Showing 18001 words to 21000 words out of 134378 words

Chapter 7 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

68

uban goyon nata ya ce fa mutumiyar banza ce.." ido ɗaya Kanne mamah ke duban Baba "anya kuwa ka ji da kyau Alhaji? Nan nan har gidan nan Nasir ya rako ta mun gaisa, ban ga alamun tambatsewa a tattare da ita ba, hasali ma kunya ta mata yawa." Numfashi Baba ya sauƙe yace "Kin san ba a gane mugu ta fuska, ubanta dai ba zai mata sharri ba saboda ba ya son ta, dole akwai ƙamshin gaskiya cikin zancen nasa."
"Uhm" mamah ta faɗa tana gyara zamanta kan kujerar parlourn "Yanzu dai Shikenan, Allah ya masa zaɓi mafi alkhairi, amma a tuntuɓe shi a ji daga bakinsa, Ni dai har yanzu in na tuna da fuskar yarinyar sai naji sam na kasa yadda da Abunda aka faɗa muku kanta. Allah dai ya kyauta."
"Amin" Baba ya ba da amsa, nan kuma suka juye kan hirarrakinsu kan abubuwan da suka shafi yau da kullum.

A ɓangaren Baffa Sule bai so suka ce sai sun yi shawara ba, ya so a ce lokaci guda an yi komai an gama, amma duk da haka dai lokaci bai ƙure ba musanman da yake tunanin samun nasara kan su Alhajin Gagidiba. Tabarmar ya naɗe tare da wucewa ciki. Ko da Inna ta Tare shi da tambayar ya suka kaya kwashe komai yayi ya sanar da ita, nan Inna ta fara tsinewa Hamra tana faɗin
"Shegiyar yarinya wallahi aure kam sai dai taga ana yi, kuma saurayin da yake ɗaure mata gindin ma ta rasa shi. "
Murmusawa Baffa yayi yace "kwantar da hankalinki Innar Khadi, ai Hamra da wahala har ƙarshen rayuwarta, idan ma tana tunanin tayi aure taji daɗi to aure kam...ba zan ce komai ba amma in ta yi ma sai dai na ƙasƙanci, iyayenta sun ja mata, zaɓin TUMUN DARE da mahaifinta yayi akaina shi ya ɓata ƙaddarar rayuwar ahalinsa wacce ba za ta taɓa gyaruwa ba sai dai in ana gyarawa a can lahira."
Guɗa Inna tayi tace "Kai, Mallam kai ma dai, Hmm, yanzu dai Ni gaskiya na gaji da zaman gidan nan har ga Allah, ya kamata kasan abun yi tunda dai ba rasawa kayi ba." Murmushi Baffa yayi yana shafa ƙasumbarsa wacce ba ta ganin gyara yace "Kar fa ki damu Uwar gida kuma amarya, muna gab da barin gidan amma sai kin ƙara himma, in so samu ne wannan tsunanniyar yarinyar mu samu mu rabu da ita sai mu ji daɗinmu."
Dariya tana tana shewa tace "Ba ka da matsala da Hajara, a cike nake in dai Ni ce."

Duk zantukan da suke yi both Rahama da Hamra na ji, ita dai Rahama murna take saboda burinta yana gab da cika za ta auri ɗan gidan ƴan gayu kuma masu kuɗi yayinda zantukan su Inna suka ƙara wanke mata rai fes. On the other hand tsoro ne da fargaba suka mamaye zuciyar Hamra yayin da duk wani kuzari da jarumta da ta samu suka bar jikinta farat ɗaya. Kalaman Baffa sun matuƙar ɗaure kanta, me yake nufi da mahaifinta da yake kwance ƙasa shi ya ruguza musu rayuwa? Wane irin zaɓi yayi akan Baffa da ya zama zaɓin TUMUN DARE? A iya saninta Baffa ɗan'uwan mahaifinta ne na jini, amma maganganun da yayi yanzu ya sa kokonta da fargaba sun mamaye ranta har tana ji a jikinta cewa tana da buƙatar sanin komai.

