Showing 1 words to 3000 words out of 135404 words
[4/21, 4:32 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SADAUKARWA GA YAN UWANA NA MUSAMMAN: Seemerh & Shaheedah, love u so much angels, u mean the whole world to me.
SHAFI NA ‘‘‘‘‘1&2’’’’’
NIGERIA
BAUCHI STATE
SHIRA LOCAL GOVERNMENT
GALLARA VILLAGE
Gudu take falfawa tamkar zata furga sama yayin da duk wani wuri da tazo wucewa suke kaucewa su bata hanya kamar wata motar da babu brake. Bayan ta shafe fiye da 30minutes tana gudun ne ta iso dai-dai wani gida ba shiri taci burki kamar tayar da ta samu friction.
Gidan ta nufa kai tsaye tana tsalle-tsalle kamar wata kwaɗo, bata tsaya yin sallama ba saboda sallamar kanta bata daga cikin jerin abubuwan da ta saka gaba balle su zame mata jiki.
Tana tafe tana tsalle har ta gama tsallake zanar da aka kewaye gidan, tana isa kuwa ta shige wata ƴar bukka wacce ba sai na tambaya ba da gani mallakin ta ne.
Ashe tun lokacin da na hango ta tana shera gudun nan Bala Mai kifi na biye da ita. Fitowa ta yayi dai-dai da isowar sa gidan, sallama ya shiga rafkawa kamar wanda aka ci bashin sa ba'a biya ba.
“Salamu Alekum, Salamu Alekum!!!”
Jin babu wanda ya amsa masa sallamar yasa ya ɗan ƙara matsawa dai-dai lungun gida.
“Salamu Alekum!”
“Wa Alaikumus Salam”
Daga bayan shi aka amsa sallamar nan take ya juyo don ganin waye, ba kowa bane face Mallam Umaru Gallara.
Murmushi Mallam ya sakarwa Bala Mai kifi yana faɗin
“Mu ƙarasa ciki mana”
Saboda tsananin kunyar Mallam da Bala ke ji yasa ya bi shi ba don ya so ba,damah shi ƙara ya kawo amma babu yadda ya iya dole bi shi.
Sallama malam yayi yana nufan wani ɗaki wanda suke jere guda biyu, bai daɗe ba ya fito da taburma ya shimfiɗa musu.
Gaisuwa irin ta mutunci suka yi bayan sun gaisa Mallam ya maida kallon sa ga Bala Mai kifi.
“Mallam Bala fatan dai lafiya koh”
Cike da jin kunya Bala yace
“Lafiya Allah shi gafarta Mallam kawai na zo mu gaisa ne” ya ƙarasa yana sosa kai da kunne.
Murmushi mai sauti Mallam yayi kafin yace
“Nayi farin ciki sosai Mallam Bala, Allah ya bar zumunci”
Bala ya amsa da
“Amin Allah gafarta Mallam Ni zan wuce, na gode”
“mallam yace Amin ”
Daga nan ya rako Bala har bakin ƙofa.
Babu yadda Bala ya iya ammah ya ɗauki alwashin yiwa Ƴar iya tsiya in ya kama ta.
KO ME TA MISHI?
THIRTY FIVE MINUTES BACK (Flash back)
Tana dawowa daga yawon da ta saba ne sakamakon yunwar da ta takura ta, ƴan hanjin ta sai juyawa suke alamun suna buƙatar kaya.
Da sauri ta karyo corner yayin da ƙamshin kifin da Bala ke soyawa ya bugi hancin ta, nan da nan hankalin ta ya tashi saboda haka da gudu ta ƙarasa zuwa teburin kifin.
Tana isa shi kuma lokacin ya kwaso kifin da ya tsame cikin matsamin sa na ƙarfe ya zuba su kan teburin.
Wani Shegen yawu Ƴar Iya ta haɗiye sai wani lumshe idanuwa da tanɗe baki da take yi kamar tsohuwar mayya.
Gaban Bala ne ya faɗi saboda ya sha jin labarin Ƴar Iya wurin samarin da ke ƙauyen tare da irin rashin mutuncin ta da tsiyar da take shukawa.
