Showing 27001 words to 30000 words out of 134378 words
aje ta. Concrete warning Ummie ta ba wa ƴan sandan that kada a ba da belinta har sai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam sun shiga zancen. Daga nan suka koma aka ci gaba da kula da Hamra.
A can gidan Inna Rahama sai Sowa take tana ihun ta shiga uku. Cikin ikon Allah wuraren Azahar sai ga Baffa ya shigo, turus yayi ganin Rahama kwance a ƙasa tana sauƙe ajiyar zuciya, da sauri ya ƙarasa wurinta yana jijjiga ta. "Shalele lafiya?" Cikin muryarta da ta dashe saboda kukan da tayi tace "Sun tafi da Inna." A matukar tsorace yace "Sun tafi da Inna, su waye?"
"Ƴan sanda" ta ba shi amsa. Kamar bai ji ba ya maimaita "ƴan me kika ce?", cikin muryarta da ba ta fita tace "Ƴan sanda Baffa, sun tafi da Inna..." Bai jira ya ji me za ta ce ba ya fice da sauri ya haye babur ɗinsa ya ja sai police station. ko da yaje ya sanar da su wadda yazo domin ta, babu ɓata lokaci ƴan sandan suka yi arresting ɗinsa, direct shima aka wuce cell da shi aka fara cin ubansa.
Su Ummie ba su zo ba sai washegari, lokacin da aka fito da both Inna da Baffa idanu sun raina fata. Da aka tambaye su ko sun san laifin da suka aikata suka ce a'a, Inna dai da sauri tace "Ni na sani" police ɗin da yayi tambayar ya nurtuƙe fuska kamar a filin daga yace "Ina jinki, faɗi laifin mijinki ya ji, ya ce shi bai sani ba kuma kin ce shi ya saka ku." Hawayen wahala na silalowa daga idanun Inna tace "Wallahi shi ya saka Ni, da Ni da Rahama da shi muka buge ta." Murmushin mugunta police ɗin yayi yace "Ka ji dai me tace, me za ka ce a kai?"
Baffa yace "Wallahi Officer sharrin shaiɗan ne da ƙaddara, amma ba za a sake bam"
"Shut up!" Police ya daka masa tsawa, ba iya Baffa ba hatta Inna jikinta ɓari ya ɗauka.
"Ai ba nan za ka zauna kana ba da haƙuri ba, za ka ce this is your first time, shatin dukan da ya fara gogewa a jikinta fa? Duk jiyan ne aka yi?"
Cikin alamun rashin gaskiya baffa yace "Wallahi Hajara ce, ba Ni ba, ka tambaye ta Ni ba...."
"Yi min shiru nace!"
"Ni yanzu babu abinda zan ce gaskiya. Abun da na sani ɗaya shine ƙungiyar kare haƙƙik dan Adam da kuma yara za su shigo zancen, dam zan miƙa ku hannunsu kwa musu bayani."
Kuka Inna ta fashe da shi tana faɗin "Don Allah ka mana rai officer, ka taimake mu ku yi haƙuri ba za ta ƙara faruwa ba, ka ga, wallahi Ni ko Hamra'u zan iya ba wa hakuri, Nikam na tuba na bi Allah, dama can ga shaiɗanin da yake zuga Ni, amma can asali Ni mai ƙaunar Hamra'u ce.."
"Wallahi officer sharri take min, Ni ba na zama a gidan ma, ku yi wa Ubangiji ku yi haƙuri ba za a ƙara ba."
"Tyson, Aliyu! Ku mayar da su cell."
"Ok sir!" Suka sarawa ogan nasu sannan suka ja su Inna suka yi cell da su sai ihu suke. (Ƴan banza sun ji jiki.)
Dpo kan su Ummie ya dawo yana faɗin
"Allah dai ya kyauta, amma Ni na yi tunanin yadda zamani ya waye ba a samun irin miyagun mutanen nan da ba su tausayin yaro, kawai in ɗa ba naka ba ne Shikenan sai izaya da bauta?"
Numfashi Ummie ta sauke tace "Wallahi Ni kaina abun ya ɗaure min kai, a ce mutane kamar babu zukata a ƙirjinansu? Anya wasu za su wanye da duniya lafiya kuwa?. Hmm"
"Gaskiya wasu kam ba a magana, amma dai ko ma yaya ne in sha Allah za su san sun yi child abuse, daga kansu za a buga misalin da duk duniya babu wanda zai ƙara ƙoƙarin kwatanta makamancin Abunda suka yi."