Wane sashe na zuciyarta kuma bai wuce baƙin cikin Abunda ake shirin mata ba, tunda ba su don zamanta a tare da su why not su aurar da ita su huta? Idan ma ta fahimta kenan juyin mulki za a yi da Rahama, lallai kuwa, alƙawari ta ɗaukarwa kanta na cewa duk abinda aka yanke ba za ta bari ya shafi lafiyarta ba, ba za ta sa damuwa a ranta ba, a da dai tana fatan mutuwa ta risketa ko ta ji sawaba abunta, amma a yanzu ta fi buƙatar rayuwa saboda burin son sanin abinda ya kasance mata a duhu tattare da ita da kuma ahalinta.
Baƙin cikinta a yanzu ya fara linkuwa tunawa da rayuwa da tayi da iyayenta da kuma wacce take kai yanzu wacce ba ƙaramar koma baya ta samu ba, fannin ilimi, ta rasa shi, ta samu giɓin da ba lallai ta cimma ba, ko ma yaya ne, ta ƙudiri aniyar nemarwa kanta mafita a halin yanzu.
Wannan kenan!

Tunaninta ya katse ne da zungure ta da aka yi take ta dungura, Rahama ce tsaye riƙe da kunkumi sai wani girgiza take, kallon da take aikawa Hamra shi ake kira da kallon hadarin kaji. Kallo ɗaya Hamra ta mata ta janye kanta tare da juyawa, hakan kuma ba ƙaramin ƙular da Rahama yayi ba, dalilin hakan yasa ta fara masifa har jijiyoyin kanta na tashi, har ta gama ba ta samu arzikin kallo ba daga Hamra, hakan kuma ya ƙular da ita sosai ganin ta mayar da ita mahaukaciya, tunani ta fara ta ina za ta yi galaba kan Hamra ta tanka mata, murmushin mugunta ta saki tace "Ko ba ki kula Ni ba Hamra na ci galaba a kanki, Nassman ɗin ma da kike gadara akansa ki shirya kwanan nan za ki ji an sa aurenmu da shi, ke kam, to wa ya sani ko a wani musakin za a bayar da ke?" Tana faɗin haka ta kwashe da dariya, juyowa Hamra tayi ta fuskanci Rahama tare da murmusawa, hakan yasa Rahama haɗe fuskarta da ke sake a da.
"Allah ya kai mu, ai ba abun baƙin ciki, kika sani ko in Na tashi na auri Ƙauran Bauchi, ai dama Nassman sai je Rahama, Ni kalar manyan mutane ne ko baki gani ba?" Ta faɗa ta kallon jikinta tare da yiwa Rahama Ishara da ta gani. Sosai ran Rahama ya ɓaci har ta gagara ɓoye ɓacin ran nata, ita kuwa Hamra zuciyarta ne tayi wasai kamar an mata albishir ɗin kujerar Makka. Da haushi ya ishi Rahama haka ta fice daga ɗakin tana sakin tsaki.

Yinin yau dai gabaɗaya gidan sun yi shi ne cikin farin ciki ganin burinsu na gab da cika banda Hamra wacce tunani da fargaba suka yi wa zuciyarta ƙawanya. Lokacin siyo waken awara da yayi haka ta karɓi kuɗin wurin Inna ta fice, bayan ta dawo aka gyara aka wanke ta fita kai markaɗe sai dai ba ta samu ba, hakan yasa ta haƙura ta dawo, Inna da takaici ya ishe ta ta kora tana masifar wallahi ba za ta sa tayi asarar kuɗinta ba, ta tafi Babban layi ta markaɗo waken kuma kada ta jima.

Babu yadda Hamra za ta yi haka ta fice da bucket ɗin markaɗe a hannunta, kai tsaye Babban layi ta nufa tana tafe tana zubarwa kanta ƙwalla saboda nakasasshiyar rayuwar da take mai cike da zallar ƙauyanci da rashin wayewa a ɓangaren addini da zamani.

