Showing 90001 words to 93000 words out of 134378 words
ko dai ka mayar da Ni daular can ko kuma ka mayar da Ni gidanmu. Ni ba kai na aura ba wallahi mugu Kawai , ka mayar da Ni gidana."
Dariya sosai ta ba wa Hamidu, sai da ya dara son ransa tukun ya gimtse fuska kamar ba shi yayi ba
"Lallai yarinya, ba ki ga komai ba ma, ba dai son duniya da zalunci sun rufe muku ido ba? To wannan shi ake ƙira da ƙarshen azzalumi." Yana kai aya ya ƙetare ta ya wuce tare da hayewa kan katifa. A matuƙar fusace ta ƙarasa kansa tare da riƙe ƙugu tana jijjiga, shi wallahi abun ma dariya yake ba shi yanda ta wani haƙiƙance.
"Na rantse da Allah ba ka isa ba, ka dame Ni ma, uban waye na zalunta da za ka ɗaukar masa fansa, wallahi in kayi wasa sai na ɗaure ka, bari na koma gidan miji na ka gani."
"Wai miji kika ce?" Ta zauna bakin katifar tana kallonsa
"E haka na faɗa, mugu kawai."
Sai dayayu dariya son ransa tukun yace "Lallai na tabbatar toshasshiyar ƙwaƙwalwa gare ki. To ai ba ki da mijin da ya wuce Ni Rahama. Ni ne nan mijinki, ke ɗin matata ce, kwaɗayi da son duniya ya kawo ki, Ni kuwa a ɓagas na samu mata."
"Me kake nufi?" Ta tambaya fuskarta na bayyana tsantsar mamaki. Cikin halin ko in kula yace "Abun da kika ji na ce, ja'ira kawai, daga ke har iyayenki kun yi kuskure, kuma ki sani ke da ƙara ganinsu hala sai a ƙiyama kamar yadda kuka raba masoya biyu."
Wasu siraran hawaye ne suka zubo mata lokaci guda don a yanzu ta fara fahimtar komai shi kuwa cikin ransa yace "ko hawayenki Zai ƙare sai na ramawa waɗanda aka zalunta." A zahiri kuma yace "Ki daina ma zubar da wannan hawayen kadar ki zauna a gidanki. Yauwa."
Kamar za ta duka shi tace "An ƙi ɗin, wallahi ba zan zauna a gidan nan ba."
"To Shi ke nan ki tafi gidan uban da za ki je, shege ka fasa, wallahi duk ranar da kika yi mafarkin kin bar gidan nan to mutuwa nayi, Gara ma ki ranƙwashi azzalumin kanki ki zauna. Ba dai ke ƴar mai son duniya ba? Ke ce mai son auren mai kuɗi ba? Hmm"
"Don Allah ba don halina ba ka mayar da Ni gidanmu. Wallahi na yafe auren Nikam."
"Babu inda za ki je"
"To wane laifi na maka don Allah? Ban san ka ba don Allah kada ka cutar da Ni."
Dariyar mugunta yayi yace
"Ai dole ki san Ni yau. Ke bari na Miki gwari-gwari, uban gidana ya sanar da Ni komai, da ke da Shegen ubanki da ke ɗaure miki gindi da kuma muguwar uwarki da ba ku da aiki sai muzgunawa marainiyar Allah. Kun raba ta da mai son ta, ba ku haƙura ba wannan karon ma kuka yi ƙoƙarin hakan sabkda don zuciya kuma kuka buƙaci ya aureki, to Shi mahaukaci ne an faɗa muku? Ya yi wasa da hankalinku ya nema min aurenki saboda na koya Miki darasi, Ni ɗin nan ba kowa ba ne face Mai gadinsa. Luma muna nan da ke har sai kin yi hankali zan sake ki. Uwar son duniya kawai, wai mayar Ni gidan mijina.." ya faɗa yana kwaikwayon yadda take masa tijara. Shiru tayi tana wurƙila idanuwa, Shikenan ita kam ta kaɗe a rayuwarta, yanzu ita yaya za ta yi? Gaskiya Hamra ta cuce ta ga shi yanzu ita tana can tana jin daɗinta. Allah ya saka mata.
