Showing 60001 words to 63000 words out of 135404 words

Chapter 21 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46346

takun mai gidan uncle Suraj na shigowa.

Bata yi ƙoƙarin sauƙe A'isha da kanta ke bisa cinyarta ba, sai ma ƙoƙarin gyara ma kanta zama da tayi. Cikin fara'a ya ƙaraso ganin A'isha a tare da Nenne duk da dama ya tsammaci hakan, coz Nenne akwai son jama'a.

Sallamar ta amsa mishi tare da sannu da zuwa, ba tare da ya damu ba shima ya wuce ya watsa ruwa. Lokacin Nenne ta raka A'isha bedroom ɗin Hamma Zaki na ƙofar in yaso in taji matsayar zamanta sai ta maida ta ɗakin su Ayrah.

Bayan uncle Suraj ya dawo ya tarar da Nenne a parlour, sabuwar gaisuwa suka yi. Abinci ta tambaye shi yace a'a baya buƙata. Hirar su suka ci gaba can Nenne ta sako zance A'isha.
“Abbi Najma inaga ya kamata a san matsayin yarinyar nan, ta nuna min ita dai bata son komawa can ma, in babu damuwa sai ka barta a nan tare da su Yesmeen”
Murmushi Uncle Suraj yayi yace “Kamar kin san me ke raina kuwa, yarinyar akwai ayoyin tambaya a tattare da ita, zata cigaba da kasancewa da mu har zuwa lokacin da zan gano ɓoyayyen Al'amarin dake cikin rayuwar ta”
Haka suka gama hirar su.

Washegari da safe kamar kullum suka tashi, bayan sunyi sallah itama ta tashi, sai dai ita bata yi sallar ba ta cigaba da zamanta a kyakkyawan ɗakin da aka bata ta kwana. Nenne da kanta ta shigo don tayar da A'isha sai dai da ta ganta kwance idi biyu sai ta tambaye ta
“A'isha kinyi sallah kuwa?”
Ido ta ƙwalalo waje tana duban Nenne. Sake maimaita tambayar Nenne tayi
“Kinyi sallah ne A'isha?”
Duru-duru ta fara hakan yasa Nenne fahimtar ta.
“Oya tashi ki shiga bayi kiyo alwala ki kuma tabbatar kinyi sallah kinji?”
Kai ta gyaɗa sannan ta miƙe tana nufar bayin, fuska da hannun ta ta wanke sannan ta wanke ƙafa, bayan ta fito ta fara kife kife ala doke tana sallah ne.

Yunwar da ta dame ta ne yasa ta fito parlourn ko angama abinci, karo taci da Yesmeen da Adda Najmah cikin shirin su na makaranta. Lokaci ɗaya taji sha'awar komawa _sukul_ kamar yadda take faɗa, a dai-dai lokacin ta tuna da Aunty Jiram ɗin ta. Murmushi kawai take yayin da hankalin ta ya gushe. Fitowar Nenne daga kitchen tana jera abinci a dining yasa Yesmeen da Adda Najma ƙarasawa dining area ɗin.

Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta, Nenne na kula da ita sarai sai dai ba tace da ita uffan ba. Sai da ta gama jera breakfast ɗin ta juyo tana kallon A'isha. Fuskar ta ɗauke da murmushi tace “Aisha babu gaisuwa ne” cikin inda_inda tace “Ina wuni”
Da “lafiya” Nenne ta amsa mata sannan tace, ki wuce dining ina zuwa” ba tare da sanin meye dining ɗin ba kawai ta tunkari wurin don iyakar ƙoƙari tayi shi, ji take kamar ƴaƴan hanjin tazasu tsinke saboda babu.

Cikin mintuna da baza su wuce biyar ba sai ga Nenne da Uncle Suraj sun fito cikin shirin sa na kayan police 👮, Aisha na hango shi ta tsura mishi ido kamar zata cinye shi, lokaci guda kuma rana tuna shegun da suka tafi da ita suka mata dukan tsiya.
“Allah yaso naci ubansu kafin na dawo ai” abunda ta furta kenan tana cije leɓen ta. Da kallon mamaki Adda Najma ke binta kawai haka nan Yesmeen, isowar Uncle Suraj ne da Nenne tayi gyaran murya.
Kujera taja mishi tare da faɗin “Good morning Abbi Najma”
Cike da murmushi ya amsa da “Morning”
Nan Najma da Yesmeen suka gaida shi banda A'isha dake bin shi da kallo.