Ƙiiiiiiiiiiiiiii, ji kake Hamra jagwab a ƙasa mota ta share ta bayan horn ɗin da mai motar yayi ta sake mata babu ƙaƙƙautawa daga ƙarshe dai ta buge ta. Daga ita har bucket ɗin waken duk sun baje ita kam ko alamun numfashi babu a tattare da ita. Kafin kace me mutane sun kewaye wajen abunka da unguwa mai cikowa da mutane, tuni mamallakin motar ya fito da sauri yana faɗin "Innalillahi wainna Ilaihi raji'una, subhanallah!" Da sauri ya ƙarasa wurin da Hamra ke kwance babu alamun rai a tattare da ita yayinda mutanen da suka kewayeta suka fara masifa wai mutane ba sa tuƙi a hankali ba sa kallon hanya, this and that, ba tare da ya bawa maganganun nasu muhimmanci ba yace, wani ya biyo NI sai mu kai ta asibiti" wani tsoho ne ya harari mai motar yace "Babu wanda ya santa a nan, kuma ba lallai wani ya bi ka ɗin ba, kawai ka sa ta mota ka Kaita asibiti in ta tashi sai ku nemi wani nata."
Tsohon na kai wa Aya mamallakin motar ya ɗago Hamra a hannunsa kamar wata jaririya sannan ya saka ta a mota. Bai tsaya jin surutan mutanen da ke wurin ba kai tsaye ya shige mazaunin driver yayi wa motar key sannan ya tayar da ita, horn ɗin da yake musu yasa suka baje har ya samu hanyar wucewa, daga haka ya ja motar da gudun gaske don ceto rayuwar yarinyar da ya ɗauko.

Kai tsaye FUHSTH Azare ya nufa da ita, da mugun gudu ya shiga ciki kai tsaye yana nufar Accident & Emergency ward, Yana daidaita parking ya fito sannan ya ɗauko Hamra a hannunsa ya nufi entrance na Ward ɗin, ma'aikatan jinya na ganinsu tun daga station ɗinsu suka yo wurinsa yayinda wasu suka wuce ɗauko stretcher suna ƙarasowa aka ɗaura Hamra kai aka wuce da ita ciki yayinda ya samu wuri a reception ɗin yana jira.

In not more than 8minutes wata nurse ta fito tana dudduba wanda ya kawo Hamra sai dai she's unable to recognise his face, da sauri ya ƙarasa wurinta ganin daga ɗakin da ta fito. Ganinsa gabanta yasa tace "Kaine ka kawo pt ɗin can?"
"Eh nine" ya ba ta amsa a gajarce.
"Ok, follow me, za a buɗe mata EHR folder yanzu, Dr in ya fito zai tura prescription nata zuwa pharmacy za ka je ka amso har da wanda aka mata amfani da shi yanzu."
Daga haka ta wuce yana biye da ita.
Reception ta ƙarasa tayi wa wani magana, daga nan ta juyo ta dubi saurayin tace "Ka zauna can, the file will be opened now!" Zama yayi ita kuma ta koma ciki.
Ko da aka buƙaci sunan majinyaciyar rasa mai zai ce yayi, daga ƙarshe dai ya furta "A'isha Tajuddeen" sunan sister ɗinsa kenan.
Bayan an buɗe ya nufi pharmacy kamar yadda nurse ɗin ta faɗa masa and luckily Har an tura prescription ɗin, yana zuwa yayi payment aka miƙa masa ledar ya dawo.


Yana komawa ya nemi ɗaya daga cikin nurses ɗin wuri ya ba ta ledar drugs ɗin daga nan ya koma reception ya zauna tare da tagumi ya faɗa wata duniyar. Wayarsa da ke vibrating ita ta dawo da shi hankalinsa, da sauri ya zura hannunsa a aljihunsa tare da fito da wayarsa ƙirar Sumsung S8, ganin mai kiran yasa ya zaro eyes nasa waje yana rufe bakinsa da palm nasa tare da ƙara wayar a kunne.
Sallamar dattijuwar matar ya amsa yana faɗin
"Ummie" a sakalce.
"Haba Baby, ina kake ne?" Kamar wani ƙaramin yaro yace "Ummie ina hospital"
"Hospital? Me kake yi?"
"Ummie na buge wata yarinya ne shine na kawo ta." A ɗan rikice tace "Wane asibiti ne?"
"FUHSTH" ya faɗa cikin rashin sanin abinda zai ce, "ga Ni nan zuwa tare da Humaira."
"Ummie" ya ƙira sunanta a shagwaɓe, amsawa tayi da "Baby me ya faru?"
Kamar tana gabansa ya kwaɓe fuska yace "It's nothing serious fa, ba sai kun zo ba, zuwa dare ma za su iya sallamarta."
Cikin muryarta da ke nuna seriousness na Abunda take faɗi tace "Ka dai san ba zan bari ba ko? Ta yaya za ka kaɗe mutum ban zo na duba shi ba? Well ka san ba haka nake ba, just wait for us."
"To Ummie, Allah ya kawo ku lafiya. A&E Muke."