A daren nan ne Rahama ta yabawa aya zaƙinta don sosai ta gurzu wurin mijin nata Hamidu, ta yi kukan har ta gaji daga ƙarshe ma Muryarta dashewa tayi kuma washe gari babu wata kulawa ya saka ta gaba ta musu abincin safe, bayan ta gama yace ta juyae duka a tray, tana juyewa ya karɓa sannan ya nuna mata wani buhu a cikin madafar yace "Ga can ƙanzo can ki daka ki kwaɗa, wannan nawa ne." Kamar za ta yi kuka haka ta yi shiru saboda babu yadda za ta yi sai yadda yace ga kuma mugun tsoronsa da ya dasa mata cikin ranta a daren jiya.
Tun daga wannan rana Hamidu ya mayar da ita kamar mai aiki, za ta yi girki ya ci, ta wanke masa kayansa, ita kuwa cimarta ƙanzo ne, sai daga baya ne ma da yaga ta fara risina yace tana ɗibarwa kanta abincin itama.
Watanni huɗu da tariyar Tata ta fara jinya kamar za ta mutu, zazzaɓi, ga amai kamar na masifa, ba ta isa ta ci komai ba, ko ruwa ta sha sai ta ji jiki. Ganin jinyar ta saka ta gab a yasa ya tausaya mata ya kai ta chemist. Bayan lissafo symptoms ɗin da take ji mai chemist ya ba ta PT-strip ya kuma mata bayanin yadda za ta yi, ya kuma faɗa ma mai gidan yadda in sun gani za su gane akwai ciki ko babu. Bayan sun koma tayi gwaji, gwaji ya tabbata cewa ciki ne da ita. A haka dai ta ci gaba da rayuwar har lokacin laulayin ya wuce ta ci gaba da rayuwa a gidan mijin nata.
Haihuwarta ta fari ɗa namiji ne, bayan suna ta buƙaci ya kai ta gidansu yace mata a'a, da ta matsa sai ya faɗa mata gaskiyar cewa ba a san takamaiman ina iyayenta suka koma da zama ba, daga ƙarshe tace don Allah ya kai ta, bayan ya tuntuɓi uban gidansa da zancen yace babu damuwa ai, shine mijinta ai. Ranar da suka je suka ga wayam tun daga ranar Rahama ta fara nadamar rayuwarta da tayi a baya, ta san ba komai ba ne, haƙƙin Hamra ne kawai ke bibiyarta. Ta yi kuka kamar ba gobe tana roƙon ubangiji ya yafe mata. Hamidu na gefenta yace "Ai Allah ba ya yafe haƙƙin wani Rahama, amma na ji daɗi da kika fahimci gaskiya, ki ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana Miki su Inna, daga nan ki nemi yafiyar Hamra da kika cutar a baya."
Hawayenta ta share tace "In Allah ya yarda, idan Hamra ba ta yafe min ba na sani ba zan yi kyakkyawan ƙrdhe ba sabkda na muzguna mata ba iyaka, sai dai duk ruɗin shaiɗan ne da kuma Inna da Baffa, gaskiya sun cutar da rayuwar Hamra fiye da Ni, sun kuma cutar da Nima ta hanyar saka min mummunar aƙida irin tasu, Allah dai ya yafe min."
Nan dai Hamidu ya yi mata ɗan wa'azi a iya saninsa sannan ya rarrashe ta, daga nan kuma sai rayuwar ta sauya, shekara na zagayowa sai ga Rahama da wani ciki. Cikin shekaru huɗu yaranta huɗu rus! Ga ɗawainiya ga kuma tsadar rayuwa da rashi, kafin me idan ka ga ga Rahama ba lallai ka gane ta ba ta zama kamar wata tsohuwa, yaran nan kuwa duk abun ƙyama saboda yanzu ba ta gyara su ma ake ba, ta abun da za a saka a bakin salati ake yi.
Wannan a taƙaice itace rayuwar da Rahama ke yi.
