Showing 123001 words to 126000 words out of 134378 words

Chapter 42 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

86

_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY NINE*

A matuƙar fusace ya wuce ciki ba tare da ya bi ta kan wayar ba, a can ɓangaren Hamra kuwa da ta ji kiran ya katse dariya kawai tayi tana faɗin "Mai hali dai ba ya fasawa, sai iya nuna kishi amma ya kasa furta kalmar soyayya.."
Daga haka ta ci gaba da abubuwan da ke gabanta.

Ya Mubeen na shiga parlour sama ya haye ba tare da tunanin cewa yanzu su biyu ne a ɗakin ba. Da kallo Ya Hamid ya bi shi yana mamakin ko lafiya? Sai dai bai kula shi ba ya ci gaba da danna wayarsa. Toilet ya shige ya sakarwa kansa ruwa, ya dade sosai kafin ya fito, ko da ya fito lokacin ya dawo hayyacinsa sai dai abun da ke damunsa bai bar ransa ba. Jallabiya ya saka sai kuma ya koma yana duba aljihun kayan da ya cire yana duba wayarsa. Tsaki ya saki da ya tuna ya yasar da ita.
Tsakin nasa ya jawo hankalin Ya Hamid har sai da ya tambaye shi lafiya?
Bai kula shi ba sai ma fita da yayi, can kuma ya dawo hannunsa riƙe da wayar tasa da babu abun da ya same ta kamar ba ita aka yasar ba, lallai kuɗi kam sun yi aiki ba shakka.

"Man" Ya Hamid ya kira sunansa
Bai kula shi ba bai kuma sa ran zai kula shin ba amma ya dake tare da ajiye wayarsa ya sauƙo daga kan bed ɗin ya dafa kafaɗarsa. Ajiyar zuciya ya saki jin hannun ya Hamid ɗin a jikinsa babu zato.
"What's wrong with you?"
Nutsuwarsa ya tattara wuri guda tare da faɗin "Nothing" can ƙasan maƙoshi.
"Babu wannan zancen," ya jawo shi ya zaunar da shi tare da bashi total attention nasa
"Na san ka na kuma san kai waye, remember we've been together since! Don Allah ka faɗa min me ke damunka"
Ganin yadda ya Hamid ya nuna damuwarsa kansa yasa ya sauƙe ajiyar zuciya,
"Ina jin ka?"
Ji yayi kamar kar ya faɗa sai kuma ya tuna cewa in ya yi shirun ma babu abun da shirun zai haifar. Hakan yasa ya buɗe bakinsa yace "Wai yarinyar nan ne take ce min wai za su daidaita da shi? Ji fa!" Ya faɗa sounding so intensed.

Ya Hamid y fahimci kan wa yayi maganar, murmushin gefen baki yayi tare da dafa kafaɗar Ya mubeen ɗin
"Calm down my friend, wai wayr kake magana a kai? Haushi ma tambaye tasa ta ba shi, sai kuma ya tuna da cewa ashe shima yana son Hamrar, hakan yasa yace "Hamra" kai tsaye.
Ba tare da nuna wata damuwa ba yace "Me ta yi?"
A fusace yace "wai Ni ƴar nan za ta cewa wai za su daidaita da guntun yaron can?"
Ajiyar zuciya ya Hamid yayi tare da jinjinawa kansa yadda Ya Mubeen ɗin ke sonta,
"Ka ga, wai kai tunaninka fushin naka ne zai sa ta so ka ko kuma me?"