Nenne ce ta katse ta da faɗin “Baki gaishe da Abbin ku ba A'isha”
Cike da basarwa tace “Ina wuni”
Cikin sakin fuska Uncle Suraj ya amsa da “Lafiya ƙalau A'isha”.

Nenne ce tayi serving kowa, daga nan baka ƙara jin bakin kowa ba sai cak cak da spoons ke bayarwa idan sun haɗu da plate. Cinyewa da tayi yasa ta zubawa plate ɗin gaban Nenne ido. Ƙaraf suka haɗa ido sai ta kawar da nata, Nenne kuma ta yi murmushi tare da jawo plate ɗin ta ƙara mata sannan ta tura shi gabanta.

Babu kunya A'isha tasa hannu taci gaba da ci har ta kammala, lokacin su Najma duk sun shige ciki don su yo brush sannan su ɗauko schoolbags nasu.

★★★★★★★

Bayan fitar su Najmah uncle Suraj suka fito shi da Nenne wacce hannun ta ke riƙe da A'isha, part ɗin granny suka nufa a tare. A parlour suka tarar da ita tana kallon Africa TV3. Bayan ta amsa sallamar su suka shiga tare da samun matsuguni. Gaishe ta suka yi ta amsa sannan ta bisu da kallo alamar tana buƙatar ƙarin bayani game da yarinyar da suka zo tare.

Cikin dakewa uncle Suraj yayi mata bayanin komai game da A'isha tun daga haɗuwar su da zaman da tayi tare da su.
Cikin farin ciki granny ta miƙe tare da kamo hannun A'isha, babu musu ta bi ta har zuwa gefenta da ta zaunar da ita tana famar murmushi.
“Kai amma naji daɗi sosai, wannan yarinya kamar ɗiyar Ramatu” (Mom)😂 da yake bata iya faɗin Rohmoh ɗin. Shafa fuskar ta tayi tace
“Yarinya kyakkyawa da ita, to babu komai amma ina neman wata alfarma daga gare ku”
Ba tare da sunce komai ba granny taci gaba.
“Ina so ku bar yarinyar a tare da ni don Allah, nasan zata ɗebe min kewa”
Cikin murmushin yaƙe Nenne tace “Babu komai ta zauna ai duk ɗaya ne,zamu wuce Inna”
Murmushi granny tayi tace “Na gode muku ƙwarai da gaske, Allah yayi muku albarka”
Da “Ameen” suka amsa sannan suka miƙe a tare. A'isha dake gefen Granny tayi luƙus don ji take yi kamar tare da Iya take. Hannu kawai Nenne ta ɗaga mata daga haka suka fice.

Sai da granny ta tabbatar sun tafi ta juyo da A'isha tana duban ta. Murmushin dake kan fuskar granny yaƙi ɓacewa saboda tsantsar farin cikin da take ciki.
“Ƴan mata yaya sunan ki?”
A'isha tace “Suna na A'isha amma ana cemin Ƴar Iya”
Granny ta wangale baki “aaaaa kice takwara ta ce ke ɗin, amma wane suna kika fi so ana ƙiran ki dashi anan?”
Ɗaga kai tayi alamun tana tunani can tace “Aisha nafi so”
“Tooo too shikenan Amma za'a sauya miki suna saboda sauran ƴan gidan basa iya kiran suna na”
Kai ta gyaɗa ba tare da ta fahimci me Granny ɗin tace ba.
“Tashi muje na nuna miki ɓangare na”
Ko ina sai da granny ta nuna mata daga ƙarshe ta nuna mata wani ɗaki
“Wannan ɗakin na baki shi ke kaɗai, amma fa in kina son kwana a ɗaki na ma bazan hana ki ba”.

Farin ciki kamar ya kashe A'isha saboda yanzu ji take har ta zama Ƴar gayu. Granny kuwa sai nan da nan take da A'isha wai tayi ƴa. Cikin ƙanƙanin lokaci A'isha ta sake da granny Kamar dai Iyar ta. Hakan yayi wa granny daɗi sosai.

Da yamma bayan su Yesmeen sun dawo daga islamiyya suka taho ita da Fauzah da kuma Ayrah zuwa part ɗin granny bayan sanar da su fauzan da Yesmeen tayi game da A'isha.