*Dawowa cikin labari*
Wani daga cikin magabatan ƙwarai yace, idan mutum ya saba da tashi sallar asuba to duk rintsi zai ke tashi da zarar lokacin ya yi sai dai kuma in ya tashi baccinsa ya ribace shi ya kasa yin sallar akan lokaci, tabbas wanda asuba ba ta wuce shi ya godewa Allah, don munafukai ba sa iya kiyayeta, da asuba Hamra ta tashi, kallon ɗakin da take ciki ta fara tare da mamakin ko ina ne? Me kuma take yi a ciki? A hankali ta fara tariyo abun da ya faru da ita a daren jiya, take ta runtse idanuwanta ta ƙara buɗe su kan jakarta da ke ajiye kan wani stool, a hankali ta shafa fuskarta zuwa jikinta sai kuma ta ji kamar mutum a gefenta, numfashi kawai ta sauƙe tare da fara ƙoƙarin sauƙa ƙasa, bin ko wace kusurwa tayi da kallo, bayan ta hango ƙofa kai tsaye ta nufe ta, a bayin kuwa ta tsinci kanta. Alwala tayi ta fito tana zazzare idanuwa, Prayin mata ta gani shimfiɗe can kusa da write closet ɗin da ke ɗakin, hamadala tayi da ta ga Hijabi a kai. Sakawa tayi tayi sallah, bayan ta idar ta koma kan bed ɗin ta kwanta da har lokacin bacci take ji.
Around 6am Ra'isa ta farka, bayi ta faɗa ta yo alwala tayi salla, tana idarwa ta fara tunanin tashin Hamra ko me ta tuna sai ta bar ta. Tana zaune tana haɗa handouts ɗin da za ta fita da su yau Ammiey ta yi sallama tare da shigowa, da sauri Ra'isa ta miƙe tsaye ta ƙarasa kusa da ita tare da ba ta side hug. "Barka da safiya Ammiey" ta furta cikin harshen larabci.
"Barka yarinyata, ya baƙuwarmu? Ba ta tashi ba har yanzu?"
"Eh Ammiey, ba ta tashi ba, ga ta nan tana bacci." Shiru tayi can kuma tace "Ammiey kada a tashe ta, tana buƙatar huhu sosai."
Ammiey tace "Haka ne, ba dai school za ki fita ba?"
Idanuwanta ta juya tare da faɗin "Ai dole na yau na fita, akwai important tests da ba na so nayi missing."
Ammiey tace "To Shi ke nan, amma da na so ki zauna tare da ita ne, ba na so ta farka taga babu kowa a kusa da ita."
"Laa kin ga Ammiey ta ma tashi, in tayi breakfast kawai sai ki zauna da ita. She really needs someone close to her, Ina tsoron ciwon damuwa ya kama ta, ki ga fa yadda jiya tayi, Ni ta mugun tsoratar da Ni."
Numfashi Ammiey ta sauƙe tace "Shikenan. Ki zaɓar mata kayan da za ta saka kafin Ɗan'uwanki ya kai ku ta zaɓo nata."
"Māshin!" (Ok) Ra'isa ta faɗa tare da komawa wajen Hamra da jikinta ya mata nauyi Ammiey kuma ta juya saboda yadda fuskar yarinyar ke tuna mata da ƴar'uwarta Hibbatullah. Ra'isa ta kalli Hamra cike da kulawa tace "Ukhty kin tashi? Yaya jikin ki?"
Sakaka tayi tana bin Ra'isa da kallo kamar ta ga TV yayin da zuciyarta ta fara haƙaito mata wasu moments na rayuwarta ta baya, anya kuwa dai ba mutuwa tayi ba ta haɗu da Mom ɗinta? If not mutuwa then Mom ɗinta ba ta mutu ba ashe?
*React and share fisabilillah.*
Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY NINE*
Lura da yanayin yadda take kallon Ra'isa yasa itama taji wani irin yanayi a tattare da ita, hausawa suka ce ai jini ya fi ruwa, wannan dalilin yasa suka shagala da kallon junansu kowa na tunanin wani abu cikin ransa, Hamra ce ta fara sauƙar da nata idanuwan tare kau da kanta gefe kaɗan sai kuma ta ɗan saki fuskarta. Murmushi itama Ra'isa tayi tare da maimaita tambayar da tayi mata "kin tashi lafiya?" Da kai Hamra ta ba ta amsa hakan yasa Ra'isa langwaɓar da kanta kamar wata baby tace "Ba za ki min magana ba sai da kai?"
