Showing 21001 words to 24000 words out of 134378 words

Chapter 8 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

67

daga babin rayuwarta.
"Shikenan, zan ba ki tawa Ni kuma Yaya na zai siya min wata, na kunna Miki kallo?" Da kai Hamra ta amsa tana mayar da kan nata ƙasa. Kallo Humaira ta kunna mata sannan ta miƙa mata wayar.

Ringing ɗin wayar Ummie ne yasa Hamra ɗagowa, cikin rashin Sa'a idanuwansu suka haɗu da na juna, tuni Hamra ta sauƙe nata tare da ci gaba da kallonta. Bayan Ummie ta gama waya ta matso kusa da Hamra, cike da kulawa tace "Daughter za mu wuce gida yanzu, Son yana zuwa in an sallame ku zai mayar da ke gida, gobe za mu zo mu duba jikin naki kinji?" Ƙarfin hali irin na matar Hamra ke jinjinawa cikin ranta. Ba ka san mutum ba kawai ka nuna kulawa a kansa, idan kuma mugu ne fa?. Fuskarta da Ummie ta shafa yasa ta dawo cikin hankalinta, murmushi ta saki yayin da lokaci guda taji kamar kada su gusa a kusa da ita.
"To Mama, na gode, Allah ya saka da alkhairi." Cikin sakin fuska Ummie tace "Amin daughter, Allah ya ba ki lafiya. Humaira" Ummie ta mayar da dubanta ga Humaira wacce ta amshi wayarta a hannun Hamra tana gyara mayafin kanta.
Cikin kulawa ta dubi Hamra tace "To Hamra, sai mun zo Ni da Ummie gobe."
"Na gode" Hamra ta amsa can ƙasa maƙoshi, daga nan suka fice daga ɗakin.

Bayan tafiyarsu kwanciya Hamra tayi cikin ranta tana tunanin ya rai tasu za ta kaya da Inna sai dai kirkin da su Ummie suka nuna mata yasa taji ta at ease, Har tana ganin kamar za su taimakawa rayuwarta kasancewar su mutane na uku bayan Su Inna da Umma da suka shigo cikin rayuwarta ba tare da saninta ba. Kiraye-kirayen sallar maghrib yasa ta fara ƙoƙarin sauƙa daga gadon asibitin. Cikin ƙarfin hali ta shiga ɗakin da take da tabbacin bayi ne sannan ta yo alwala ta shimfiɗa kwalinta tayi sallah, har tayi AZKAR ba ta tashi ba, wata nurse ce ta turo ƙofar don duba yanayin jikin Hamra. Ganinta ƙasa ta ƙaraso da sauri tana tambayarta me yasata zauna ƙasa.
"Ba kya tsoron ki shafi cututtuka?" Kai ƙasa Hamra tace "Salla nayi, babu abun shimfiɗawasai nayi a kan kwali na." Nazartarta Nurse ɗin tayi sannan tace "Ki tashi haka, kwalin kuma ki jefa shi kwandon shara gudun kar cutukan da suka shafe shi kema su shafe ki."
Gyada kai Hamra tayi ta ɗaga kwalin ta nufi green dustbin ta saka ciki. Tana dawowa Nurse tace "Zan saka Miki sauran ruwan ne, da ya ƙare kuma likita zai sallameki."

Jin hakan yasa gaban Hamra bugawa amma ta dake ta haye gadon asibitin, babu ɓata lokaci Nurse ɗin ta saka mata ruwan sannan ta fice. Bacci ne ya fara fizgarta hakan yasa ta lumshe fararen idanuwanta, hakan ya yi daidai da shigowar wanda ya kawo ta asibitin. Sallamar da yayi yasa ta buɗe idanuwanta, suna haɗa ido ta janye nata daga gare shi, murmushi yayi kawai ya shigo yayi wa kansa mazauni da plastic chair ɗin da ke kallon gadon.
Can ƙasan maƙoshi Hamra tace "Ina yini."
Fuska sake ya amsa da "Lafiya lau, ya jikin naki?" Ba tare da ta kalle shi ba tace "Da sauƙi."
"Ma sha Allah, har yanzu babu wanda yazo daga gidanku?"
Shiru tayi masa har sai da ya maimaita tambayar kana tace "Ai babu wanda zai zo."

