Showing 84001 words to 87000 words out of 135404 words
fadi daga haka ta kutsa zuwa cikin dakinta.
Bayan ta cire kayan ta sauya zuwa night wears ta kunna wayarta. Whatsapp ta hau ai kuwa group din babes taga sabbin chats da alanu yanzu ake yi. Sunyi hira sosai yadda suke ta korafi wai meye alakarta da Hamma Zaki, ta sanar da su babu amma sunki yadda. Fauzah har da fadin “In tayi tsami zamu ji ai” emoji na dariya ta tura tace “Kar ku damu yanzu in kuna so ai sai na kai masa wayar ya fada muku amsar tunda kunki yadda, la'alla in shi yace babun zaku yadda ba sai tayi tsami ba”. Ta karashe da Emojin murguda baki.
Hakuri suka fara bata suna fadin “Ki rufa mana asiri khairy in ba so kike yau mu kwana ana gasa mana jiki ba” Ayrah tace “Ai kuwa dai, don wollah ina da tabbacin a daren nan zai ce zai zo shi”
Dariya Yesmeen tayi tace “Don Allah khairy ki dan kai masa tunda su basa neman zaman lafiya” ta karasa da emoji na daga gira. Nan dai suka sha hirarsu suka gaji.
Hamma Zaki ko da ya kaiwa pretty abincin bedroom dinsa ya nufa, sai da ya watsa ruwa kafin yasa sleeping weara nashi, haka kawai ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi mai dadin gaske sai dai abu daya ya tsaya masa a rai “Me yasa nake yawan tunaninta?” barin zuviyarsa ta bashi amsa da “Ka fada soyayyarta ne” da sauri dayan yace “Nooo ni da ban taba soyayya ba ta ya zaa ce ina sonta?” “To in ba sonta kake ba me kake?” daya zuciyar tace masa “Saboda tana kyautata min shiyasa amma ba sonta nake ba”. Haka dai aka cigaba da cakawa tsakanin Hamma Zaki da kuma 2-hearts dinsa.
Washegari da safe tayi breakfast kamar kullum, sanye take cikin wata white shirt sai blue pencil trouser ta kuma daure gashinta da blue ribbon. In mai karatu ya ganta dole ta burgeshi. Sai da ta kaiwa pretty tukun ta deba nata ta wuce bedroom dinta. Ko da taci bata fito ba sai around 11:00am, ganin alamar Hamma Zaki har ya ci ya fita yasa tayi murmushi sai ta zauna a parlour ta kunna kallo.
A nasa bangaren ko da ya fito bai tarar da ita a parlourn ba kamar ko yaushe da ta bawa kanta aikin serving dinsa sai yaji wani iri. Ya jira ya jira bata fito ba kawai sai ya hakura yayi serving kansa cikin ransa kuma yana tunanin ko lafiya. Da yazo fita sai da ya tunkari kofar dakin nata kawai sai zuciyarsa tace “Nooo, me kuma zaka yi haka?, ai sai ta raina ka” da wannan shawarar kawai ya wuce duk da zuciyarsa bata yi masa dadi ba.
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa gidan Hamma Zaki, pretty da khairy basu kara samun sabani ba haka babu wata good relationship tsakanin Hamma Zaki da pretty sai dai kowa yana kulawa da kowa cikin zuciyarsa kuma kowa yakan yi tunanin dan uwansa a mafi yawan lokuta.
Khairy sam bata da damuwa don kullum sai sun sha hirarsu da granny haka kuma tana kiran Nenne, Mom da Mommah ma wasu lokutan takan kira su gaisa, hakan kuma ba karamin kara mata daraja da kima yayi a idonsu ba. Ita da babes kam baa magana, voice call, video call, normal phone call babu wadda basa yi, credit, data duk basa rasawa don weekly Hamma Zaki kan turawa dukkansu duk da cewa bai san wannan na wannan bane kawai turawa yake.
