Showing 30001 words to 33000 words out of 135404 words

Chapter 11 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46376

tabbatar Baba Haro baya nan suka ɗale bishiyar kashu tare, suna tsinkowa suna ɗaurewa cikin kwalayen su. Da yawa suka tsinka sannan suka sauƙo suka ajiye ƙullin a gefe.

Basu tsaya ɓata lokaci ba suka hau bishiyar mangwaro. Tun akai suke Sha in sun sha sai su wullo ƙasa.

Suna cikin haka ko tarawa basu yi ba Baba Haro ya shigo lambun. A dai-dai lokacin ne kuma Ƴar Iya ta wullo ƙwallon mangwaron da ta lashe shi har ya zama fari sol.

Bai yi aune ba kawai yaji ƙwallon mangwaro akan sa. Duk tunanin shi irin wanda jemagu suka sha ne shi yasa bai samu ya duba ƙwallon ba.

Ba zato babu tsammani yaji wasu ƙwallayen har biyu da suka iso kan sa lokaci ɗaya.
“Ashh" ya furta tare da sunkuyawa ƙasa. Arba da lasassun ƙwallayen yayi ai kuwa ya ɗaga kai sama. Mutane biyu ya gani kan bishiyar mangwaron. Nan ya fara musu magana kan su sauƙo.
“Ku sauƙo yanzu ko na hawo na ci ubanku”
Dariya suka kwashe da ita Ƴar Iya tace
“Kaji tsoho da wani zance, har ya bani dariya...hhhhhhh..to ka hau ɗin mu gani ina zaka iya”

Haushi ne ya cika Baba Haro Jin Muryar yarinya tana masa baɗala a bishiyar da ke cikin lambun sa.
“Wallahi in na hau duk sai kun raina kan ku, ƴan iskan yara marasa tarbiyya”
Daga sama Ƴar Iya ta ƙara jefo wani ƙwallon mangwaron tana faɗin.
“Shegu tsofin nan sai shegen son girman tsiya kamar gyambo, Toh ina ka isa ka hau”
Baba Haro yace
“Ammah dai kukan Allah yayi matasa albarka, tsofait-sofai da ni kuke wa ɗiban albarka, Toh yau kuwa baku isa barin lambun na nlafiya ba.

A'i tayi dariya cike da raini da gatsali tace
“In mun zo fita lafiya ka zare lafiyar tamu. Kaji tsoho da ɗan banzan mugun baki”
Ƴar Iya tayi caraf tace
“Ni shi yasa bana sararawa tsofin nan, da lanƙwasassun ƙafafuwan su kamar agwagi”

Duk wannan tsiyar da suke wa Baba Haro kawai ya ƙyale su ne, rigar sa ya ɗage tare da naɗe ƙafar wando sai kan bishiya.

Ganin yana hawa bai sa sun ji tsoro ba saboda sun san salon su zai ƙayatar. Sai da Baba Haro ya fara nisa a hawan bishiyar su kuwa dariya kawai suke yi ganin yadda yake wani kama bishiya kamar ba namiji ba.

Daf da reshen da suke ya bi hakan yasa suka fara niyyar barin reshen, duk inda suka yi sai yace sai ya bisu. A haka suka yi ta kewaya wa da Baba Haro ɗan ƙarfin hali har sai da suka tabbatar ya wahala ba kuma zai iya cigaba ba.

A'i ce ta fara sauƙa ta can wani bangare ita kuma Ƴar Iya tabi wani tsililin reshe. Baba Haro ganin babu nisa tsakanin shi da wannan hatsabibiyar yarinya yasa yayi azamar bin ta.

Tsam ta dire ƙasa abun ta tana kaɗe ƙasar da ta buɗe jikin ta sannan ta tsaya dakon faɗowar rigimammen tsohon.
Tiiiiiiiiim kake ji sai ga Baba Haro a ƙasa.

“Wayyo Allah na, na shiga uku Ni Haro, shikenan wayyoh Allah na”

Dariya mugunta Ƴar Iya ta sheƙe da ita tana yima Baba Haro gwalo.
“Shegen tsoho ai sai muga ƙarshen abun naka, yanzu sai ka bi mu ai. Babu ko kunya kana bin Ƴaƴan cikin ka don sun hau mangwaro.” ta ƙarasa tana wulla masa harara tare da ke cewa da wata dariyar. A'i kuwa dariya ta hanata faɗin komai sai iya nuna Baba Haro take d yatsa tana dariya.

