Showing 108001 words to 111000 words out of 134378 words
ke Tambari Housing Estate, a gajiye suka isa, wanka kawai dukkanninsu suka yi sannan suka ci abinci don Mubeen sai da ya tsara komai suka taho. A dai ranar kam suna gama cin abinci Kowa ya nemi makwanci don huce gajiyar da aka tara.
Washe gari da safe wuraren ƙarfe takwas lawyer ɗin da Mubeen ya tanadar don tsayawa kan al'amarin ya zo, ya samu tarba mai kyau ƙwarai da gaske daga wurin mutanen gidan, tattaunawa suka yi kan ta yaya za su fara dirarwa case ɗin tare da tsaida matsayar cewa a fara zuwa can garin da Hamra ta yi aure a biya basussukan da ke kanta sannan a fara binciken Malam sai a haɗa hujjojin da suka samu, daga nan a nemo shi uban gayyar wato Baffa shi ma a gurfanar da shi gaban hukuma.
Hakan ce ta kasance kuwa, washe gari, da Mubeen, da kuma Hamra sai Barr. Khalid suka wuce Isawa. Cikin yini guda kuwa suka gama biyan basussukan wanda ashe tun tafiyar Hamra wasu daga cikin wanda ba ta biya ba suke kai ƙara sai dai rashin samun ta yasa suka yi ƙunci amma a yau da aka biya su sosai suka yi farin ciki don irin bashin nan in ba a biya su ba an cutar da su tun da ba kaɗan ba ne.
Bayan wannan kuma an binciko Malam saboda ba barin garin ya yi ba ashe, ya ɓace ne lokacin saboda ya san za a iya nemansa daga baya kuma ya dawo tare da sabbin amare har biyu wanda yanzu haka su ke kula masa da yaransa. Sosai Aminaye ɗiyar Hajjaju ta yi farin ciki da ganin Hamra musamman da ta ganta ta sauya gaba ɗaya, sai dai kuma ta tuna mata da Mahaifiyarta da har yau ba ta ƙara ganinta ba tun ranar da suka tattare suka tafi.
Tabbas ba kaɗan ba Mubeen ya yi takaicin ganin Malam a matsayin mutumin da ke aikata shirka bayan yana da sani, amma y dake bai nuna hakan ba saboda a siyasance suke so su tattara hujjojin da za su yi maganinsa suke. Bayan sun samu kuwa, ciki har da gidajen iyayen matansa da ba sa nan, da kuma adreshin gidajen, sannan kuma ya sanar da su game da tsohuwar amaryarsa da shi har yau bai san yadda take ba, amma dai ya ba su tabbacin yadda za su samu iyayen riƙonta da suka aurar masa da ita, duk wannan bayanin da yake yi kuwa, ko kaɗan bai san naɗarsa Barr. Yake ba. Bayan sun gama samun abun da suke ganin sun samu ne suka masa sallama sannan suka fito, Ganin sun fito yasa Hamra yi wa Aminaye Sallama ta kuma ba ta wasu kuɗaɗe tare da tabbatar mata da cewa nan b da jimawa ba gaskiya za ta fito, mahaifiyarsu za ta dawo ta ɗebe su su koma wurinta, za kuma su ga danginsu da ba su san su ba. Sosai ta ɗan ji sanyi daga nan ta rako Hamra har ƙofar gida.
Tana shirin juyawa Hamra ta ce "Daure mu je ki gaisa da Yayana."
Babu yadda za ta yi tun da da hijabi a jikinta ta bi bayan Hamra suka je suka gaisar da CEO Mubeen, sannan Barr wanda ya bi Aminaye da wani irin kallo har yana jin wani irin abu a ransa game da ita. Daga nan Aminaye ta juya, su kuma suka hau mota a gajiye suka wuce.
