Showing 120001 words to 123000 words out of 135404 words
ya jikin Mijinta kowa ke tambaya, kamar zata yi kuka tace “Kuma baku kyauta min ba babes,”. Voice note tayi musu na tsawon mintuna shida daga nan ta kashe data ta ajiye wayar, bathrobe ta sanya kana ta shiga wanka.
Wanka tayi ta ɗauro Alwala sannan ta fito tana tsane gashin kanta da ya jiƙe da towel. Gaban dressing morrow ta zauna bisa stool sannan ta janyo hand dryer ta tsame gashin, mayuka ta shafa da kuma different varieties of Humras sannan ta shafa powder, lip gloss ta shafa ta kara saita girarta daga nan kuma ta nufi closet.
Atamfarta Super wacce ta sha ɗinkin riga da skirt ta saka bayan saka undeewears, daga nan ta ɗaura kwalinta irin ɗaurin da ake kira da ture ka ga tsiya. Zamanta kenan sai ga ƙiran Amrah, da sauri ta sauƙo ta dawo parlourn ƙasa, a nan ta tarar da ita. Tana isowa Amrah tace
“Masha Allah, Kinga yadda kika yi kyau kuwa?, ga yadda ɗaurin nan ya amshe ki kamar don ke aka fara yinsa” dariya khairy tayi tana faɗin “Irin wannan zuzutawa haka Amrah, ai sai ki sa na daina kallon mutane” ita ma dariya tayi tana faɗin “Honestly speaking kina da kyau, mijinki yayi dace” bata rufe baki ba Khair ta ce “Kin ga kuwa yanzu fitar shi ma, ko ki tambaye ni ya mai jiki”
“Sorry khairy wallahi ina ciki ciki sai kuma kwalliyarki ta sa na ɗan manta, yaya mai jikin?”
Hararar wasa khairy tayi mata tace “Alhamdulillah, da sauƙi”
“To Allah ya ƙara sauƙi” daga haka suka fara tattaunawa akan batun da ya shafi rayuwa.
“Yauwah Amrah ɗazu a wani group na ga wata mata tayi posting wai tana neman shawara”
Amrah tace “Ina sauraron ki”
“Kina ji, wai irin sabon auren nan ce kamar dai Ni, to dama auren nasu haɗawa aka yi babu wanda ya san wani cikin ita da mijin, so har aka yi auren basu taɓa ganin juna ba, aka kawo ta gidan nan ma haka har tsawon wata guda. To sai wata rana dalili ya sa suka haɗu a wurin mutuwar kakarta ba tare da sun fahimci su ɗin ma'aurata ba ne. Wani abun mamaki kuma to ita dama ta daɗe wai tana don mijin tun kafin tayi aure, tayi burin Allah ya bata shi sosai, shima a nasa ɓangaren hakan take, ita ce wacce zuciyarsa ta faɗa akai, to wai shine take tambaya, wai ya zo neman yafiyarta, shij zata tsaya ja masa aji ne ko kuma kawai ta bada kai?”
Gauron numfashi Amrah ta saki tace “Toooo babbar magana, har ga Allah duk suna da laifi, Ni Kinga ko auren ƙiyayya aka yi min wallahi zan zauna tunda an riga an ɗaura, zanyi haƙuri na jure na ja hankalin mijin har ya so Ni, amma sunyi sakaci ita da mijin nata, duk da haka dai in nice zan yafe masa tunda ya gane kurensa daga nan na bada kai mu ƙulle abun mu”
Ajiyar zuciya khairy ta sauƙe tace “Ba kya tunanin kuma ya ƙara tafka kwatankwacin hakan?”
“Aah ai da sun daidaita jan kayanta a jiki ya kamata tayi ta nuna masa soyayya, ina tabbatar Miki ba zai guje ta ba, kin san an ce shi namiji ɗan gata ne, idan kina tarairayarsa mantawa yake da kowacce mace bayan ke”
khairy ta ce “Haka ne, yanzu mu ci abinci sai na tura mata tamu shawarar” daga haka suka nufi dining, Wanda ta ware domin ta shi ta yi serving nasu suka ci.