Dariya ta so ba wa Hamra sai dai ba ta dara ba sai ta fara motsa laɓɓanta kamar za ta yi magana amma hakan ya gagara.
Cike da kulawa Ra'isa ta ranƙwafo tare da haɗa jikinta da na Hamra tace "Is ok, kada ki damu, ba sai kin ce komai ba, sorry." Kai ta gyaɗa kamar kurmiya daga haka ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Ki je toilet ki yi alwala gari ya riga ya yi haske." Shiru ta mata kawai, hakan yasa Ra'isa shiga mamakin baƙuwar, to me yake damunta? Ya kamata by now a ce ta ware ai.
Cikin wata dasasshiyar murya Hamra tace "Na yi salla"
With smile on Ra'isa's Face tace "Alright, ba ki son zama ke ɗaya ko?" Kanta tayi nodding.
Ra'isa ya saki murmushi tare da rungumarta cike da kulawa tace "You Are still afraid abi?" Hamra nodded
"You are ok here ukhty, za ki raka Ni school yau?"
"Eh" ta ba ta amsa da sauri.
"Ok, mu shirya sai mu fita da wuri, now ki huta kaɗan bari na fara yin wanka."
Bayan Ra'isa ta fito daga wanka ta nunawa Hamra toilet, daga nan ta fara shiryawa, fitowar Hamra ya yi daidai da ajiye wasu Black expensive set, an abaya with veil, handbag da kuma takalmi. Juyawa tayi suka haɗa ido da Hamra take suka sakarwa junansu murmushi.
Ra'isa ce tace "Ki shirya, Ni na gama, na miki kyau?" Ta ƙarasa tare da ɗage mata gira. Ƴar dariya Hamra tayi tare da gyaɗa kanta.
Cike da kunya ta shirya tsaf, kayan kuwa sun yi suiting nata kamar don ita aka yi su. Ƙofar da aka ƙwanƙwasa yasa su duka biyun suka mayar da hankulansu ga ƙofar, Ra'isa ce ta ba da izinin shigowa, Taqiyya ce riƙe da tray wanda abinci ke jere kansa. Ƙarasowa tayi ta ajiye tare da ficewa, Ra'isa da ke tsaye ta dubi Hamra fuska sake tare da fara buɗe flasks ɗin ɗaya bayan ɗaya tare da lumshe idanuwanta.
"Wanne za ki ci nayi serving ɗin ki?" Shiru dai Hamra ta kuma yi. Murmusawa Ra'isa ta ƙara yi ta fara serving nata dankalin turawa da aka soya da ƙwai, ta miƙa gabanta itama ta saka, yau dai a ciki suka yi breakfast abun su, suna gamawa Ra'isa ta fita da tray ɗin, ko da dawo ta iske Hamra bakin gado tace "Mu je ki gaida Ammiey sai mu wuce ko?"
Tare suka jera su biyun kamar wasu ƴan'uwan juna, banbancinsu ɗaya, Ra'isa hutu da kuma wayewa sun game jikinta amma bayan haka ba su da wani banbanci sai kuma fatar Hamra da ta fi ta Ra'isan Haske.
Ɗakin Ammiey suka ƙarasa lokacin ta gama shirya Rigima girl ɗinta, tana ganinsu ta saki fuska tare da furta "Ma sha Allah" nan kuma ta shiga duniyar tunanin yadda yarinyar ke resembling da sisternta when she's at such age.
Ganin yadda ta yi shiru yasa Ra'isa wavong hands ɗinta ga fuskar Ammiey, ƴar zabura tayi tace "Ya Allah"
Ra'isa tace "Me ke damun Ammiey haka? Your daughter is here to greet you" tana gama faɗin haka ta kalli Hamra ta mata alama da ido.
Kai ƙasa Hamra tace "Ina kwana"
Fuska sake Ammiey tace "Matso kusa yarinyata, kin tashi lafiya?"
