Showing 108001 words to 111000 words out of 135404 words
kayan wanki tana kwanciya.
Daren ranar in banda bacci ɓarawo ne da babu abinda zai sa ta iya rintsawa. Da asuba da ya tashi sai da yayi alwala zai fita ya tashe ta, bai dawo ba sai around 8:00am, ganin abinci jere a dining yasa ya ci, daga nan ya haura sama don yin shirinsa na fita.
A ɓangaren Khairy da safe bayan tayi breakfast ta wuce part ɗin Nenne tare da abubuwan da zata buƙats don yanzu can kaɗai zasu zauna ba batun kallon hasken rana talkless of tafiya cikinta kuma.
***************
*Five days later (Bayan kwanaki biyar)*
Zaman lafiya dai ya kaurace masa kamar yadda yayi tunani, don kuwa a ranar da ya sanar da ita batun washegari ta sanar da Maminta, tashin hankali sosai ita ma ta shiga don ko kaɗan bata tsammatawa ɗiyar tata zama da kishiya ba tunda ita ma bata zauna da ita ba. Nan ta lallaɓata tace ranar ba sai gobe ba zata je wurin malamin tsibbu nan da suka samo ita da aminiyarta Hajiya Ramatu.
Ƙawayen da tayi a nan Adamawa su ma duk sun bata shawara wasu ma faɗin ta haƙura kawai tunda ta san halin mijinta babu fashi aure wasu kuma na zuga ta s Kan tayi ta hauka laalla sai ya hakura. Da yake ƴan tayi hauka ɗin sun fi yawa sai ta ɗauki shawarar, nan ta fara hauka da tuburan, don da zarar ta ji shigowarsa zata ɗauko wuƙarta ta yi kansa, abunka da mazan fama sai yayi dabara ya ƙwace, in ya shiga ɗaki ta bi shi tana surutai ita ala dole maras hankali. Ai kuwa kallon da yake mata shima kenan shiyasa ma ba ya biye mata duk da cewa abun na damunsa don baya son rikici amma don ya nuna mata shi ke da gidan yasa ya shashantar da batun.
A yau Alhamis wanda yayi dai-dai da sauran kwanaki goma biki aka kawo lefen ƴan matan gabaɗayansu, shi ma Hamma Zaki ranar ya kawo nasa saboda a kai.
Masha Allah Kaya sunyi kyau don kuwa babu wani cheap Abu cikin kayayyakin, su kan su akwatunan abun a kalla ne bare kuma kayayyakin dake ciki. Kowa farin ciki banda Khairy da take cikin damuwar irin nata mijin.
Kyau sosai ƴan matan suka yi kamar ka sace ka gudu, Khairy da bata daɗe da farawar ba ma yafi amsarta saboda in ta sanya sari ta saki gashin kanta da shi ma ya gaji da gyara mai karatu zai yi tunanin ba jinin Nigeria ba ce.
A ɓangaren yallaɓai Hamma Zaki kuma haka ya kai wa uwargidansa pretty kayan da ake wa take da “Dannar kishiya”. Da farko kamar ba zata ɗauka ba sai da ta ga akwatinan ba na wasa bane yasa ta kwashe duk da ranta cike yake da kishin me yasa ba zai yi wa amaryar irin wanda yayi wa mata ba lokacin da zai aureta. Ko da ta buɗe sai da ta sha kukanta sosai ganin kaya masu tsada, kukan ba wai na tausayi bane, a'a, kukan na baƙin cikin ya kayan amarya zai kasance da ita ma ta mallaki ya wannan.
_Share Lillah_
_Itz Diamond Bhatool 💎_
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““107&108”””
Ba tare da ya kalle ta ba yace “E” jinjina kai tayi tana faɗin “Ai nima bani da surutu” ƴar dariya yayi yace “Kamar ban san ki ba?” shiru suka yi daga nan ya ƙara maida Hankalinsa kan tuƙin da yake cikin ransa yana jin wani farin ciki maras misaltawa. Tunaninsa kwacakom ya koma ga masoyiyarsa wanda lokaci ɗaya ya kamu da matsananciyar ƙaunarta ba tare da ya shirya ba, wani lokacin ya kwaɓe fuska kamar wani ƙaramin yaro wani lokacin kuma yayi murmushi.
