Showing 132001 words to 134378 words out of 134378 words

Chapter 45 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

83

da addu'oi, hakan ne ya rage mata jin zafinsa da take. Nan ya lallaɓa ta suka koma baccin. Washe gari kuwa asuba ma a gida yayi, sannan ya fara tilawar Alqur'ani a kan sallayar. Muryarsa ce ta tayar da ita. Babu ɓata lokaci kuwa ta fara mutsuniya, da sauri ya ajiye Qur'an ɗin ya ƙarasa wurinta. Nan ya taimaka mata zuwa bayi ya haɗa mata ruwa masu zafi kamar yadda yayi da dare, sosai kuma ta ji daɗin jikinta, ko da ya bar tayi alwala sai ya dawo. Bayan ta yi salla awurin bacci ya ƙara kwashe ta. Fuskarsa ɗauke da murmushi Alaramma Ya Mubeen ya ɗauke ta zuwa bed, sannan shima yayi joining nata. Babu ɓata lokaci kuwa bacci ya kwashe su.

Ba su suka tashi ba har 11, eleven ɗin ma sabida kiran da Ya Hamid yayi masa ne, sai wani tsokanarsa yake wai ya kame a ɗaki. Shi kuwa da abun ya ishe shi yace "Don ka sauke gajiyarka kan ƙanwata shine kake tunanin nima zan yi?"
Ai kuwa sai yayi shiru tare da kawar da zancen, ganin sarauniyar tasa na motsi yasa ya datse kiran. Da kanta tayi wanka bayan ƙara gada jikimta da tayi, tabbas ta ji daɗin jikin nata sosai don har ƙara gyara ɗakin tayi ta saka turare lokacin shi kuma ya shiga wanka. Ma sha Allah kawai ya furta yana ƙara godewa Allah da ya ba shi wannan adananniyar kyautar. Tabbas shi ɗan baiwa ne, shi da auren bazawara amma kuma cikakkiyar budurwa? Wannan ai sai ɗan baiwa.

Kammonta yayi yana sakin murmushi ita kuma ta galla masa harara. Bai tsaya ba ya shirya cikin wasu ƙananan kaya da suka amshe shi sa fesa turarukansa da Hamra ke mamakin yaushe kayansa da turarukansa suka zo mata.
Ganin dai da rigima take ji yasa ya dauki wayarsa ya fice, can sai ga shi ya dawo da tray a BBC, kazar jiya ce ya yi warming nata bayan searching yadda ake yi ɗin da yayi a YouTube. Gefe ya ajiye, sannan ya koma ya shigo da madara masu sanyi da kuma cup ɗaya.

Da kansa ya ɗaukota duk da yadda take bugun ƙirjinsa kan ya sake ta, a kan carpet ɗin ya direta sannan ya zauna, da ƙin ci tayi sai da yace zai maimaita irin na jiya, ai babu shiri ta rufe idanuwanta da hannayenta. Ko da ya fara feeding nata ba ta ƙi ci ba, yana ci yana ba ta har suka cinye sannan ya ba ta madarar ta sha tukun ya sha.
"Alhamdulillah" suka furta a tare.
Hakan yasa ya miƙe ya tattare komai. Yana dawowa ya ce mata su fito, ganin ta ƙi yasa ya daga ta, bai dire ba sai da suka je downstairs sannan ya ajiye ta kan kujera. Key ya saka ya buɗe ƙofar sai kuwa ya ci karo da basket shaƙe da abinci. Murmusawa kawai yayi tare da sosa kansa sai kuma ya shigo da shi ya kai dining, dawowa yayi wurinta yana faɗin "Zan fita amma yanzu zan dawo, kar kuma ji ce za ki fita a haka, baƙin za su shigo su miki sallama kafin su wuce.