Dakewa yayi saboda shi babu abun da ya taɓa haɗa ta da shi. Ganin ya ƙi ƙunsa mata kifin a leda kamar yadda duk inda taje ina ana sayar da abu kafin tayi magana suke ƙalla mata salin alin ta tafi abun ta yasa ta ƙara zaro dara-daran idanuwan ta tana duban shi kafin tace
“Kai kifin nake jira ka bani dai”
Ta faɗa cike da ƙosawa tana hararar Bala mai kifi. Shi kuma irin ya gwada mata shi bai san ta ba yasa yace
“Na nawa za'a baki?”
Mamaki ne ya kama Ƴar Iya jin batun raini da Bala ya kawo mata, gashi ita duk ta ƙosa ya bata don zuwa jimawa in bai bata ba zata iya mutuwa.
“Duk na kan teburin nake so ka juye min”
Tana faɗan haka taga ya juya zuwa wajen abun suyar shi yasa ta janyo leda ta fara kwashe kifin. Leda uku ta cika fal sannan ta juya zata tafi. A lokacin ne Bala ya dawo gaban teburin shi ganin wayam babu kifi babu mai siyan kifi yasa shi bin bayan ta da gudu.
Ai kuwa kamar tasan zai iya biyo ta yasa tana matsawa gefe ta fara tura kifin a bakin ta ba tare da ta damu da cire ƙayar ba. Within 2Minutes har ta kammala da leda biyu, (Ni kaina Bhatool sai da na zaro idanuwa tsananin mamaki). Ta janyo ledar ƙarshe zata fara ci ta hango Bala na tahowa ai kuwa babu shiri ta arta a na kare. Tana gudu tana cusa kifi har ta cinye ta wulla ledar ta ƙara wa jikin ta mai, tuni tayi wa Bala nisa.
Duk da haka bai daina bin ta ba har ta iso wurin wasu mutane da suka taru, ai babu shiri ganin Ƴar Iya yasa suka matsa don sun san abu mai sauƙi ne duk ta bangaje su ta wuce. Duk irin nisan da ta yi wa Bala bai hana shi bin ta ba har ta iso gidan su.......
WANNAN KENAN!
BACK TO STORY.
A lokacin da Bala ya koma wurin suyar kifin shi yayi mamaki sosai, kifin da ya zuba tasss ya ƙone babu yadda za'a yi ya sayar da shi. Nan da nan wani ɓacin rai ya ziyarci zuciyar shi, gashi bashi da wani kuɗin a hannu ballantana ya ƙara zuwa kogi ya saro wurin masinta....
Ganin ba shi da wata makama yasa yasa ya sauƙe mayin da ya rage ya shigar da shi cikin shagon ajiyar shi. Yana fitowa yazo ya rafka uban tagumu ga wasu hawayen baƙin ciki da suke gangarowa daga idanun shi.
Yana cikin yanayin nan ne ya ji an dafa shi, abokin sa ne Tanimu wanda ya ƙure shi da ido ganin hawaye a idon shi.
Tanimu ya tambayi Bala cike da kulawa
“Aboki na ya naga hawaye a idon ka, ko dai baka jin daɗi ne”
Cike da takaici ya goge hawayen nasa ya ce:
“Kai dai ka bari kawai, wannan ai gwanda ace jinya na nake yi da abun da ya faru”
Tanimu ya maida hankalin sa kan abokin sa yace
“Ina sauraron ka”
Gyara zaman shi yayi yace
“Ina yarinyar nan da kuke bani labarin rashin mutuncin ta ɗin nan?”
Tanimu yace
“Wai Ƴar Iya kake nufi”
“Eh ita dai in ma Ƴar Baba ce”
Cike da zaƙuwa Tanimu yace
“Baka faɗa min me tayi maka ba ai”
Bala yayi tsaki yace
“Hmmm aboki na yarinyar nan na soya kifi na na kwashe zan zuba wani tazo, bayan tace na bata sai naje duba wanda na zuba”
Ɗan dakatawa yayi saboda yadda zuciyar sa ke ƙuna. Shi kuwa Tanimu duk ya ƙosa yaji artabun Bala da kuma Ƴar Iya.