Wannan karon a fusace ya miƙe da ƙyar ya Hamid ya ba shi hakuri ya yadda
"Ka yi hakuri my friend, amma magana ta gaskiya, ya kamata ka nutsu, sai mu yi magana"
Shiru yayi na tare da ya ce komai ba ya zauna Kamar yadda Ya Hamid ɗin ya faɗa.
Bayan sun zauna ya Hamid ya dube shi yace "Yanzu ita yarinyar ta san kana son ta ne ko kuwa jiji da kanka ya sa ba ka faɗa mata ba?"
Ransa in ya yi dubu to ya ɓaci, amma tun da maslaha yake nema dole ya cinye fushin nasa
"Ta sani mana"
"Ka faɗa mata kenan?"
Ya jijjiga kai
"To yanzu kai kana tunanin za ta ƙi wanda ya riga ya furta mata cewa yana son ta ne saboda kai don kawai ta san kana son ta?
"Wannan ai ba magana ba ce, in ma kana ganin ka fi karfin faɗa mata ai sai ka yi wa Ammiey magana, ita kam za ta san yadda za ta yi ta ga komai ya tafi daidai. Amma ka duba fa, shi wancan kai tsaye ai iyaye ya saka a zancen, kai ka fi karfi kenan?" Shiru yayi cikin ransa kuma yana tabbatar da cewa hakan ne.

A gajarce yace "To yanzu dai mene ne maslaha?"
"Maslaha ɗaya ce dude, kawai ka tunkari yarinyar first, sai kuma ka yi wa Ammiey magana."
Babu yadda zai yi tabbas hakan ne kaɗai zai iya ƙwato masa Hamra daga wancan guntun mutumin kamar yadda yake faɗa.
Daga nan ya furta "Thanks bro" sannan ya mike ya fita.

Kamar a ba zata sai ga kiransa, mamaki ne fal a ran Hamra har sai da fuskarta ta nuna.
Ɗagawa tayi ta kara a kunnenta tare da yin sallama. Kamar ba shi ba haka su ka ɗan taɓa zance, abun mamaki yau dai Ya Mubeen ya tona asirin zuciyarsa duk da cewa dai ba a Nutse yayi ba, wannan ɗin shi ne karo na farko a rayuwarsa sai yake jinsa saƙayau kamar ya sauƙe wani nauyi. A bangaren Hamra za ta iya kiran ranar yau da rana mafi soyuwa gare ta, ta kuma saka ta cikin jerin ranakun da suka zama na tunawa gareta. Ba iya a ranta take jin farin cikin ba, ranar kowa sai da ya fahimci hakan.

Ya mubeen kam fita yayi tsabar yadda yake jin sa, kai tsaye ya nufi wani orphanage mafi kusa da su, sosai ya faranta ran jama'ar wurin tare da ba su kyaututtuka, hakan ya matuƙar sanya yaran kuwa cikin nishaɗi. Bayan ya koma cikin Sa'a ya ci karo da Ammiy ita kaɗai a parlour don Ummie tana ciki kamar bacci take. Sosai yaji dadin hakan don kuwa dai dama ce da zai yi abun da ya dace.

Lallai kuwa so babu ruwansa da girma ko matsayi, babu kunya Ya Mubeen ya yi wa Ammiey maganar, da ta tambaye shi ko Hamra ta sani? Kai tsaye yace mata e, abun kuwa sosai itama ya faranta mata, nan tace masa za ta yi wa Alhaji Isma'il magana kan al'amarin. Daga haka ya tashi yana wani sosa kai, ita kuwa da murmushi ta raka shi.

Washe gari da misalin tara na safe Ammiey na shirin kiran Daddy kawai sai ga kiransa, gabanta ne ya mugun fadi da ganin kiran, faranta dai Allah yasa ba abun da take gudun faruwarsa ba ne zai faru, karfafawa kanta guiwa tayi ta daga, bayan sun gaisa take ce masa dama itama yau take son kiransa. Yace "Ma sha Allah, faduwa ta zo daidai da zama ke nan. Ko dai a kan yarinyar ki ne?"
Gaban Ammieys sai da ya amma ta dake tace "E"
" Ma sha Allah, dama dai ina son magana da ke ne kan yarinyar nan, Humaira wacce suka zo tare da Hamra"
Wata mahaukaciyar ajiyar zuciya Ammiey ta sauƙe jin dalilin kiran.
Da sauri ta murmusa tace "Ma sha Allah "
Daddy yace "Dama ina son sanin wace ce ita da kuma inda zan samu iyayenta, yaron wajena nan, Ja'afar."
"E na gane shi"
"Yauwa to dama ya nuna soyayyarsa ne gare ta, to matsalar ba mu san ina za a samu manyanta ba tun da ba saninta muka yi ba sai ta dalilin ku."