Sun kuwa ci Sa'a A'isha na zaune a ɗaya daga kujerun parlourn. Cikin sakin fuska suka nufe ta gabaɗayansu.
Ayrah tace “Sannun ki, ke kyakkyawa ce” murmushi A'isha tayi tace “Aradu ku kun fini kyau, duk gidan nan Aradu babu maras kyau kamar aljanu”
Dariya suka shaƙe da ita kafin Fauzah ta dakatar dasu da faɗin
“Ni suna na Fauzah, wannan Ayrah, wannan kuma Yesmeen, ki ɗauke mu a matsayin ƴan uwanki”
Dariya A'isha tayi tace “Babu komai, sunayen ku na ƴan birni ne Aradu, ko dan kuma ƴan birnin ne” ta ɗan dakata sannan tace “Ni suna na Ƴar Iya, Amma fa Nenne wacce nake ɗakinta jiya tace daga yau ba haka sunana ba”
Dariya su duka suka yi, Ayrah tace “To meye asalin sunan ki?”
“A'isha sunana fa, don sunan Iya gare ni, amma acan Gallara Ƴar Iya mai hannun ɓarna ake cemin, Aradu kowa ya Sanni a can, hhhh” ta ƙarasa tana sakin dariya.

Kallon mamaki duka suka bita da shi, can Fauzah tace
“Ba zamu ƙira ki da wannan sunan a nan ba, sunan ki kuma sunan granny ne, za mu tambayi Mom ɗina sunan da ya dace da ke”
“Waye kuma Mom?” Aisha ta tambaya
Murmushi Ayrah tayi kafin tace “Ke maman ta ce, Ƴar Indiya ce, baki ga Fauza ma na kama da su ba?”
Ba tare da ta fahimta bata gyaɗa mata kai.
Nan suka yi ta hira abun su har lokacin maghrib, kowa yayi sallah banda Ƴar Iya wacce ta make akan kujera sai hura hanci take wai ita Ƴar Birni.

Granny da kanta ta tsaya kan Ƴar Iya har saida ta buga sallar tata. A nan ɓangaren granny suka yi ta hirar su har bayan Ishã, bayan sunyi dinner suka yi wa Ƴar Iya sallama daga nan kowa ta wuce part ɗin su.
Babu laifi sunyi sabo sosai cikin ƙanƙanin lokaci, Fauzah ta sanar da Mom batun Ƴar Iya tace mata gobe su rako ta wajen ta.

[8/18, 10:03 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA””” “““63&64

A daren ne Granny ta aikawa surikanta da kuma ƴaƴan ta tana son tattaunawa da su.

Washegari kuwa duka gidan suka ɗunguma part ɗin Granny. Bayan sun gaisa cike da girmamawa take yi musu bayani akan Ƴar Iya, wacce a lokacin aka sauya mata suna da _Ummul-khairy_ domin sunan granny gare ta.

Daga ƙarshe Granny ta rufe taron da faɗin “Wannan yarinya ina so kowa ya nuna mata ƙauna tamkar yadda zai nunawa ɗiyansa, ku ja ta a jikin ku domin akwai wani al'amari a tattare da wannan yarinya, ku so ta don Allah”
Gaba ɗaya suka amsa da “In sha Allah Hajiya zamu kula da ita”
Nan taron ya watse.

Ɓangaren Khairy kuwa bacci take kwasa a lokacin ma, sai bayan wucewar su Granny ta tayar da ita. Daga jiya zuwa yau granny ta fihimci abubuwa da dama game da yarinyar shiyasa bata wani takura mata ba.
“Tashi Khairy kiyi sallah”
Ba musu ta miƙe tsaye tana miƙa kamar wacce zata cinye na gefenta, hakan ya bawa granny dariya sai da ta dara.
“Ja'ira wuce kiyi sallah”
Bayi ta nufa ta wanke fuskarta da hannayenta, daga ƙarshe ta wanke ƙafa ta fito. Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da sallar ta.

★★★★★★★★

Rayuwa kenan, yau kaine gobe kuma ba kai bane, haka Ƴar Iya wacce a yanzu ta koma Khairy ta cika sati guda cikin Naira family, abubuwa sun faru cikin satin, a ciki akwai ganawarta da Mom, wacce lokaci guda taji ƙaunar yarinyar cikin ranta, sai kuma hutun makaranta da sauran yara suka samu. Duk tsawon wannan lokaci, Hamma Zaki bai antayo gida ba, wayar da yake yi musu ma yanzu ba sosai ba.