Ba su suka isa ba sai wuraren Isha, Hamra da kanta ta roƙi Barr. Da ya ƙaraso in sun ci abinci ya wuce gidansu tunda ba aure gare shi ba. Da haka suka shige ciki su Ukun, kamar sun sani kafin dawowarsu Ammiey ta sa an girka musu lafiyayyen abinci da abun sha, suna isa kuwa akan abincin suka dira, bayan sun ci sun ƙoshi Barr ya musu sallama Ammiey sai godiya take masa. Wanka Hamra ta wuce ta ɗauro da ruwa mai ɗan karen zafi sannan ta yi sallar Isha, daga nan kuwa baccin wahala ya kwashe ta ba tare da sun yi hirar dare ba yau.
Washe gari da safe bayan sun karya Ammiey ta buƙaci ƙarin bayani akan abun da suka saka gaba, nan ya fayyace mata komai da suka gabatar da kuma hujjojin da suka tare cikin sauƙi, murna tayi sosai tare da musu addu'ar fatan nasara. Da "Amin" ya ƙare wanda hakan ya yi daidai da sallamar Barr. Fuska sake Ammiey ta tarbe shi, gaishe ta yayi daga nan tace
"Zauna mana Khalid, Hamra!" Ta ƙwala ƙiran Hamra, daga bedroom ɗinsu ta fito tana faɗin
"Ga Ni nan Ammiey" tana ƙarasowa parlourn.
"Ki haɗo wa Khalid breakfast ki kawo masa nan"
Da "To" ta amsa tana duban Khalid ɗin tace "Ina kwana Yaya Khalid."
Fuska sake yace "Lafiya ƙalau Hamra, ya gajiyar jiya kuma" tana murmushi tace "Gajiya ta bi lafiya."
Tana faɗin haka ta juya za ta nufi dining ta tsinkayi muryarsa yana faɗin
"Kin ga Hamra." Ta juyo tana sauraronsa
"Ki bar shi kin ga yanzu na gama na fito, just ki magana da Mubeen ya zo mu samu mu fita tun da wuraren zuwan yau suna da yawa."
Fuska babu daɗi Ammiey tace "Haba Khalid, me yasa ba za ka taɓa ba?"
Cike da kulawa ya fara magana ganin Ammiey ba ta ji daɗi ba "Wallahi Ammiey ina gama ci na fito"
"To shike nan" ta ba shi amsa a gajarce sannan ta ce da Hamra "ki yi wa Ɗan'uwanku magana'
Da "To" ta amsa sannan ta fara takawa don kiran Mubeen ɗin, taku biyu ta yi kawai ta jiyo ƙarar buɗe ƙafarsa.
"Ma sha Allah" ta furta ganin yadda ya yi matuƙar kyau cikin shigar jamfa ga kuma daddaɗan ƙamshinsa da ya buɗe mata hanci, babu shakka Ya Mubeen ya kai duk yadda ake buƙatar namiji ya je har ma ya wuce, maganar zucin da take ta katse ne sakamakon jin sa da tayi kusa da shi da tayi, hakan yasa ta kau da kanta gefe ta gaida shi cike da girmamawa, yana amsa mata kuma ta wuce bedroom nasu ta ɗauko veil ɗin Abayarta ta saka, tana fesa turare Ra'isa ta fito daga toilet tana faɗin
"Gaskiya Ukhty yau kam da Ni za a tafi don ba za ku bar Ni Ni ɗaya kamar mayya ba. jira Ni na ɗauko nawa veil ɗin." Ga faɗa tare da janyo veil ɗin ta yafa sannan suka fito tare.
Kallon da Ya Mubeen ya banka wa Ra'isa yasa ta ci burki tana Turo baki
"Gaskiya dai yau kam ba za ku ɗauke min ƴar'uwa ku bar Ni ba, mu je tare kawai."
Baki buɗe Ammiey tace "Yau na ga ja'ira, in kika bi su kuma to Ni kaɗai za ku bari sai kuma Nihla ke nan?"
"Babu yadda za ki je, ki zauna tare da su." Ya Mubeen ya faɗa a kausashe daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin Barr. Na biye da shi, sai kuma Hamra a baya.
Kai tsaye Gwaram suka fara zuwa, suka isa gidansu Hajjaju, abun ka da babban gida da ba ya rasa mutane suna isa aka kawo musu kayan taɓawa a can babban parlourn Mahaifin Hajjaju wanda ya tsufa sosai amma tunani da hankalinsa basu gushe ba. Sosai Hamra ta yi ta mamakin da hakan tana kuma ƙara gaskata cewa mutanen kirki ba sa wulaƙantacciyar tsufa.