Ummie ta dubi Dpo tace "Amma na ga nadama a idanunsu, za mu ba su dama ta biyu, for now a ci ubansu kada a sallame su sai zuwa maghrib, yarinyar kuma in ta ji sauƙi za a mayar ta muga yadda al'amarin zai kasance."
"Shikenan Hajjaju, as you said." Murmushi Ummie tayi daga nan ta fito suka wuce gida.
Wuraren magriba aka saki su Inna, a tare suka dawo, ko da suka koma gida Rahama ta tare su da gudu bayan ta ake Khadi da ta hana ta rintsawa, suna haɗa idanuwa ta kwashe da dariya ganin yadda goshin Inna yayi molo ga kuma laɓɓan Baffa kamar an jawo su gaba. Galala suka yi suna kallonta tsabar mamaki da ya cika su. Sai da tayi mai isarta tace "B**a uba, gaskiya ƴan sandan nan ba ƙaramin lafta suka muku bi, dubi bakin baffa kamar tiyo ɗin Bohol!" Sai kuma ta ƙara kecewa da dariya. Hannun da Inna ta kawo mata yasa ta goce da sauri tare da nuna Innar da yatsa tana faɗin "kan bala'i, Inna wallahi kin yi kyau da kika yi dogon goshi. Amma dai Gara ke wallahi akan Baffa."
Sumi-sumi kamar munafukai suka keta gefen Rahama wacce ke musu shega suka wuce ciki, Inna kam ko ta kan autarta Khadi ba ta bi ba Gara Baffa ya kalleta kafin ya shiga, can sai ga Inna ta fito ɗaure da zani a ƙirji sai cogala ƙafa take har abun dariya. Ita kuwa Rahama ina ruwanta, kwasar dariyarta kawai take ba ƙaƙƙautawa.
Wuta taje ta hura sannan ta ɗaura ruwan ɗumi ba su suka sauƙe ba sai da ruwan ya gama tafasa ta kwashe ta kai bayi, ita ta fara gasa jikinta sai Baffa shima ya hasa nasa. Bayan Isha' suka zauna suna ƙara jajanta Abunda ya faru da su. Inna ta dubi Baffa tace "Malam a gaskiya Ni yanzu fa na gaji da wannan zaman talaucin, kana da shi ba baka da shi bare kace babu ne ya saka, zuwa yanzu ya kamata kawai mu fantama son ranmu, ga dukiya har dukiya amma tsoron mutane yasa ka bar mu a wannan hali, zance na gaskiya Malam Nikam na gaji, ka samu wani wayayye haka, kamfanonin nan du a sake buɗe su sai a sauya musu suna, Nifa in so samu ne a yau ma mu bar wannan jarababben gidan."
Baffa ya ɗago ya dubi Inna yana jujjuya maganarta, gaskiya ta faɗa masa amma sai dai me, da buƙatar wanda ya san kan harƙar kafin su dira kanta. Gyara kwanciyarsa yayi akan katifa sannan yace "Ban ƙi ta taki ba Hajara, a yanzu kam ina daidai da gwabzawa da uban kowa ma, yanzu Fisabilillahi ki dubi yadda aka ƙwamushe mu a caji ofis akan ɗan ƙanƙanin abu wanda in ba shisshigi ba me me za a kira shi?"
"Hmm, Malam kenan!" Inna ta faɗa tana riƙe haɓarta tunawa da wahalar da ta sha a police station.
*Kuma fa Ni yadda na lura ma wallahi don an gan mu a cikin wannan gidan ne, amma zan yi maganinsu gabaɗaya, sai na nuna musu cewa Ni Sulw ba kanwar lasa ba ne, musamman ita shegiyar da ta janyo mana wulaƙancin."
Yana rufe baki Inna tace "Gane min hanya, ai shiyasa nazo maka da wannan shawara, muma mu zama cas abunmu, mu yi yadda muke so kamar yadda kowa ke shanawa. Ka san wani abu Malam?"
Baffa yace : "A'a sai kin faɗa."