_Comment Please_
[26/09, 8:47 a.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““119&120”””
A ɓangaren Hamma Zaki ko da ya fita gidansa ya nufa, yana daidaita parking ya fito fuskarsa ɗaure kamar an aika masa saƙon mutuwa. A haka ya nufi entrance na Parlourn, kamar kullum yau ma dai haka yake, babu datti amma kuma babu ƙamshi kamar parlourn khairy, staircase ɗin ya haye tare da nufar bedroom nasa, locker ya buɗe ya ɗauko wani Memo 📝 Wanda ke haɗe da Biro ciki, rubutu yayi ya naɗe takardar sannan ya mayar da su yadda ya ɗauko daga haka ya fito ya nufi bedroom ɗinta.
Kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar, chatting ɗin da ta ke ta ajiye tana juyowa, da sauri ta diro ƙasa har tana shirin faɗuwa ta nufo shi.
“Gaskiya Sweetheart abinda kake baka kyautawa, ai ka ƙare kwanakin da zaka mata sai ka raba mana kwana amma sai ka kama hanya ka koma saboda rashin adalci...”
Tsawar da ya yi mata ne yasa ta risina jikinta har ɓari yake. Baby Humairah ma Dake bacci a cot ɗinta sai da ta Calla ihu.
Ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba ya ɗauko baby Humairah yana saɓa ta a kafaɗarsa nan tayi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba. Ita dai pretty ikon Allah yau take gani, uwa uba irin kwarjinin da ya ƙara mata yasa ta nutsu.
“Kina ji na ko?” ta ɗago ta kalle shi. “Tsawon rayuwar aure da nayi da ke kin cutar da Ni babu iyaka yayin da Ni kuma a koyaushe nake ƙoƙarin ganin na sauƙe nauyin ki da ke kaina” sai kuma ya dakata. “Nabila, nayi tunanin soyayyar da kike yi min ta tsakani da Allah ce shiyasa na ci gaba da zama da ke bayan fallasar zubar da ciki da kika yi wanda Ni ina da tabbacin ba nawa bane amma na haƙura na yafe Miki, daga ranar da hakan ta faru kuma ban ƙara zargin ki ko da sau ɗaya ba. Amma yanzu na matuƙar fahimtar ke ɗin wacece, kina so na ne don wani cikar burinku ke da iyayenki saboda haka ina mai sanar da ke na datse igiyar aure da ke tsakani na da ke!” daga haka yasa hannunsa ɗaya a aljihu ya ciro takardar ya miƙa mata.
Idan hankalinta million ne to gabaɗaya sun gama tashi don bata yi tsammanin faruwar al'amarin nan a nan kusa ba, duk a nata tunanin zata ci albarkacin babynsu ya ci gaba da zama da ita ko da ya gano hakan daga baya, ashe yaudarar kanta take.
Ganin taƙi karɓa ya sa ya ce “Karɓi mana Nabila” babu musu ta karɓa sai kuma yayi wani murmushi irin na ƙarfin hali yace “Kuɗin da iyayenki suka amsa daga gare mu mun yafe, ke ma na yafe Miki duk wani cutarwa da kika yi min, ina fatan ke ma ki yafe Ni idan na cutar da ke, a ƙarshe ina roƙon Alfarmar ki tafi da Baby Humairah ki shayar da ita zuwa watanni biyu zan karɓi ɗiya ta, idan ba zaki iya Alfarmar ba kuma sai muyi yarjejeniya na biya ki”.
Ganin tayi shiru yasa ya miƙa mata baby Humairah yana faɗin “Zan tura Miki kuɗin Flight sai ki je kiyi booking” karɓarta tayi ta ajiye ta a kan cot ɗinta. Juyowar da zata yi taga yana ƙoƙarin fita. Da wani irin mahaukacin gudu ta iso gare shi tana riƙe ƙafarsa.