Bayan sun gaisa da shi cikin mutuntawa ya dube su ɗaya bayan ɗaya, sannan yace
"Ƴan samari ban fa shaida ku ba"
Murmusawa Barr yayi sannan yace
"Allah ya gafarta Malam Ni sunana Barrister Ibrahim Khalil Abdu, wannan kuma" ya nuna Ya Mubeen "Sunansa Muhammad Mubeen Ahmad, mamallakin babban kamfanin EL-MUBEEN da ke Lagos, sai kuma wannan ƙanwarsa ce A'ishatul-Hamrā'Abubakar."
Fuska sake Malam yace "Ma sha Allah, To me ke tafe da ku? Allah ya sa lafiya."
"Lafiya ƙalau sai Alkhairi." Ya Mubeen ya faɗa a mutunce.
Nan Barrister ya sanar da shi maƙasudin zuwansu da kuma yadda suka samu gidan cikin sauƙi. Cike da ɗumbun al'ajabi yace
"Ikon Allah ikon gaske, kenan dai wannan yarinya ita ma mutumin can Yusha'u ya cutar da rayuwarta?" Su jinjina kai
"Kai amma mutumin nan Allah ya yi maganainsa." Suka amsa da "Amin". Malam ya ci gaba da faɗin
"Yanzu dai bari na sa a ƙira ita Shafa'atullah ɗin sai ta faɗa muku duk abun da kuke buƙata."
Ba tare da ɓata lokaci ba Malam ya ƙwala kiran wani jikansa da ya zo wucewa, abun ya ba su mamaki ganin dai tsufarsa mai kyau ce, Yaron da ya ƙira mai suna Ali ya ƙaraso yana gaida su Barr. Sannan ya ce "Ga Ni Jadda"
"Yi maza ka ƙira min Shafa'atullah."
"To" Ali ya faɗa tare da wucewa cikin gidan.
Bayan wani lokaci kaɗan sai ga Hajjaju cikin ƙatoton Hijabi, tana zuwa bakin ƙofar parlourn mahaifinta tayi sallama. Ya amsa mata tare da faɗin "Ƙaraso Shafa'atullah "
Umarnin mahaifinta ta cika tana mai shiga ciki ta zauna itama a ƙasa kamar yadda su Ya Mubeen ke zaune sannan ta fara bin su da kallo, sai dai kaf cikin su ba ta shaida kowa ba sai da idanuwanta suka sauƙa kan Hamra wacce kanta ke duƙe, gabanta ne ya faɗi sannan ta fito da idanuwanta waje alamar mamaki.
Gyaran murya Malam Gwani yayi sannan yace "To Shafa'atullah, waɗannan baƙin naki ne, Muhammadu ku mata bayani."
Babu ɓata lokaci Barr. Ya koro mata jawabi kamar yadda ya yi wa Gwani, take wasu hawaye suka zubo daga cikin idanuwanta, hawayen da ta kasa fahimtar dalilinsu, abu ɗaya da ta sani shi ne, ta yi matuƙar farin ciki da jin ƙudirinsu na ganin sun cafke babban azzalumi sannan kuma ganin Hamra da ta yi kamar ba ita ba Allah ya gani ta yi farin ciki da hakan don babu ranar da za ta fito ta faɗi ba ta yi zancen Hamra ba.
Ita kam ta Hamrar tana lura da yadda Hajjaju ta sauya sannan ta yi matuƙar jin daɗi da ta ganta cikin aminci. Barr. Ne ya buƙaci yi wa Hajjaju tambayoyi, ta kuma amince tare da alƙawarin faɗar gaskiya, nan ya fara hero mata tambayoyi tana amsawa shi kuma yana naɗar su sannan yana rubuce-rubuce. Bayan ya gama ya shaida mata cewa ya gama, Gwani ya ba ta umarnin komawa ciki, sai dai ta buƙaci alfarmar su shiga da Hamra su ɗan gaisa. Ya Mubeen ya ce babu komai. Nan suka bar Gwani da kuma Barr da Ya Mubeen suna ci gaba da zantukansu su kuma suka yi ciki.