Kai tsaye part ɗin Ammiey ya wuce, bayan sun gaisa da bakin ne suka bukaci zuwa yi mata sallama. Shi ya raka su har bakin kofa tukun ya ci birki. Aunty Murjanatu sosai ta ƙara nanatawa Hamra karatun wacce a yanzu ta fara shiga ajin, ta ba ta wasu kayayyakin amfanin kafin su fito su wuce. Da kansa ya kai su airport sannan ya musu Alkhairi kafin ya dawo. Da zazzaɓi a jikinta ya tarar da ita, ai bai bata lokaci ba ya kira wata Nurse ta zo ta duba ta.

Tun daga ranar Ya Mubeen ya ci gaba da lulluɓe Hamra da soyayyarsa mai tsarki, yana kuma nuna mata tattali kamar wata jaririya, a nata ɓangaren itama tana iyakarta wajen ganin komai ya tafi daidai. Ta ɓangaren Ammiey ta yi iyakar iyawarra itama wurin ganin Hamra ta sako jiki da ita don tun da aka yi auren take wani ja baya da ita. Satinta biyu ta tattara ta koma school, yawanci colleagues ɗinta sai tsokanarsa suke wai ko ta taho musu da tsarabar ɗan baba. Murmusawa kawai take daga nan ta ci gaba da abun da take ba tare da ta tanka musu ɗin ba.

Ana haka wata rana lecturer ɗin su bai zo ba, ita kam note ma take kwafa sai dai ta ɗan dakata jin ana zance da wata ƴar ajin nasu. Though ba wani yi suke da ita ba, amma ta ja hankalinta a yanzu jin tattaunawar da suke game da littafin A BABBAN GIDA, sai kuma shi kamar an ce ita ce marubuciyar. Babu shiri ta ajiye note ɗin ta ƙaraso wurinsu tana faɗin
"Na ji kuna magana akan littafin A BABBAN GIDA, dama ba iyi Ni ba ce nake karatun littafan Hausa ba?"
Wata dariya ɗaya daga cikinsu tayi tana faɗin

"Ai Ni kam na jima ina karantawa."
Ɗayar kuma tace "Ni kin ga, ta dalilin Diamond Lady na fara karatu, don zan iya ce miki dai ita ce ta fara ba Ni littafin da ta rubuta, na ɗauka ƙarya ma take ashe dai da gaske ita ta rubuta"
Cike da zumuɗi Hamra tace"Wai wannqn ce marubuciyar?"
Ta faɗa tana nuna marubuciyar da hannu
"Ƙwarai"suka ba ta amsa a tare.
"Ma sha Allah kawai tace, sannan ta ƙara da faɗin "Na karanta littafin A BABBAN GIDA kuwa? Na dai ga ana posting dinsa, zan so na karanta gaskiya."
Jamila tace "Ma sha Allah, ai sai na tura miki zuwa yadda aka tsaya."
"Ki tura min ta Whatsapp kawai."
"To shi ke nan, ba Ni number ɗinki"


Nan Hamra ta ba ta number ɗin tare da faɗin "Na gode, za mu karanta littafin midwife colleague kenan, Allah ya ƙara basira."
Daga haka ta mike ta koma sear ɗinta ta ci gaba da rubutun ta. Ba ta samu damar karanta littafin ba kasancewar suna gab me da fata weeding exams nasu. Bayan sun yi jarraba ne suka tafi hutun sati biyu tare da alhinin jiran result ɗinsu.
A ranar da result ya fito kar ku so ku ga Hamra yadda take murna ganin itama ta haye dukka darrusa babu na gyarawa ko kuma kora. Ganin ta kammala yasa tace da ta karanta books a sauran kwanakin da suka rage mata.

Ma sha Allah, bayan ta fara karanta littafin A BABBAN GIDA ne taji ya mata daɗi, musamman wurin da Mamah ta bar Zahra a hannun Aunty Amarya. Hakan yasa taji kamar ita ce lokacin tana gidan Inna. Ganin har lokacin a book one suke kuma tana kan rubutawa yasa Hamra ci gaba da bibiyar littafin. Sashe guda kuma tana mamakin wai ta yaya Diamond Lady ke rubutun? Ita kam ba za ta iya ba, ko dan kowa ma da irin ƙwaƙwalwarsa da haka ta waske ta ci gaba da hidimominta.