Shirun da ya ishe ta ne ya sa ta ɗauko wayarta ta saka charge daga nan kuma ta fara danna kayarta cike da ƙwarewa. Lokaci zuwa lokaci kuma yakan ɗago ya dube ta ganin hankalinta na kan wayar shima sai ya maida nasa ga titi. A nata ɓangaren ita ma takan ɗago ta saci kallonsa sai kuma ta koma danna wayarta. Shirin da ya ishe shi ne yasa ya kunna Ƙira'ar Muhammad Ayyub yana ɗan bin baki.
Ita kam cikin ranta take bin baki saboda yadda take tsananin son karatunsa. Haka tafiyar tasu ta kasance, da suka kai Bauchi kuma suka tsaya suka ci abinci a restaurant daga nan kuma suka ƙara ɗaukar hanya. Ba su suka isa ba sai wuraren la'asar don ma suna tsayawa su yi salla.
Sai da ya daidaita parking tukun ya fito, gateman da ya rufe gate yayi wa nuni da ya zo ya shiga da kayan dake cikin Boot, ita kuwa saboda kewa da ɗaulin ganin mutanen gidan da gudu ta shiga ɓangaren Granny tana ƙwalla mata ƙira. Jin Muryar shalelenta yasa ita ma ta fito da sauri tana washe baki.
Bayan ta huta kuma ta zaga sauran part ɗin gaida su tare da isar da gaisuwar mutanen Gallara gare su. Ɓangareb Nenne ne ƙarshen zuwa ai kuwa can ta tarar da Babes an sha kyau don tuntuni an fara yi musu gyaran jiki. Don Aunty Baraka ba baya ba wurin sanin Sirrin gyaran jiki. Rungume juna suka yi suna murna yayin da take koɗa yadda suka sauya sosai, sunyi kyau da haske ga fatarsu kamar ba a Nigeria suke rayuwa ba.
Hayaniyarsu ne yasa Aunty Baraka fitowa don ta san halin ƴaƴan nata, ko da ta fito ganin Khairy sai ta tsaya tana bin ta da wani kallo, ita ma Khairy nata ɓangaren kallonta take yi don babu shakka ta san fuskar amma ta gagara tuna ina ta santa. Ganin tunanin yana shirin yin tsayi yasa ta ɗan kau da kai tare da gaida Aunty Barakar da take mata kama da wata fuska da ta sani.
Cikin sakin fuska Aunty Baraka ma ta amsa, tana murmushi ta ce “Da gani wannan ita ce Khairy ko” murmushi tayi tana gyaɗa kanta. Yesmeen tace “Kin kuwa canka dai-dai ita ce Khairy, cikon quadruplets kenan” dariya dukkansu suka yi, Aunty Baraka ta ce “Matso nan Khairy” babu musu ta ƙarasa kujerar da Aunty baraka ta ke, ganin hakkan yasa suka fara shagwaɓa wai khairy ta ƙwace musu Aunty Baraka, ita dai Khairy mamaki take ganin irin wannan sauyi bata san lesson ɗin da aka ɗaura musu bane bayan tafiyarta.
Cikin ƙanƙanin lokaci Khairy ta sake da Aunty Baraka wacce ta ja ta a jiki, hirarsu suka kasa bayan sunyi sallah. Nan Aunty Baraka ta fara kawo musu abubuwa iri-iri suna ci da sha amma na Khairy haɗin daban ne saboda ita ma ta kamo ƴan uwan nata, sai da Aunty Baraka ta tashi Khairy ta ke tambayar su murya ƙasa-ƙasa. “Kai Babes irin wannan sauyi haka daga tafiya ta? Meye Sirrin ne?” Fauzah ta ce “Ai babu wani sirri da kike gani sai abunda yanzu kema kika fara amsa” ta ƙarass tana ɗage mata gira.