A wannan lokacin kuwa cikin pretty ya kara girma don haihuwa yau ko gobe ake tsammata mata duk da cewa can Naira Family babu wanda ya sani, sun dai san cewa tana da juna biyu amma basu san girmansa ba, to ma su da babu wanda ya taba taka gidan a cikin su in ka cire Hamma Saleem da suka zo kafin su koma Abuja, sai kuma su khairy da suka je.
Soyayya mai zafi ta kullu tsakanin Yaya Khalil da abar kaunarsa yesmeen, kullum suna tare, phone calls, chat duka ba a barsu baya ba amma kullum cikin takura mata yake akan don Allah ta barshi yazo gidansu. Tunawa da fadan da Hamma Zaki tayi musu yasa tace shikenan zata yi shawara. Nan ya bata lokaci.
A bangaren Fauzah da Ya Ishaq sai son barka don kuwa pure love suke shukawa, rana daya idan bata ji daga gareshi ba sai ta rikice haka a nasa bangaren don soyayyar da yake mata ta ninka wadda take masa. Ko da yace tunda sun gama school da anyi speech & prize givibg day nasu sai ya turo, bata musa masa ba don ta dade da mugun kamuwa.
A daya bangaren itama Ayrah tayi nata masoyin, Yaya Hammad Cousin brother dinta ne, dawowarsa Nigeria kenan daga Italy suka hadu da ita a gidansu taje gaida Mommynsa wacce take yaya ga Mommah. Tun daga nan suka dinke kamar chewing gum, shima dai sya tsaya a kan da anyi speech and prize giving daya nasu zai bayyanar da kansa a matsayin manemin aurenta.
A wannan lokacin ne kuma aka sanya ranar speech & prize giving na school dinsu, kowannensu shiri yake na musamman.
_Wannan kenan, Kuci gaba da bibiyar alkalamin Diamond Bhatool don jin yadda zata kaya_
_COMMENT & SHARE PLEASE_
[30/08, 12:00 PM] 💎Diamond_Bhatool💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““85&86”””
Shirye-shirye suke babu kama hannun yaro, tun daga kan kayan da zasu saka, takalma, jakakkuna, earrings, necklaces, wrist watches, rings duk sun tanada. Abunda ya rage suje printing centre ne don suna son Memo da kuma Jaka sai kayan ciye-ciye su snacks da mom ta dauki nauyin yi musu.
A yau juma'a ne kuma pretty ta tashi da matsanancin ciwon mara, ihunta da pretty taji yasa tayi sauri tazo tana tambayar lafiya, nan ta sanar da ita abunda ke damunta. Wayarta ta dauka, da face recognition nata ta bude ta shiga call logs a birkice, Sweetheart ta gani kawai tayi dialling, har kiran ya katse bas daga ba sai da ta kara a na biyun ya daga. Cike da tashin hankali tace “Hello Hamma, kazo gida Aunty Nabila ba tada lafiya kayi sauri don Allah ”. Daga haka ta katse sai sannu take jera mata ita kuwa banda zufa da ihu babu abunda take.
Few minutes sai gashi yazo, cak ya dagata suka nufi mota shima cike da tashin hankali yace Khairy ta biyo su. Wayarta kawai ta dauka ta bisu. Nearest hospital ya mikata, da sauri suka karbe ta sai Labour ward. Nan suka bar Hama Zaki yana ta zuwa da komawa. Ita dai khairy granny ta kira ta sanar mata suna asibiti Aunty Nabila ne zata haihu, kan kace me sai ga granny da Nenne sun iso.
Sai da ta shafe awanni kafin ta haifo yarinyarta fara sol mai mugun kama da Hamma Zaki, koda Midwife din ta sanar da su ta sauka lafiya kowa yayi farin ciki, nan ta tambaye shi kayan baby, sai a lokacin suka tuna baa zo da komai ba, Su kansu Midwives din sai da suka dara, nan suka rubuta masa abubuwan da zai siyo, tare da khairy suka fita ya ajiye ta a gida sannan ya kawo kayan babyn.