Mom ta shiga matsanancin tashin hankali game da hakan, amma kullum addu'a kawai take yiwa yaron nata kan Allah ya kuɓutar da shi daga sharrin wannan matar tashi.

Yau juma'a, Mom da kanta ta saka yaran su shirya zasu je shopping, basu wani ɓata lokaci ba kowa ya shirya, fuskar kowa ɗauke da farin ciki da annashuwa banda Adda Salma, wacce haka kawai taji ta tsani Khairy, ba don komai sai tsananin kishin yadda kowa yake nan da nan da ita yayin da ita Khairy bata ma san tana yi ba.

Mall suka fara nufa, Mom tace kowa ya ɗauki abun da yake buƙata, ta saka Adda Najmah zaɓarwa Khairy kayayyakin buƙata. Kayan da aka loada mata kamar wata ƴar gata (ko dan, yanzu kam ƴar gatan ce ai). Bayan sun gama aka wuce da su wurin gyaran jiki, kowacce ta ƙara kyau kamar ba gobe, tabbas familyn Naira babu na yarwa.

Ban tsinke da mamaki ba sai da na hango Khairy wacce duk ta zarce kyawawan ahalin kusan kowanne fanni. Fuskar nan tata ta ƙara haske, ga wani ƙyalli da take yi, ban gama dawowa hankali na ba na cilla ido na kan gashin da aka gyara sai ƙyalli yake. In da badan da ido na na kalli gashin nan ba da sai nace ba na Khairy bane, wannan danƙararren gashin nata ya koma wani miƙaƙƙen gashi.

Ayrah ce ta kalli Khairy tace “Khairy kin ganki kuwa?”
Wani murmushi ta sake, take wasu fararen haƙware jere ras da su suka bayyana, yayinda kuncin ta ya lotsa. Cikin Muryar ta mai daɗi tace “Aradu kuma kunyi kyau”
Mom dake kallon su cike da sha'awa ta cilla wa Khairy harara, ba shiri tace “Yi haƙuri Mom, na manta!”
Sake fuska mom ɗin tayi tana rungumo Khairyn “Is ok daughter, kiyi ƙoƙarin gyara maganar ki, yanzu in wani yaji kina cewa Aradu to ko kallon ki ba zai kuma ba duk irin kyan da kika yi”
Zaro ido tayi tace “Zan ma gyara ai” ta ƙarasa a yangance har sai da ƴan uwanta suka dara. Daga nan suka fito suka wuce gida.

Cikin hutun su Fauzah Khairy ta ƙara wayewa, Mom na janta a jiki, haka Mommah yayin da duk kulawar da suke bata Nenne ta kere su a wannan fanni.
Daf da zasu koma ne Granny ta shawarci uncle Suraj game da karatun Khairyn.
“Eh Hajiya nima Ina son tuntuɓar ki Kan hakan amma ina laifin a fara nema mata mai Lesson daga baya sai ta shiga makarantar?”
Granny tace “Babu laifi, dama kawai saboda yadda naga itama ta fara sha'awar karatun ne”
“To Hajiya zanyi wa Nennen yara magana, ta nema mata Malama mace in yasa ko na 1month tayi mata sai a Kaita makarantar”.
“Toh madalla, Allah amfana”.
Daga nan suka shiga hirar su ta Duniya.

Nenne da kanta ta zaɓawa Khairy ɗaliba, ranar da Madam Ajimola ta fara zuwa tayi iyakar iyawarta ganin Khairy ta fahimci darasin, babu laifi ta gane sosai. Malama Ruƙayya ma tazo tayi mata karatun Alkur'ani sai dai babu wani cigaba, hakan yasa ta nemi ganawa da Nenne kan batun.

★★★★★★★★

*ALEE POV*
Kwance yake akan makeken gadon sa ya rasa me yake masa daɗi a duniyar, a hankali ya miƙe tare da ziraro kyakkyawar ƙafarsa ƙasa, parlourn ya fito ya duba ko ina Pretty ta shiga. Cike da ƙyanƙyami yake takawa duk da akwai takalmi a ƙafar tashi, fuska ya yamutsa a hankali ya furta “bullshit”
Ƙarar fitar motar ta da yaji yasa ya maida dubansa ga window, ganin tabbas motar ta ce ta fita yasa yaja tsaki tare da dafe kanshi.
Cike da takaicin Hali iri na pretty ya koma bedroom ɗinsa.