Dukan wasa Khairy ta kai mata tana faɗin “Ke meye haka kina wani ɗage min gira?” Ayrah ta ce “Kin ga Fauzah ki ɗan bawa Khairy lokaci naga yanzu bata samu karatun ba amma tunda ga Aunty Baraka lafiya lau zata fahimta” dariya Dukansu ukun suka yi Yesmeen na faɗinn “Ai kuwa dai Ayrah haka ne, mu jira muga nata....” shiru tayi ganin Aunty Baraka ta shigo.
Wani haɗin ta ƙara basu daga nan Khairy ta ce zata wuce kada Granny tayi zaman kaɗaici. Cike da tsokala Yesmeen ta ce “Uhm ke da kin kusa ma ki rabu da Grannyn?” zuciyarta ne ta yanke lokaci ɗaya don ita har ga Allah ta ma manta da batun auren, waskewa tayi kawai tace “Ku dai kayan mamakinku baya karewa, kunga mu kwan lafiya nikam”
Daga haka ta wuce part ɗin Granny da sauri har tana harɗewa kamar zata faɗi, ko da ta shiga ɗakinta hawaye ta sake tana faɗawa kan gadonta. A hankali yayin da hawaye ke zubowa daga idanuwanta tace “Allah sarki Ni Aishatu, wannan wanne irin aure ne za'a yi min?, ace two weeks ya rage ayi biki amma bansa ango a idanuwa na ba! To in ma baya kusa ne ba zai nemi number na ya ƙira ni ba at least na San ko da sunansa ne” hawayen fuskarta ta share tana mai ƙarfafawa kanta guiwa tace “Ko ma waye ne tunda yayi silar rashin cikar burin zuciya ta kuma muradi na sannan ya zama shamaki tsakaninmu da wanda na ke so dole ne ya karɓi kowanne hukunci na yanke masa” daga haka tayi alwala tare da gabatar da shafa'i da kuma witr daga nan tayi shirin bacci tana mai gabatar da addu'ar ta.
************************
A daren yau ne Hamma Zaki ya shirya sanar da shalelensa kuma uwar ƴarsa wato pretty game da auren nasa da ke zuwa cikin wasu makonni masu zuwa. Har ga Allah baya son tashin hankalinta a halin yanzu musamman da take ƙoƙarin ganin ta gyara wasu banzayen ɗabi'unta, uwa uba yana jin daɗin rayuwarsu da suka fara ginawa baya son a samu wani abu da zai zama shamaki da zaman lafiyarsa da abokan rayuwa.
Ganin tunda ya shigo yana cikin damuwa yasa ta kawo masa drink a cikin glass cup tare da zaunawa gefensa tana ɗaura hannunta a kafaɗarsa. “Sweetheart!” ɗan ɗago kansa yayi yana dubanta tare da sanya fuskar murmushi don gudun kada ta gano sai ya sanar da ita. Sajen fuskarsa ta shafa tana faɗin “Watz wrong with u sweetheart?, kana cikin damuwa don Allah ka faɗa min”
Bai ce komai ba duk da cewa tana jiran amsarsa sai ta ɗan sharar. Sai da suka wuce bedroom tukun ta Kai baby Humairah cot nata suka kwanta tukun ya ƙira sunanta a sanyaye. “Nabila” sai kuma ya ɗanyi shiru kafin ya ci gaba “Ina so ki saurare Ni da kunnenki na basira ki ji me zan ce” zuciyarta ne ta tsinke don kuwa ta tabbatar wannan babban al'amari ne yake son sanar da ita.
Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya ce “Nan da sati biyu in sha Allah za'a ɗaura aure na” dumm gabanta ya faɗi, a zabure ta tashi ta zauna tana dubansa “A'a sweetheart wasa kawai kake min na sani, babu wacce zata shigo rayuwarmu, wasa kake yi ka faɗa min” ta faɗa tana tsayar da kallonta a kansa babu ƙiftawa.
