Showing 18001 words to 21000 words out of 135404 words

Chapter 7 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46379

ba ya fara masa bayani.
“Baba gaskiya kazo ka ɗauki ɗiyar ka don ba zamu ci gaba da zama da ita a nan ba, hak kawai a yau ta illata fiye da mutane bakwai”
Baffi yace
“Ka dubi darajar Allah Misbahu, duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, kada laifin ta yasa aikin ladan da kayi niyyar yi ya wargaje”

Da ƙyar dai Baffi ya shawo kan Principal ya amince Ƴar Iya ta ci gaba da karatun a makarantar.


★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Cikin ƙanƙanin lokaci Ƴar Iya ta yi sabo da Ajiram, ƴan room ɗin su kuwa mamaki suke yadda Boss ɗin nan ke taɗi da Ajiram.

Lokacin Sallah nayi Ajiram ta saka Ƴar Iya gaba kan su je suyi sallah.
“Hamrah, tashi muje muyi salla”
Da kallon mamaki Ƴar Iya ke kallon Ajiram tana tuna wai ma meyeh sallar ne. Ƙara maimaita mata tayi
“Ki tashi muje muyi sallah”
“Bana yi” abinda ta tsinci Ƴar Iya na faɗa.
Zaro ido Ajiram tayi, na ta saka ta gaba ala dole sai sun je sun yi. Yadda take threatening Ƴar Iya yasa ta miƙe ta bita.

Da ido ta bita gani tana alwala, ita fa bata taɓa yin salla ba tunda Innar ta haifeta. Haka dai ta jiƙa fuskar ta da hannun ta matsayin Alwala. Bayan sunyi suka wuce mosque don yin sallah. Ƙememe Ƴar Iya tayi ita wallahi bata iya ba kuma bazata yi ba. Da Ajiram ta takura mata sai ta fashe da kuka.....


JAMA'AH KUN JI MUTUNIYAR YAU HAR DA KUKA??
TO AKWAI ƘURA FA!
MENENE SILAR FARA SAUYUWAR ƳAR IYA?
A TUNANIN KU SAUYI NE YA FARA SAMUWA?
ANYA ƳAR IYA ZATA IYA KARATUN NAN???
MUJE ZUWA ƳAN AMANA KU CI GABA DA ZUBO COMMENTS INA ZUBA MUKU UPDATE!

Oum Zainab ce😍💋💫
Garkuwar Nazari Writers.


[5/1, 1:14 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*








__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA ‘‘‘‘‘19&20’’’’’

Da Ajiram ta takura mata sai ta fashe da kuka. Ganin hakan yasa ta ƙyale ta tare da ɗumbin tambayoyi a ƙasan ranta.

Yinin ranar haka ya Ƴar Iya ta shafe shi tare da sabuwar ƴar uwarta Aunty Ajiram ba tare da ta ƙara shiga sabgar kowa ba.

★★★★★★★★★★★

*ALEE POV*

A nutse ya koma part ɗin su ganin Sarah a parlourn duk sai yaji gidan ya fita a ranshi. Sarah ɗiyar uncle ɗin shi ne haka kawai yarinyar bata burge shi musamman saboda rashin kamun kai irin nata. Har ya juya zai koma part ɗin Nenne tunda can akwai extra room da aka ware don shi kasancewar shi ɗan ɗakin ta.

Step ɗaya yayi ya jiyo Muryar Daddy da a lokacin ya fito daga bedroom ɗin Mom.
“My son Ina kuma zaka je?”
Babu yadda ya iya haka ya juyo yana sakin murmushin yaƙe don sam baya son ganin Sarah.
“Sweet Daddy zanje mu gaisa da Granny ne, I don't even know u're back”
Ya faɗa tare da shigewa parlourn. Side hug yayi wa Daddy tare da manna mishi peck a kumatu.

