Showing 57001 words to 60000 words out of 135404 words

Chapter 20 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46356

tayi ƙara, ba tare da tayi picking ba ta fice kai tsaye, gateman na sakin gaisuwa amma ko kallo bai samu ba sai ma tsarabar tsakin da ta bishi da shi.

Motar da pake a ƙofar gidan ta nufa, directly seat ɗin gaba ta buɗe ta shiga. Wani matashin saurayi ne da bai wuce 34years ba a ciki, baƙi ne mai ƙaton kai, bai cika kyau ba ga kuma sanƙo da yake da shi. Kallon shi Pretty tayi tana murmurshi tace
“Sugarplum nayi kewar ka tsawon week ɗin nan ban ganka ba”
Ɓata rai yayi yana maida hankalin shi ga tuƙin sa kafin yace “Ba wani nan, kinyi aure kin ma manta da Ni, kin barni da tsantar kewa da buƙatar ki, Please ki sama mana time don gaskiya Ni bazan iya ba”

Shu'umar dariya Pretty tayi sannan tace
“Baka da damuwa sugarplum, in dai wannan batun ne ka saka ranka a inuwa akwai wani shiri da nake mana”
Murmushi guy ɗin yayi yace
“Yauwa hotbabe na!”
Daidai wani katafaren gida yayi horn, bayan gateman ya buɗe mishi ya tura hancin motar zuwa ciki, parking yayi sannan ya fito ya zagayo ya buɗewa Pretty motar itama ta fito. Tun kafin su shiga gidan suka fara kissing junan su kamar wasu Mayu.
A parlourn suka yada zango nan suka cigaba da sheƙe ayar su daga haka nace bari na basu wuri.

(Sun shafe kusan hour guda tukun naji maganar su hakan yasa na shige domin ɗauko muku report).

Hannun su saƙale da na juna suka wuce bedroom ɗin tare da nufar Toilet,bayan sunyi wanka sun fito suka kimtsa sannan suka fito suna hirar su.
“Gaskiya hotbabe ki nema mana mafita, yanzu ma kawai na haƙura ne saboda kince kina da abun yi kuma baki so ya dawo yasan kin fita, but ki sama mana mafita”
“Nevermind sugarplum, yanzu me zan samu?”
Murmushi yayi irin nasu na ƴan duniya tare da ciro wayar shi yayi mata transfer na ₦500k daga nan yaja motar zuwa gidan Mami kamar yadda Pretty tayi mishi umarni.

Bayan sun isa tayi kissing nashi sannan ta fita, daga nan yaja motar shi ita kuma tayi ciki.
“Oyoyo Mami na” ta faɗa tana rungume mami dake zaune a kan kujera.
“Auta ta kinzo kenan”
Kwaɓe fuska tayi kamar zata yi kuka tace
“Ai Mami tun washegari naso zuwa ban samu dama ba”
Ido ta tsurawa ƴar tata tace
“Lallai Kam, hankalin ki kwance saboda burin ki ya cika kin manta da mami ko?”
Zaro ido tayi tace
“Habadai mami kullum kina raina, yanzu dai ba ma wannan ba akwai matsala!”
“Too matsalar me kenan?” mami ta tambaya
“Mami ina ga za'a ƙara yiwa guy ɗin nan aiki, wallahi ya cika tsauri da yawa, ni yanzu damuwa ta ma kawai ya ɗauko ƴan aiki yanzu ma na baro gidan duk datti, Ni kuwa ba iya gyarawa zanyi ba”
“Gaskiya kam kiyi masa magana ya nemo miki ƴan aiki tunda ko a gidan ku ba yi kike yi ba”
Kai ta jinjina tace
“Kallai Mami, captain Alee ya wuce tunanin ki, kinga yadda yake wani bani umarni kamar Daddy” ta ƙarasa tana yamutsa fuska.

Mami tace, “Kar ki damu auta, zanje gun bokan nan na ƙara samo miki magani ta yadda sai abunda kika ce” murmushi tayi tace “Yauwah Mami na shiyasa nake sonki, bari na wuce kafin ya dawo ya tarar bana nan”

[8/17, 6:12 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““59&60”””

Cikin hanzari suka rabu, yaja motar shi ita kuma ta shige ciki da sauri, taji daɗi sosai ganin Hamma Zaki bai dawo ba and dama bata yi expecting dawowar shi ba.

