Showing 135001 words to 135404 words out of 135404 words
kuma akwai ƙarin matsayi da za'a yi mishi daga Captain zuwa Major.
Haka rayuwa ta ci gaba da wakana har satin yayi, nan Hamma Zaki ya samu ƙarin matsayi to Major Alee Muhammad Naira, A nan Lagos suka ci gaba da zama, watansu uku da dawowa kuma khairy ta ƙara samun ciki. Aman kuwa banda rigima babu abinda ya saka gaba, sn baya barin bakinta yayi shiru, in ta zo zata dake shi kuma Abie ɗin sa ya hana sai yace “Haka nan dai kowa yayi yarintarsa, watakila ma rashin jinsa bai kai nawasu ba” haka dole zata barshi.
Sannu sannu babu wuya a wurin mai rai, watanni tara Khairy ta haifi ɗiya mace, wannan karan kuma yarinyar sai ta kwaso kamannin khairy sak kamar an tsaga kara. Ranar suna taci sunan Innarta Barira ana ƙiranta da Mimah.
A wannan shekarar ne kuma Hamma Zaki ya nemi transfer zuwa Adamawa don yayi settling da familynsa, tun kafin ya koma ya tura kuɗaɗe aka fara gina sabon estate nasu, abunka da aikin kuɗi, wata ɗaya yaci suka kammala gin estate ɗin, aka ƙawata shi sosai. Daga nan kuma duka family suka koma can da zama har da su Fauzah da suka kasance suma a da familyn ne, su Iya da Baffi ma Flat guda aka Basu, Baba ma da Amaryarsa aka Basu. Babu abinda khairy ke yi sai godiya ga Allah.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cike da farin ciki da kuma ƙaunar juna, Yanzu haka khairy yaranta huɗu, Aman, Mimah, Jahad, Zahrah, Sai kuma auta Na'eem.
*Alhamdulillah!!!*
_Nan na kawo ƙarshen wannan littafi Mai suna *_ƳAR IYA Mai hannun ɓarna_*. Kuskuren da nayi cikin sa ina roƙon Ubangiji ya yafe min shi, abubuwa na magana da kuma alkhairi da ke ciki ina roƙon Ubangiji ya sa muyi tarayya cikin ladan._
_Sannan fans ɗina ina ƙara tunatar da ku cewa ƙofar gyara a buɗe take, don Allah duk wani abu da kuka nayi ko nake shirin yi da bai kyautu ba kada ku tsaya ku min magana, wannan shine soyayya ta gaskiya da kuma zaman tare._
_Ina matuƙar godiya gare ku fans ɗinah, masoya na har abada, ƙaunar ku gareni maras iyaka ina godiya, nima ina matuƙar ƙaunar ku har cikin raina, kuma ina jin ku tamkar ƴan uwa na ne._
_Masu Neman number waya na ga shi nan +2347061707238 ko kuma +2349027383866, na gode_
_Nan zan dakata, ku kasance da alƙalami na cikin littafai na masu zuwa, AYA DA TSAKUWA....and others._