A suƙure ta ƙarasa jikin Ammiey sai taji tamkar tare da Mom ɗinta take musamman yadda bugun zuciyarta ya daidaita lokaci guda.
Kallon sha'awa Ra'isa ke bin su da shi with smile all over her face yayin da zuciyarta ke raya mata wata dangantaka tsakaninsu though ta tabbatar babu ɗin.
Sun kwashi kusan five minutes a tare kafin su saki juna, Ammiey ce ta dubi Ra'isa tace "Ba dai tare za ku fita ba ko?"
"Tare za mu fita, barinta ita ɗaya is dangerous in respect of her condition, za mu biya ta wurin Yaya ya gan ta."
"Kul Ra'isa" Ammiey ta dakatar da ita "Kin san halin Yayanku, just in ya dawo ya gan ta."
"Shike nan Ammiey since You insisted."
"Good!" Ammiey ta faɗa with smile over her face "Sai kin dawo."
Waving hands ɗinta tayi tare da riƙo hannun Hamra da ke tsaye kanta ƙasa
"Here we go" ta faɗa tare da fara takawa.
Ra'isa ce ta tuƙa su har LASU, zuwa department ɗinsu na LAW, lokacin da za su shiga test ɗin ma tare suka shiga sai dai Hamra ba abun da ta rubuta, bayan sun gama tayi introducing Hamra ma ƙawayenta as her twin sister, mamaki sosai suka yi da batun nan, amma yanayin kamannin da suka gani. Ƙasa sakin jiki Hamra tayi a cikinsu saboda ko kaɗan zaren ba kalar yadin ba ne, wayewarsu ta sha banban, fahimtar hakan da Ra'isa tayi ysa ta yi wa ƙawayenta sallama daga nan suka wuce, wuraren shaƙatawa mabanbanta suka je wanda hakan ya ragewa Hamra tulin damuwar da ke ranta, kafin su koma ta ware har tana jin kamar tare da familynta take.
Around 4pm suka koma gida gabaɗaya jikinsu a gajiye, a parlour su duka suka yada zango. Wata irin miƙa Hamra tayi wacce ta ba wa Ra'isa dariya, sautin dariyarta ya sa Ammiey fitowa tana bin ta da kallon mamaki yayin da zuciyarta ta yi sanyi ganin yanayin Hamra.
Ƙarasowa tayi ita ma ta zauna
"Sai yanzu kuka dawo?"
Ra'isa ta amsa da "Wallahi Ammiey, mun ɗan zaga gari ne, yunwa ma nake ji"
Kallon da Ammiey ta aika mata yasa ta saka yatsarta a baki tana zazzare idanuwa.
"I'm sorry Ammiey."
"Za ki yi bayani, daughter kun dawo kenan?" Ta faɗa tana kallon Hamra. "Hope kin ji daɗin fitar?"
Kai Hamra ta gyaɗa. Ammiey ta tsayar da kallonta ga Hamra tare da faɗin "Matso kusa da Ni daughter." Ta nuna mata gefenta.
Cikin jin kunya Hamra ta miƙe ta dawo gefen Ammiey, Ammiey ta sa hannunta ta janyo ta zuwa jikinta, the feeling is different, kowannensu shiru ya yi kamar babu su a parlourn. Tsayuwar mota da suka ji daga waje ya tabbatar musu da dawowar Ya Mubeen. Ammiey ce tace da su "Ga ɗan'uwanku ya dawo ko abinci ma ba lallai kun ci a can ɗin ba, Ra'isa, help my daughter fresh up."
Tura baki Ra'isa tayi sannan tace "Yau nake ga wariya a wurin Ammiey, Ni ɗin kin daina so na ne ko me?"
"Say whatever, Here's my daughter, ki yi abun da na saka ki."
Yadda ta yi maganar yasa Ra'isa jin daɗi at least dai Hamra will feel welcomed. Murmusawa Ra'isa tayi tare da duban Hamra tace "Mu je ko ukhty?" Miƙewa tayi daga nan suka nufi corridor ɗin da zai kai su bedroom ɗin Ra'isa. Sallamar su Ya Mubeen yasa Ammiey janye kallonta daga gare