Showing 102001 words to 105000 words out of 135404 words
ƙira number na Hamma Zaki, ko da ya ɗaga bayan sun gaisa yake sanar da shi cewa in ya shigo gidan ya neme shi.
Ya Ishaq ya sanar da Fauzah cewa an saka bikin su watanni biyu masu zuwa, haka sauran ma suka sanar da su, zo ku ga murna don haɗuwa suka yi dukkansu a ɗakin Khairy.
“Kai wallahi can't wait in zama Mr. Hammad, gabaɗaya na ƙosa, Kai kun san yadda nake son shi kuwa?” duka Khairy ta kai mata tace “Kina ɗiyar fillo amma babu kunya” Ayrah tace “Kunyar lafiya kuma, ai ba wani Fulanin nan, yanzu fah we're civilised ” ta ƙarasa tana ɗaga wa Khairy gira. Ƙwalalo ido tayi tace “Kina nufin da ba'a waye ba kenan, elaborate Mrs...to be” ita ma ta kanne mata ido.
Yesmeen da bata ce komai ba sai murmushi take saki tace “Rabu da ita dai, Ni dai Kinga ban ce ina ɗokin zama Mrs. Khalil ba” ta ƙarasa a shagwaɓe, dariya dukkansu suka yi Khairy tace “Amma Yesmeen kin fi kowa iya shege ” “Ai kuwa dai” Ayrah ta amsa mata.
Suna zaune suna haukarsu Nenne ta shigo har ɗakin, har ga Allah suna matuƙar burgeta yadda kansu yake a haɗe kuma suke ƙaunar juna. Murmusawa tayi tace “Ina neman ku” daga haka ta saka ƙafa tayi waje. Ganin lokacin sallah yayi yasa suka yi sallah, bayan sunyi sallah suka nufi part ɗin Granny don amsa ƙira.
Ɓangaren Mamin Pretty ta ƙira wayarta, bayan ta ɗaga suka amsa take tambayarta flight na ƙarfe nawa zata biyo?. Ƴar ƙaramar dariya pretty tayi tace “Mami ai ba zuwa zanyi ba, kawai in zaki turo mai taimaka min shikenan don mun samu daidaito da Sweetheart ”
Wani uban ashar ta lailayo tace “Lallai Nabila yau na tabbatar da. Cewa baki da hankali, ki haihu kuma ki ce ba zaki dawo gida ba, to uban waye zai gyara ki?”
Shagwaɓe fuska tayi tace “Ni dai Mami na faɗa miki ai mun daidaita da shi, kiyi haƙuri ki turo mai taimaka min kawai, I'm adult na San me ya dace da rayuwa ta”
Cike da sarewa Mami tace “Shikenan tunda haka kika zaɓarwa kanki sai na sallamar masa ke tunda shi kika zaɓa, zan turo Nasiba ƴar gida Yaya, aurenta ya mutu zata zo sai ta taimaka miki”
“Yauwa First love, sai an jima ”
“Ki shafa kan jika ta” daga haka ta katse ƙiran.
_Sorry for the late update_
_COMMENT PLEASE_
[12/09, 9:59 a.m.] Famanté 💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““103&104”””
Ko da suka tafi ɓangaren Nenne, sallama suka yi suka shiga, basu tarar da ita a parlour ba suka zauna. Ko da Nenne ta fito ta tarar da su ita ma zama tayi.
In a serious tone tace “Ku sauarare Ni!”
Kai suka duƙar don basu taɓa jin Nenne tayi magana da irin Muryar nan ba kasancewr ta mace mai son Raha.