Dama ya san za'a yi haka tabbas sai dai kuma ba zai bata damar tasiri akan hakan ba, shi ne mijin ai ba ita ba. Ɗan dakewa yayi yana faɗin “Yadda kika ji zan ƙara aure ne, kuma nan da sati biyu” jin maimaicin abunda ta ji a maimakon amsar da tayi tunani yasa ta sauƙa a gadon babu shiri tana tsaye gabansa idonta kuma na kansa tace “Ai wallahi ba zai taɓa yiyuwa ba!, ta ya ma zan yi sharing miji da wata banza, Allah sweetheart tun wuri ma ka ce ka fasa don kuwa ko wacece ta kuskura ta shigo zan iya kashe ta a kan miji na”
Hayaniyar tata ne ta fara damunsa hakan yasa ya ɗaure fuska yana faɗin “Sai ki kashe ta ai tunda ke kika yi ta!, bari ki ji aure babu fashi kamar anyi, babu gudu babu ja da baya cikinsa, in kin so ki nutsu ki zauna da ita lafiya in kin so kiyi hauka lafiya lau kika aikata wani laifin duk hukuncin da aka miki babu abunda zan ce.”
Kan sa ne ya sara saboda doguwar maganar da yayi hakan yasa ya ja blanket ya juya gefe ya kwanta abunsa yayin da ita kuma take tsaye tana huci kamar mayunwacin zaki. Ganin tsayuwar ba zata fisshe ta ba yasa ta faɗa gadon kamar kayan wanki tana kwanciya.
Daren ranar in banda bacci ɓarawo ne da babu abinda zai sa ta iya rintsawa. Da asuba da ya tashi sai da yayi alwala zai fita ya tashe ta, bai dawo ba sai around 8:00am, ganin abinci jere a dining yasa ya ci, daga nan ya haura sama don yin shirinsa na fita.
A ɓangaren Khairy da safe bayan tayi breakfast ta wuce part ɗin Nenne tare da abubuwan da zata buƙats don yanzu can kaɗai zasu zauna ba batun kallon hasken rana talkless of tafiya cikinta kuma.
***************
*Five days later (Bayan kwanaki biyar)*
Zaman lafiya dai ya kaurace masa kamar yadda yayi tunani, don kuwa a ranar da ya sanar da ita batun washegari ta sanar da Maminta, tashin hankali sosai ita ma ta shiga don ko kaɗan bata tsammatawa ɗiyar tata zama da kishiya ba tunda ita ma bata zauna da ita ba. Nan ta lallaɓata tace ranar ba sai gobe ba zata je wurin malamin tsibbu nan da suka samo ita da aminiyarta Hajiya Ramatu.
Ƙawayen da tayi a nan Adamawa su ma duk sun bata shawara wasu ma faɗin ta haƙura kawai tunda ta san halin mijinta babu fashi aure wasu kuma na zuga ta s Kan tayi ta hauka laalla sai ya hakura. Da yake ƴan tayi hauka ɗin sun fi yawa sai ta ɗauki shawarar, nan ta fara hauka da tuburan, don da zarar ta ji shigowarsa zata ɗauko wuƙarta ta yi kansa, abunka da mazan fama sai yayi dabara ya ƙwace, in ya shiga ɗaki ta bi shi tana surutai ita ala dole maras hankali. Ai kuwa kallon da yake mata shima kenan shiyasa ma ba ya biye mata duk da cewa abun na damunsa don baya son rikici amma don ya nuna mata shi ke da gidan yasa ya shashantar da batun.
A yau Alhamis wanda yayi dai-dai da sauran kwanaki goma biki aka kawo lefen ƴan matan gabaɗayansu, shi ma Hamma Zaki ranar ya kawo nasa saboda a kai.