“Ina jin ka”
“Kawai kafin na dawo duk ta kwashe kifin ta tafi, ina bin ta kan hanya naga har ta kusa cinyewa”
Dariya Tanimu ya kwashe da ita kamar mahaukaci hakan yasa Bala tunzura ya miƙe. Da ƙyar Tanimu ya tsayar da Bala tare da riƙe hannun shi yana mai tsagaita dariyar.
“Haba aboki na, ai baka gama bani labarin ba”
“Shikenan ai tunda ma dariya zaka yi min kana gani dai sana'a ta kenan kuma kasan ita ce jari na, saboda ita na baro ƙauyen mu na dawo nan”
“kayi haƙuri aboki na, yanzu dai ƙarasa min sai mu nemi mafita”
Shiru Bala yayi can ya ci gaba
“Bayan na sha wahala na bi yarinyar nan har ta isa gidan su ina doka sallama sai Mallam Umaru na gani kenan shine baban ta?”
Kallon baka da wayo Tanimu yayi masa yace
“Lallai kuwa, Baffan ta ne ɗan uwan uban ta, kuma wai kai da ka bita ɗin uban ne zaka yi mata?”
Ya tambaye shi in a serious tone
“Wallahi Babu abun da zai hana na ɓalla ta da na kamata” ya faɗa cikin zafin rai.
Kallon wawa Tanimu ke aika masa daga nan yace
“Lallai yau na tabbatar baka da hankali, ai kuwa in baka ɓalla ta ba Kai ka dawo da ɓallallen hannu ka rasa na suyar kifin”
Zaro ido Bala yayi yace
“Habadai....yanzu maganar da nake maka kaga can wanda na zuba cikin mai da na dawo duk ya ƙone” ya faɗa yana nuna masa kaskon suyar da ya mayar cikin shagon.
“Lallai aboki na, baka san wace ce Ƴar Iya ba shiyasa ka sha wahalar bin ta, ammah shawarar da zan baka ka fita sabgar ta in ta zo tace ka bata kifi to salin alin ka bata ta tafi”
Daga haka suka koma taɗin su na rayuwa..
ƳAR IYA
Tunda taji dawowar Baffa Umaru ta lallaɓa ta fice daga gidan tana tafe tana raira waƙar ta.
“Dan maliyo maliyo, *Maliyo*
Ɗan maliyo nawa, *Maliyo*
Yaje ina ne?, *Maliyo*
Ya tafi Illorin, *Maliyo*”
Haka ta ci gaba da tafiyar ta tana daga garin kamar marar aikin yi, tana cikin tafiya tayo hanyar fada, yanke shawarar zuwa can taci abinci tayi saboda haka kai tsaye ta wuce.
Dakaru biyu da suke gadin fadar na ganin ta suka bata waje sun sani tsaf duka hana ta zata kwaɗe su ne ta shige abun ta.
Tana shiga kai tsaye ciki ta wuce can sashen mahaifiyar Arɗo Innani. Ai kuwa taji daɗi ganin tukunya akan wuta nan da nan ta washe haƙwaren ta masu kama da na mage, gashi duk datti ya danƙare haƙwaren babu daɗin gani.
Fara ƙwalla ƙiran Innani tayi
“Ke Uwar Arɗo! Fito manah yau a nan zan ci abinci”
Innani na jin Muryar Ƴar iya ta dogara ta fito da sauri tana yin yaƙe don ita a gaskiya in ba don fin ƙarfi irin na iblishiyar yarinyar nan ba da ta surfa mata ruwan Bala'i ammah babu yadda ta iya tunda yarinyar ta Addabi kowa cikin garin.
Ganin irin dariyar yaƙe da Innani keyi yasa ta haɗe rai tamau tace
“Ki ma daina yaƙe ɗin nan don yau ko mutuwa zaki yi sai naci, shegiyar tsohuwa sai shegen rowa ni ban ma san ya aka yi kika zama uwar sarki ba bayan baki cancanta ba”
Ta ƙarasa tana hararar Innani. Innani da ran ta in yayi dubu toh ya ɓaci ta juya zata koma ɗaki caraf ta ji Muryar Ƴar Iya na cewa
“In ma mutuwa zaki yi Aradu sai naci, don ko ɗan ki da ya siya bai isa hana ni ci ba, da kwalmaɗaɗɗiyar ƙafar ki a nan kamar agwagwa”
Innani da ta shige ɗaki ta rasa abun da ke mata daɗi, wannan yarinya duk ta addabi rayuwar su, a da can ita ke da iko da gidan saboda baki da masifa irin nata amma yanzu sam yarinyar nan ƴar da tayi jika da ita sai mulkar ta take.