Ba tare da ta ji me yace ba tayi hanging call ɗin hakan yasa ya sauƙe ajiyar zuciya tare da mayar da wayar pocket ɗinsa. Attention nasa ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi drawing tare da faɗin "Find something for your patient Mr. Man, if possible something nutritious, da ta tashi sai a ba ta taci."
"Ok" kawai ya furta daga haka ya fice don nemar mata abun ci. A nearest restaurant ya tsaya yayi ordern abinci da kuma Kaza, yana daf da shigowa cikin asibitin ya tsaya ya saya drinks da kuma ruwa, daga nan ya dawo, lokacin su Ummie ma har sun iso.

*React and share Fisabilillah.*
*Oum_Zainab ce!*

#diamond_bhatool
#tumun_dare


[23/05,2025 5:44 PM] Diamond Bhatool 🦋.:




°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER SEVEN: New Family.*

Kiran Ummie da ya gani ne ya hana shi ƙarasawa cikin asibitin, picking yayi tare da karawa a kunnensa yace "Ummie, ok bari na zo." Juyawa yayi yana waige-waige har ya hango motarsu da suka faka can baya, ƙarasawa yayi wurin sannan ya miƙawa Humaira ledar abincin hannunsa tare da ɗage mata gira. Daga haka suka nufi cikin asibitin a tare. Kai tsaye ɗakin da Hamra ke kwance ya raka su ba tare da ya shiga ba ya tsaya har suka shiga, daga haka ya fice ya bar asibitin duk da cewa zuciyarsa ba ta masa na'am da tafiyar amma yana da abubuwa da yawa da zai yi idan yaso zuwa maghrib ya dawo, zuwa lokacin dai ya tabbatar yarinyar regain her strength da za ta iya mishi bayani ko ta ba da numbern wani nata ya ƙira a san dai a yadda take, tsaki kawai yayi tare da faɗin "Damn it!" Yana buga steering wheel Na motar.

Ɓangaren su Ummie lokacin da suka shiga sun tarar da Hamra zaune kan gadon asibitin tana share hawaye. "Ma sha Allah!" ummie ta furta tana yabawa da kyakkyawar halittar da tayi tozali da ita. Har suka ƙarasa Ummie ta zauna kan plastic chair ita kuma Humaira ta ajiye ledar hannunta kan bedside drawer da ke manne da gadon ta samu wuri gefen Hamra ta zauna amma Hamra ba ta san da su ba.
Sosai Ummie ke nazartar Hamra ganin sun shafe kusan mintuna biyar da zama amma ba ta sani ba yasa Ummie yin gyaran murya, still dai Hamra ba ta yi responding ba. Humaira ce ta kai hannunta kan Hamra tare da ɗan tapping bayanta, a matuƙar zabure Hamra ta ɗago tana zazzare idanuwa waje tare da bin su da wani irin kallo yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri.

Cikin rawar murya ta gaida matar, wacce ta amsa mata fuska sake tare da faɗin "Sannu ƴan mata, ya jikin?"
Hamra ta ba ta amsa da "Da sauƙi" cikin jin kunya.
"Ma sha Allah, Allah ya tsare gaba." ummie na dasa aya Humaira ta dubi Hamra cike da kulawa tace "Sannu Sister, yaya jikin naki?"
"Alhamdulillah " ta faɗa tana sauƙe kanta ƙasa kamar tana gaban sarki. Tunani ne fal ranta gane da mutanen, ko su waye? Ina suka santa? Oho musu, ta dai san cewa ita ba ta da alaƙa da su tunda za ta iya cewa kaf familynsu babu wani mai kuɗi kamar waɗannan. Tunaninta ya katse ne lokacin da Hamaira ta ajiye mata take away Na fried rice da kuma pepper meat a gabanta. Wani irin yawu muƙur Hamra ta haɗiye ganin lafiyayyen abincin da ke gabanta.