“Tashi mana ɗan tsoho rigimamme” Ƴar iya ta faɗa cikin shaƙiyyanci.
Baba Haro kuwa danasanin biye su yake yi, ya haɗa uban zufa kamar wanda yayi gudun ceton rai, fuskar nan shaɓe-shaɓe da hawaye da majina.

A gaban sa suka koma kan bishiyar tunda ya kasa ko da tashi ne yana ma tunanin ya karye. Tun daga bishiyar suke wullo ɓula ɓukan mangwaro ƙasa kuma sai sun saita kan Baba Haro su wullo. Baba Haro dai yau yaga ta kanshi, sai da suka wullo fiye da mangwaro hamsin tukun suka sauƙo daga bishiyar.

Tsam ko ɗaya basu bar mangwaron ba suke kwashe abun su cikin wani daro dake cikin lambun. Bayan sun kwashe suka ɗauko ƙullin kashu ɗin su suka yi hanyar fita, har zasu wuce Ƴar Iya ta juyo tare da zaro mangwaro ɗaya daga daron dake kan Ai.

A gaban Baba Haro ta tsugunna haɗi da miƙa masa mangwaron sannan ta ce:
“Allah ya sauwaƙe Baba Mai mangwaro, sai mun zo ciran na gobe.
In an tambaye ka waye yayi maka haka kace Ƴar Iya mai hannun ɓarna ce.”

Daga haka suka fice daga lambun suka ɗauki hanyar gidan Halima.

(Nace wannan ƙawance haka, daga haɗuwa ɗaya har anyi wa Iya hijira?”


TOH FAH!
ƳAR IYA ANYI ƘAWA FA DA GASKE.
GA KUMA SU HAMMA ZAKI FARIN CIKIN ƳAN MATA.
YANZU FA WASAN ZAI FARA
KU CI GABA DA KASANCEWA DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY

SHARE & COMMENT PLEASE!


[5/9, 7:59 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*








__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA ‘‘‘‘‘31&32’’’’’

[*Gare ki ƴar uwa mai albarka, ki riƙe ibadar ki yadda ya kamata a gidan auren ki*. *ko da wasa kada kiyi abota da mutanen banza, ko kin san illar alaƙar mace mai aure da mutanen banza?*
*To kaɗe kunnuwan ki kiji alaƙa da mutanen banza tsaf zai sa ki rasa ƙimar ki a wurin mai gida saboda ko yaushe zasu kasance cikin baki gurɓatacciyar shawara ne wanda in baki yi hankali kin lura da wuri ba kan sa ki rasa mijin gabaɗaya*
*Saboda haka a kula da ƙawayen da za'a yi mu'amala da su a gidan aure, da zarar kin fahimci ƙawar nan ba ta ƙwarai bace to tun wuri ki sallame ta kafin tayi galabar koya miki miyagun halaye.*
*A ko da yaushe, ki riƙe wannan ƙawar da in kin samu saɓani da mai gida bayan kin sanar da ita zata yi ta baki haƙuri tare da nusar dake laifin ki cikin zaman auren ki*.]



Daga haka suka fice daga lambun suka ɗauki hanyar gidan Halima.
“Salamu Alekum, masu gidan suna nan?” A'i ta faɗa tare da shigewa gidan Ƴar Iya na bin bayan ta.
Daga cikin ɗaki Halima ta fito tane washe baki
“Wa alaikumussalamu, masu gidan suna nan...maraba da baƙi ku iso ciki manah”

Ƴar Iya da suke tsaye bakin bishiyar yandi dake tsakar gidan suka fara ajiye shirgin su, A'i ta sauƙe daron mangwaro Ƴar Iya ta jiye ƙullin kashu ɗin su a ƙasa.

Halima ce ta ƙaraso yadda suke ɗauke da taburma a hannun ta. “Maraba da Ƴar Iya mai hannun ɓarna” dariyar shaƙiyyanci Ƴar Iya tayi yayin da take ƙoƙarin zama kan taburmar da Halima ta shimfiɗa musu.