Sassanyar murmushi Ammiey ta saki tare da faɗin
"Ma sha Allah, na matuƙar yin farin ciki da hakan, Allah ya sa albarka, ita kuma dai yarinya Humaira mahaifinta ne aminin Mahaifin Mubeen, sannan Ni da mahaifiyarta ma aminai ne, dangin mahaifinta a nan Gombe suke, zan yi magana da ita mamar tata sai a tura maka cikakken details ɗin, Allah dai ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin" Daddy ya amsa yana murmushi.
"Rayhana"
Ammiey ta amsa da sauri
"Kila ce za ki kira Ni?"
"Eh"
"To ina sauraron ki"
"Kusan batun ɗaya ne, shi ma yaron wajena Mubeen ne, ya nuna nasa interest ɗin kan ɗiyarku Hamra, to kar kuma wani yazo a. Bashi tun da duk ku hala ba ku sani ba, shi ne yace na muku magana kafin ya tura magabatansa shima."
"Ma sha Allah ma sha Allah, abu ya yi kyau, fatanmu Allah ya sa albarka, ya kuma nuna mana, ma sha Allah, kar ki manta a tura adreshin don Allah."
"In sha Allah " daga haka suka katse kiran.

Sosai Ammiey ta yi farin ciki da wannan al'amari, Allah dai ya yi da rabon ɗanta, ɗaya barin kuma na ranta na farin ciki ma abokiyar da ta ɗau matsayin ƴar uwarta bisa samun suruki na ƙwarai, don kuwa dai ita kanta shaida ce kan Ja'afar, ko da kuwa Allah ya yi aurensa da Hamra ba za ta yi baƙin ciki ba wai don ɗan ta ma na so.
Ko da ta tuntubi Ummie da maganar sosai ta nuna farin cikinta game da al'amarin tana sanya Alkhairi, ba ta samu sanar da Ya Mubeen ba sai washe gari. Ai kuwa ya nuna farin cikinsa da yaji labarin har sai da ya guntsawa Ya Hamid wanda shi ma ya taya shi murna.

Sati guda kenan da maganar Ya Mubeen da Hamra, Humaira da Ya Ja'afar, Humaira ta kai wa Ammiey gulmar soyayyar da ke tsakanin Ya Hamid da kuma Ra'isa, wanda sai lokacin Ummie ma tunaninta ya ka ga hakan, ta kuwa yi farin ciki sosai, ta kuma kasa ɓoyewa sai da ta sanar da Ammiey wacce itama ranta yayi mata daɗi da haɗin nan..sosai ta yi wa Ubangiji godiya bisa wannan kyakkyawan hadi tare da rokon Ubangiji ya tabbatar musu da Alkhairinsa.

Ranar Alhamis kuwa abun mamaki su Daddy suka je gidan kakannin su Humaira da ke Gombe, sosai aka tarbe su tun ba a san su waye ba, ko da suka sanar da abun da ke tafe da su ne ma suka ga mutuntawa, sosai suka yi farin ciki da hakan suka kuma bayar da izinin daidaitawa da yarinyar, sannan sun buƙaci a ba su lokaci su yi bincike kamar yadda addini ya ce, ba kuma wai don kawai sun ga wani naƙasu ba ne game da su Daddyn ba hasali ma ganin manyan mutane suka yi musu.

