Showing 9001 words to 12000 words out of 135404 words
daga guiwar sa zuwa idanuwan sawun shi. Bai cika tsayi sosai ba sai dai yana da ƙira mai kyau wacce ke nuna zallar mazantaka da kuma jarumta...irin wannan physique nashi ake kira da *athletes*
Fari ne tass kamar madara, da ganin skin nashi zaka san hutu da jin daɗi ya zauna jiki, uwa uba yadda fatar tashi ke wani glowing tamkar wani tauraro. Yana da idanuwa manya manya wanda suke farare tas sai kuma ƙwayar idon shi da ta kasance brown. Colour na ƙwayar idon ne ya sa idon nashi ke ruɗan mata ga kuma eyebrows nashi masu yalwatuwar baƙin gashi.
Yana da siririn hanci da bai fiye faɗi ba sai kuma ɗan madaidaicin baki mai ɗauke da thick pinkish lips. Sajen da ya kewaye fuskar shi kamar wadda aka zana shi ba ƙaramin ƙarawa fuskar shi kyau da kamala yayi ba.
Kan sa bai fiye girma ba ga kuma wata Black shiny suma da ta cika kan wanda ta sha wani haɗaɗɗen hairstyle da yasa na kusa sumewa.
(“Masha Allah, Tabarakallahu Ahsanul Khaliqiin”, abunda na iya furta wa kenan).
Ganin yana shirin sauƙowa yasa wasu daga cikin sojojin matsowa kusa da shi suna sara mishi yayin da ya ƙara haɗe fuskar shi tamau ya fara tahowa.
Amsar Briefcase dake hannun shi ɗaya daga cikin sojojin yayi wasu kuma suka take mishi baya har zuwa cikin wannan white Zenvo ST1 ɗin. Shigar shi kuma yayi dai-dai da sanya trolley nashi a Boot da ɗaya daga cikin sojojin yayi.
Basu tsaya ɓata lokaci ba suka tayar da motocin yayin da jiniya kaɗai ke tashi kan titin. Sun yi tafiya sosai kafin su iso wani katafaren unguwa wacce naga an mata alama da “BANANA ISLAND... Billionaires' paradise”.
*LAGOS STATE*
*BANANA ISLAND*
Banana Island da ake wa take da billionaires 'paradise yanki ne cikin Lagos, yankin da in ka shiga zaka iya manta cewa bauta Ubangiji ya turo ka nan duniya, yankin da ba kowanne mahaluki ke iya samun matsuguni a ciki ba. Yankin da ya tara manya-manyan masu kuɗi dake a faɗin Nigeria.
Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin suyi horn a dai-dai wani big and luxurious mansion, tuni gateman ya buɗe zirrrrrrr convoy ɗin ya wuce ciki. Dai-dai parking space suka yi parking, sojan da ke tare da wannan kyakkyawan guy ɗin ya buɗe mishi ƙofar matar, bayan ya fito wasu daga cikin sojojin wanda nake kyautata zaton sune Guards nashi suka biyo bayan shi. Dai-dai ƙofar da zata sada ka da cikin mansion ɗin ya ɗaga musu hannu, tuni suka juya suka bar ɗaya wanda ke riƙe da Briefcase nashi da kuma trolley.
Da hannu yayi mishi alamar ya miƙa Briefcase ɗin sannan ya nuna trolley ɗin, babu ɓata lokaci shima ya koma wajen sauran sojojin yayin da motoci biyu suka fice sauran kuma suka fito, wasu na tsaye bakin gate wasu kuma suka kama wurare daban-daban suka ƙame.
Riƙe da Briefcase a hannun shi na dama wanda ke sanye da wristwatch ƙirar Amelia Erhats sai left hand ɗin shi da ke janye da trolley ɗin. Tsam ya aje trolleyn ya danna password na entrance door na mansion ɗin.
Janye da trolleyn ya shiga ciki (nimah na bishi don ɗauko wa fans na report).