Ita dai Sarah idon ta ƙyam akan Yaya Zaki ganin irin wani kyau da ya ƙara ga kuma girma da ya ƙara yi a zuciyar ta take faɗin har ya so ya fi yayan nashi ma girma. Ganin yayi wa Daddyn shi peck yasa ta saki wani murmushi, kiss is normal to her tunda su gaisuwa da kowa in zasu yi haka suke a India to ammah wannan ɗin yafi burge ta musamman da taga Daddyn nashi Nigerian ne amma kuma wayayye. Ji take kawai ina ma ita ta samu wannan dama Yaya zaki ya sumbace ta.

“Baka ga Sarah bane, jiya tunda taji labarin ka dawo Nigeria ta bi ta dame su sai da suka barta ta taho nan, she'll stay with us sai ka tashi tafiya ita ma ta koma”
Ran shi ne ya ɓaci a lokacin, don meyasa zata zo saboda shi, shifa ya tsani mutum maras kamun kai more especially mace.

“Good morning brother” faɗin Sarah tana wani smiling as if tana tare da boo nata ne. Banza yayi mata sai ma ƙara haɗe fuska da yayi.
“Kayi shiru son, ain't u happy to see her here?”
Sai a Lokacin yayi murmushin gefen baki wanda ba lallai ka fahimci yayi shi.
“I am” kawai yace tare da miƙewa.
“Son....wait where are u heading to?”
Narkar da face nashi yayi kamar wani ƙaramin yaro saying
“Zan je na gaisa da Granny kafin tace na zo banje ba” ya ƙarashe cike da ƙosawa. Coz shi bai son yin magana a gaban yara musamman wannan good for nothing cousin sister ɗin tashi.

“Alright son, we'll have time da dare coz I'll be attending Quranic Memorization walimah of a friend's daughter, and gobe da safe ina son zuwa Bauchi.
Murmushi Yaya zaki yayi tare da kissing Daddy a cheek daga nan ya fice ya bar Sarah Baki a wangale.

Directly part ɗin Nenne ya wuce bai tarar da ita a parlour ba kawai ya wuce kai tsaye izuwa bedroom nashi na part ɗin.

Wayar shi dake aljihun jallabiyar ce tayi ƙara, da sauri ya fito da ita yana kwantawa bisa makeken bed ɗin shi. Picking call ɗin yayi ya kars a kunnen shi.
Daga ɗaya ɓangaren aka yi sallama kafin ya amsa
“Buddy ba kada kirki ko kaɗan, yanzu har ka shigo Nigeria bazaka sanar da Ni ba ehh?, Ka kyauta”
A hankali cikin Muryar sa ta jaruman maza yace
“Sorry Man, ɗazu isowa ta gida and na so kiran ka sai na manta”
Kamar an sa shi dole haka yayi maganar.
“Alright zan shigo zuwa yamma”
“Ohk” daga haka bai jira me za'a ce ba ya katse ƙiran.

Yusuf da ke office nashi a asibiti ya janye wayar daga kunnen shi yana ƙare mata kallo cike da mamaki ya furta
“He'll never change, zan so naga lokacin da zaka faɗa soyayya, u'll suffer” ya faɗa yana cije leɓe.

Yusuf kenan, aminin Hamma zaki ne, Abbien Yusuf abokin Daddy ne ƙut da ƙut haka Amma maman shi suna shiri da Mom sosai. Unlike Hamma Zaki Yusuf mutum ne mai fara'ar gaske ga kuma kirki uwa uba barkwanci irin nasa. Ta yadda halayen su ya banbanta kenan sai dai duk da haka suna matuƙar ƙsunar junansu.

Bacci ne ya ɗauke Hamma Zaki ba shi ya tashi ba sai around 11:30am. Toilet ya faɗa ya wanko fuskar shi ya dawo. Wayar shi ƙirar Samsung Galaxy S24 ya ciro wacce tunda ya diro Naija ban ga yayi amfani da ita ba. WhatsApp ya shiga don ganin messages ɗin da ya tara. Yana kunna data kuwa suka fara zubowa kamar babu gobe, ganin sunyi yawa yasa ya ajiye wayar. Kusan 10 minutes messages na shigowa tukun ya ɗauki wayar don fara reply.

Daga can ƙasa Hamma Saleem me yayi mishi magana, “Hi brother, please when you're going home text me so that I can book flight to spend the holiday with u”
Emojij surprise ya tura sannan yayi typing “Sorry Dear, I'm already home, banga ni da wuri ba”.

