahi bani da lafiya ne shiyasa, har ila yau kuma ina barar addu'o'nku na neman sauƙi wurin Ubangiji, nagode_
_COMMENT PLEASE_

OMMENT PLEASE_
[26/09, 8:49 a.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““121&122”””

Zaune ta tarar da Hamma Zaki zaune a kan abinda ya shimfiɗa ɗin, da hannunsa ya mata alamar ta ƙaraso, ba musu ta ƙaraso ta zauna can nesa da shi, hakan bai wani dame shi ba ya cire kazar farko wacce already an maida ta pieces ya zuɓa a plate, calmly yace “Come closer”, kamar bata so ta ɗan tura baki gaba caraf kuma a kan idonsa ne, murmushi kawai yayi ganin ta matso ɗin. “Eat”, ya faɗa yana kallonta, kamar zata yi kuka duk irin ƙaunarta da Kaza haka ta kasa sakin jiki ta ci, shi kuwa master he's enjoying every best of the moment, Jin da yake tamkar yafi kowa dace a duniya, the Amazoing part of the story is kasancewar shi tare da ita muradinsa. A nata bangaren haka dai ta taɓa sama sama, ganin ta cire hannun ta gaɓadaya yasa ya ɗago yana kallonta, “Why?” kasa magana tayi kawai sai ta duƙar da kanta, Yoghurt ya zuba mata a cup sannan ya miƙa mata sayin “Have this”, karɓa tayi tayi sipping na wani lokaci kafin ta miƙe tsaye ɗauke da cup ɗin a hannunta, sai da ta kusa ƙofa ta ji yace “To where” cike da ƙosawa da wannan sabon halin nasa tace “Zan kai kitchen ne”
In an authoritative manner ya ce “Ki jira na kammala, come and sit here”.

Ba musu ta dawo ta zauna har ya kammala, ta kwashi plates ɗin zuwa kitchen ɗin Sama, kamar ba zata dawo ba sai kuma ta koma. Samun shi tayi tsaye kan sallaya alamar ita yake jira, da hannu ya nuna mata toilet, ita ma bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce, sabunta alwalarta tayi daga nan ta fito, ɗan baya da shi ta tsaya, jin wanzuwarta a wurin yasa ya tayar da kabbara.

Kamar yadda Manzon tsira ya koyar haka ya ja su raka'a biyu, bayan ya sallame ya kama goshinta sannan ya karanta addu'ar da Manzo ya koyar. Bayan nan yayi mata wasu tambayoyi a kan addini, alhamdulillah she's able to answer them in a logical manner Hakan ya mugun ƙara mata matsayi. Bed ɗinsa ya nuna mata ya ce “You can sleep there,” tare da janyo wani file yana dubawa. Babu yadda ta iya ta nufi bed ɗin Allah ya so ta fito da wayarta, tana hawa WhatsApp group nasu na Ƴaƴa mata ta ci karo da wani hot story akan matar da ta kashe mijinta saboda auren dole da aka yi mata. Tana bibiyar comments ɗin ta ji ya amshe wayar a hannunta da sauri ta maido da dubanta gareshi, gira ya ɗage mata yace “Time to sleep Nour”, ƙwaƙwalwarta kasa fassara me Nour yake nufi ta yi, kamar wata wawuya ta kwaɓe fuska a shagwaɓe ta ce “Ni...Ni...Ni gaskiya bedroom na zan koma” zaro ido yayi yace “What?” kamar munafuka ta maida kanta, cikin ransa yace “Hmm yarinya kenan ”

Tattara tablet da file ɗin yayi sannan ya wuce closet ya Sanya wasu sabbin white pyjamas masu taushin gaske, ita dai khairy gaba ɗaya bata yi tsammanin zuwan wannan rana ba ko kaɗan, ta saddaƙar yau kam ta shiga hannun babban soja sai ɗan buzunta na Gallara wanda Bara wankewa. A hankali Hamma Zaki ya jawota yana faɗin “remove this black hijab” kafin ta Kai hannu ma ya cire mata shi, ƙamshin jikinta da ya bugi hancinsa har sai da ya lumshe idanuwansa, a ransa yace “unlike that bitch” sai kuma ya kai hannunsa ya gyara mara kwanciyar. Ganin kamar bacci take yasa ya kai bakinsa zuwa kyakkyawar fuskarta ya sumbata, niyyarsa ya kwanta since she's asleep but he can't afford to do so, daga nan kuma fa sai salon ya sauya, ba shiri Diamond Bhatool ta fito da gudu.