Bayan su Daddy sun dawo ya sanar da Ya Ja'afar yadda ta kasance, sosai ya yi farin ciki ya kuma yi wa Daddyn nasa godiya.
A ɓangaren Ya Hamid ma Ummie da kanta ta masa magana akan Ra'isa, ya kuma tabbatar mata da cewa zai je can Gombe don maganar ba ta waya ba ce, sosai ta sa masa albarka sannan ya tafi.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya, har aka ɗau tsawon watanni biyu, a ɓangaren masoyan nan sai dai mu ce ma sha Allah, haka ta kasance kuma a ɓangaren Hamra wacce ake jiran makarantar Adamu Adamu College of Nursing and midwifery su fara sayar da Form a nema mata, da yake Daddy yana da alaƙa da ƴan siyasa don kuwa Sa'adatu ma shi ya sa aka samar mata gurbi a can.
Ɓangaren soyayyarta ma da Ya Mubeen sai dai mu ce ma sha Allah, jin Ya Mubeen ɗin ya yi shiru yasa Ammiey ta masa magana kan ya tuntuɓi Uncle ɗinsa, in kuma ya tsaya wani zai iya shan gabansa ya aure Hamran da yake taƙama ƴar'uwarsa ce. Ai kuwa Kamar Ammiey ta tunzura shi cikin satin shi da Ya Hamid suka tafi Gombe, da yake dama can Mahaifinsa Alhaji Mohammed Yusuf ɗin ɗan can Gomben ne, kuma sun yi zaman Gomben suma kafin su koma Abuja, zuwa Lagos.

Sosai Uncle ɗinsa wanda shi ne babba gidan su Abinsa ya tarbe su, don ba kaɗan ba yake son ƴaƴan autan nasu ba, Alhaji Usman Kumo ya nuna farin cikinsa kan ƙudirin Ya Mubeen ɗin ya kuma ɗaukar masa alƙawarin cewa za su je tare da sauran ƴan'uwansa ko biyu ne a nema masa auren Hamra ɗin ya ƙare da faɗin
"Abun ma ai ya zo gidan sauƙi tun da ka ce na. Jigawa ne."
Kai sunkuye suka yi wa Tsohon godiya tare da masa sallamar in sun dawo a nan ɗin za su kwana.
A can ma familynsu ya Hamid ma dai abun ya musu daɗi. Har kakansa na tsokanarsa.
"Ta kwana gidan sauƙi ai Hamidu, nan gidan Alhaji Usman Kumo ai ba wani rata, ga shi ma kamar ɗa yake a wurina, kai amma dai ma sha Allah Allah ya sa albarka."
Cike da kunya suka amsa da "Amin."


Daren ranar kuwa a gidan Alhaji Usman Kumo suka kwana wanda sosai aka tarbe su da abincin dare, babu yadda za su yi sai da suka taɓa duk da cewa sun ci a can gidan B Babba (Da yake haka ake kiran kakansu Hamid ɗin."
Kwana biyu suka ƙara sannan suka musu Alkhairi suka wuce. Ranar da suka koma da labarin both Ammiey da Ummie rasa game wa yafi farin ciki aka yi nan dai suka ɗaura da addu'ar Allah ya sa a dace.
Washe gari kuwa B. Babba ya sa ƴaƴansa uku suka je har gidan Alhaji Usman Kumo, sun kuwa dawo masa da sakamako mai daɗi hakan yasa yace su sanar da maneman Humaira an ba wa yaron saura kuma a saka ranar aure, babu ɓata lokaci kuwa suka isar da sakon ga Ummie, shima Alhaji Usman bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da Ammiey cewa sun bayar da Ra'isa ga Hamid, saura kawai saka biki. Kai kar ku so ku ga murna a gidan nan ranar, don kuwa ko dinner ranar ba su yi a gida ba.

A cikin satin ne kuma, Alhaji Usman Kumo tare da ƙannensa biyu, Alhaji Sadis, Musa Kumo suka je har Jigawa suka tambayo aure wa ɗan su, ai kuwa su Daddy suka ba da auren ma kai tsaye tun da dama can an san da batun kuma dai an tabbatar ma yaran na son junansu. Hakan ta yi wa ahalin Alhaji Kumo dadi ganin yadda aka mutunta su. Suka dawo tare da isar da saƙo ga Ammiey, ai fa farin ciki dai ya gagara yankewa a gidan, Ya Mubeen da ya ji wannan zance haka yayi ta kyauta duk da cewa dama can shi mutum ne mai yawn kyautar.
Bayan wasu kwanaki kuma su Ummie suka koma can Abuja tun da dama hutu ne ya kawo su, shi kuma Ya Hamid ya zauna saboda zai ci gaba da aiki ne da EL-MUBEEN LUXURIES.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya, cikin farin ciki da kuma akasin haka. A lokacin da su B. Babba suka fahimci abun ƴar gida ce, sai suka haɗu suka yanke rana ɗaya ta auren, amma kuma a nan Gombe za a yi, ban da na Hamra da za a yi a Jigawa.