Ta ƙara da faɗin “Kamar yadda kuka sani don nasan kun riga kun sani, yo kun sani mana samarin zamani sun faɗa muku” ta ɗan yi shiru tace “Ɗazu iyayenku suka tsayar da ranar bikin ku zuwa watanni biyu ea zasu zo, saboda haka ku saurare ni ko dan Baraka zata taro nan gobe in Allah ya kaimu zata muku bayani” daha haka ta miƙe tana faɗin “Khairy biyo ni”
Tana shigewa suka haɗa idanuwa suna sakin dariya, harararsu Khairy tayi tana faɗin “Ƴaƴan zamani” daga haka ta wuce zuciyarta na wani irin bugu, ko me yasa Nenne ke son keɓewa da ita oho. Ganin ta tafi suka kalli juna Fauzah tace “Allah yasa Khairy da Hamma za'a haɗa su” “Ameen sauran suka amsa”
Ko da Khairy ta isa bedroom ɗin Nenne ta tarar da ita zaune a bedside, hakan yas ta zauna a ƙasa daidai ƙafafuwan Nennen. Kanta ƙasa bata ɗago ba tace “Gani Nenne”.
Nenne tayi gyaran murya tace “Khairy! Wane matsayi kika bamu?, ina nufin Ni, Mommahnku da kuma Mom ɗinku?” rasa ina tambayar Nenne ta nufa tayi sai ta tsinci kanta da faɗin “Matsayin iyaye na”
Murmushi irin na manya Nenne ta saki kafin tace “Naji daɗin hakan, Allah yayi miki albarka”
Kanta ƙasa tace “Ameen”
Ɗan shiru ne ya wanzu sai Nenne tace “To Khairy, ina fatan ba zaki ƙi Abunda zan faɗa miki yanzu ba”
Khairy tace “E Nenne in sha Allah, ai kun wuce haka a wuri na, duk abunda kuka yi min nasan ya dace da ni”
Murmushi a karo na b adadi Nenne ta kuma yi sannan tace “Yauwa Ummul Khairy, kasancewar ƴan uwanki sun fitar da mazajen aure ko in ce an zo neman aurensu yasa Hajiya wato Granny tace ba za'a yi babu ke ba, ba wai don kin rasa mai son ki ba ko wani abu yasa tace Daddy Ku ya duba wani makusanci da zai haɗa ku wanda zai kula da ke kuma ya riƙe ki amana” dumm gaban Khairy ya bada cikin ranta tace “Na shiga uku, shikenan na rasa shi” Nenne ta cigaba da faɗin “Shine daddyn ku yayi wa wani abokinsa magana kasancewar yanada yaro da matarsa ta rasu kuma kwanaki ya taɓa tambayar Daddyn naku ɗaya a cikin ku, to Ummul Khairy, duk da bani da tabbacin zaki amince ɗin, amma zan so hakan gaskiya saboda mutum ne mai nagarta da sanin ya kamata, ina da tabbacin kika aure shi ba zaki yi da na sani ba.”
Shiru Nenne tayi tana jiran ji daga Khairy. Wani yawu da ya maƙale a maƙogoronta ta haɗiye wanda ya bada sautin ƙut!, a hankali tace “Nenne ku ɗin iyaye na ne, nasan ba zaki yi min zaɓin da zai cutar da Ni ba, Allah yasa albarka ciki ” ta faɗa tana ƙara sauƙar da kanta ƙasa gudun kada Nenne ta ga hawayen da ke shirin zubo mata. Murmushi Nenne tayi tace “Ameen ameen Allah yayi miki albarka Khairy”
“Amin” ta faɗa a gajarce.
“Shikenan zaki iya tafiya”
A hankali ta miƙe ranta babu daɗi ga yadda zuciyarta ke bugu da sauri da sauri, kamar wata ƴar maye da ta fito sai ta rasa hanyar bi. Da ƙyar ta ga hanya ta fito da sauri ta koma part ɗin Granny, hamdala tayi ganin Granny na can bedroom nata. Ɗakin ta ta shiga tare da faɗawa kan gadonta tana sakin wani kuka mai ban tausayi.
Cikin ranta ta furta “Shikenan na rasa wanda nake so!” hawayen ta ta goge cike da karfin guiwa tace “Dama meye amfani, wanda nake so ma ba sani yayi ba, Ni kaina ban san ina don shi ba ai sai yanzu”. Ɗan kwaɓw fuska tayi tace “To meye laifi, Allah yasa dai mutumin ya so Ni, dole yanzu na manta da kai Qalb!” haka ta ƙarashi surutunta har bacci ya kwashe ta.