Ƴar Iya na kai ƙarshen maganar ta ta nufi tukunya, tana buɗewa tayi ido huɗu da sulalen kajin da ke ciki, tuni ta fara haɗiye yawu tana farin ciki.
“Shegiyar tsohuwa ƴar baƙin ciki, yanzu Ni zata yi wa buƙulun cin kajin nan, kwarangwatsa in naga dama guduwa zan yi da shi gaba ɗaya”
Bata tsaya wata wata ba ta bi shawar zuciyar ta ai kuwa ta cire kwalin da ta ɗaure kan ta da shi tuni mummunan gashin ta da ya danƙare wuri guda kamar gonar mahaukaciya ya bayyana ga wani uban bugu da ke tashi daga gashin. Ɗaure kwalin tayi a kunkumin ta yayi da ta sa hannu ta rungume tukunyar a jikin ta.
A haka ta sanya gudu sai waje.........
[4/26, 8:44 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘3&4’’’’’
A haka ta falfala da gudu sai waje, duk irin tiririn da ke tashi daga cikin tukunyar hakan bai sa Ƴar Iya ajiye ta ba sai ma ƙara rungumar ta da tayi.
Basu yi aune ba suka ji su duk a ƙasa, ɗagowar da zasu yi suka yi arba da Ƴar Iya mai hannun ɓarna wacce yanzu har tayi nisa don kuwa shegen gudu gare ta kamar barewa.
Tana bangaje su bata tsaya bi ta kan su ba sai gida, tana shiga ta tarar da iya na tankaɗe garin dawar da zata yi tuwa. Bata yi sallama ba ta dire tukunyar gaban wani faifayin sannan ta hau kan faifayin.
Tana zama Iya da ta kasa haƙuri tace
“Ƴar Iya daga ina kuma kika samo wannan tukunya kuma miye a ciki? Kar dai ɓarnar da kika saba yiwa mutane kika je kika yo”
Gurmuɗa ɗan ƙaramin bakin ta tayi tana buɗe tukunyar sulalen da ta ɗauko daga gidan sarki sannan tace
“Ke iya dana wallahi kin fiye takura da sa ido...Ni har wata ɓarna nake yi ne in ban da sharri irin na mutane”
Ta ƙarasa tana tura baki gaba.
Iya da ta fahimci ɗiyar tata ta hau kuma bata son fishin ta saboda tsab zata musu aika-aika tace
“Yi haƙuri shalelen Iya, ni kaina na san ƴan baƙin ciki ne suke son shigga tsakanina da ke, yo ƴan baƙin ciki manah, Aradu su ne sai su zo su ce kinyi kaza kinyi kaza, rabu da su duk ranar da kika je birni ba zaki yi musu tsaraba ba.”
Lallashin da iya tayi mata yasa ta ɗan sauƙo ammah da tayi niyyar gurza wa Iya rashin mutunci.
Ɗaya bayan ɗaya Ƴar iya ta fara ɗauki dunƙula dunƙulan sassan kajin da aka fara sulalawa basu ma dahu ba. Sai da ta ciro kusan dunƙule goma ta ajiye kan murfin tace
“Iya ga kaza nan kizo ki soya mana sannan ki jira na dawo sai na raba kinji?”
Bata jira amsar Iya ba ta wuce waje a guje....
Kaɗe jikin su dogaran dake a bakin gidan sarki suka yi. Ɗaya daga cikin yace
“Lamara kai na ɗauka fa dokin ranka shi daɗe ne ya ƙwace har ya take mu”
Wanda aka ƙira da Lamara yace
“Toh Aradu ai gwanda ma ace dokin ne ya buge mu da wannan shaiɗaniyar yarinyar....""
Rufe masa baki yayi saboda hango Ƴar Iya na dawowa da yayi sai dai kash bakin alƙalami ya bushe tun daga can ta jiyo me dogaran ya faɗa.