Masha Allah! Wani makeken haɗaɗɗen parlour da nayi arba da shi sai da zuciya ta ta yanke, babu abun da ke tashi a parlourn sai wani sassanyar ƙamshi mai kwantar da zuciyar mai shaƙar sa, haɗaɗɗun kujerun dake ciki wanda aka yi L-Shape arrangement da su white color ne, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci Naira tayi kuka, da yake ɗakin akwai duhu sai da ya janyo remote na light ɗin tare da switching nashi on, nan da nan haske ya gauraye, sai a yanzu na fahimci ashe komai na parlourn white colour ne kama daga kujerun, Centre table, curtains har zuwa paint na parlourn. Tsaf-tsaf Kamar dai akwai mai rayuwa a ciki haka parlourn yake haka makeken plasma dake manne jikin wall na ɗakin babu ko alamar ƙura ajiki. Jikin wall na ɗakin kuwa frames ne masu ɗauke da pictures iri-iri.
By the side kuma wani keɓaɓɓen waje ne da nake kyautata zaton dining area ne. Ban bi wurin ba ganin ya wuce ta wani corridor Wanda zai sada ka da staircaae na gida, a nutse yake takawa kamar ba zai wuce ba har ya iso saman, wani irin tsari da wurin ke da shi ba'a magana, ta wurin da muka bi dai 2bedrooms ne yayin da guy ɗin ya shiga first one.
A nan na ƙara tabbatar da cewa favourite colour nashi is white duba da yadda komai na ciki yake fari tas including the furnitures.
Bisa makeken bed ɗin dake shimfiɗe da white bedsheet ga kuma white blanket jikin pillow ɗin da ke sanye da white colored pillow cases ya ajiye Briefcase nashi yayin da yaja trolleyn kusa da white closet dake gefe.
Bai tsaya ba yayi undressing kayan da ke jikin shi, ya bar iya wani Black boxers sannan ya nufi wata ƙofa da nake kyautata zaton toilet ne.
Sai da ya shafe fiye da mintuna 35 kafin ya fito ɗaure da white towel a ƙugun shi yayin da yake drying sumar shi da ta jiƙe da ruwa ta samu damar kwanciya lufff.
A gaban dressing mirror dake ɗauke da creams, perfumes, jail, and others jere ya zauna, sai da yayi drying sumar shi da hand dryer kafin ya fara shafa mayukan wurin ɗaya bayan ɗaya. (Haba dole skin nashi yayi glowing irin wanga provision duk na fata haka😂).
Yana gama shafa mayukan ya miƙe ya nufi closet ɗin shi, wata white jallabiya ya janyo daga jikin hanger sannan ya sanya ta daga nan ya fara fesa perfumes dake jere gaban dressing mirror ɗin, nan da nan wani sassanyar ƙamshi mai tsuma zuciya ya gauraye ɗakin.
(Ni kuwa nace waɗannan perfumes Bamu da su a nan Nigeria wataƙila daga wani wajen ya zo da su).
Bayan ya gama kimtsawa tukun ya samu damar zama a bedside tare da janyo Briefcase nashi, phones biyu naga ya ciro daga ciki, ɗaya ƙirar Samsung Galaxy S24 ultra sai kuma wata Nokia brand phone.
Zaro da laptop ɗin shi ƙirar Luvaglio wacce tunda nake ban taɓa ganin irinta ba.
Briefcase ɗin ya ajiye a sidedrawer dake ɗakin sannan ya haye makeken bed ɗin shi. Nokia phone ɗin ya ɗauko tare da dialling wata number, ana picking call ɗin yace: “Assalamu Alaikum” cikin wata murya da na gagara gane larabci ne ko turanci ko dai wani Yaren na daban sai dai cikin zuciya ta yaba wanna murya mai daɗin sauraro nake.
Banji meh aka ce a ɗaya ɓangaren ba can yayi murmushi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskar shi.
“Barka da rana Mom”
“Eh ban jima da isowa ba, yea, I'll be there tomorrow morning in Sha Allah.... can't wait to see u Mom.... alright don't forget to prepare my favorite please....ohk bye Mom I love u” ya ƙarasa yana sakin kiss 😘 ta wayar sannan yayi hanging call ɗin.
(Ni Bhatool mamaki ya hana ni magana jin harshen Hausa a bakin wannan haɗaɗɗen guy Wanda Sam bai yi kama da Nigerians ba)
Phone nashi ƙirar Samsung ya janyo bayan ya latsa ta na tsawon five minutes ya ajiye ta kusa da Nokia ɗin tare da janyo Laptop ɗin shi.
GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU ƳAN UWA NA ABABEN ƘAUNA TA DA KUKE ƘARFAFA MIN GUIWA A KOWANE LOKACI.....Seemah and Shaheeda! ALLAH YA ƘARAWA RAYUWAR KU ALBARKA.
FANS ƊINA NA LITTAFIN ƳAR IYA KUMA GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU MUSAMMAN MASU BIBIYA TA DA KUMA ZABGA MIN COMMENTS HAR DA MASU TAYA NI SHARING....ALLAH YA BAR ƘAUNA....
KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY (GARKUWAR NAZARI WRITERS).
PLEASE COMMENT & SHARE.
[4/28, 8:18 AM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘11&12’’’’'
Danne-danne ya fara almost 24minutes kafin ya aje laptop ɗin tare da phones ɗin shi.
Ƙaramar wayar shi da tayi ringing yayi picking tare da kara ta a kunnen shi. Ban san me aka ce ba a ɗaya ɓangaren can guy ɗin yace
“Alright, I'll be there now"
Daga haka yayi hanging call ɗin.
A hankali ya ziro kyawawan ƙafafun shi ƙasa tare da sanya takalmin dake bedside ɗin. Sauƙa downstairs yayi tare da buɗe door. Wani soja ne ya miƙo mishi manya-manyan leathers ɗin da alamau yayi order ne and it seems like abinci ne.
Kallon sojan yayi tare da faɗin
“Let me have one, the remaining is yours”
Kamar yadda ya umarta haka ya miƙa mishi tare da faɗin “Thank You sir” ba tare da nuna alamun ya ji shi ba ya koma yana rufo ƙofar.
A dai-dai dining area ya ajiye leather tare da wuce upstairs, ganin lokacin sallah ma yayi yasa ya shiga toilet, watsa ruwa yayi tare da ɗauro Alwala. Yana fitowa ya shimfiɗa praying mat tare da tada sallah.
Captain Alee Muhammad Naira Kenan, kyakkyawan matashi son kowa ƙin wanda ya rasa.
Ɗa na biyu wurin Gen. Muhammad Naira da kuma Dr. Rohmoh Isiaq.
Su uku Allah ya bawa iyayen su, Yaya Saleem shine babba, sai shi daga nan kuma Autar su Fauzah.
Daddyn shi Haifaffen jihar Adamawa ne bafulatani Usul wanda da ka gan shi zaka fahimci haka, Mom ɗin shi kuma daga India Daddy ya auro ta Lokacin sun je wani muhimmin taro ta maƙale masa ita ala dole sai ya aure ta. Irin kyau na Mom da kuma goyon bayan iyayen ta da ta samu kan batun yasa ya amince suka yi aure.
Alee Matashi ne mai jini a jika, shekarun sa bazasu wuce 26years ba sai da yana da ƙirar jikin wani ɗan 30's ɗin. kyakkyawane ajin ƙarshe ga kuma uwa uba iya ɗaukar wanka. Duk da kasancewar shi youngest captain a Nigeria sai dai yanayin kwarjinin da yake da yasa colleagues nashi bashi wani girma na musamman, baya shiga abinda bai shafe shi ba haka shi ba ma'abocin yawan magana bane....miskili number 1 toh Yaya Alee ne shiyasa duk jarabar mata hardly kaga sun samu ko da kalma ɗaya ne daga bakin shi.
Main house nasu a can Adamawa yake, Uncle Suraj da Uncle Bello da kuma Daddyn shi duk a family house nasu suke. Rayuwar su rayuwa ce irin ta ƴan gayu kuma ƴan boko duk da kasancewar su Fulani ne, Granny kaɗai ke ƙaƙabewa al'adun su na Fulani.
Cikin familyn su kuwa babu wanda baya shakkar Hamma Alee....laƙabin da suka manna masa kan bayyanar da hakan “Zaki”.
Shi sam a rayuwarsa baya son hayaniya komai ƙanƙantar ta...in kaga yana dariya kuwa to tare da Areef ne son ɗin Yaya Saleem.