“Don Allah sweetheart Kada kayi min haka, wallahi ina sonka ba zan iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimake Ni ka mayar da auren mu albarkacin Babynmu” ta ƙarasa tana fashewa da wani kuka mai ban tausayi. Ganin yana janye ƙafar tasa tasa ta ƙara ƙanƙame shi tana faɗin
“Ka taimake Ni sweetheart Kada Ka datse auren nan, ka mayar da shi sweetheart na bi Ka na bi Allah da Manzonsa, kada ka datse shi da wurwuri haka, ka taimakaaa”
Ganin zata ɓata masa lokaci yasa ya fuzge jikinsa ya ja mata ƙofar, zubewa ƙasa tayi tana sakin kuka mai ban tausayi. Tabbas tayi sake da damarta amma duk da haka ita da shi mutu ka raba takalmin kaza, dole ya dawo gare ta. Cike da ƙwarin guiwa ta nufi wayarta tana share hawayen da suka zubo mata. Numbern Mami tayi dialling, tana ɗagawa ta fashe mata da kuka.
“Shalele me ya faru ne?” bata kula ta ba ta ci gaba da kukanta. Hankalin Mami ne ya tashi ta ce “Kinga Daughter me yake damunki ne?, yi shiru ki faɗa min.”
“Mami Sweetheart ya gano komai har cikin da na zubar kwanaki, yanzu haka ya sake ni”
A zabure Mami tace “What?, ya sake ki fa kika ce?”
“E Mami ”
“Shikenan yanzu share hawayen ki ki saurare Ni, saki nawa ne ma wai?”
“Ɗaya”
Dariya Mami tayi tace “Da sauƙi ma ai, kinga yanzu ki yi booking flight ki taho nan, in kin zo zamu san yadda. Za'a yi ki koma”
Nan ta yanke ƙiran ta fara haɗa kayanta da na baby Humairah, daga nan ta ɗauki key na motarta ta nufi airport. Allah ya so akwai Flight ɗin za zai tashi 3:00pm zuwa Abuja kuma baki cika ba, nan ta dawo ta ƙarasa haɗa kayan nasu. Sai da ta bi ta kan ƙawarta tukun suka taho, ita kuma ta dawo da motar zuwa gidansu.3:00pm jirgin su pretty ya ɗaga zuwa babban birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.
(Nace safe journey pretty, a gaida na gaba, na baya su samu lafiya).
A ɓangaren Hamma Zaki tunda ya fito daga gidan yaji ransa wasai kamar ya sauƙe wani nauyi, direct gida ya wuce, su Granny na ta tsokanarsa wai jarumi da kwanciya a asibiti. Murmushi kawai yake yi don kuwa yana cikin farin ciki kasancewar abun da yayi muradin mallaka ya mallake shi, addu'a kuma babu irin wacce bai yi wa iyayen nasa ba da suka haɗa wannan aure.
Sai wuraren 5:00pm ya baro gidan ya nufi gidan shi dake GRA, babu kowa a parlourn sai wani sassanyan ƙamshi da ke tashi, lumshe idanuwansa yayi yana faɗin “Everything about her is unique”, a haka ya tako har tsakiyar parlourn, idanuwansa ne suka sauƙa a kan flasks da ke jere, hakan ya sa yayi murmushi ya nufi wurin, duk da ya ci abinci amma ya rasa me yasa baya ƙoshi da girkinta ba kuma ya so yayi missing ko sau ɗaya, kamar bai ci komai ba haka cikinsa ya koma, da sauri ya zauna yayi serving kansa. Sai da ya ƙoshi yayi hamdala tukun ya tashi ya nufi bedroom nasa.
Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kaya wanda suka matuƙar amsar jikinsa, yayi kyau kamar ka sace ka gudu, daddaɗan ƙamshin da ke fita daga jikinsa ke fara isa duk wurin da ya nufa. Kai tsaye motarsa ya nufa daga nan ya wuce gida Dr. Faruq, sosai Aunty Rahima ta tarbe shi, nan yaron Dr wato Mahmud ya zo ya ɗale shi yana faɗin “Uncle! Uncle” fuska sake ya ɗaga yaron yana faɗin “Oyoyo yaron uncle ”.