Alhamdulillah kawai za a ce, don kuwa ta ko'ina shiri ake babu kuma hannun yaro. Nan gidansu Hamra ma sosai ake shiri da yake za a haɗa ne da bikin Ramlah da Sa'adatu wanda ita Sa'adatu za ta auri ɗan gidan Hon. Alhaji. Audu (boss) kuma Azare za a kawo ta. Ita kuma Ramlah a nan Jigawa za ta zauna.

Ana saura wata biyu bikin, Sanarwar sayar da Form ɗin AACNS ya riski Daddy. Bai kuwa yi ƙasa a guiwa ba ya siyo Form ɗin aka cika mata, aka yi submitting, bayan an mayar kuma ya ƙira Ya Mubeen ya sanar da shi, duk da cewa bai so hakan ba amma babu yadda zai yi, haka ya haƙura, don ma dai shekara uku ne karatun ba wani yawa. Cikin satin aka saki admission list, kuma alhamdulillah Hamra ta samu, za ta karanci course ɗin Midwifery. Sosai ta yi farin ciki ganin itama ashe dai da rabon za ta yi karatun boko duk kuwa irin yadda Baffa da Inna suka ga hakan bai faru ba. Lallai kuwa Allah na yin abun da ya so ne.
Bayan an mata registration dole a hostel za ta zauna, hakan yasa aka mata shopping na komai ta wuce. Abun sam bai wa Ra'isa dad'i ba har sai da ta yi wa Ammiey magana, Ammiey ta rufe ta da faɗa wai tana yi wa ƴarta hassada, ita lokacin da ta yi nata wa ya ji? Fuska ɗaure ta bar ɗakin Ammiey tana faɗin "Daɗinta ma dai duk jimawarta a nan za mu zauna." amma

Su Hamra uwar gayya haka aka wuce AACNS sannan aka fara karatu, sosai lamarin makarantar ya sa ta gaba don kuwa da farko dai ba gane komai take yi ba, amma a hankali da ta nace sai komai ya fara tafiyar mata. Sosai karatun ya saka ta gaba don har wata rama ta yi, su ne in suka fita sassafe sai 3:30, tana dawowa take wanka tayi girki, daga nan kuma ta wuce area class karatu, sauƙinta ma wata rana Sa'adatu na yin girki ta aiko mata.

Watansu biyu da fara karatu, komai kuma a yanzu yana tafiya wa Hamra daidai sai ma sha Allah. A ɓangaren Mammahn Sa'adatu kuma so take a fara musu gyaran jiki, ko da ta yi wa Ammiey maganar sai Ammieyn tace ta yi yadda ya kamata. Nan kuwa ta sanar da ita batun ƙanwarta da ke Azare, kuma Gwana ce sosai a fannin nan, hatta ƙannensu mu ita take yi musu don ba kowa ma take yi wa ba. Don haka su koma gidanta da zama, idan ya so kullum sai su ke zuwa lectures, sosai Ammiey ta yi na'am da shawarar Mammahn sannan ta mata godiya.

Cikin satin kuwa suka tura request a student affairs office na tafiya, ai kuwa babu musu aka amince, nan suka haɗa akwatunansu suka wuce gidan Aunty Murjanatu da ke unguwar Makara huta, daga ranar kuma aka fara musu gyaran jiki, duk da haka Hamra ba ta wasa da karatunta tun da jarrabawar weeding ne gabanta, ita dai Sa'adatu ta riga ta tsallake, kuma su da exams ma da sauran watanni kusan biyar.

*React and share fisabilillah.*


[9/16, 10:45 AM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*


https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login