Salim Umar Baloli shine matashin da ya ɗauki Pretty, ɗa ne ga wani mai kuɗi a ESTATE ɗin su, kuɗin da yake ɓarar mata yasa ta amince da shi har suka ƙulla alaƙa.

Bayan ta cire kayan jikin ta ta saka wasu, sai ta tuna da cewa mami tace ta lallaɓa shi ya kawo mata ƴar aiki. Ɗan yamutsa fuska tayi sannan ta fara tattare parlourn, sama sama ta ɗan share and babu laifi dattin ya ragu.

Sai wajen 4:00pm Hamma Zaki ya dawo gidan, ba tare da ya duba ta ba kamar yadda ya fara a farkon aurensu ya ajiye abincin da ya dawo da shi kan dining daga nan ya wuce zuwa bedroom nashi. Wanka yayi sannan ya sauya kaya ya fito. Sai a lokacin ya tuna ashe fa yana da mata, cikin rashin son zuwa ya nufi bedroom ɗin ta.

Chat take a wayar ta sai dai ƙamshin turaren shi ne ya sanar da ita shigowar shi. Da gudu ta miƙe tayi hugging nashi.
“Oyoyo Sweetheart, ka dawo”
Bai ce komai ba sai ma zame ta da yayi daga jikinsa.
“Ga can abinci a dining”
Kuka ta saka mishi wai don me iya abinci zai nuna mata bayan ta riga da tayi missing nashi. Kukan mace da baya so a rayuwar shi yasa ya ɗan riƙe ta. Cikin nuna kulawa yace “Alright nayi laifi yanzu dai kici abinci sai muyi magana”

Bayan sun ci abinci tace
“Sweetheart ina buƙatar Ƴar aiki to keep the house clean, yanzu ma kana complain akan datti Allah da ƙyar na gyara parlourn nan”
Cike da mamaki yake kallon ta wai ta gyara parlourn, parlourn da ko alamar gyara bai gani ba, lallai ma ƴar nan ta raina shi, amma zai saita ta ne.
“Shikenan yanzu me kike so ayi?, Ni bana cin girkin Ƴar aiki ko a gida Mom ke dafa abincin da nake ci”
“Ni dai gaskiya ka nemo, in yasa kai sai ka cigaba da shigowa da naka”

Maganartata ta matuƙar bashi mamaki, irin wannan halin ko in kula da take nuna mishi yasa kawai yayi shiru.
“Kayi shiru Sweetheart”
“Ok ki nemo”
Rungume shi tayi tace
“Thank You my love, I love you”.

*ƳAR IYA POV*

A hankali ta fara buɗe idanuwan ta da suka yi mata nauyi har ta buɗe su gabaɗaya suka sauƙa a kan fuskar Nenne dake zaune a kujerar dake side ɗin gadon.
Ganin ta buɗe idon yasa Nenne farin ciki, da sauri ta miƙe tayo kanta.
“Kin farka?, Sannu sannu bari a ƙira likita”

Ita dai Ƴar Iya da kallon mamaki kawai take bin Nenne har ta fice daga ɗakin. Tunanin ta ne ya dawo, ta tuna ta shiga Mota daga nan kuma motar tayi ta buguwa. Tunanintaa ne ya katse Saboda shigowar doctor sai Nenne dake biye da shi.

Cikin sakin fuska Doctor ɗin ya ƙaraso bakin bed ɗin tare da taɓa wuyan ta da goshin ta, jin babu zafi yasa ya fara mata magana cikin kulawa.
“Ya jikin naki?, Me kike ji yanzu?”
Kai kawai ta girgiza masa saboda wani irin farin ciki da ya lulluɓe ta lokaci guda. Cikin ranta tace
“Shikenan na zo birni yanzu kam, wayyo daɗi” ta faɗa tana sakin murmushi yayin da Nenne ke murmushin itama. Bayan Doctor ya tabbatar tana cikin hayyacin ta kuma babu wani abu dake damun ta a wannan hali yasa ya fice. Nurse on duty ta shigo ta gyara mata shimfiɗa sannan ta tallafa mata ta shiga toilet, toilet bath tayi mata, tare da oral care, bayan nan ta tallafa mata suka fito daga bayin, daga nan kuma tace a bata abinci.