Ɓangaren su Ayrah suna bedroom ɗin Yesmeen ne suna jiran dawowar Khairy ganin shiru babu alamarta yasa suka yi tunanin ko ta wuce ne, su ukun suka jera har zuwa part ɗin Granny. Ko da suka shiga bedroom ɗin Khairy mamaki ya cika su, when ta taho har tayi bacci?. They've no other choice but to leave.
Bacci tayi sosai wanda da ka ganta zaka tabbatar ba daɗinsa take ji ba. Around 3:19pm ta Farka ɗauke da addu'a a bakinta, miƙa tayi tana turo baki gaba ita kaɗai. Sai da ta ƙara wasu ƴan mintoci kafin ta ziro kyawawan ƙfafunta ƙasa, toilet ta shiga ta watsa ruwa, bayan ta saka kaya ta fito don cin abinci. Duk irin yadda take jin bakinta babu ɗanɗano hakan bai hana ta naɗar abincinta ba saboda har yanzu Khairy bata wasa da cikinta.
Bayan ta ci abinci ta ɗauki wayarta tare da shiga gallery tana ƙara kallon pictures ɗinsu har ta zo kan waɗanda suka yi ranar sauƙarsu, ita da Hamma Zaki ne tsaye, duk da cewa fuskarsa babu dariya amma sihirtaccen kyansa a bayyane yake, “Handsome” ta furta a zahiri sai kuma ta turo baki gaba. Ganin lokacin sallah yasa ta tashi ta gabatar da Asr ɗinta. Tana idarwa bayan tayi azkar nata ta wuce part ɗin Mom.
Ba ita ta dawo ba sai bayan maghrib hakan kuma saboda ta ragewa kanta zaman kaɗaici ne.
Kamar kullum yau ma ya shigo suka gaisa da Granny, ya jima zaune suna hira da Granny sai dai rabin hankalinsa baya kanta, in kaji maganar sa to uhm ne ko a'a. Ganin shiru bai ga giftawarta ba yasa ya ɗan ji babu daɗi, ba kuma ya so ya tambayi Granny don sai tayi masa wata fassarar, duk irin yadda yaso ganinta bata fito ba, hakan yasa shi fita ransa babu daɗi.
Sallar Isha ya gabatar, tare da Daddy suka dawo suna ƴar hirarsu. Daga shi sai Daddy sai kuma Mom suka yi dinner coz Fauzah suna can part ɗin Mommah. Bayan sun kammala Mom na jefo hira, can dai Daddy yayi gyaran murya yace “Baba na”
Hankali sa ya mayar ga Daddy saboda in dai yaji ya ƙira shi da sunan nan to magana mai muhimmanci zasu yi.
Daddy yace “Kana ji na ko?, a wancan karon ka kawo matar da zaka aura da kanka though Baka cikin hayyacinka a lokacin” gaban sa ne ya faɗi sai kawai ya gyaɗa kai
Daddy yaci gaba “To Hajiya ta sane mu da zancen rashin jin daɗin zama da iyakinka shiyasa ta saka a nema maka auren jikarta ina nufin jikar ƙawarta, fatan mu dai ba zaka watsa mata ƙasa a ido ba”
Har ga Allah bashi da burin hakan don zuciyarsa ta riga ta kamu da son wata, ya riga da ya yanke shawara a kan wannan zaɓi sai dai kashi Daddy yayi masa katanga don ba zai iya ƙetare umarninsu ba. Jin shirun yayi yawa yasa Daddy faɗin “Kayi shiru Ubana” kamar babu wata damuwa abunka da namijin duniya ya dake yace “Allah ya amince Nagode Allah. Ƙara girma” murmushi Mom da Daddy suka yi tare da amsawa da Amin. Mom ce ta ƙara da faɗin “Sannan ga kuma ƙannenka, su ma duk an saka ranar bikin, sai ka samu Hajiya ta faɗa maka gidansu yarinyar ku fara shiri don tuni Daddyn ku sun tsayar da magana da iyayenta.