Haka yayi ta replying messages ɗin da yaga suna da muhimmanci saurann kuma yayi ignoring coz mostly Ƴan mata ne ke mishi safe journey sun ƙira wayar shi bata tafiya, wasu kuma neman soyayyar shi suke yi. Shi har mamaki yake yadda mace zata zubar da mutuncinta ta tunkari namiji wai tana son shi abun haushin ma wasun kamar Mayu...duk da baya buɗewa bare ya gani amma yakan ga subject ɗin.
Tsaki yayi shi kaɗai jin hayaniya kamar ana faɗa.

Rashin son hayaniyar yasa ya fito saboda ya koma part ɗin su. Karo da Najma yayi tana bugun Yesmeen wai tayi mata rashin kunya, ita kuma duk dukan da tayi mata sai tayi Allah ya Isa.

Duk tsiyar da suke shukawa basu san ya dawo gida ba sai da suka ji mayetaccen ƙamshin sa. Kamar a mafarki da haɗin baki su duka biyun suka juyo. Ganin shi tsaye bakin ƙofar bedroom nashi yasa suka fara Ƴan kame-kame.

Najma da ke son kuɓutar da kanta ko gaida shi bata yi ba ta fara
“Eh...am...eee....damah Haa...ha...mma...za...ki Yesmeen....ce..ke...ja...min Allah ya isa wai don sunyi faɗa ita da Fauzah a mota na duka su.”

Itama Yesmeen don son kuɓutar da kanta daga wahalar Hamma Zaki ta buɗe baki tana sakin hawaye.
“Aaah Hamma Zaki ƙarya Adda Najma take ban zage ta ba.”

Sai da ya samu waje ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake parlourn ya ɗago yana kallon su. Irin kallon da yake aika musu yasa Yesmeen risinawa ta gaishe shi.
“Good afternoon Hamma zaki”
Da sauri Najma ma tace
“Good afternoon Hamma”
Kamar ba zai yi magana ba coz ko gaisuwar bai amsa ba yace
“Be on your kneels”

Ba shiri suka zube, nan da nan su duka suka fara hawaye don sun saddaƙar yau sai kashin su ya bushe wurin Hamma Zaki.

Maimakon ya hukunta su ma wayar shi ya ciro yana dialling number Hamma Saleem.
“Assalamu Alykum”
Fuskar nan tamke haka yayi wayar har ya gama suna zube a kan guiwowin su. Gashi sun matuƙar gaji ga yunwa uwa uba kuma zuwa Islamiyya su ƙara tarar da dukan Ustaz Umar.

Nenne ce ta fito daga kitchen ɗauke da warmers ta fara jerawa a dining, kamar daga nesa ta hango shi da sauri ta fito, ganin Najma da Yesmeen durƙushe yasa ta juya ko ba komai yanzu zata samu salama tunda dodon su ya dawo, rashin kirkin su dole zasu daina.

Sai da ta gama jera komai ta dawo parlourn, bata ko kalli inda suke ba ta wuce sama ɗon ta samu tayi wanka. Har ta fito suna nan yadda ta barsu shi kuwa Hammma Zaki wayar shi ma yake dannawa.

Murmushi Nenne tayi tare da ƙarasawa gefen shi,
“Damah kana nan ne yaushe ka shigo ko tun zuwan ɗazu baka fita ba”
“A'ah” kawai yace daga nan yayi shiru. Ita ma Nenne bata sa a ranta zata ji wani amsan ba bayan wannan.
“Son, food is ready”
Daga haka ta juya zuwa dining.

Kallon su Hamma Zaki yayi yace
“Ku je kuyi LUNCH in kun dawo daga Islamiyya ina neman ku” daga haka ya wuce dining ba tare da ya ƙara bi ta kan su ba.

Da ƙyar suka miƙe hawaye da majina shaɓe-shaɓe a fuskar su har abun tausayi,suna ɗingisawa suka ƙarasa bedroom ɗin su, sai da suka yi wanka suka sanya uniform ɗin islamiyya suka taho dining ɗin. A lokacin Nenne ma ta wuce bedroom haka Hamma Zaki ya fice.