Nenne da kanta tayi feeding Ƴar Iya sai dai ta sha mamaki kamar ba maras lafiya ba, tas duk girman warmer ɗin ta cinye abincin cikinta.

Bayan ta ƙoshi aka bata Nutri-milk ta kora da shi. Ciki ya ɗauka sai Ƴar Iya ta fara murmushi.

Yarinyar ta burge ta, gata kyakkyawa ce sai dai daga gani daga ƙauye ta fito ko gidan masu ƙaramin ƙarfi.

Tunanin Nenne ya katse ne sakamakon ihun da Ƴar Iya ta fara
“Wayyo Allah na, ina jaka ta da kuɗaɗe na, wayyo shikenan nikam”
Da sauri Nenne ta ƙarasa wurin ta tana riƙe ta tare da tallafa bayan ta tana tapping bayan.
“Ki shiru maza, kinga baki da lafiya”
Samun kanta tayi da gyaɗa kai tace
“Toh jaka ta ban ganta ba, kuma akwai kuɗaɗe na da yawa har da wanda Arɗo ya bani da zan taho”

Arɗo da Ƴar Iya ta ƙira yasa Nenne faɗin kenan bafulatana ce cikin ranta. A zahiri tace “Kar ki damu Ni inada kuɗaɗen da suka fi naki yawa, ki nutsu zan baki in Zaki tafi”
“To kawai Ƴar Iya tace.
Nenne tace “Yaya sunanki?”
“Suna na A'isha amma Ƴar Iya shine sunan da ake kirana da shi”.

“Ashe takwarar Granny CE, Masha Allah. A wane gari kike kuma?”
Cikin burus tace
“A Gallara nake, amma na baro can ɗin ne gabaɗaya saboda ina son birni, ina so nake saka kaya irin nakin nan, nake kwalliya kuma na zama mai matsayi” ta ƙarasa yayin da ƙwalla ke zubo mata.
Cike da tausayawa Nenne tace mata
“Kina son zama da Ni?, Zaki zauna a tare da Ni?”
Kai ta gyaɗa tace “Eh zan zauna”
“Shikenan zaki ke iya ƙira na da Nenne, ina da yara da kuma ƴan uwa sosai. Zamu koma can da zama, amma kimin alƙawarin zaki zauna lafiya da kowa”
“Eh Nenne”
Murmushi Nenne tayi daga nan ta bata labarin hatsarin da suka yi da yadda ya faru. Cikin ƙanƙanin lokaci alaƙa ta ƙullu tsakanin Ƴar Iya da kuma Nenne, Ƴar Iya najin cewa wannan matar ta cancanci zama uwa gare ta tunda yanzu babu Iya.

Ba'a jima ba Doctor yayi discharging nasu. Uncle Suraj Nenne ta ƙira ta sanar dashi, yace su wuce gida kawai. Babu musu suka wuce cikin motar da Nenne tazo da ita.

Tun a bakin Gate Ƴar Iya ta saki baki da hanci tana kallon gidan, cikin ranta tana faɗin “Aradu na huta, na kusa zama ƴar gayu nima”. Bayan sunyi parking Nenne ta fita, sannan ta buɗe side ɗin da Ƴar Iya take tare da janyo hannun ta suka fito. Part ɗin ta ta wuce da ita, lokacin babu kowa su Najma duk suna Islamiyya.

Bayan sun shiga Nenne taja hannun Ƴar Iya tace “Muje ki gyara jikin ki, ranar Saturday sai muje a gyara muku jiki tare da su Najma” ba tare da ta Musa ba tabi Nenne. Toilet ɗin su Najma ta kaita, tare da nuna mata yadda zata yi wankan, ta nuna mata brush da MacLean ta nuna mata yadda zata yi daga nan ta fice. Ita dai mamaki duk ya cika ta wai nan ne bayi?, “To a can ai babu komai kawai kewaye wurin aka yi da zana sai ramin shadda”