"Malam ba ka ganin cewa mutanen nan za su iya cewa mu bar musu yarinyar nan kuwa?"
Tambayar da Inna ta jefowa Baffa yasa ya miƙe zaune daga kwanciyar da yayi.
"Me kika ce Hajara?"
Inna ta maimaita Abunda ta faɗa tana bin Baffa da kallo
Kansa ya jinjina sannan yace "Kin gano take-takensu ko? To wallahi Hajara ban ga wani mahaluki dazai sa na ba da Hamra a hannunsa ba saboda fitarta a hannunmu zuwa wani kyakkyawan hannu ba ƙaramar barazana ba ce gare mu, kin ga ko sun zo da maganar nan ba zan amince ba!" Ya ƙarasa cikin kaushin murya da ke ƙara tabbatar da Abunda ya faɗa ɗin.
"Gaskiya ne malam, a bayanin da dipi'o yayi Mana yace za ta dawo ai, Ni a gani na kawai yanzu ka sa a fara gyara mana ɗaya daga cikin gidajen da suke hannunka, a mana sabon gyara tunda an jima ba a zama ciki, da zarar ta dawo sai mu ƙaura abunmu ta yadda babu wanda zai ƙara jin ko da labarinta ne. Kuma ka ga yarinyar nan Rahama." Inna ta dakata kaɗan ta waiwaya don tabbatarwa ba ta kusa sannan taci gaba.
"Ya kamata ace itama yanzu ta samu wayewa irin ta ƴaƴan wane da wane, sutura, ƴar waya ƴar shafen nan, ta samu jin daɗi ta yadda itama za ta zama kadara mai tsada."
"Haka ne Hajara, yanzu dai mu jira su maido da wannan mai zubin aljanun."
"Yauwa Malam, mun kusa dai muma mu fara kutsawa cikin manyan mutane" ta faɗa tare da murmusawa shima Baffa ya saki dariya abunsa.
A ɓangaren Hamra kulawar da take samu rabon da ta samu kwatankwacinta tun iyayenta na rayuwa, wannan dalilin ne yasa taji sanyi a rayuwarta yayin da kewa da raɗaɗin rashin iyayenta ya ragu kasantuwar ta hadu da masu son maye mata wannan gurbi. Sabo ne mai ƙarfi ya shiga tsakaninsu musamman da Ummie, jin Ummie take sosai cikin jikinta, haka itama Ummien tana matuƙar jin Hamra a jikinta kamar yadda take jin Humairah da Yaya Hamid. Alaƙarta da Humairah kuwa sai son Barka, kowa yana so da kuma ƙaunar ɗan'uwansa. Yaya Hamid, wanda a yanzu ya kasance tamkar bango a gare ta yana kulawa da ita fiye ma da yadda yake kulawa da tasa ƴar'uwar, tarairaya kuwa kamar wata ƙwai haka yake mata, ba ya son damuwarta ko ɓacin ranta, da zarar ya shigo gidan yana ganinta shiru zai fara tambayar "lafiya? Me ya sameki? Wani abu ya ɓata ranki ne? Ko kin tuna rayuwarki ta baya? Please ki manta da wannan rayuwar, Ni ba zan bari ki koma cikinta ba, zan inganta Miki rayuwarki sweet sister, yauwa sweet sister, oh yah! Smile, lemme see" kalamansa ko yaushe gare ta cike suke da kulawa har wani lokacin takan ji kamar ba ta kai matsayin da za a kula da ita haka ba.
Matsawar Yaya Hamid na gida, ba zai taɓa barinta ita ɗaya ba, shiyasa kowanne sakan da daƙika da za su wuce tunaninsa ba ya barin ranta.
Kwananta huɗu a tare da su amma shaƙuwar da suka yi ta wuci tunanin mai karatu, ta riga ta zama su, suma kuma sun zama ita. Kamar koyaushe tunda ta dawo gidan kullum sai sun je hospital an duba raunukan jikinta, duk da sun warke yau ma haka sai da Yaya Hamid ya ɗauketa ya Kaita. A hanyarsu ta dawowa ya dube ta cike da kulawa yace
"Sweet sister, ko za mu biya na siya Miki waya kema?"