Yana fita gym room nashi ya wuce coz yana da tabbacin yanzu suke dinner a part ɗin su and he don't wanna see that creature. Ta ƙofar baya ya shiga bai fito ba sai bayan 1hour, yana fitowa jikin shi duk gumi ya wuce part ɗin shi.

Wanka yayi ya shafa mai sannan ya sanya wasu light T-shirt da Trouser sannan ya fesa turare daga nan yayi sallah ya kwanta.

Ɓangaren Najma da Yesmeen a duddurƙushe suka ci abincin don ba ƙaramin jin jiki suke ba gashi ita ma Nenne ko ci kanki bata ce musu ba.

Bayan sun ci abinci suka fito wanda yayi dai-dai da fitowar sauran but wannan karon har da Ayra. A cikin motar kuwa duk sun yi wani iri da su, damuwar su basu san wani irin hukunci zasu karɓa daga Yaya Zaki ba.

Fauzah ce ta kalli Yesmeen tare da ƙare mata kallo.
“Yesmeen ya naga kin yi wani iri, ɗazu mun rabu ƙalau ko baki iya haddar Ustaz Umar ba ne?”
Cike da jimamin abunda ya faru da su ta kalli Fauzah tana kwaɓe fuska ga wani hawaye da ya zo mata. Dukkan su hankalin su suka mayar kanta banda Najma da ta san MEH ya faru. Duk jira suke suji me ya samu talkative Yesmeen ɗin su.

“Kun san cewa Hamma Zaki ya zo?”
Abun da ta fara faɗa masu kenan. Idanuwan su suka fara zarewa take fuskar su ta bayyanar da ainihin tsoron da ke tattare da su. Ganin basu sani ba yasa ta fara basu labarin abun da ya faru da su.
“Yanzu ma yace in mun dawo daga Islamiyya muje...Ni....baaaaan san wani hukunci Hamma Zaki zai ƙara bamu ba, kin san tun dukan da Adda Najma tayi mana ɗazu shi ya jawo? ”

Ta ƙarasa wani hawayen na zirarowa daga idanuwan ta, tausayi ta Basu coz duk sun san waye Yaya Zaki, sun san irin punishment ɗin shi.

Haka suka ƙarasa islamiyya kowa bai jin daɗin ranshi...su ma da basu da appointment da shi sun maida hankali saboda tsaro.

Mom da tun ɗazu take jiran shi ya dawo suyi dinner shiru shiyasa tace ma Sarah tazo tayi nata.

Ƙarar wayar shi ne yasa ya fara juyi alamun baccin bai ishe shi ba. Laluɓo wayar yayi yana picking ido rufe tare da kara ta a kunnen shi.
“Hello Buddy, muna kan hanya ni da Sameer da Faruq.”
Cikin Muryar bacci Yaya Zaki yace
“Alright sai kun zo”
Jin alamun bacci yake yasa Yaya Yusuf ƙara cewa
“Buddy, Are u asleep”
“Uhm kawai Hamma Zaki ya iya furtawa”
“Please wake up now, ka ma yi sallah ne?”.
Cikin baccin da ya fara sakin shi yace a'a I'm about to”
“Oyah tashi manah, it's almost past four”

Sallama suka yi Hamma Zaki yayi hanging call ɗin.

Wanka yayi daga nan yayi sallah, yana idarwa ko gama kimtsawa bai yi ba wayar shi ta fara ringing.
“Buddy, we're here...ka zo ka shigar da mu”
“Idan gidan baƙon ka ne ka zauna a yadda kake bayan ka nuna wa sauran hanya.” daga haka yayi hanging call ɗin yana tsaki.

Sun jima tare da su Yaya Yusuf, Barr. Sameer, da kuma Dr. Faruq. Sai wajajen maghrib suka fice tare zuwa masjid daga can suka wuce.


[5/1, 1:16 PM] 💎Diamond Bhatool💎:


🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*








__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA ‘‘‘‘‘21&22’’’’’

Sai bayan ya dawo daga masallaci su Fauzah suka zo yi mishi Barka da dawowa tare da sauran yaran gidan.