*Wannan kenan*
★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Tunda suka ɗunguma cikin kasuwar ta fara tunanin me zata ci ne mah, dai-dai wata rumfa da Iliyasu ke saro bread yayin da sauran ƴan gari ke sara a wurin shi suka biyo. Yana ganin su ya cillo wani tsumma da yake goge daron bread da shi kan bread ɗin, All this saboda kada su Ƴar Iya su gani ne sai dai abu ya riga ya faru.
Kai tsaye rumfar suka nufa tare da faɗin
“Iliyasu akwai burodi ne?”
Cikin inda-inda yace
“A...aa..eh..akwai guda.. shida da suka rage”
Ba tare da ta ce uffan ba ta nufi wurin tsumman nan ta yaye shi ai kuwa A'i ta saki baki tana salallami.
“Innalillahi wai dama akwai burodin shine kace ƙwara shida suka rage, lallai ka cika ƙatoto kuma zungureren maƙaryaci”
Ƴar Iya kuwa tuni ranta ya soma ɓaci da halin ƴan ƙauyen nasu, kowa sai shegiyar rawar tsiya. Tsaki ta ja sannan tace
“Ni na kasa gane halin ku ƴan garin nan gaba ɗaya kun addabi jama'a da rowa, to kowa baƙin cikin ciyar da kai yake...Ni Autar Iya ina ganin jalala, to Aradu burodin nan duk ka juye man shi cikin buhu yanzu ka miƙo man” ta faɗa tana banka mishi harara.
Ba tare da ya musa mata ba ya juye bread ɗin baki ɗaya coz shine kwanciyar hankalin shi. Bayan sun ɗauki bread ɗin su suka wuce abun su sai gida Iya....babban buhu guda na bread suka sanya gaba sai da suka ga bayan shi tasss...ƙwara ɗaya suka bawa Iya wanda shima da ba don Iyar ta ɗauke shi ba da tuni sun gama da shi.
Da yammaci ne Baffi yayi baƙo, amininsa ne wanda suka yi karatun Allo da shi a tsangaya ɗaya sai dai shi Haifaffen garin Galdimari ne ammah a can Sakwa yake da zama.
Sun yi taɗi sosai da Baffi daga bisani ya tafi. Bayan tafiyar shi Baffi ya tunkaro Iya da batun da suka tattauna da abokin sa duk da cewa gabaɗaya kusan a kan Ƴar Iya aka yi shi.
“Iyar Shalele dama wata magana nake so muyi da ke”
“Toh ina sauraron ka, Allah dai yasa lafiya”
“Lafiya ƙalau....damah ɗazu Amini na Shehu ai baki dai manta shi ba?” kai ta ɗaga shi kuma yaci gaba.
“Toh shine muke tattaunawa akan matsalar Yarinyar nan mai sunan ki, toh ya bani shawara wacce ina kyautata zaton in mun bi ta zamu samu nasara da Izinin Allah kuma la'alla yarinyar ta daina wasu daga cikin halayen ta”
Ganin Iya ta tsura mishi ido tasa ya ɗan dakata yana kallon ta.
“Ammah baka tunanin haka Allah ya halicci yarinyar ne?, Ba ma wannan ba wace shawara ne kuka yanke kai da shi Malam Shehu ɗin?”
Sai da Baffi ya gyara murya sannan ya ce
“Malam Shehu ya bani shawara kan kai takwarar ki makarantar kwana, idan har bata ganin na kusa to za'a samu sauyi, kuma a can zata ƙara sanin rayuwa tunda mutane ne iri iri idan muka ci Sa'a sai tayi koyi da wani daga ciki”
Jimm Iya tayi ta rasa abun faɗi can tace
“Ammah baka tunanin in taje can ma tayi musu halin ne?”
Murmushi irin nasu na manya yayi sannan yace
“A'ah bana fatan hakan, fata na ta samu sauyi cikin rayuwar ta, itama tayi rayuwa kamar yadda kowa yake yi, ina da tabbacin ba haka ainihin yarinyar nan take ba saboda na sha yin mafarkai iri-iri game da ita ba a irin wannan yanayi ba”
Hawayen da ya zubo masa ya goge, tuni zuciyar Iya ta karye don zata iya ƙirga sau nawa taga hawayen mijin nata saboda ba ƙaramin abu ne zai taɓa zuciyar gwarzon mijin ta ba.