Kamar ba ta ji ba tayi shiru saboda ba ta so ta ƙara ɗaura musu Abunda bai zama musu dole ba duba da yadda suke ɗawainiya da ita kamar su ne ahalinta.
"Sister ba Kya so ne?" Jin ya ƙara maimaitawa ya tabbatar mata da cewa he's serious, murmushi tayi tace "Ina so mana Yayana."
Ba tare da ya kalleta ba yace "is alright, mu biya ta Shatu plaza sai mu saya ko?" Kai ta gyaɗa masa daga nan shima bai kuma cewa komai ba har suka isa, cikin jerin shagunan da ke plaza ɗin suka tsaya a no. 8, Apple store. iPhone 16 pro max ya saya, a lokacin yasa aka saka mata guard da kuma cover sannan suka fito bayan sun yi confirming payment ɗin da ya musu.
Kai tsaye mota suka wuce, bayan ya tayar da motar ya dube ta yace "Sister" juyowa tayi with smile on her face ta amsa da "Yayana" shima smile ɗin ne yayi escaping kan fuskarsa sannan ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake yace "Wanne school kike zuwa yanzu?"
"School?" Ta maimaita in an interrugatng way
Kai ya gyaɗa mata still hankalinsa na ga titi yace "Yes! I mean makaranta." Ya faɗa don a tunaninsa tambayar da yayi da turanci ko ba ta fahimta ba ne.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sassanyar muryarta tace
"Tun ranar da Mom da Dad suka mutu..." Sai kuma ta fashe da kuka tunawa da ranar da ta kasance mata rana mafi muni a rayuwarta, ranar da ta zama silar shigar ta ƙangin rayuwa.
A ɗan rikice ya gangara gefen hanya ya tsayar da motar sannan ya mayar da hankalinsa kwacakom gare ta. Bai yi yunƙurin dakatar da ita ba saboda in yayi hakan kamar babu amfani Gara ya barta ta cire damuwar da take ji, ai shi kuka maslaha ne, wasu ta hanyar kuka suke cire damuwar wasu abubuwan a ransu, da zarar sun yi kukan kuma Shikenan. Mintuna biyar tayi tana kukan tukun ta fara goge fuskarta tana sauƙe ajiyar zuciya.
Daga cikin aljihunsa ya zaro purple handkerchief nasa da ke ƙamshin turarensa mai daɗin gaske. Miƙa mata yayi ba tare da yace komai ba, hannunta tasa ta amsa tare da kai shi kan kyakkyawar fuskarta ta fara goge hawayen a hankali lokaci guda kuma tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Ganin ta gama ta miƙo masa yasa ya amsa ya zaro bottle water ya buɗe sannan ya miƙa mata, cike da kulawa yace "ki sha ruwa." Kamar ya san tana da buƙatar hakan ai kuwa tana karɓa ta kafa kanta ta fara shan ruwan, sai da taji ya ishe ta tukun ta miƙa masa bottle ɗin tana faɗin "Thank you".
Murfin bottle ɗin ya mayar ya rufe sannan ya juyo ya dubeta yace "Oh yea! Now take a deep breath! Ki shaƙi iska" kamar yadda ya faɗa taja numfashi yace "Now blow out, ki fesar da iskar"
"Good girl, ki daina kuka in kin tuna su Mom, Addu'a za ki ke musu kinji?" Kai ta gyaɗa masa ya ci gaba da faɗin "Ba su buƙatar kukanki, addu'ar ki ita kawai suke buƙata, ko kina so ki ƙara musu nauyin azaba ne?"
"A'a" ta ba shi amsa tana jijjiga kai
"Good, to in ba ki so ki daina yi musu kuka ok?"
Kai ta ƙara gyaɗa masa. Daga haka ya juya yana gyara zamansa don su ci gaba da tafiya. Sai dai suka hau titi tukun yace "Aji nawa kika tsaya?"
"Jss 3" ta ba shi amsa kai tsaye.
Bai ce komai ba sai kansa da ya gyaɗa saboda hankalinsa gabaɗaya na kan hanya.
Suna isa gida suka yada zango a Parlour, Hamra ta zube gefen Ummie tace "Mun dawo Ummie"
Cike da kulawa Ummie tace "Ma sha Allahu, me Dr ɗin yace?" Bakinta ta ɗan tura sannan tace "Ki ji wai Ummie, ciwon fa duk ya warke amma wai sai mun koma gobe tukun ya sallamemu." Jawota jikinta Ummie tayi tana faɗin "In banda abunki Hamra miye yau miye gobe in da rayuwa? Allah ya kai mu goben."