Idanuwansa waɗanda ke ɗauke da ayar tambaya ya zuba mata har sai da ta ƙware. Ganin hakan yasa ya furta "Subhanallah!" Tare da taimaka mata ta tashi zaune a hankali kuma yana tapping bayanta har tarin ya sarara.
"Sorry, I don't mean any harm, kin ce babu wanda zai zo, then ki ba Ni mumbern wani na kira sai a faɗa musu yadda kike kada hankalinsu ya tashi."
Ji tayi duk ta muzanta jin yadda yake saka turanci cikin maganarsa kamar dai yadda mamansa da kuma ƙanwarsa ke yi, Ba tare da ta kalle shi ba tace "Ban iya mumbern Baffa ba, Inna da Rahama ba su da waya." Kansa ya dafe yana mamakin wai dama a yadda zamani ya waye akwai gidan da babu waya, in akwai ma dai a ce mace kamar Hamra ba ta da waya? Kawar da tunanin yayi yana faɗin
"Shikenan, amma za ki iya gane gidan ko? A wace unguwa kike?"
Kai ta gyaɗa tana faɗin "Zan gane, a Matsango ne gidan mu."

Wayarsa ya duba sannan yace "Ok, zan mayar da ke sai in faɗa musu komai." Kai kawai ta gyaɗa masa daga haka ta juyar da kanta gefe, fargaba da tsoro ne suka mamaye zuciyarta jin batun zai mayar da ita gida, tsoronta Allah tsoronta Inna, asarar waken awara da bokiti ko kuma asarar rashin yin awarar kanta? Ba ta san ciki yau akan wanne Inna za ta huce ba, asali ma za ta iya cewa sai ta biya ta, a ina za ta samu? Wanda yake ba ta ma yanzu ga shi suna son yi mata katanga da shi." Ba tare da ta sani ba hawaye sukaa fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta. Jin ta yi shiru yasa Saurayin kallonta, ta juya fuska ba ya iya ganinta sai dai jikinsa na ba shi ba lafiya ba. Kasa haƙuri yayi hakan yasa shi gyara muryarsa sai dai ba ta yi yunƙurin juyowa ba.

"Ƴan mata” still dai ba ta juyo ba, in fact ma ba ta cikin wannan duniyar ta lula samaniyar tunani. Bakin katifar ya buga da hannunsa hakan yasa tayi saurin goge hawayen fuskarta ta juyo, this time also suna haɗa ido ta janye nata.
"Kuka kike yi?"
"A'a" ta ba shi amsa tana jijjiga kai.
Fuskarsa ya haɗe kamar ba shi ba yace "Ni za ki yi wa ƙarya? Na miki kala da wanda za ki yi wa ƙarya?"
Tsorata tayi hakan yasa ta fara jijjiga kai tana faɗin "Ka ka kayi haƙuri" a rarrabe.
"Ba haƙuri za ki ba Ni ba, amsa za ki bani"
"Kuka nake yi" ta faɗa tana ƙara share wata ƙwallar.
Sanyaya muryarsa yayi a wannan karen yana jin tausayin yarinyar cikin ransa.
In a caring manner yace "Me yasa kike kuka?"
Shiru tayi sai dai ya maimaita tambayar sannan ta fashe da kuka mai taɓa zuciya tana jijjiga kai tace "Babu komai" ganin yadda ya haɗe fuska yasa tayi saurin faɗin "Inna! Inna, na shiga uku."

Bai hanata kukan ba har sai da ta gaji don kanta sannan ya dube ta cike da tausayawa da kuma kulawa yace "Ya isa, ki yi shiru ki min magana a nutse kin ji?"
Kai ta gyaɗa masa, ya miƙa mata handkerchief nasa mai ƙamshi ta amsa ta goge fuskarta sannan ta fara wasa da yatsunta
"Ina jin ki, mrye sunanki?"
A sanyaye ta amsa masa da "Hamra"
Murmusawa yayi yace "Nice name, as you are." Ƙiƙƙifta ido ta fara jin ya saka turanci cikin maganar har sai da ya fahimci dalilin hakan, bai mayar da hankali ga hakan ba yace "Me yasa kike kuka? Waye Inna? Me za ta Miki?"
"Innata ce, a wurinta nake, matar Baffana ne, ina mata tallar awara, yanzu ban san ina wakenta da bokitin suke ba, wallahi za ta jya kashe Ni a kan su."
Cikin sigar lallashi yace "Kin ga yi shiru maza, yi haƙuri babu wanda zai duka ki, ina tare da ke, ki ɗauke Ni matsayin ɗan'uwanki kin ji?"