Sauƙe shi yayi ya zaunar da shi shima ya zauna a gefensa, bayan sun gaisa Aunty Rahima ta kawo masa drinks, nan Mahmud ya fara zuba kamar gidan Radio 📻.
“Uncle wai da gaske ne kayi wani aure?” kai ya ɗaga masa yana faɗin “Eh boy”
“Daddy na ne ya faɗa min da nace ya kai Ni wurinka, amma ina zaka kai Ni wurin amaryar?”
“Zan kai ka boy, zan kawo ta ma ta ganka”
“Yeee Uncle zan ga amaryar uncle, Daddy yace....”
“Kai Mah friend, yi min shiru haka” Aunty Rahima ta katse shi.
Shi dai murmushi kawai yayi yana fatan shima wata rana gidansa ya kasance kwatankwacin haka. A nan suka yi sallar maghrib da Isha tukun yayi musu sallama. Kai tsaye gidansa ya nufa, bedroom nasa ya shige tare da buɗe closet, wata farar shadda ƙal da ke ƙyalƙyali ya janyo yana murmushi. Saurin faɗawa toilet yayi ya samu yayi wanka, a hanzarce ya shirya sannan ya shafa dadddaɗan turarensa na Império majesté. Tuni ɗakin ya ɗauki ƙamshi.
Duk wanda ya san Hamma Zaki ba zai ce yau ka rana ɗaya da ganshi cikin manyan kaya ba, yayi kyau sosai kamar me, babbar rigar da ya saka ita ta ƙara haskaka shi. Da sauri ya ɗauki key ɗin motar ya fice daga gidan. Kai tsaye suya spot ya nufa, bayan ya amshi kajin ya ƙarasa ya siya Yoghurt don yau ya ƙudirin faranta wa amaryar tasa, ya kuma yi aniyar buɗe mata Sirrin zuciyarsa la'alla ta tausaya masa ta kuma bashi damar nuna mata irin tarin don da yake mata, zai baje mata kolin soyayyarsa har sai ta karɓe shi.
Yana isa yayi horn, bayan gate man ya buɗe gate ya shiga, a parking lot ya daidaita tsayuwar motar daga nan ya fito hanunsa ɗauke da manyan ledodin guda biyu. Zuciyarsa ne ta fara bugawa da sauri sauri amma a haka ya nufi entrance na Parlourn, yana shiga ya rufe. Directly bedroom ɗin sa ya nufa, lumshe idanuwansa yayi yana zuba mata albarka, ya tabbatar yanzu ne yayi aure, gashi dai kullum cikin faranta masa take duk da irin tarin laifukansa gare ta, sai da ya ajiye ledodin ya dawo zuwa bedroom nata, a zaune a kan sallaya ya tarar da ita, bayan ta amsa sallamarsa ba tare da ya shigo ba ya ce mata “Ummul khairy ki same ni a bedroom ɗina”
Daga haka ya juya ya nufi bedroom ɗinsa, yana shiga ya cire babbar riga ya lanƙaye ta, sannan ya zauna bakin gadon. Da sallama a bakinta ta shigo, ya amsa mata fuska sake tare da miƙewa ya nufe ta, hannun ta ya riƙo ya zaunar da ita bakin gadon sannan ya ɗan ranƙwafo kanta yace “Yau na ke ango fah” yana wani kanne mata ido, kamar ta binne kanta haka ta ji don wata irin kunyarsa da ta dirar mata. Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Ita mamaki ma abun ya bata, mutum irin Hamma Zaki dama yakan rasa ta ido ne?, a duk tsawon lokacin auren su bai san lafiyarta ba sai cikin kwana biyu da ya gane zai fara mata rawar kai!.