Gabansa ya ƙara bada wani sautin cikin ransa yace “Shikenan ta faru ta ƙare, wai anyi wa mai dami ɗaya sata” hope ɗinsa kenan, to shima ya ruguje, wata iska ya furzar tare da sauƙe ajiyar zuciya. Bai wani jima ba kuwa yayi musu sallama don har ga Allah jikinsa ma ba wani daɗi yake masa ba.
Ko da ya koma gidansa ne damuwarsa ta ragu don yadda pretty ke ɗan nuna kulawarta gare shi, baby Humairah ma dai ba baya ba, yarinya sai kyau take ƙarawa abunta.
Washegari da safe Khairy sun tashi da aikace-aikace saboda zuwan mazajen ƴan uwan nata, abun mamaki su ukun duk sun san juna, hakan ne ma yasa suka haɗa wannan zuwa wuri ɗaya, ita dai Khairy kawai tana dagewa ne amma kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa she's not in mood, in sun tambaye ta sai tace babu komai.
Sai wuraren Zuhr suka kammala don ma Mom na taimaka musu da wani abun. Guest house Dake cikin gidan suka gyara tsaf, bayan sun kammala suka kai kayan tarbar baƙin zuwa can daga nan suka sheƙa wanka da kwalliya banda Khairy da taƙi ko da shafa mai ne, duk yadda suka yi sai haƙura suka yi, a cewarta ita ma sai nata zai zo tukun tayi. Dariya ma ta basu tunda sun riga sunji batun daga wurin Mommah inda take sanar da su ai ɗan gidan abokin Daddy zata aura wanda kwanaki wai matarsa ta rasu.
Da yamma baƙin suka iso tare da wasu friends ɗinsu, sai da suka raka su ɓangaren Granny, Mom, Nenne da Kuma Mommah suka gaida su kafin su raka su guest apartment ɗin da yasha gyara ƙamshi kawai ke tashi. Dining ɗin da ke ɗauke da dogon table da kuma chairs goma sha biyu well arranged suka nufa. Khairy da ke son kawar da damuwarta tace “Na hutar da ku kada ku gaji, bari nayi serving baƙin, ku kuma yayyen mu a sha love” ta ƙarasa tana dariya. Da yake tare ake da mazajen aure basu tanka mata ba sai ma murmushi kawai da suka yi.
Bayan tayi serving ɗinsu ita ma ta zuba nata, friends ɗin su kuwa sai kallonta suke don kuwa ta tafi da imaninsu. Ga kyan jiki ga kuma murya zazzaƙa. Ganin irin kallon da suke Binta da shi yasa ta miƙe tana faɗin “Bari na ɗan baku space naga kamar ya Ishaq na harara ta”
“Innalillahi, Ni na isa, ƴar uwa guda zan harara?, Baby ki faɗa mata ban harare ta ba” ya ƙarashe yana kwantar da murya tare da maida dubansa ga Fauzah wacce ke famar sakin murmushi.
Khairy tace “wasa nake, amma zan ɗan fita ne ina da wani uzuri, yayyen mu na bar muku sisters na amana Please, ko ƙuda ban yadda ya taɓa su ba”
Dariya suka yi gabaɗaya, Hamma Hammad yace “Kada ki damu sister, har ki dawo babu abunda zai taɓa su, musamman my Queen, zanfi kula da ita” caraf Yaya Khalil yace “Kada ki damu nima dai ba zan bar wani abun ya taɓa sugerplum ba.”
Ɗan harara Yaya Ishaq ya kai musu sannan ya yamutsa fuska yace “Zaki samu Heartbeat cikin aminci sister sai kin dawo” murmushin ƙarfin hali tayi tana waving musu hand. Daga na ta koma bedroom nata.
Tana fita Prince Jalal, ɗan Sarkin Adamawa ne wanda shi ma yana cikin gang nasu Hamma Hammad, tare suka yi secondary school gabaɗayansu sai dai karatunsu na gaba ne kowa ya raba gari zuwa ƙasashen ƙetare mabanbanta ya sauƙe ajiyar zuciya tare da dawo da dubansa ga mutanen dake cin abincin. Murmushi yayi yana faɗin “Allah yasa ba tsuntsun wani bane, don na riga nayi gamo yau”. Abulbashar da ke gefen sa ya make shi “Kai fa baka isa ba, don na riga ka” nan fa rikici ya kaure Prince na faɗin wallahi ba zai haƙura ba ya riga Abulbashar shima abulbashar na faɗin wallahi baya haƙura sai dai kowa tashi ta fisshe shi. Iya ruwa iya fidda kai in ji hausawa.