Mintuna 30 ta kwashe tana zuba ƙaiyancin ta, thank God ma ita kaɗai ce, Nenne dake zaman jiran fitowar ta taji shiru. Daidai door ɗin ta saka kanta tace
“Baki gama wankan bane?”
Sai lokacin ta tuna wanka fa aka ce tayi, cikin wata irin murya tace
“Nenne bana iya amfani da abubuwan”
“Bari na zo na koya miki”

Nenne da kanta tayi wa Ƴar Iya brush, duk irin damɓare damɓaren dattin da ya fita bai sa haƙwaren fita tas ba, ƙara wanke nata tayi sosai, lokaci guda suka fita kamar ba dai Ƴar Iya ba, har da su mouthfresh aka fesawa Ƴar Iya, ita dai ikon Allah kawai take kallo. Bayan nan Nenne ta sunce towel ɗin da ta ɗaura mata tare da ajiye shi, tas ta wanke Ƴar Iya tana mamakin irin dattin dake jikin ta, gashin kanta kuwa kasa gyara shi tayi tace sai sunje wurin wankin kai.

Bayan sun gama Nenne ta ɗaura nata towel ɗin tare da jan hannun ta zuwa bedroom ɗin ta, tas ta shirya ta, mayuka daban-daban ta shafa mata, powder sannan ta shafa mata wetlips a pinkish leɓen ta.

_Ƴar Iya Fans in kun ganta ba zaku gane ta ba_

Wata doguwar riga Nenne ta saka mata sannan ta saka mata hula. Masha Allah kawai nace tayi kyau kamar ba ita ba.

★★★★★★★★

Motar ce tayi packing a dai-dai parking space. Bayan ta tsaya gabaɗayan su suka fito kowa suka nufi sashen su.
A parlour Fauzah ta tarar da Mom tana aikin nata da ta tsiro na tunani.
Ɗauke da sallama ta shiga sai dai Mom ko sallamar bata ji ba.

A gefenta ta zauna sa'annan ta ɗaura hannun ta a kafaɗar Mom ɗin. Sai a lokacin Mom ta dawo daga duniyar da ta faɗa.
“Mom wai tunanin me kike yi ne haka?, Har fa na shigo baki san na shigo ba” ta faɗa cike da shagwaɓa.
Murmushin da bai kai zuci ba Mom ta sake tare da hugging nata
“Sorry Daughter Ina tunanin Hamman ku ne, gabaɗaya yanzu ya fara mancewa da mu, 2days kenan bai neme Ni ba” ta ƙarasa cikin sigar da ke nuna tsantsar damuwa.
“Kiyi haƙuri Mom kina yiwa Hamma Zaki addu'a, tunanin bashi da amfani.”

Sanyi Mom taji a ranta saboda ƴar maganar da suka yi da Fauzah.
“Oya fresh up muje wurin Granny ko?”
“Toh Mom”

Bayan Fauzah tayi wanka ta biyo bayan Mom, tare suka jera har suka isa part ɗin granny. A can suka tarar da Mommah da Ƴaƴanta ammah Nenne bata nan.

Sai wajajen maghrib suka watse kowa ya wuce, Fauzah ta cewa Mom bari taje wurin Yesmeen ne. Daga nan Mom ta wuce zuwa part ɗin ta.

A nan suka yi salla, bayan sunyi suka kafa dandalin hirar su wanda duk sun kafa ta ne a kan Shagalin da zasu yi a JSSCE nasu.
Har aka yi Ishã suna can sai da suka yi Najmah ta ƙira su suzo suyi dinner.

Idon su ne ya sauƙa kan Ƴar Iya da ta make a ƙasa tana harba lomar dambun couscous da ke gaban ta yayin da idon Nenne ke akanta tana sakin murmushi. Mamaki da kuma tsoro ne suka dira cikin zukatan su lokaci guda su basu ƙaraso ba kuma basu koma ba, ita kuwa wacce suke abun a kanta bata ma san da su ba.