Da kansa ya ɗauko jakar kajin, ya shimfiɗa wani lallausan abu kafin ya jiye, ita dai ido kawai take binsa da shi, ko da ya shimfiɗa kitchen ya nufa ya haɗo plates da kuma bowl ganinta zaune a yadda ya barta yasa yayi murmushi a ransa yace “Silly and classic girl”. Ajiyewa yayi sannan ya nufi toilet har zai shige ya juyo yace “Ki yo Alwala, I'll be waiting for you ”
Kamar wata wawuya ko maras fahimta ta koma, it's after some seconds ta fara comprehending abunda ta ji ɗin, miƙewa tayi ta wuce zuwa bedroom nata, tana shiga ta tura ƙofar tana Turo bakinta gaba. “Oh lallai maza ba su da kunya, na San dai Hamma ba so na yake ba, kawai ya karbi auren na ganin Ni ce zaɓin da aka masa, amma ina fan ya so ni ɗin kamar yadda nake addu'a, ganin zata ɓata ɓ masa lokaci kan zancen zuci ya ta nufi toilet, sai da ta watsa ruwa sannan ta ƙara shafa different perfumes sai suka bada wani daddaɗan ƙamshi. Kaya ta sauya zuwa nighties ta zumbula ƙatoton Hijaɓ ɗinta sannan ta nufi bedroom nasa tana mai fargaba duk da ta san me hakan ke nufi, ta karanta sosai bugu da ƙaro groups ɗin da su Ayrah suka saka ta yasa ta san abubuwa da dama. A hankali ta tura ƙofar da sallama a bakinta.
_kwana biyu kun jini shiru, I'm sorry wallahi bani da lafiya ne shiyasa, har ila yau kuma ina barar addu'o'nku na neman sauƙi wurin Ubangiji, nagode_
_Chttps://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““119&120”””
A ɓangaren Hamma Zaki ko da ya fita gidansa ya nufa, yana daidaita parking ya fito fuskarsa ɗaure kamar an aika masa saƙon mutuwa. A haka ya nufi entrance na Parlourn, kamar kullum yau ma dai haka yake, babu datti amma kuma babu ƙamshi kamar parlourn khairy, staircase ɗin ya haye tare da nufar bedroom nasa, locker ya buɗe ya ɗauko wani Memo 📝 Wanda ke haɗe da Biro ciki, rubutu yayi ya naɗe takardar sannan ya mayar da su yadda ya ɗauko daga haka ya fito ya nufi bedroom ɗinta.
Kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar, chatting ɗin da ta ke ta ajiye tana juyowa, da sauri ta diro ƙasa har tana shirin faɗuwa ta nufo shi.
“Gaskiya Sweetheart abinda kake baka kyautawa, ai ka ƙare kwanakin da zaka mata sai ka raba mana kwana amma sai ka kama hanya ka koma saboda rashin adalci...”
Tsawar da ya yi mata ne yasa ta risina jikinta har ɓari yake. Baby Humairah ma Dake bacci a cot ɗinta sai da ta Calla ihu.
Ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba ya ɗauko baby Humairah yana saɓa ta a kafaɗarsa nan tayi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba. Ita dai pretty ikon Allah yau take gani, uwa uba irin kwarjinin da ya ƙara mata yasa ta nutsu.
“Kina ji na ko?” ta ɗago ta kalle shi. “Tsawon rayuwar aure da nayi da ke kin cutar da Ni babu iyaka yayin da Ni kuma a koyaushe nake ƙoƙarin ganin na sauƙe nauyin ki da ke kaina” sai kuma ya dakata. “Nabila, nayi tunanin soyayyar da kike yi min ta tsakani da Allah ce shiyasa na ci gaba da zama da ke bayan fallasar zubar da ciki da kika yi wanda Ni ina da tabbacin ba nawa bane amma na haƙura na yafe Miki, daga ranar da hakan ta faru kuma ban ƙara zargin ki ko da sau ɗaya ba. Amma yanzu na matuƙar fahimtar ke ɗin wacece, kina so na ne don wani cikar burinku ke