_Toh fah kunji Wata badaƙala, na so a ce Hamma Zaki ya auri Khairy ko dan ta gyara zaman pretty da kyau amma ƙaddara ta riga fata. Ga Hamma Zaki da yake da hope shima an ruguje shi ba shi da makama. Kunji Hajiya Khairy kuma ashe she's in love, ko waye wannan wanda take so ɗin da ƙaddara ke shirin raba su?, Jalal and Abulbashar Suma sunce sai Khairy, ko ya kuke tunani?, comments ɗin ku ne kaɗai da kuma reacting zai sa na bada himma wurin post. Diamond lady ce._
_SHARE & COMMENT FISABILILLAH _
[15/09, 10:00 p.m.] Famanté 💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““105&106”””
Ko da Khairy ta bar ɗakin direct bedroom na ta ta nufa, bisa makeken gadonta ta faɗa tana sakin wani kuka mai ban tausayi. Haƙiƙa auren mai son ka ma wani abu ne, tunawa da yadda zaɓin babes suke tarairayarsu da kuma nuna tsantsar kulawarsu gare su yasa ta sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya. Haƙiƙa ta cutar da zuciyarta da saurin amincewa da tayin ɗan abokin Daddy, me yasa ba ta faɗi nata zaɓin ba bayan ba hana ta zasu yi ba?. Ita kaɗai ta jijjiga kai tana faɗin “A'a! Sun cancanci su zaɓar min Miji ba sai wanda nake so ba, to Ni wanda nake so ɗin ma ai bani da tabbacin yana so na, dole fa na cire shi na rungumi kyakkyawan zaɓin da aka yi min.” miƙewa tayi ta nufi toilet tare da wanke fuskarta ta goge sa towel sannan ta koma kada suyi tunanin ko akwai wani abun.
Shigarta ke da wuya ta nemi seat kusa da Prince ta zauna coz iya shi ya rage, kallonta yayi yana murmushi yace “Ƴar uwarmu ke kika yi serving namu duka, oya nima bari nayi serving naki” kamar wata wawuya ta dube shi tace “A'a baƙo guda, kada ka damu zan iya ai, na gode” daga haka ta saka cakes biyu a bowk ta fara ci a tsanake.
Ko da Abulbashar yaji wani sabon kinibibi wurin Prince, harara kawai yake aika masa, amma da yaji amsar Khairy gare shi sai ya mas gwalo. Bayan sun gama ci suka koma parlour suka zauna, ita kuma Khairy ta ce bari ta bawa masoya wuri, jin hakan yasa Prince faɗin “Nima bari na basu wuri” Ba shiri Abulbashar yace “Nima da nake single pringles Bari in yi waje” su dai su Hamma Hammad dariya suka yi suna faɗin “Ku dai kuka sani, ku bamu wuri ko ma ɗan sake”.
Steps uku tayi bayan ta fita ta jiyo muryar Prince na faɗin “Sister!” ɗan dakatawa tayi amma bata juyo ba, sai da ya ƙaraso dai-dai da ita yace “Ina kuma zaki je?, kin tafi kin barin?” cikin ranta tace “Wannan kuwa lafiyarsa ƙalau?” sai kuma ta kauda kai gefe tace “Sorry, mu zauna can” tana nuna masa balcony da ke a guest apartment ɗin. Sun zauna kenan sai ga Abulbashar da sauri ƙafarsa har harɗewa ta ke kamar zai faɗi. Yana isowa yayi sallama shima ya zauna. Duk da cewa Prince bai ji daɗin zuwansa ba amma sai ya waske ya fara jan Khairy da taɗi, tun tana replying sama-sama har ta ware.
Sun