Suna fita Hajjaju ta rungumo Hamra tana faɗin
"Ashe za mu ga juna Hamra? Kullum sai na yi zancenki kamar yadda nake na su Aminaye, mu ƙarasa mutanen gida su ga Hamra da suka ƙosa da jin sunanta a bakina."
Nan suka shiga gidan,. Duk waɗanda ke gidan ranar sai da suka gaisa da Hamra, daga nan kuma Hajjaju ta ja ta ɗakin da take yanzu, bayan sun zauna suka bi juna da kallo kowannensu na tunano wasu moments na rayuwarsu ta baya. Hajjaju ce ta katse shirun da faɗin
"Hamra na shiga matsanancin tashin hankali sosai a kanki da na dawo, wanda ko su Aminaye ba sa raina kamar ke musamman saboda matsalolin da na baro ki ciki, ya aka kaya?"
Nan Hamra ta labarta mata komai a gurguje, Hajjaju tace "Ikon Allah ikon gaske, wallahi na matuƙar jin daɗi da kika haɗu da ainihin danginki, ina labarin su Inna da Baffa kuwa?"
Hamra ta jinjina kai tana faɗin "Hmm, ban ƙara ji daga gare su ba, amma wanna fitowar yau ɗin da yiyuwa har can za mu saboda Su ma Yayana ya ce ba za a bar su ba, kin san ashe Baffa ne suka kashe min Iyayena?"
Zaro ido waje Hajjaju tayi tana faɗin "Ikon Allah ikon gaske, kai amma Allah ya tsinewa wannan Baffan, gaskiya dai akwai miyagu a duniyar nan, amma na ji daɗi da ya kasance akwai tsayayyun da za su ƙwatar miki ƴanci."
Hamra ta ce "Ai jiya mun je can gidan Malam, Allah dai ya ba mu nasara a wannan shari'ar don kuwa Malam bai saduda ba, yanzu haka sabbin mata biyu ne a gidan, Aminaye kuwa ita ke kula da ƴan'uwanta."
Gaban Hajjaju sai da ya faɗi jin halin da yarinyarta take, tabbas sai Allah ya saka musu irin cutarwar da Malam ya musu Duniya da kuma lahira. Ganin yadda yanayinta ya sauya yasa Hamra tace "Kin ga kar ki wani damu Hajjaju, Allah ya na sane da mu, mu dai ci gaba da addu'a in sha Allah komai ya zo ƙarshe",
A gajarce Hajjaju tace "Allah ya sa" Hamra ta amsa da "Amin" wanda ya yi daidai da shigowar Ali yana faɗin "Baba Shafa wai baƙuwar ta fito za su wuce."
Hajjaju ta ce "Ka ce tana zuwa." Daga haka ya juya su kuma suka miƙe
Hajjaju ta dubu Hamra tace "sai kuma yaushe?"
Hamra ta rausayar da kai tare da faɗin "Sai yadda Allah ya yi, amma da zarar komai ya daidaita zan tambayi Ammiey ta bar Ni na zo ko kwana biyu na yi a nan ɗin"
"To Allah ya sa" Hajjaju ta faɗa sannan ta ƙara da "Mu je, kar su gaji da jira." Daga haka Hajjaju ta rako Hamra har bakin mashigar gidan sannan ta juya.
Mota duk shiga suka bar Gwaram cike da fatan nasara ga abun da suka sa gaba, kai tsaye Zubo suka nufa a yau ɗin, a Hanya suka yi sallar azahar, sannan suka ƙarasa, suna isa Zubo kai tsaye fada suka nufa, kafin a musu iso a gun sarki kuma suka buƙaci yin Sallah, Hamra ta shiga ciki su kuma suka ƙarasa masallaci duka yi salla, suna idarwa kuma suka koma, cikin Sa'a kuwa Lokacin Mai martaba Sarkin Zubo ya fito, tsaye suka yi sai da ya zauna su ma suka zauna, a ladabce suka gaishe shi, sannan ya buƙaci sanin ko su waye su? Kuma me ya kawo su?, Nan Barr ya yi bayani kamar yadda ya yi a gidan Gwani.