Sai da suka zauna ɗamas sannan suka fara janyo mangwaro da kashu ɗin.
Murmushi Halima tayi tace
“Mangwaro haka daga ina?”
Ƴar Iya ta amsa da faɗin
“Cirowa muka yi a lambun Baba Haro”
A'i ta ƙyalƙyale da dariya tace
“Yana can mun bar shi ma a ɓalle”
Zare ido Halima tayi tana ƙara kallon su alamar tana buƙatar ƙarin bayani.
A'i tace
“Munje cira inji in gaya miki tsohon ya hana mu, shine muka masa kwaskwarima muka cira daga nan muka yo nan”
“Hmm” Halima tace “Ku dai kam bakwa gajiya da tsokala, ko da yake akwai mai hannun ɓarna cikin ku.” ta ɗan dakata ganin irin kallon da Ƴar Iya ke bin ta da shi, cikin wayincewa taci gaba
“Duk da haka gaba ta kaimu Ni da sabbin ƙawaye na, To yanzu dai bari na wanke mana uku uku sai mu sha”

Tashi Halima tayi ta wanke mangwaro goma ta jawo su suka fara sha suna hira. Daga ƙarshe dai tas suka shanye wannan mangwaro haka kashu, daga nan suka yi mata sallama Ƴar Iya na faɗin zata tafi neman halal ɗin ta ita ma. Daga haka A'i tayi gidan su Ƴar Iya ta nufi gidan Iyar ta.

★★★★★★★★

*ALEE POV*

Shirye-shirye ake cikin gidan General Muhammad Naira. Ta kowanne ɓangare shiri ake yi babu kama ƙafar yaro. Kowa ka gani cikin farin ciki yake yayin da Hamma Zaki yaƙi fitowa gabaɗaya.

Zaune yake a bedside kamar kullum cikin white pyjamas, ƙafarsa ɗaya na kan ɗaya yayin da fuskar shi ke a ɗaure. Hakan ya bani damar fahimtar ba don hidimar yake ba duba da yadda ahalin sa ke ɗauki akai.

Wayar shi da yake latsawa ce tayi ringing bai yi niyyar picking ba saboda sam yau baya son a dame shi. Can ganin mai ƙiran nashi da niyyar dainawa yasa ya zaro wayar da niyyar kashe ta gabaɗaya, sunan Dude da ya gani yasa yaja tsaki tare da picking. Can ƙasan maƙoshi ya amsa sallamar Dr. Faruq ɗin
“Wa alykumussalam” Dr faruq kuwa murmushi Mai sauti yayi tare da faɗin
“Buddy duk cikin magagin rashi don taron ne har nayi kira uku baka yi picking ba?
“Mtss” Hamma Zaki yayi tsaki kamar wanda aka yiwa dole yace “Idan abun da ka ƙira ka faɗa ne, lemme hang the call.”
Cak Dr. Faruq ya tsaya da dariyar da yake yi coz ya san halin mutumin nashi.
Cikin son danne dariyar tashi yace
“Yau Buddy shiru naji daga ɓangaren ka, Hamma Saleem ɗazu ya ƙira yana tambaya ta ko ya batun shirye-shiryen namu, I told him baka ce komai ba sai yanzu dai yace nayi maka magana”
“Ok” kawai Hamma Zaki yace. Cikin takaici Dr. Faruq yace
“Alright tunda ok kaɗai zaka ce, sai mutum ya dage yayi maka magana ka wani ce ok. Shikenan nimah zan cewa Hamma Saleem ɗin kace ok kawai”
Cike da ƙosawa da maganar ɗin tuni kan shi ya fara sarawa yace
“Sorry Buddy, ban hana ku shirya komai ba, kawai ni ɗin ne bana buƙatar shiri dole ta sa zan yi attending ma”
“Na fahimce ka Buddy, worry less please zan kula da komai and ka daure ka fara sabawa da jama'a da kuma hayaniya ko don saboda gaba.”
“Ok” Hamma zaki ya faɗa tare da katse ƙiran yana jan tsaki.

Sauƙa yayi tare da sanya bathrobe ya nufi toilet. Yana fitowa yayi drying jikin shi tare da shafa creams nashi. Cikin closet ya ɗauko wata white jallabiya ya sanya, ko turare be samu damar fesawa ba ya nufi sidedrawer tare da ɗauko pcm tablet, fridge ya nufa ya ɗauko warm bottle water tare da Shan pcm ɗin yana yamutsa fuska. Yana gama sha ya haye bed Don ya huta.