"Ki ci abinci, ga drugs ɗinki can sai a ba ki."
A kunyace Hamra ta jijjiga kai don kuwa matsananciyar Kunyar dattijuwar matar take. "Kina nufin ba za ki ci ba? Wait Yaya ma sunanki?" Humaita ta tambaya tana tsare Hamra da ido. Can ƙasa ƙasa Hamra tace "Hamra"
"Ma sha Allah " Humaira tayi complementing tana faɗin "Suna mai daɗi ga ki kuma mai kyau abunki, kinga Hamra please eat, kin ga ba ki jin daɗin jikinki, ko sai Ummie ta ba ki a baki ne?" Sarai ta fahimci waye Ummien hakan yasa ta jijjiga kanta da sauri tare da ɗaukar runner spoon ɗin ciki ta fara ci tana wasa da yatsarta ta hannun hagu. Ummie na lura da ita ta gefen ido, sosai yarinyar ta burge ta gashi kuma dai ba ƴar BABBAM GIDA ba ne tunda suturar jikinta ta nuna amma kuma kyau na halitta irin nata yasa Ummie shakku akan hakan yayinda tausayin yarinyar ya mamaye kowacce kafa ta jikinta tana jin kamar ma ta santa.

Ganin Hamra ta tsaya da cin abincin yasa Ummie ɗagowa a wannan karan tace "Daughter, ki ci abinci fa sosai in ba haka ba ba zan mayar da ke gida ba." Wuri-wuri tayi da ido lokaci guda kuma tsoron abunda za ta tarar a gida ya mamaye zuciyarta, ba ta yi aune ba wani zazzafan hawaye ya fara silalowa daga idanuwanta. Da maɗaukakin mamaki Ummie da Humaira ke kallonta har Ummie ta kasa shiru tace "Ba ki son cin abincin ne?" Kai ta jijjiga mata alamar a'a, "Then why are you crying?" Ta tambaya tana tsare Hamra da ido. Kaifin idanuwan Ummie yasa Hamra fara wasa da spoon ɗin hannunta lokaci guda kuma ta lula izuwa duniyar tunanin rayuwarta ta baya, first in history da wani ya mata magana da harshen nasara tun bayan rabuwar ta da Mon ɗinta, to dama ina za ta ga wanda ya iya ma bare su yi? Gidan nasu ma da babu Arabic ba boko sai shegiyar masifa da neman kuɗi?"

"Kin yi shiru daughter " Ummie ta ƙara magana ganin Hamra ta yi shiru. Da sauri ta ɗago, suna haɗa ido da Ummie ta sauƙe nata idon kasa tana cigaba da jujjuya spoon ɗin hannunta.
Ganin ba ta wani sake da su ba yasa Humaira kwashe abincin ta ajiye gefe sannan ta buɗe bottle water ɗin da ke cikin ledar ta mikawa Hamra, karɓa tayi har hannunta yana rawa tace "Na gode" sannan ta kai baki.
"Kaɗan za ki sha kada ya maki yawa kinga ga drugs za ki sha." Sauƙe bottle ɗin Hamra tayi ta amshi drugs ɗin da Humaira ta miƙo mata. Ko da ta gama sha hamdala tayi ta mayar da kanta ƙasa, her being uncomfortable yasa Humaira miƙa mata wayarta tana faɗin "Ko za ki yi game ne? Ko kallo?" Hamra dai kallon Humaira tayi tana faɗin "Ai ban iya ba yanzu."
Mamaki fal ransu jin batun Hamra, budurwa da ita ace ba ta iya danna waya ba?" Cikin rashin daɗi da hakan Humaita tace "Sorry sister, kina son wayar? Ta burge ki?" Kai Hamra ta ɗaga tunawa da wani lokaci shuɗaɗɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login