A lokacin yana zaune a sofa dake parlourn, ɗauke da sallama a bakin su suka shigo. Ƙasa-ƙasa ya amsa sallamar tasu ba tare da ya ɗago ya kalle su ba sai ma hankalin sa da ya mayar ga system ɗin dake gaban shi.

Ƙasan lallausan carpet ɗin dake shimfiɗe a parlourn suka tsuguna yayin da Hamma Zaki bai ma nuna ya sa su ba neh.
Fauzah ce tayi ƙarfin halin faɗin.
“Ina yini Yaya ka iso lafiya?”
Banza yayi da ita ammah hakan bai sa sauran buɗe baki su maimaita abun da ta faɗa ɗin ba saboda sarai sun san halinsa, tsab in suka yi shiru suna jiran amsar yace zai hukunta su. Dukkan su miƙewa suka yi a sukwane zasu wuce suka ji gyaran Muryar shi. Nan suka dawo suka zube kamar bayi a gaban sarki.
“Wa ya baki izinin tafiya?”
Rarraba idanu suka fara wannan ta kalli wannan sai su sunkuyar da kai ƙasa.
“Kayi haƙuri Yaya Zaki”
Ayrah ta faɗa a tsorace. Wani irin kallo da yake bin su da shi yasa suka ƙara shiga taitayin su.
“Yaya ko?, Haven't I warned u several times ku daina ce min Yaya?, Idan bazaku kira Ni da yadda yare yace a faɗa ba U better keep ur dirty mouths shut, ohk?”
Duk wannan jawabin yana yin sa ne cikin harshen fulatanci, nan da nan na ƙara jin ya fi burge Ni fiye da da.

Kawunan su suka ɗaga tare da faɗin
“Toh Hammah Zaki”
Banza yayi da su can yace
“Better”.
Sun share fiye da mintuna 30 a zaune ba tare da yace su tafi ba su kuma suna tsoron tafiya ya hukunta su. Duk zaman nasu gashi ya takura shi can ya ɗago yana musu alama da hannu da su tafi.
Tsam suka miƙe suka wuce banda Najma da Yesmeen da suke durƙushe still.

Lokacin su da suka ga yana ƙurewa yada Najma yin ta maza tace
“Hamma Zaki ɗazu ka ce mu zo mu same ka Ni da Yesmeen”
Har sai da ta cire ran tankawar shi taji yace.
“Kuna ji na koh? Ke Yesmeen bana son rashin kunya kina ji?”
Kai ta ɗaga sannan can ya ci gaba “Idan kika ƙara yi wa wanda ya fiki Allah ya isa to ranar Ni da ke a gidan nan.”
Kamar wanda aka sa dole ya ɗanyi shiru na wasu mintuna dan ba ƙaramar jarumta yayi ba, har kan shi ya fara sarawa.
“Ke kuma Najma banda cin zali kina ji na?, Idan anyi miki abu ki kai ƙara ba ki ɗau hukunci a hannun ki ba, ohk?”
Kai suka kaɗa suna faɗin “Eh”
Daga haka ya musu alama da su wuce.

Ya jima zaune a parlourn yana aiki a nutse cikin system nashi, har lokacin da Sarah ta leƙo ta gan shi.
Komawa tayi tare da sheƙa wanka ta sanya wasu nighties masu bayyana jiki, sai da ta fesa turare mai uban yawa ta fito. Tray ɗin abinci ta haɗa masa tayi sama sai ɗakin shi.

Lokacin da ta shiga ya fito daga wanka daga shi sai bathrobe sai kuma towel ɗin da yake goge sumar shi. Kallon da ya aika mata yasa tana ajiye tray ɗin ta fita da sauri. Shi kuwa Hamma Zaki duk ranshi ya gama ɓaci, shin wai duk mata haka suke ne?, Basu da kamun kai gabaɗaya?, If yes to su sani shi babu budget ɗin aure ma a rayuwar shi. Bai taɓa ko da hasashen kan shi a matsayin wanda zai yi aure ba.

(Nace ayi dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login