Vibration na wayar shi ya tayar da shi
Major Kabir Joda ne hakan yasa yayi picking tare da kara wayar a kunnen sa.
“Assalamu Alykum” aka ce daga ɓangaren can. Sai a lokacin Hamma Zaki ya fara motsa baki tare da yamutsa fuska.
“Wa alykumussalam” ya amsa can ƙasa-ƙasa.
“Captain?, Ain't u preparing anything there?”
“Nothing sir!” ya bashi amsa a taƙaice.
“Toh akwai sabbin uniform da zaka sanya a wurin taron, Please ka aiko a amsa maka”
“Ok sir!”
Sanin Halin Captain yasa Major Kabir hanging call ɗin.

Lokaci ya duba ganin 12:22pm yasa shi nufar Toilet, bayan ya watsa ruwa ya ɗauro Alwala. Masjid da ke cikin estate ɗin ya wuce. Bayan sun idar ya dawo.
Tun daga bakin entrance door na part ɗin yake jin ƙamshin girki, sai a lokacin ya tuna ko breakfast bai yi ba coz lokacin da Mom ta aika Sarah Koro ta yayi da girkin.

A hankali ya shiga ciki, lokacin dukan su suna zaune a dining ɗin, Daddy, Mom, Fauzah, sai kuma Sarah. Ɗan yamutsa fuska yayi tare da ƙarasawa wurin cikin takun shi na zaratan maza.

Tun kafin ya ƙarasa Mom da Daddy ke sake mishi murmushi yayin da Fauzah ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sarah Kam ko ƙifta idon ta batayi coz gani take kamar za'a iya cire wani abu daga jikin shi a lokacin da ta ƙifta ɗin. Kyau sosai yayi mata sai dai hararar da ta gani ya aiko mata yasa babu shiri ta janye kanta. Ita ma babu laifi tayi kyau, sanye take cikin yellow Sari yayin da ta zubo da kwantacciyar baƙar sumar ta har gadon baya.

Yana isa ya gaida Mom da Daddy a tare coz he's eager to start eating yadda cikin shi ke wani irin ƙara.
“Good afternoon Daddy and Mom”
Cikin sakin fuska suka amsa mishi yayin da Mom ta miƙe tayi serving nashi, white rice ne with stew, sai cips da ta soya saboda shi. Hot coffee ta zuba mishi a cikin mug ɗin dake gefe kafin ta zauna.
Fauzah da kanta je ƙasa tace
“Good afternoon Hamma Zaki”
Itama Sarah bakin Fauzah tabi
“Good afternoon Brother”

Harara ya banka wa su biyun ba tare da ya amsa gaisuwar ba, babu shiri Fauzah ta miƙe zata bar dining ɗin ai kuwa suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu. Mom da Daddy ma miƙewa suka yi don cigaba da shirye-shiryen su.
Hanjin cikin Fauzah sai da ya kaɗa yadda su Mom suka tashi suka barsu da Hamma zaki, babu abinda take cikin ranta sai addu'a Allah yasa ba wani laifin tayi ba.

Sai da ya gama tas sannan yayi wiping bakin shi tare da ɗauko hot coffee nashi yana sipping a nutse kamar wani mace.
Sauƙewa yayi tare da kallon Sarah da Fauzah wanda kawunan su ke ƙasa.
Cikin sassanyar murya yace
“Ku baku san lokacin gaisuwa bane sai mutum ya fara cin abinci?”
Kasa magana suka yi musamman Fauzah dake wasa da yatsun ta. Ɗago fararen idanuwan sa yayi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya sannan ya maida hankalinsa ga Coffee ɗin da yake sha.
“Alright since You don't know how to talk kada yarinya ta ƙara gaishe ni idan ina cin abinci” ya faɗa cikin Muryar da ke tsantsar nuna umarni, bai jira amsar su ba ya wuce bedroom nashi.