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kai
"Yauwa, good girl, yanzu dai kada ki damu, in za mu koma sai mu biya ta kasuwa mu sayo waken har bokitin in case in ta ce sai kin biya ta sai a ba ta, maza ki daina kuka kinga ke ƴar gata ce." Wani irin daɗi ne ya mamaye fadar zuciyarta tuni ta saki murmushi har gefen kumatunta ɗaya na lotsawa. Binta da kallo yayi yana murmusawa sannan yace "Kyakkyawa, kina murmushi, kin fi kyau, kin ji?" Hamra ta gyaɗa masa kai sannan yace "Good girl, yanzu ki ba Ni labari mai daɗi, ina jinki."
"Ai ban iya ba" ta ba shi amsa kai tsaye.
"Kin fa iya, kawai ba ki son yi min ne."
Kamar za ta yi. Kuka tace "Allah ban iya ba, Da ne Mom take yi min, amma Inna ba ta taɗi da Ni, iya dukana take yi."
"Duka kuma, babba da ke?" Ta gyada masa kai
"Kar ki damu ta daina dukanki daga yau in sha Allah."

Cikin ƙanƙanin lokaci Hamra ta sake da Hamid wanda shima tuni zuciyarsa ta amince da ita sanadiyyar tausayinta da ya mamaye ruhinsa, tabbas a iya kallon da ya mata ya tabbatarwa kansa akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da ita, and he promised to help her out from the hardship she's in now." Sallar Isha' ya fita yayi, ita dai ba ta yi ba saboda ƙarin ruwan hannunta, hirarsu suka ci gaba da yi har yana ba ta labarin Ummie da Humaira, that Mahaifinsa ya rasu, Ummie ce ke kuka da shi da ƙanwarsa ɗaya, wacce suka zo ɗazu.

Cikin ranta kuwa sosai taji duk damuwarta ta kau musamman da ta ga yadda suke da kirki, fatanta Allah yasa silar samun farin cikinta kenan. Har ƙarin ruwan da aka mata ya ƙare suna hira abunsu kamar sun shekara da sanin juna, fita yayi ya ƙira nurse aka cire mata, can Dr. Ya zo ya rubuta musu sallama, daga haka suka fara shirin fita, tsayar da ita yayi yace ta zauna zai amsa ƙira.
Yana fita ya ƙira Ummie yace mata za su zo da Hamra, da ta tsare shi da tambaya sai ya faɗa mata komai da yaji daga wurin Hamran, hakan yasa ta amince masa. Ko da ya dawo ya faɗawa Hamra ba ta wani damu ba, at least yau za ta yi kwanan daɗi itama.

Kai tsaye gidansu da ke Gandun Wambai ya nufa da ita. Tun da take a Azare ba ta taɓa tsammani akwai gidaje masu kyau irin waɗannan ba, daidai wani makeken gida yayi horn, gateman ya buɗe, ita dai Hamra sai kalle-kallenta take yi babu ruwanta, har Yaya Hamid yayi parking ba ta san sun iso ba, sai da ya ɗan kaɗa mata keys ɗin hannunsa ta ɗan zabura ta dube shi. Gira ya ɗage mata yace "We're home." Ƙoƙarin buɗe motar take ta kasa kasancewar yanzu kusan shekaru huɗu rabonta da ganin mota, talkless of ta taɓa ta bare kuma ta dhiga ciki. Kallonta yayi yayi murmushi daga nan ya miƙa hannunsa ya buɗe mata sannan ta fita, ja tayi ta tsaya har sai da ya fito yace "Mu je" tukunna tabi bayansa.