*React and share fisabilillah*

*Tap the link below to follow my TIKTOK account.*


https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER FOURTY TWO*


Ranar wata juma'a da yamma ta shirya zuwa gidan Aunty Murjanatu don yi weekend a can. Lokacin da ta isa ta fito daga adaidaita kenan ta hango wata mata wacce ta yi wa kallon sani. Kamar za ta wuce saboda zuciyarta na faɗa mata ba ita bace gaskiya duba da ganinta a wurin Masu karban sadakar abinci. Har za ta shige gidan kawai sai ta ji bukatar zuwa wurin matar. ƙarasa tayi suka gaisa sosai ita matar na mamakin yadda ƴar gayun ke gaisawa da ita babu ƙyamata.


Murmushi Hamra tayi sannan tace
"Ba ki gane Ni ba ne Umma?"
"Hana yarinya, ai ban ma san ki ba nikam, ballantana a zo gandun gane ki"
Da mamaki Hamra ke bin Umman Amira kafin ta ce "Yanzu dai mu shiga ciki, daga nan zan miki bayanin Ni wace ce."
Har za ta yi musu sai Hamra ta lallaɓa ta suka shiga, ta gabatar da ita wa Aunty Murjanatu a matsayin wacce ta mata abun Alkhairi a shekarun baya. Ai kuwa Aunty ta sake da ita tace Hamra ta zubo mata abinci. Sosai Umma ke jin daɗin yadda suka mata musamman ma da ba ta san ta ba.

Tas sai da ta cinye abinci ta kora da zoɓonta mai ɗan karen sanyi. Bayan ta gama suka ƙara gaisawa Hamra na tambayarta Amira. Umma ta amsa mata da "Amira ai ta yi aure, yaranta biyu na yanzu kam."
"Ikon Allah, ko don ma, ai an jima sosai, Umma Hamra ce dai."
Da farko ba ta gane ta ba, sai da ta mata bayani tukunna ta gane, ai kuwa sai kuka, Hamra kuma na aikin rarrashi, maganar Hausawa na faɗin ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...ta fa tabbata. A nan take faɗa mata cewa su Inna sun dawo nan Azare da zama bayan wasu shekaru, sai dai saɓani ya shiga tsakanin Inna da Baffa har sun rabu, an ce ma wai Innar gefen jikinta ɗaya ya shanye, Khadi ƴarta kuwa tun kafin ta tafasa ta ƙone, don bin maza take sosai, wasu sun ce ma ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV), ita kuma Rahama mijin nata ba wani Mai hali ba ne.

Sosai su Hamra suka ƙara jinjinawa ƙudirar Ubangiji, tabbas Allah ba azzalumin bawa ba ne, ubangiji ya haramta zalunci, ya kuma yi bushara ga azzalumai kan cewa zai ƙwatarwa waɗanda suka zalunta haƙƙoƙinsu. Ga shi tun ba a je ko ina ba kowa ya fara amsar sakamakonsa. Haka dai suka yi jugum kowa na yin zancen zuci. Ko da Umma ta tambaya wai Aunyy Murja kishiyarta ce. Dariya kawai Hamra ta yi tace, ita ba ma a nan ɗin take ba, karatu ta zo. Gidanta a Lagos yake.. Umma dai yau an kashe ta da kayan mamaki. Ko da za ta tafi Aunty Murjanatu ta ba ta kayan abinci mai ɗan yawa, ta kuma mata alƙawarin in har mijinta ya amince za a samar mata kwano a gidan. Sosai Umma ta yi farin ciki tana ta zuba godiya. Ko da Hamra ta fita raka ta sai da ta ƙara mata da dubu goma da ta ciro a wani shagon POS kusa da su.