Masha Allah Kaya sunyi kyau don kuwa babu wani cheap Abu cikin kayayyakin, su kan su akwatunan abun a kalla ne bare kuma kayayyakin dake ciki. Kowa farin ciki banda Khairy da take cikin damuwar irin nata mijin.
Kyau sosai ƴan matan suka yi kamar ka sace ka gudu, Khairy da bata daɗe da farawar ba ma yafi amsarta saboda in ta sanya sari ta saki gashin kanta da shi ma ya gaji da gyara mai karatu zai yi tunanin ba jinin Nigeria ba ce.
A ɓangaren yallaɓai Hamma Zaki kuma haka ya kai wa uwargidansa pretty kayan da ake wa take da “Dannar kishiya”. Da farko kamar ba zata ɗauka ba sai da ta ga akwatinan ba na wasa bane yasa ta kwashe duk da ranta cike yake da kishin me yasa ba zai yi wa amaryar irin wanda yayi wa mata ba lokacin da zai aureta. Ko da ta buɗe sai da ta sha kukanta sosai ganin kaya masu tsada, kukan ba wai na tausayi bane, a'a, kukan na baƙin cikin ya kayan amarya zai kasance da ita ma ta mallaki ya wannan.
_Share Lillah_
_Itz Diamond Bhatool 💎_
[19/09, 8:50 a.m.] Famanté 💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““109&110”””
Ana saura kwana huɗu kuma aka je gidan amaren aka yi musu jere.
Cikin ikon Allah duk abunda aka sanya wa rana yake zuwa, yau ta kama saura kwana biyar a ɗaura auren ƴan matan. Komai da zasu yi amfani da shi sun tanada, dama ba wani events zasu yi ba, Fulani day ne kawai sai kuma waleema.
Ranar Laraba aka gabatar da Fulani day, amaren sunyi kyau har sun gaji, kana ganinsu kaga jinin Fulani don yadda kayan suka karɓe su sosai.
Ranar Alhamis kuma aka gabatar da walima a makeken family hall Dake cikin gidan su. Walimar da aka ci aka san anci, sannan aka samu kayayyakin amfani kamar atampa, shadda, jaka da sauransu. Mutane da dama sun halarci walimar don mutanen Gallara ma Babbar Mota suka cika suka zo bikin.
Tun ranar walima da suka dawo bakin su ya mutu, duk azarɓaɓin da ake yi sai jikinsu yayi sanyi ganin da gaske dai aure ya tabbata kuma wai barin gidansu zasu yi na har abada, in ko sun zo to na wani lokaci ne.
Ranar juma'a bayan gabatar da Sallar juma'a a babban masallacin juma'a na garin Adamawa aka ɗaura aurarrakin guda huɗu rus wanda dubban mutane suka shaida.
_Fauzah Muhammad Naira da angonta Ishaq Umar Hamma._
_Yesmeen Suraj Naira da Kuma angonta Ibrahim Ahmadu Bello._
_Aminatu (Ayrah) Bello Naira da angonta Hammad Yusuf Usmanu._
Da Kuma
_Alee Muhammad Naira da amaryarsa Aishatu Umar Gallara._
A kan sadaki Naira dubu ɗari (₦100, 000) lakadan ba ajalan ba ma kowacce amarya.
Har aka ɗayra auren hankalinsa baya wurin don kuwa Uncles Suraj ne ya karɓa masa, ba tare da ya ji ko da sunan amaryar ba don babu amfanin sanin ya sauƙe ajiyar zuciya. Fuskarsa haɗe ya fito daga Masallacin yayinda abokansa including Dr. Faruq, Captain Sulaiman, da sauransu suke biye da shi sai tsokalarsa suke. Bai kula su ba ma sai wucewa zuwa motarsa da yayi ya fige ta da mugun gudu. Dariya suka yi suka bi bayansa don sun san ba zai wuce garden ɗinsa ya nufa ba.
A can suka tarar da shi kuwa ƙarƙashin canopy da aka tanada don shan iska idanuwansa lumshe kamar mai