"Amin Ummie " ta ba ta amsa tana lafewa jikin Ummien.
"Ko shi yasa kika yi kuka don Dr ya ce za ku koma gobe?" Wuri wuri tayi da ido tace "Ban fa yi kuka ba Ummie, kin san meye?"
"A'a sai kin faɗa"
Kallon Yaya Hamid Hamra tayi sai kuma tayi shiru tana zare ido. Ummie wacce idonta ke kan Hamran cikin ranta tace "How I wish, wata alaƙar da tafi wannan ta ƙullu a tsakaninsu" a zahiri kuma tace "Kun je wani waje ko?"
"Kai Ummie, ba fa ko ina na kai ta ba, mun je na sayo mata waya ne."
"Oh ai ka kyauta kuwa, muna godiya."
Ƙoƙarin sauya akalar zancen nasu yayi da faɗin "Ummie, next week za a kai ta school." Kamar ya san me yake cikin ran Ummien, saboda haka daɗi ya kama Ummie har ta gagara ɓoye hakan a kan fuskarta ta dube shi tace "Allah ya yi maka albarka Abdul."
"Amin Ummie na..."
"Ummie..." Humaira ce ta katse masa maganar da yake son faɗa, hararata yayi tuni ta dawo kan hanya "Wai ke Kam me yasa ba za ki girma ba? Must you shout everytime before ki ji daɗin rayuwarki?"
Jin ya hau ta da faɗa yasa ta fashe da kuka shagwaɓa ta faɗa kan Ummie. Haɗe fuska Ummie tayi tace "Ke kuma miye hakan? Za ki ɗaga Ni ko kuwa?"
Ƙwafa yayi yana jin daɗin yadda Ummie ta tsarewa Humairahn.
"Kai Ummie...ku min laifi kuma ku hana Ni kuka?" Humaira ta faɗa tana tura baki
"Uban me aka miki?" Ya tambaya yana jifanta da harara.
Bakinta ta turo gaba tace "To ba tafiya hospital kuka yi kuka bar Ni ba?"
Kansa ya dafe tare da sauƙe muryarsa yace "Is ok, ki yi shiru, gobe ai za mu koma tare ai."
Hamra ce ta bar jikin Ummie ta dawo gefen Humaira ta zauna tana ban baki tukun tace ta haƙura.
Wayar ya miƙawa Humairah yace "Make sure kin saita mata komai kin ji?"
"Ta waye? Ta Hamra? Wow!"
"Dalla Ni ba tambaya nace ki cika Ni da ita ba
"Kai Yaya Hamid, Ni yanzu duk ka daina so na, daga tambaya sai ka hau Ni da faɗa?"
Numfashi ya sauƙe tare da faɗin "Is ok, Shikenan yi haƙuri autar Ummie, na daina."
Miƙewa tayi tsaye tana kallon Hamra baki washe tace "Ma sha Allahu, sister ta faso latest iPhone, Yaya Mun gode,bari na saka caji zuwa jimawa mu saita komai." Daga haka ba ta jira amsar kowa ba ta ruga da sauri ta koma bedroom.
Bayan wayar ta yi caji a tare suka saita komai, ita dai Hamra nata ido ne saboda babu abinda ta iya a ciki, a haka Humaira sai nuna mata abubuwa take tana mata ƙarin bayani, nan dai ta fara fahimtar abubuwa kan wayar.
*Da daddare*
Tunda suka yi dinner Yaya Hamid ya wuce part ɗinsa, wanka yayi ya sauya zuwa silky night wears ɗinsa, ko bottle Bai ɓalle ba ya haye kan gadonsa yana sauƙe numfashi. Hannunsa ya miƙa ya kashe hasken ɗakin zuwa dim light sannan ya janyo wayarsa. Daddanawa yayi na tsawon wani lokaci har ya rasa abinda zai yi, tsayawa yayi yana fafatawa da zuciyarsa can dai ya samar da matsaya........
*There'll be update tonight, wannan wanda ya goge ne.*
*Share and react Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._