Fara zazzare ido yayi yana tunanin shi kam yau kashin sa ya bushe.....A gadarance ta ƙaraso wajen da suke tsaye ta fara bin su da kallon tuhuma.
“Dallah can meyeh kuka bi kuka tsira min ido ko naci na uwar ku ban biya ba?”
“A...a....h kiyi haƙuri ƴar iya ba zamu ƙara ba” Lamara ya faɗa yana maida kallon shi ƙasa yayin da ɗaya dogarin kuma jikin sa in in banda rawa babu abun da yake yi. Kamar wadda ta tuna wani abu kawai ta miƙe zata shiga gidan tana faɗin
“Kun ci sa'ah yau ina farin ciki na ci kifi ga kuma nama na jirani Aradu yau da na karya ƙafafuwan ku musamman wannan me gemu irin na tauren nan.
Ƴar Iya na shiga gidan bata wuce ko ina ba sai ƙofar matan sarki, don ko hauka take ba zata shiga ƙofar tsohuwar can ba sai ta kawo mata tukunyar ta.
“Gafara dai gafara dai matan sarki” Ƴar Iya ta faɗa yayin da ta sauya tafiya sai wani lanƙwashewa take kamar hawainiya, farfara idon da take yi ne ya ƙara bawa Saratu Matar sarki ta tsakiya dariya.
Babu tsammani kawai suka ji Muryar Saratu na sheƙa dariya.
“Kan babar uban can, ke ni kike wa dariya?”
Saratu da ta kasance Ƴar duniya gaba ɗaya ta takurawa uwargidan sarki Salamatu da iyalen ta ga kuma shegiyar rashin kunyar da take fama da ita.
Salamatu tun ba yau ba ta san Ƴar Iya shiyasa tayi miƙit da bakin ta, ita kuma Saratu dama daga Kahin (ƙauyen da ke kusa da su) aka auro ta. Kuma Ƴar Iya bata fiye biyo ƙofar sarki ba iyakarta ƙoƙarin waccar tsohuwar.
Saratu kuwa dariya ta ke sheƙawa kamar wanda aka sheƙawa laughing gas. Can ta tsagaita ta kalli Ƴar Iya irin kallon da uban wa kika zo tace.
“Lallai kuwa yau naga iya shege, Salamatu kina ji wai ni yarinyar nan take kwatamawa rashin kunya, Aradu yau Sai ubanki ma yaci uban sa, dogarai zan sa su ɗauko tsumangun zane Dawaki su ci ubanki" Ta faɗa tana kama fuska wai ita babba, miƙewa tayi da niyyar fita don ƙiran dogari ai kuwa a lokacin Ƴar Iya da ta hasala ta ja ƙafar Saratu ji kake tiiiiiiiiim! Kamar faɗuwar buhun kaya. Bata yi wata wata ba ta samu saitin bakin Salamatu ta buga mata naushi tuni jini ya fara zuba kamar famfo....hango wani kashin shanu da ke can gefe tayi ai kuwa kafin ƙifta ido ta ciko hannun ta da shi ta dawo. Bakin Saratu da ke jini gashi sai ƙwala ihu take tana son tashi ma ta kasa. Buɗe bakin tayi ta fara cusa mata kashin shanun nan tana faɗin “Shegiya haɗiye ko naci ubanki, haɗiye maza, yauwah maza dai haɗiye” sai da ta cinye kashin nan tas har abun tausayi tukun ta ƙyale ta tana sakin dariyar mugunta, su Saratu kuwa anji jiki baki ya mutu, hawaye ne kawai ke zubowa.
(Nace maganin maras kunya kenan, dama an ce kin ishe su ai, yanzu kin haɗu da gamon ki).
Miƙewa tayi ba tare da ta damu ba ta bar gefen Saratu, Salamatu kuwa kame kanta tayi tana maida kan ta ƙasa.
“Ke kuma sai kace wata munafika dallah ɗago kanki, wato mata dai sun iya tsula tsiya da munafurci, dubi kan ta kamar asusun boka, ja wannan lafcecen jikin naki ki bani wuri ko na dawo kan ki”
Ai da gudu Salamatu tayi ɗakin ta. Maida kallon