Around 5:00am ya farka, yana tuna moment ɗinsa na Daren jiya, komai ya fara zuwa mai daki-daki, murmushi kawai yake yana lumshe idanunsa, she's damn cute and expensive, and yayi alƙawarin sai khairy ta so shi ko da kuwa rabin yadda shi yake son ta ne. A hankali ya sauƙa ƙasa ya nufi toilet, wanka ya fara yi sannan ya ɗauro Alwala daga nan ya nufo ɓangaren da take kwance, gently ya ɗan buga pillow ɗin shi kuma ya ce “lokacin sallah” daga haka yayi waje.

Yana fita ta miƙe zaune tana murmushi, all she remembers is yesterday but she couldn't believe all about it, sleeping on same bed with Hamma Zaki, sai kuma ta buɗe idanunta saying “A hope will soon be fulfilled ” daga haka ta nufi toilet ɗinshi tayi wanka, tana fitowa ta wuce bedroom nata tayi sallah. Ganin kamar bai dawo ba yasa ta koma ta tattare sannan ta gyara ɗakin tas, ta wanke toilet, burner ta ɗauko ta sanya wasu daɗaɗan turarukan ɗakin tuni ƙamshi ya karaɗe ko ina, sama sama ta tattare bedroom nata sannan ta wuce kitchen don haɗa musu breakfast.

Around 8:35am ya shigo gidan, tun daga parlourn sama ya tabbatarwa kansa rayuwarsa ta sauya, idanunsa kumshe ya nufi staircase ɗin har ya ƙarasa Saman, wani sassanyan ƙamshi da ya bugi hancinsa yasa ya furta “Alhamdulillah” da sauri ya ƙarasa zuwa bedroom nasa, ganin bata ciki yasa ya ɗauro wanka don yau fitar 9:00am yake da, yana gama shirinsa na fita ya nufi bedroom nata, knocking ya ɗanyi sai kuma ya shiga but she's nowhere to be found, a ɗan ruɗe ya fito, ji footsteps a bayanshi yasa ya juyo. Ganin tray ɗauke da abinci kai yaji wani irin sanyi a ransa, cike da kulawa ya buɗe baki zai yi magana ta riga shi “Good morning Hamma” sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa tuna moments ɗin jiya murmushi yayi yace “Morning Nour, how's your night? Ba tare da ta amsa masa ba ta ce “Hamma food is ready”
“Hamma food is ready” shima ya faɗa yana kokoyan muryarta, fuskar ta kwaɓe a shagwaɓe kamar zata yi kuka tace “Zan faɗawa Granny Allah ban sooo” idanuwansa ya zuba mata ganin ikon Allah, kamar wata ƴan 7-8years yadda take acting, marairaice fuska
Shima yayi ya ce “Im sorry, I'm leaving, take care Nour, bye”

Hakan da yayi ma kawai don ya ga reaction nata ne, ya juya kenan yaji ta ƙira sunansa da wani irin ja “Hammaaa” juyowa yayi yace “What Nour?” a shagwaɓe tace “Please eat something before you go” Kai ya gyaɗa ya bi bayanta zuwa dining, serving nasa tayi sannan ta wuce don yin wanka. A nutse ya cinye har da ƙari kafin ya koma ya tsaftace bakinsa, haka dai ya fita ransa fes da shi yana jerawa Nour ɗinsa albarka.

Around 5 ya dawo gidan bayan biyawa ya gaisa da su Granny, nan fa granny ta tada masa rigima wai ya kawo mata ƴar ta ta gani. Shi dai jin ta kawai yake don ko giyar wake ya sha ba zai bar matarsa tana yawo haka ba, yo yaushe ma aka yi auren ne.

Wanka ya faɗa kai tsaye daga nan ya nufo dining sai ga ta cikin wata expensive atampa wacce ɗinkinta yayi mugun fita sosai. Tunda ya fito yake Binta da kallo a ransa yana ayyana yau kam babu fashi, lumshe idanunsa yayi ya furta “Tabarakalla”. Fuskarta fayau babu kwalliya sai tsantsar natural beauty nata ta nufo wurinsa, “Sannu da dawowa Hamma, ” ba ta jira amsarsa ba tayi serving nasa, har sai da ya gama ta tattare ta wuce kitchen.

Da daddare jiya-i-yau haka yasa ta baro nata ɗakin ya dawo da ita nan, a yanda yayi alƙawari hakan ta faru ni dai na ja baya da alƙalami na, sai wuraren 3:00am naji sautin kukan khairy ya ragu ya tabbatar min da bacvi tayi. Ƙiran sallar asuba yasa ya buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyin gaske yayinda jikinsa kuma yayi masa wasai, from the his arrival from work to night, the moment he spends with his Nour yasa ya ƙara lumshe idanuwansa yana buɗewa, he actually enjoyed it, the way he feels the moment looks different, Hakan ya tabbatar masa khairynsa virgin ce unlike Pretty that comes as jarabatun, abinda ya ƙara fuzgarsa ga tarawa da Khairyn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login