Makeken mansion ɗin nasu ya nufa tana biye da shi yayinda idanuwanta suka kasa zama wuri guda, cikin ranta kuwa tunani ne fal, dama a garin nan ma akwai gidaje irin waɗannan kamar a London? She asked herself. To her surprise lokaci guda ta rasa Ya Hamid a kalle-kallenta. Jin ya daina jiyo footsteps nata yasa juyo, ganin bai ganta ba yasa ya saki murmushi tare da juyawa, hango ta yayi daga can nesa tana zazzare idanuwa, da sauri ya ƙarasa ya riƙo hannunta yana faɗin "Me kika tsaya yi a waje, let's get in" cike da jin kunya ta bi shi suka ƙarasa tana ta jinjina kyau irin na gidan ta wani ɓangare kuma wani sashe na rayuwarta na baya na dawowa cikin zuciyarta.

Ko da suka shiga a nan ne tayi kallo, don kuwa kasa ɗauke idanuwanta tayi daga duk wani abu da ya burge ta. A Parlour ya zaunar da ita sannan ya wuce bedroom ɗin Ummie ya sanar da ita zuwansu. Fitowa Ummie tayi ta tarbe hannu bibbiyu sannan ta ƙwalla kiran Humaira. Ko da Humaira ta ƙaraso wani ihun murna ta saki har sai da Yaya Hamid ya aika mata kallonsa tukun ta dawo daidai tana shagwaɓe fuska kamar za ta yi kuka tace "Kai Yaya, ina farin cikin ganin Sos Hamra ne shiyasa, I'm sorry." Ta Idasa tare da rufe bakinta da hannunta. Harararta yayi, hakan yasa ta ƙaraso wurin Ummie tana faɗin "Ga Ni Ummie"

Itama Ummie kallo ta cilla mata tace "Sai yanzu kika tuna na ƙira ki ashe" shagwaɓe fuska tayi tana faɗin "I'm Sorry Ummie, duk ɗaukin ganin Sis Hamra ne, haba Ummie ta, hana kuka." Kunnenta Ummie ta ja har sai da ta saki ƙara sannan ta saki tana faɗin "kya sani ai, maza ki taya Hamra tayi wanka, cikin sabbin kayan ki ki bata wani ta saka."
"To Ummie." Daga haka ta karasa wurin Hamra ta taimaka mata ta miƙe suka shige bedroom nata. Zaunar da kta bakin bed tayi sannan ta wuce toilet ta haɗa mata ruwa, daga nan ta fito tace "Ki shiga ki yi wankan, bari na fitar miki kaya kafin ki fito." Kai Hamra ta gyaɗa tana ƙara jinjina karamci irin na Ummie da iyalanta, lallai da za a samu kowacce mace ta kasance mai irin halin Ummie, da babu shakka waɗanda iyayensu duka riga mu gidan gaskiya ba za su yi maraici ba.

Bayan Hamra ta fito Humairah ta nuna mata mirror tace ta shafa mai. Ganin ba ta da niyya yasa Humairah ta taimaka mata, har kwalliya sai da ta mata, sosai Hamra ta koma kamar wata jinin larabawa. Cikin sabbin ɗinkinta da Yaya Hamid ya mata ta ciro wata atampa ɗinkin doguwar riga ta ba ta ta saka, kai! Ma sha Allah! Gaskiya ne, mace tana zama mace ne kawai idan ta ja kaya, tana gama shirya wa tace muje wurinsu Ummie jiranmu suke a Parlour.
Tun kan su ƙaraso both Ummie da Yaya Hamid suka ƙure Hamra da kallo ganin yadda tayi kyau da ta ja kaya, sosai ta burge dukkansu har Ummie na fatan inama iyayen Hamra su bar mata ita ta haɗa da Humairah, sai dai babu tabbas, fuska sake suka tarbe ta da ta ƙaraso suna yaba irin kyan da tayi har sai da kunya ta kamata, ta san tana da kyau ita kanta amma dai ba kamar yadda suke zuzutawar ba. Abinci Ummie ta yi serving ɗinsu ita da Yaya Hamid, kaɗan taci ita kam saboda kallon da yake Bin ta da shi. Bayan sun ci abinci Ummie tace taje ta kwanta ta huta. Kayan bacci Humairah ta ba ta ta cire waɗancam daga nan ta baje kan makeken bed ɗin,kafin kace me bacci ya kwashe ta har da minshari.