Har ya shiga ya tuna da wayar su da Major hakan yasa ya ƙira Dr. Faruq ya sanar da shi.
“Please Dude, in zaka shigo ka biya ta barrack ka amsa min saƙo wurin major Kabir” cikin ƙosawa da maganar ya tsaya haka.
Dr. Faruq yayi murmushi mai sauti yace
“In zaka zo ka amshi abun ka to in kuma baka zuwa shikenan, ni ba ɗan aiken ka bane”
Jin amsar aminin nasa yasa ya katse ƙiran without pleading...Sam shi bai san wani abu rarrashi ba in fact bai ma iya ba.

Ɓangaren Dr faruq murmushi yayi coz ya san halin aminin nasa sarai kuma abun da yayi expecting kenan. Ƙasa ƙasa yace
“Watarana dai zamu ga ƙarshen wannan izza taka da zarar mace ta samu muhalli cikin ƙalbin ka”
Daga haka yaja motar shi zuwa barrack da yake basu da nisa. Yana karɓowa ya taho gidan su Hamma Zaki.

A parlour ya haɗu da Mom, bayan sun gaisa ya wuce sama. Knocking door ɗin yayi wanda kawai tsokala ta saka shi haka. Tsaki yaja daga ciki yace “Yes come in”.
Maimakon ya shiga sai ya cigaba da Knocking ɗin. Cikin hasala ya miƙe daga bakin gadon tare da nufar ƙofar da niyyar hukunta koma waye wannan.
Dr. Faruq jin ana ƙoƙarin murɗa handle ɗin yasa yayi baya, ai kuwa kamar ya san meh zai faru Hamma Zaki yayi niyyar cafke kowaye ya hukunta shi shi yasa yaja baya yana dariya.
“Kai Buddy, irin wannan cafka ai sai ka kashe mutum in ka samu nasara.” ya ƙarasa yana dariya. Tsaki yaja ya koma ciki abun sa, duk haushi ya cika shi bayan ma yace bazai amso masa saƙon ba shine zai wani zo ya dame shi.

Ƙarasawa cikin ɗakin Dr. Faruq yayi hannun sa ɗauke da babbar army bag. Bakin gadon a gefen Hamma Zaki ya zauna tare da ƙura masa ido. Ganin yadda ya wani haɗe rai kamar wanda zai mutu yasa ya kece da dariya. Tsaki yaja tare da shirin miƙewa Dr. Faruq ya maida shi mazaunin sa.
“Haba Buddy, me kake yi haka ne kam?”
Harara kawai ya aika masa tare da ƙara miƙewa.
“Since baka amsomin saƙon ai ban kuma ce ka zo ba”
Cikin sigar rarrashi Dr faruq yace
“Haba Buddy yi haƙuri mana, ai na riga na amso” ya faɗa tare da miƙa mishi babbar army bag ɗin.
“Thanks” kawai yace haɗe da ajiye ta gefen sa. Sanin hali yasa Dr faruq bai ji haushin sa ba sai ma murmushin da yayi tare da cewa
“Ba za'a buɗe mu gani bane?”
Banza Hamma Zaki yayi mishi.
Miƙewa yayi zai ɗauka ai kuwa Hamma Zaki ya riƙe hannun sa.
“Auch! To sake min hannun in ba so kake ka nakasa Ni ba, nimah na haƙura”
Ganin ya saduda yasa ya sake mishi hannun. Haka suka zauna har wuraren 2:30pm daga haka Dr. Faruq ya wuce don samu ya shirya on time.


COMMENT & SHARE PLEASE


[5/10, 10:03 AM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*







__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA ‘‘‘‘‘33&34’’''’

[ *Gare ku mata masu sanya turare idan zasu fita waje, haramun ne sanya turare a lokacin da zaki fita waje domin baki san wa da waye zasu ji ƙamshin ba AMMAH babu laifi ki sanya yadda iya ke zaki ji ƙamshin abun ki.*
*Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, duk matar da ta sanya turare a lokacin da zata fita, bayan ta fita kuma wani da ba muharramin ta ba yaji ƙamshin har ya yaba, toh za'a rubuta mata zunubi kamar wacce tayi zina a ka'aba.*
*SABODA haka ƴar uwa idan zaki fita unguwa ki kiyaye, addini bai hana ki tsafta ba amma bai ce ki bayyana adon ki ga waɗanda ba muharraman ki ba. Babu laifi kiyi wankan ki a gida ki saka turare cikin trailer ma idan kina so matsawar ba zaki fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login