Sosai abun da ya kawo su ya faranta ran mai martaba, bai iya ɓoye hakan ba kuwa sai da ya furta musu, sannan suka yi ta jajantawa juna abun da Malam ɗin yayi kafin fitowar Lantana. Ta yi mamakin ganin Hamra wani ɓari na zuciyarta kuma ta yi farin ciki saboda ita kanta duk da babu sabo tsakaninsu amma ta bugu da jin wace ce Hamra wurin Hajjaju, ta kuma yi mata addu'ar fita daga jarrabawar da Malam ya jefa Hamra lokacin da suka baro Isawa.
Bayan ta zauna mai martaba ya faɗa mata dalilin zuwansu a taƙaice sannan ya roƙar musu alfarmar ta faɗa musu duk abun da ta sani idan suka tambaye ta, ai kuwa ta faɗa musu gaskiya akan duk wata tambaya tasu yayin da Barr. Ya naɗe bayananta a abun sauti sannan ya buƙaci Alfarmar nemanta idan da buƙata. Mai martaba yace babu komai, Allah dai ya kawo ƙarshen wannan azzalumi. Da "Amin" suka amsa, daga nan kuma suka yi musu godiya sannan suka yi musu sallama, kai tsaye suka wuce duk da cewa Magrib ta gabato, sai da suka isa gari mafi kusa sannan suka yi sallar Magrib da Isha tun da lokacin isha ɗin suke, ba su suka koma Bauchi ba sai wuraren ƙarfe 9:00pm na dare. A gajiye Barri ya sauƙe su ya wuce shi ma.
Yau kam sosai jikinsu ya gaya musu, wanka kawai Hamra ta yi sannan ta ci abinci, yau ma dai ba su samu sukunin hira ba, haka ba ta bi ta kan mitar da Ra'isa ke mata ba ta ajiye wayarta sai bacci. Washe gari kam ba su fita ko ina ba suka huta abun su da shirin wayewar gari za su shiga Jos don nemo Baffa sannan a riƙe shi hannun hukuma kafin su gama haɗa hujjojinsu.
*React and share fisabilillah.*
[9/7, 10:08 PM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER THIRTY FIVE:Plan B*
Ranar talata suka shirya tafiya Jos, a wannan karon ba da Hamra aka tafi ba kasancewar case ɗin ba irin wancan ba ne. Lokacin da su Barr da Ya Mubeen suka isa Jos ba su nufi gidan Baffa kai tsaye ba sai suka wuce police station suka cika ƙorafi a kan Baffa sannan aka haɗo su da ƴan sanda kai tsaye zuwa adreshin da Malam Yusha'u ya ba su. Cikin ikon Allah kuwa da aka yi sallama a gidan sai ga Baffa ya fito hankalinsa kwance, lokacin da ya farga da ƴan sandan take hantar cikinsa ta kaɗa, juyawa yayi da niyyar komawa ɗaya daga cikinsu ya yi maza ya cafko shi yana faɗin "Ina kuma za ka je?"
Cikin kame-kame yace "A'a Yallaɓai kaya zan sauyo"
Sa mamaki Police ɗin ya dube shi don gano laifin kayan yana tambayarsa "Ko meye laifin waɗannan ɗin?"
"E ban yi wanka ba"
Ɗaya daga cikin polices ɗin da ke cikin mota ne ya diro a hasale ya ja Baffa zuwa motar ƴan sandan daga nan aka wuce da shi ba tare da sanin iyalansa ba. Da aka isa police station ƴan sanda sun yi aikinsu yadda ya kamata, da farko Baffa ya so ƙin karɓar laifin da ake tuhumarsa da ya ji uwar bari, cikin kwana biyu ya amsa cewa gadon Hamra na wajensa amma kuma bai da masaniya akan wa ya kashe Dad ɗinta.
Azabar da ya ji yasa ya amsa wannan laifin ma a karo na biyu sai dai ya ce ba iya shi ɗaya ba ne, shi da yaransa ne TJ da kuma Norah. Bisa