*React and share Fisabilillah.*


[27/05,2025 10:36 AM] Diamond Bhatool 🦋.:

°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_




*CHAPTER EIGHT: Back in a saddle.*


*This chapter is dedicated to AYSHER ANGEL, the brilliant and special writer who writes not only to impress readers, but to pass important messages regarding our daily life. _MUTUWA A MAƘOSHI, MUGUN ABU JAKADA, na daga cikin littafan marubuciyar, tabbas Akwai saƙonni masu girma a ciki, kada ku bari a yi babu ku, masu son karantawa sai su biya kuɗi ta asusun bankin marubuciyar, 9169472057, ko su tuntuɓeta ta lambar WhatsApp ɗinta +2349169472057, kar ku manta ba iya waɗannan ba ne littafanta, akwai sauran, duka dai za ku same su idan kun magantu da ita.*



*INNA*

Shiru-shiru tana jiran dawowar Hamra daga markaɗe ta samu a ɗaura awarar sai dai har aka yi la'asar babu Hamra babu alamarta. Sosai ran Inna ya ɓaci sai surfa bala'i take tana ɗaukar alwashi iri-iri akan Hamra. Inna dai ba ta yi tunanin ko wani mummunan abu ya faru da ita ba, damuwarta dai a dawo ayi awara amma shiru. Ganin yamma liƙis babu Hamra babu alamarta yasa Inna ƙwala ƙiran Rahama, ba ta amsa ba sai can tazo ta tsaya kan Innar wacce ke zuba masifa kamar za ta bugi babu.
"Inna ga Ni nan"
"Maza Rahama saɓa Hijabinki ki fita ki dubo Babban layi, yarinyar nan har yanzu ba ta dawo ba, hala ta tsaya yawon nata na barbaɗa mana, in kika ganta ki ci ubanta tun a can kafin ku zo gida, wallahi ba ta isa ta sa Ni nayi asara ba, shegiyar yarinya kawai."
Tura baki Rahama tayi tana buga ƙafa kamar yarinya "Gaskiya Ni Inna babu inda zan je, kawai ki jira ta dawo iya ci ubanta."
"To Shikenan, bari naga iya gudun ruwanta."

Shiru-shiru dai Hamra har aka yi maghrib, ganin har lokacin ba ta dawo ba yasa Inna saka Hijabinta ta nufi babban layi, duk wanda ta tambaya sai yace gaskiya bai ganta ba. Daga ci gaba ƙarshe dai haka ta dawo. Ko da Baffa ya dawo ta sanar da shi abinda ya faru ce mata yayi "Rabu da ita, Allah yasa ta tafi har abada, kai Allah yasa ma mota ce ta murtsiketa ta mutu..." Kafin ya ƙarasa Inna tace "Amin"
"Yo gwanda ma ai ta mutun, mu samu mu kafa daular duniyarmu. Yanzu jira nake yau mutanen can sun ce za su dawo, a saka ranar bikin Rahama daga nan kawai mu bar garin don gaskiya na gaji da rayuwar nan da nake bayan ina da ababen rayuwar.

Suna cikin hirarsu sai ga yaro ya shigo sallama. Bayan Baffa ya fita ya tarar da su Alhajin Gagidiba. Kamar wancan karen shi ya ɗauko musu tabarma suka zauna, ba su ja zance ba suka sanar da shi abinda ke tafe da su. Shiru Baffa yayi can yace "Idan na fahimce ku dai ba ku buƙatar auren ƴar wajen nawa ko?"
Babu ja Alhaji Suraja yace "Ƙwarai kuwa, yaro ya ce ba ya so, waccar yake so, haka uwarsa ma dai ta ce waccar take so."
"To shikenan, Ni kuma bani da hannu akan waccar kuma ba Ni da niyyar aurar da ita yanzu. Inaga Shikenan. Za ku iya wucewa" Baffa ya faɗa a hasale. Ba su biye masa ba kasancewar su ɗin manyan mutane ne, daga haka suka yi masa sallama suka wuce wuce abunsu.


Ko da ya koma yayi wa Inna bayani suka hau sau faɗa suke kamar ana dole, Rahama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login