Can sai ga Nenne da farfesu da yaji hadi, a nan aka basu damar ganin baby, kowa masha Allah yake furtawa ganin tsantsar kamar da babyn keyi da Hamma Zaksan Kafin kace me dangi sai zuwa suke ana ganin baby.
Ko da khairy ta koma whatsapp ta hau tana babes labari ai Aunty Nabila ta haihu. Nan suka fara magana suna ta dariya. Video call tayi musu nan dukka suka yi connecting.
“Ayrah tayi gyaran murya tace Babes ina da magana da ku fa” khairy tace “To Ayrah muna sauraronki, kunsan ance in kaji kira to an samu”
Dariya tayi tace “To dama dai ina son magana da ku ne, kun san Hamma Hammad na gidan Dada Safina?” Ido Fauzah ta kanne tace “To me faru da shi, mun gane shi” Cikin inda-inda tace “Dama wai yace yana sona ne kuma wai zai turo manyansa bayan speech, ya kuke gani babes? ” a tare suka yi dariya Yesmeen tace “Haba no wonder naga kwana biyun nan kina yawan yin waya, ashe dai..” Fauzah tace “Yesmeen ni ina Yaya Khalil ne kam?” sai da ta juya ido su abunma dariya ya basu can tace “Wallahi yana nan, ya wani takura min wai zai turo kiji fah?” Khairy tace “To kuma meyeh don Allah ki bashi dama kawai musha biki kinji kawas” hararar wasa ta cilla. Khairy ta kara cewa “Ke zabiya Fauzah ina yaya Ishaq ke kuma, sai tisa jamaa kike gaba ke ina nakin?”
Dariya tayi tace “Har kin tuna min da barin zuciyata, yana nan dai nima dai cewa yayi zai turo nace ya bari nayi shawara”
Ihu khairy tayi tace “Kai zan zamo kirjin biki, to wai me kuke jira baku basu dama ba eh?” caraf Fauzah tace “Jira muke ke da Hamma Zaki ku bayyana abunda ke ranku” su duka suka kwashe da dariya ita kuma khairy ta hade fuska “wai ce muku aka yi ni da shi akwai abu a tsakanin mu?, to in ma mafarko kuke ku farka” Yesmeen tace “Ba wani mafarki ba khairy, ni na dade da gano ku, idan zaku cire girman kai ku fada ma to...” khairy tace “Lallai yau na tabbatar babes kunci kai! In banda haka ina hadin Hamma Zaki da _Yar Iya?_ ai abun babu hadi, ni dai kuyi min addua nima Allah ya bani mashinshini.”
Dariya dukkansu suka yi ba tare da sun yadda da zancen nata ba suka ce “In tayi tsami maji ai” dariya tayi tace “Ai babu abunda zai yi tsami, ku dai yanzu ku sanar da rabin zukatan naku kum amince don Allah. Amma fa har na fara kishi da su sun fara shiga tsakani na da babes ” Nan suka yi dariya suna fadin “Shikenan ta gidan Hammanmu”. Nan dai suka yi hira sosai, sai wajajen Azahar ta daura gurki sanin mutane zasu zo. Bata wani sha wahala ba ta kammala.
Sai la'asar aka sallamo pretty, sai gata tare da babynta kyakkyawa. Baa dade ba Fauzy kawarta da kuma Mami suka iso, kowa sai yaba kyan yarinya yake yi.
Washegari da safe tayi breakfast sai dai Nenne ta kira tace mata take yi da farfesu ko na kifi ko na nama, ai kuwa ta hadawa pretty sannan ta kai sama tare da na bakin nata. Tunda ta shiga suke binta da kallo, cikin ransu kowa yaba kyanta da haduwarta yake. Sai da ta fita Mami tace “Daughter wannan zankadediyar yarinyar fa?” yawu fauzy ta hadiye tace “She looks so awwn”. Murmushi kawai pretty tayi tace “Yar gidansu sweetheart ne amma ba mamarsu daya ba, watannin mu kusan shida da ita ”.