Da kanshi ya tattare ya gyara bed ɗin sannan ya share, ya fesa room freshener, nan da Nan ɗakin ya gauraye da ƙamshi, Yana yi Yana tsaki. Cikin ranshi kuwa Allah wadaran aure irin nashi yake yi, to me ma Wai yakai shi Auren pretty ne?”
Kanshi da ya Sara ne yasa ya bar tunanin ya nufi toilet, cikin ranshi Yana ayyana dalilin da yasa idan zai yi dogon nazari Akan pretty sai kanshi ya Sara.

A daddafe ya fito ya shirya cikin khakin sojoji Wanda ke matuƙar amsarshi, fuskar nan tamau Kamar a filin yaƙi. Yurare ya buɗa sannan ya fito. Direct parking lot ya nufa, daidai farar motarshi ya ysaya Yana ɗan yamutsa fuska, ko ta Kan gateman dake gaisuwa bai bi ba ya figi motarshi sai barrack.

Captain Stanley wanda ya zamo sabon aboki gare shi ya fahimci Hamma Zaki na cikin damuwa.
“Dude, watz wrong, you look so worn out, why?”
Har sai da ya cire ran zai amsa mishi can yaji muryarsa na faɗin “I want to go home friend” ya faɗa cikin tsantsar nuna damuwa. Captain Stanley kuwa mamaki ya cika shi, tunani yake wai dama Captain Alee na da relations a Nigeria?, If Yana da why baya ziyarar su. Murmushi yayi Yana kamo hannun sa
“C'mon friend tare Zamu je ai, naga Kamar baka da lafiya ma”
Shiru Hamma Zaki yayi Yana bin Captain Stanley da Ido.

A ranar yayi musu booking flight, sannan ya koma gida, har lokacin pretty Bata dawo ba. Tsaki yayi ya wuce Zuwa bedroom ɗin shi sannan ya haɗa kayansa cikin trolley.
Ko tsaraba bai yi musu ba ya nemi wajen baccin sa.

Washegari da safe suka wuce airport, sai Adamawa, Dr. Faruq ne yazo ya miƙa su gida. Lokacin Mom na haɗa snacks a kitchen Kamar daga sama ta jiyo ƙamshin turaren da ko giya ta Sha in taji tasan na waye.

Cikin sauri ta juyo Dan ganewa idon ta abun da take tsammani. Ai kuwa shi din ne, Bata yi aune ba Hawaye suka fara zubo mata, Shima hawayen ne yake zubowa daga idanuwan sa, idan yace bai yi missing mom din NASA ba to yayi ƙarya.
Hamma Zaki ne yayi ƙarfin halin share hawayen dake ambaliya daga idanuwan Mom ɗin.
“Is ok Mom, I miss u, ”
Ya faɗa Yana hugging Mom ɗin,
Murmushi Mai haɗe da Hawaye ta sake itama tana hugging nashi tightly Kamar zaa ƙwace mata shi.

A parlour suka yada zango, ganin yadda ya rame yasa Mom ƙara tausaya mishi, ko Bata sani ba tasan yana Jin jiki. Trolleyn shi yaja zuwa bedroom ɗin shi, daidai frame ɗin dake ɗakin ya tsaya Kamar wani dolo ƴana nazari. Wayar shi da tayi ƙara yasa ya zabura Yana sakin tsaki. Ganin Mai ƙiran yasa yayi picking. Ba tare da yace komai ba yaji muryarta na dukan dodon kunnen sa.
“Haba Aliyu, yanzu FISABILILLAHI don zaka je wurin iyayenka kawai sai ka tafi babu wani notification, ba za ka ma iya jura na ba kenan....?, Naji ka rasa wa zaka barwa saƙon ma sai maigadi, to lallai lallai Sati ɗaya na baka ka tabbatar ka dawo kaji ko?”
Kamar tana gaban sa ya gyaɗa kai Yana hanging call ɗin.

“Kai Fauzah, kin san Allah a duniyar nan ni babu abunda nike tsoro, ina daidai da komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login