Har ta gama cinyewa Allah bai basu ikon koda kuwa motsawa ba. Tana cinyewa ta ɗago da kanta, sai a lokacin idonta ya sauƙa kan kyawawan Ƴanmatan da ke tsaye suna kallon ta, lokaci ɗaya ta fahimci kallon tsoro suke mata. Murmushi ta sake sai da dimple nata ya bayyana. Kallon ta ta mayar kan Nenne da ke aiko mata da murmushi.
“Nenne na cinye,”
Nenne tace
“Ti kice alhamdulillah”
Ɓata fuskar tayi ƙasa-ƙasa tace
“Alhamdudillah”

Dariyar su Najma ne ta sa ta dawo da duban ta gare su, sai kuma ta marairaice fuska tana kallon Nenne.
Harara Nenne ta aika musu tana faɗin
“Kar ku saka min yarinya a gaba, ku bani waje in ba zaku ci abincin ba”
Wani iri suka ji hakan yasa suka ƙarasa a sukwane zuwa dining ɗin suka zuba abinci suka fara ci.


Ƴar Iya ta dubi Nenne tace
“Nenne ku dukan ku masu kyau ne, waɗannan Ƴan gayun su ma ƴaƴan ki ne?”
Murmushi Nenne tayi tace “Bari su gama ci sai na faɗa miki su waye ne”
Kai kawai ta gyaɗa taci gaba da kallon ƙauyen ta a parlourn.

TO FAH, ƳAR IYA A NAIRA FAMILY, KO YA KUKE TUNANIN WASAN ZAI KAYA? KUCI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND BHATOOL DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA.

MUCH LOVE MY ESTEEM FANS
COMMENT & SHARE FISABILILLAH!


[8/17, 6:17 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““61&62”””

_Afwan masoya bayan wani dogon zango In Sha Allah yau na ɗaura alƙalami na kuma bana jin zan sauƙe sai na kammala muku wannan littafi, COMMENTS ɗin ku kawai nake so, ku taya ni SHARING kowanne update ta haka zan ƙara tabbatar da ƙaunar ku gare ni, Ina son ku irin loadi-loadin nan_💃🤩❤️

Bayan Najmah sun kammala cin abincin su, duka suka kwaso jiki suka dawo parlour, bisa lallausan carpet ďin dake shifide a parlourn suka zube tare da maida hankulan su kan Yar Iya da kuma Nenne.
Cikin karfin hali Najmah tace
“Nenne ina kika samo wannan?”
Harara Nenne ta jefa mata kafin tace
“To uwar tambaye-tambaye ban sani ba”
Marairaice fuska tayi tana faɗin
“I'm sorry Nenne an, kawai ta bani dariya ne, kiga fa yadda take cin abinci” ta faɗa cikin sigar zolaya. Ayrah da bata ce komai ba tunda suka dawo parlourn ta kece da wata irin dariya
“Kai Adda Najma, itama fa mutum ce”

Ran Nenne ne ya fara ɓaci da tsiyar da suke tsulawa hakan yasa ta daka musu tsawa “Is ok, bana son sakarcin banza, ku baku iya mutunta ɗan Adam bane?” ta jefa musu tambayar da ta saka lokaci ɗaya jikin su yayi sanyi. Cigaba da magana Nenne tayi
“Ahalinku sun san ƙimar mutane saboda haka bana son na ƙara gani ko jin makamancin abinda kuka yi yanzu not only to her but to anyone, ok?”

Gyaɗa Kai su duka suka yi yayin da Najma tace “Kiyi haƙuri Nennen mu ba zamu ƙara ba”.
Murmushi tayi musu sannan ta ɗora da
“Ban san ko a nan A'isha zata zauna ba, idan zamanta a nan ɗin ya tabbata ku shirya ɗaukar ta matsayin ƴar uwar ku. Kun gane”
“Eh Nenne” suka bata amsa. Daga haka bata ƙara ce da su uffan ba ta mayar da duban ta zuwa ga A'isha. Bata ga alamun rashin jin daɗin abinda suka yi mata a fuskar ta ba amma sai da ta bata haƙuri a kan hakan.

Cike da mamaki nake duba A'isha da tayi murmushi tace
“Babu komai Nenne, nima Iya ta da kuma Baffi na suna yawan cewa na koyi haƙuri saboda bani da shi kuma ban sanshi ba, amma yau sai naji na fara shi”
Dariya kaɗan Nenne tayi tace “Ai kuwa Iya sun kyauta, haƙuri yana da kyau sosai cikin rayuwa” kai ta gyaɗa alamar gamsuwa yayin da Nenne ke ƙara nazartar A'isha. Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauƙe jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login