Baki bude Mami ke kallonta, can tace “Lallai daughter kin ban mamaki!, ina wayonki yake zaki bar wannan budurwa masha Allah a gidan mijinki?” kawar da zancen pretty ke son yi saboda haka tace “Kai Mami na, she's not that bad, babu ruwanta nace miki ita taje kuka da gidan fa yanzu”
Harara Mamy fa Fauzy suka aika mata. Mami tace “To mara hankali, wai anya ba sauyaki aka yi ba?, to bari kiji barin gidan nan zata yi, don kina zaune sai dai kiji ance zata aure shi”
An tabo mata wurin dake mata kaikayi ai kuwa tace “Bura uba! Ai dole ma ta tafi ta bar gidan nan, don akan sweetheart har kisa zanyi”. Harararta Mami tayi sannan ta dubi Fauzy tace “Fauzy dan bamu waje” ba musu ta fita ai kuwa Mami ta maiso da dubanta ga Pretty. “Ke mahaukaciyar ina ce Daughter, har kisa zaji iya a kansa ko kin manta da kudirin Daddyn ki ne?”
Ido ta kwalalo tace “Kai na manta wallahi Mami, kinsan ina son mijina Allah kuwa, nasan in na rasa shi bazan samu ya shi ba” “waye ya fada miki?” Mami ta katseta “To tunda kinfi sonsa fiye da mahaifin da yayi dawainiya daje shikenan, ni zan wuce gida yau dinnan ma” da sauri tace “A'ah mami wasa fa nake yi, ina na isa, yanzu dai miye abun yi?, nina ina so mu dauki fansa amma to ta yaya zamu fara, nidai gaskiya a hukunta babansa tunda shi yayi laifin ba shi ba”
“To sakarya” Mami ta fada “Bari kiji, in ba zaki bamu hadin kai ba shikenan sai mu sallama masa ke indai namiji ne”
“Yi hakuri Mami na, yanzu dai meye target dinku?”
Murmushi Mami tayi tace “Yauwah yar albarka anzo wajen, kinsan asarar da suka saka Daddynki yayi wancan lokacin, to shine muka yanke shawarar ranar sunanki ayi kidnapping dinsa, sai a saka tarar ninkin kudin tare da barazanar in ba'a bayarba zaa kashe shi, ina tabbatar miki zasu bada kudin don yadda suke mugun son sa” dariya pretty tayi tana rungume Mamin “Da sauki, ni zan taimaka kwarai saboda farin cikin Daddy na”
Nan suka cigaba da hirarsu.
Bangaren Fauzy gajiya da jira tayi hakan yasa ta sauka parlourn kasa tayi zamanta. Taga wucewar khairy zuwa sama sai wani mayetaccen kallo take binta da shi, ita kuwa bata san ma tana yi ba. Dakin Hamma Zaki zara gyara sai taji alamar magana kawai sai taji bata yadda da maganar ba hakan yasa ta kashe kunne don taji. Abu daya taji ance “Kinga dole zasu bada kudin don yadda suke sonsa” daga haka taja baya tana dafe kirjinta, “Waye wannan zaa bada kudi akansa?” a tsorace ta shige ta gyara masa dakin zuciyarta babu dadi.
Ko da ta dawo bedroom dinta tunani taje akan abunda taji Aunty Nabila na tattaunawa da Mamarta. Ganin bata fahimci komai ba yasa ta sharar da zancen tana fadin “Idona akanku kuwa” daga haka taci gaba da harkokinta.