Tun da Hamra ta koma school ta zama wata shiru abunta, masu zuciya irin ta Hamra ƙalilan ne, irin zaluncin da Inna ta mata amma halin da ta shiga wai tausaya mata take, lallai Hamra ta cika mai farar zuciya.
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har suka samu wani hutun, Hamra ba shiri aka harba Lagos aka ci gaba da shan soyayya na tsawon two weeks sannan aka dawo. Ranar da ta dawo kamar an ce je facebook, kawai ta shiga bayan kuma ba amfani ma take da shi ba, kawai dai tana da account ɗin ne. Wani shafi ne a sahar suka wallafa cewa Malam Allah ya masa rasuwa. Kuma dai musabbabin mutuwar tasa shi ne, haukar da yayi tuburan yana yaƙushi da kartan jikinsa da faratunsa sai kuma wasu surutan banza da yayi ta yi.

Labarin tabbas ya daki zuciyar Hamra, ta dai bi shi da addu'ar Allah ya jikansa.

A gajiye suka gama lectures yau, saboda haka ba ta tsaya karatu ba kamar yadda take yi a baya, sai ma wucewarta hostel da tayi. Sai da ta ci ta ƙoshi tukun tayi wanka. A wurin bacci ya fizge ta, shigowar wata maƙwafciyar room ɗinsu yasa ta farka. Nan ta tattari kayan karatunta da Sallaya ta wuce school Library nasu. Karo suka ci da Diamond Lady wacce aka ce mata ita ta rubuta littattafin A BABBAN GIDA. Gaisawa suka yi a tsattsaye Diamond Lady ta musu sallamar za ta wuce gida.

Washe gari kuwa Hamra na zuwa school ta waiga, gani Diamond Lady ta zo yasa ta ƙarasa wurinta. A nan suka yi ƴar hira, har Hamra ke tambayarta ko in ta ba ta labari za ta iya rubuta mata? Ai kuwa ta amsa mata da za ta yi.


Karon farko da ta faɗawa Ya Mubeen cewa yayi a'a, da ƙyar ya haƙura bayan ya sa an bincika masa ita kanta marubuciyar da kuma gidansu, har da alaƙarta da mutane.

A lokacin hutunsu na semistar farko ta aji biyu ta fara ba ba wa Diamond Lady labarinta, wanda sosai ya taɓa zuciyarta ba kaɗan ba. Sai dai kuma ƙarshen labarin ya yi, ko ba komai tun a duniya azzalumai sun fara karɓar sakamakon su.


*Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah*

Duka duka a nan na kawo ƙarshen littafin TUMUN DARE, wanda ya kasance labari na gaskiya ba kuma ƙirƙira ba, abun da zan iya cewa ɗaya, sunayen mutanen an sauya saboda wani dalili na privacy. Ina fatan za ku ɗauki darrusa masu kyau daga gare shi tare da fatan taya Ni roƙon gafarar mahalicci akan duk wani kuskure da nayi cikinsa. Fatan za ku kasance biye da Ni cikin sabon labarina mai taken RIKITACCIYAR ALAƘA, wanda a baya na masa take da AYA DA TSAKUWA.

_Godiya ta musamman ga ƙungiyata ta MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION tare da ɗaukakin mutanen cikinta. CEO I tamu Queen Nasma har da CEO II, Hamza Muhammad Hamza, Alkhairin Ubangiji Ya kai gare ku a ko'ina kuke._
_Ɗumbun godiya gare ku masoya bisa haƙuri da juriyarku na bibiyar wannan labari. Ina fatan Ubangiji ya saka muku da Alkhairi ya kuma haɗa fuskokinmu a aljanna._
_Yayata kuma marubuciya Maman Muhibbat, mamallakiyar littafin ZAMAN ƳAƳANA godiya dubu bisa bibiyar labarina da kika yi. Ina rokon Ubangiji da ya jiɓanci al'amuranki, ya ci gaba da kulawa dake tare da haɗa ki da nasarori marasa yankewa._
_Ina na isa na manta da ke Ƴar'uwata Sa'adatu Abdullahi, soyayya da kuma kulawar ki daban take. Ina roƙon Ubangiji ya bar mu tare._

Diamond Bhatool 🦋
©®2025

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login