“Shikenan Ni kam duk hukuncin da ka yanke zanyi maraba da shi, fatan mu bai wuce samar wa jikar mu ɗaya tilo salama a rayuwar ta ba. Saboda haka sai a fara shirye-shiryen tafiyar ammah ina ne za' kai ta?”
Iya ta jefawa Baffi Tambayar.
“Can wani gari ne wai Sakwa, akwai makarantar kwana to can za'a kai ta”
Cikin sanyin guiwa Iya da Baffi suka gama hirar su daga ƙarshe suka tsaya kan kaiwa Ƴar Iya makaranta.
A daren Iya ta siyo sabulun wanka da kuma alimun har da soda da kanwa...ta haɗo da dutsin kaushi. Bayan ta siyo bata wuce gida ba sai da ta nemo Ƴar Iya cikin ƙauyen suka dawo.
Kallon tuhuma Ƴar Iya ke bin Iya da shi tana ƙara wari idanuwan ta waje.
“Lafiya Iya kika ɗauko ni ko dai wani abu ya samu ne”
Murmushi Iya tayi tace
“Jika ta kuma Shalele na birni nake so kije, shiyasa na bi kasuwa na siyo kayan gyara ko baki son zuwa birnin?”
Caraf tace
“Tab ɗijam, Aradu ina son birni Iya, baki ganin irin kayan da suke sakawa ga ginin su masu kyau ba irin bukkokin mu ba”
Ta faɗa tare da nuna bukkokin su da yatsa tana yamutsa fuska. Cikin zumuɗi Iya tace
“Toh ke a ina kika san birni ke da iyakar ki ƙauyukan kusa da mu ne”
Kallon baki da wayo ta jefi iya da shi tana banka mata harara tace
“Kiji Iyar nan, toh bari kiji in gaya miki a gidan kallo ne a can Zubo, idan naje sai na laɓe ina kalla...Aradu Iya kin ga wasu kyawawan samari kuwa?”
Murmushi Iya tayi ganin ba zasu samu matsala da shalelen ta ba tace
“Toh ai kema zaki zama irinsu musamman in Kika je kika yi karatun boko”
“Miye kuma boka Iya, Ni ba zan yi tsafi ba” ƴar dariya iya tayi tace
“Bokoooo nace ba boka ba”
Ganin Iya na mata dariya yasa ta ɓata fuska tare da miƙewa zata fice, kamota iya tayi tana faɗin
“Yi haƙuri shalelen Iya, boko shine karatun Ƴan birnin, kuma tunda suna burge ki ai zaki yi shi ko?”
Kai ta gyaɗa tunda ita yau ta fara jin kalmar boko a rayuwar ta.
Daga nan Iya ta sata gaba kanta ta gyara mata jikin ta tun yanzu kada in taje su raina ta.
Babu musu suka shiga bayi, daga baki Iya ta fara, dama ta riga ta daka gawayin ta da gishiri haka ta gurza mata, irin gudajin datti da aka cire ba'a magana, sai dai har lokacin akwai su danƙare kamar gona.
Daga nan iya ta fara wanke mata sumar kanta wacce in ka ga irin dattin dake fita sai kayi amai. Abun mamaki ana jiƙa sumar gashin ganta ya ware, Masha Allah sumar tana da tsayi ashe sai ɗan banzan datti. Fatan jikin ta ma ta sha wanka tuni ta ɗan ƙara haske.
Babu laifi Ƴar Iya fa kyakkyawa ce 1st class sai dai rayuwar ƙauye da kuma ƙazanta yasa muke ganin ta kamar kashi.
Bayan an gyara jikin ta, suka fita kasuwa tare da Iya ta ɗan zaɓa mata wasu kayayyakin amfani, har powder irin _buɗa ni jaka_ ɗin nan, jan baki ne da kwalli da dai sauransu. Daga nan suka dawo.
Kwana biyu saboda ɗaukin zuwa birni Ƴar Iya bata fiye fita yawo ba, ko da A'i tazo su fita Ƴar Iya ta bata labarin ita fa birni zata je kuma Baffi yace zata yi karatun Ƴan birnin shiyasa ma ta daina fita.
A'i tayi mamaki sosai daga ƙarshe har da kukan ta Aminiyar ta zata bar ta ita kaɗai.
“Ko dai baƙin ciki kike da ni ne?”
“A'ah