A bangaren Fauzah kwanan nan sai takurawa Mom take wai Hamma Zaki da khairy soyayya suke. Mom bata musata ba don kuwa sunga Zahiri ranar sauka amma sai ta share. Ganin Mom taki bata hadin kai yasa ta koma wurkn granny, gabadayansu suka hada kai suna nunawa granny lallai fa Hamma Zaki soyayya suke da Khairy. Granny tace “Ashe kuwa?, lallai zasu hadu da ni, shine ko su fada min daga Mazan har ita Ummul khairyn?” kasa-kasa suka ce “Granny muma bata fada mana ba, zahiri muka gani, baki ga yanzu Hamma baya zuwa gidan ba?” granny tace “Kwarai kuwa” murmushi sukayi suka ce “To kin gani, soyayyarsu suke zubawa kinga matar gidan ita koyaushe a daki take” granny tace “Yar banza ba, barni da ita ai ban manta rashin albarkar sa tayi min ba kuma sai na saba mata, Bari dai lokaci yayi, ni kunje kun duba jaririyarta mai kama da Maza kuwa?”
“A'ah” granny tace “To maza ku shirya gobe driver ya mika ku ko?, kunga bai dace ace baku je dunata ba.” da “To” suka amsa daga nan kuma suka fice suna farin ciki don kuwa sun hamgo nasara a tafiyar tasu. Burinsu yanzu bai wuce su hada wannan alaka ba dkn tun ba yau ba suka lura da Hamma da khairy na son junansu, shi takama, izza, uwa uba miskilanci ita kuma shariya. Sun kuwa yi alkawarin sai sun hada ko dan wannan shegiyar Aunty Nabilar.
Ko da suka shirya cewa Mom suka yi zasu je café ne wurin yin Memo, Atm nata ta basu daga nan suka wuce. Lallai yaran nan, siyayyar jakakkuna suka yi sosai sannan suka wuce café din, nan suka bayar ayi musu stamp na graduation sannan ayi musu Memo. Bayan ya ciri kudinsa suka wuce can gidan Hamma Zaki zukatansu wasai.
Ko da suka ga baby ta matukar tafiya da imaninsu saboda tsananin kamarta da Hamma Zaki. Sai da suka huta tukun suka kira driver yazo ya mayar da su amma kafin nan sai da suka bi suka amshi kayansu a can café din da suka je, daga nan suka koma gida.
Da suka nunawa Mom abunda suka siyo bata ce komai ba sai ma yabawa da tayi da kayan, nan ta amshi ATM dinta, Fauzah tace “Mom gidan Hamma muka je ganin baby dai, wallahi kin ganta kamar Hamma Zaki tsabagen kama” murmushi kawai tayi tace “Zaku cika ni da surutu ko, To Allah ya raya ta, ku wuce ku adana abubuwan naku” daga haka suka kwashi shirginsu suka nufi part din granny, a dakin khairy suka ajiye sannan suka fadawa granny sun dubo baby, khairy ma na gaiisheta.
Wannan kenan!
_Toh fans kunji shirin Mami da pretty ko? Ya kuke tunanin zaa kare? Wai ma me ahalin Hamma Zaki suka yiwa baba n pretty ne kam har yake shirin daukar wannan fansa? Ga kuma Babes sun hadawa khairy tarko bayan babu alakar komai tsakaninta da Hamma Zaki, ko me kuke tunanin zai faru? Kuci gaba da bibiyar alkalamin Diamond Bhatool don jin cigaban labarin._
_COMMENT & SHARE FISABILILLAH_
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““87&88”””
Washegari khairy bata yini a gidan ba, tare da babes suka wuce don karasa hada abubuwan bukatarsu. A daya bangaren kuma pretty ta kudiri aniyar korar khairy saboda hudubar shaidanci da mahaifiyarta tayi mata.
*FLASH BACK*
A shekarar 2005, lokacin Alhaji Saminu Hambali na rike da mukamin Special adviser na Maigirma governor of Katsina state, matashin dan siyasar yana da son abun