Showing 93001 words to 96000 words out of 134378 words

Chapter 32 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

100

su, ƙanƙame ta Nihla tayi tana dariya.
"You Are welcome dear, me ya saka ki farin ciki haka naga sai dariya kike."
"Ammiey, yau Abie ya ce zai kai Ni shopping."
"Good of him, ya goge laifin da ya miki" ta faɗa tana hararar Ya Mubeen wanda ke sosa kansa.

Kasa magana yayi hakan yasa ya fara ƙoƙarin shigewa ciki, Ammiey ba ta dakatar da shi ba har ya haye bene, Nihla ta dubi Ammiey tace "Ammiey ina Ammiey Ra'isa?"
"Tana bedroom ɗinta, me ya faru?"
"Zan ce mata ta shirya Abie zai kai mu shopping."
Shirun da Ammiey ta mata yasa ta bar jikinta ta ruga da gudu, da murmushi Ammiey ta bi ta, daga nan ta ƙwalla ƙiran Taqiyya ta sanar da ita dawowar Angel, nan ta wuce nata ɗakin zuciyarta na mata wani irin daɗi.

Shigar Nihla da Hamra ta fara cin karo instead of Ra'isa, ɗan baya tayi ta fara sosa idanuwanta kamar wata babba, mamaki take yi ganin dai abun da ta gani ɗin zahiri ne. Saurin rungume Hamra tayi tana sakin wani Marayan kuka. Lallashinta Hamra ta fara ba tare da ta raba jikinta da na Nihla ba.
Tun fitowar Ra'isa ta ci karo da su, hakan yasa ta daskare a wurin tana aika musu kallon mamaki.

Nihla ce ta fara janye nata jikin tace "Ammiey Hamra dama kin san Ammiey? Dama ke ɗin twin sistern Ammiey Ra'isa ne Abie ya kore ki a companynshi? Ai kuwa Ammiey za ta sa ki koma aikin ki? Kullum sai na yi kuka idan na tuna ki."
Hawaye ne suka ziraro daga idanuwan Hamra, Nihla ta saka hannu ta goge mata shi.
"I'm sorry Ammiey Hamra. Abie bai kyauta ba."
Jijjiga kai Hamra tayi tare da faɗin "Shhhh, kul kika ƙara cewa Abie bai kyauta ba, what he has done is good, ba a questioning iyaye akan wani hukunci da suka yanke, and worry not, Ni nace ba na son aiki ba korana ya yi ba. Kin ji ko?"
Kai Angel ta gyaɗa fuskarta cike gal da annashuwa.

Gyaran murya Ra'isa tayi tare da faɗin "So You people know each other before?" Kai Hamra ta gyaɗa tana murmushi duk da cewa cikin ranta tsoro take ji, gani take kamar ba za ta yi dogon zango a gidan nan ba tunda ta fahimci cewa gidansu mugun mutumin nan ne wanda ya fara saka mata tsanarsa a ranta shi da kansa, take yanayin fuskarta ya sauya zuwa na ɓacin rai, hakan yasa Ra'isa jin wani iri, sai ta ga kamar ita tayi switching mood ɗin Hamra. A saɓule ta samu ta saka kaya Nihla kuma sai zuba take wa Hamra wacce sam hankalinta ba ya kan abun da Nihla ke faɗi.

Ƙofar aka ƙwanƙwasa, Ra'isa ta ba da izinin shigowa, Taqiyya ce ta shigo cike da girmamawa ta ce "Dama Amma ce tace na shirya Nihla za su fita."
"Ok, Angel, daga ganin Hamra kin liƙe mata, maza ki je ki shirya za ku fita, tana zuwa."
Taqiyya ta juya daga nan Ra'isa ta ce "Ke da waye ne za ki fita?"
Cikin zumuɗi tace "Da Ammiey Hamra da ke, da kuma Abiey, ya ce, za mu je shopping."
Cikin jin daɗi Ra'isa tace "Kai! Amma na ji daɗin fitar nan" don tunaninta ya san da batun Hamra shi ya sa ta shirya fitar.

Haɗe fuska Hamra tayi ta dubi Nihla tace "Kina ji ko Nihla?" Da kai ta ba ta amsa tare da ba ta duka attention ɗinta.
"Kul kika bari Abiey ya san ina nan, in kuwa Ya sani yau zan bar gidan nan ba za ki ƙara gani na ba, in kin shirya ki ce masa Ammiey Ra'isa ta ce ba za ta je ba kanta na ciwo."
"Amma.." ta dakatar da ita tana faɗin "Shhhh"
"Ko kina so na tafi ne da gaske?" Ta jijjiga kai
"Alright, do as I say" Nihla ta jinjina kai.
"You can go." Daga haka ta fice da gudu.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da goge siririyar ƙwallar da ta zubo mata, Ra'isa da ke nazartar ta sai ta ji babu daɗi da wannan yanayi da Hamra ta shiga lokaci guda ɗaya ɓari na zuciyarta kuma na son sanin ta yaya ta san Nihla har suka samu irin wannan shaƙuwa da ta gani. Gefenta Ra'isa ta zauna ta riƙo hannunta

"I'm sorry ukhty, me yasa kike da saurin kuka haka? Be strong please, ban takura miki Ki faɗa min komai ba amma na roƙe ki ki ƙarfafa zuciyarki, tattare da kowanne raɗaɗi akwai sauƙi, believe me you're safe here ok?"
Ta gyaɗa kai, Ra'isa ta sumbaci gashinta da ya kwanta a bayanta tare da faɗin "Good, now za mu je shopping ɗin ai ko?"
Kai Hamra ta jijjiga mata, ta amsa mata da "Why? Kina tsoro ne?"
"I'm not in mood of going out, ku je kawai." Cike da kulawa Ra'isa tace "Kada ki damu ukhty, I'm here for you, mu bari in kin ƙara sakewa sai mu fita, bari na kawo mana abinci ko."

Ba ta jira amsarta ba ta fita, babu kowa a parlourn sai Ammiey, ɗauke da mamakin ganinsu a fuskarta yasa ta ce "A'a, ya dai ba ku tafi ba ne?"
"Where?"
"Ɗan'uwanku ya ce za ku fita."
"Yanzu muka dawo, we need to rest, ma je some other day."
Daga haka ta wuce, abincin da ke baje kan dining ta buɗe, fuska yamutse ta rufe su, ba ta ɗauki ko ɗaya ba ta koma bayan wani lokaci suka fito tare da Hamra.

Dining area suka wuce Ra'isa ta bubbuɗe tana tambayar Hamra wanne za ta ci, abinciccika irin wanda ba namu na hausawa ba sai dai kwaɗayin da taji na cin su yasa ta miƙe ta zuba wa kanta ba tare da ta jira an mata hakan ba yayin da ta bar Ra'isa cikin mamaki da tunani.
Spoon ɗin farko da ta kai bakinta yasa ta lumshe idanuwanta, shekaru da yawa rabonta da ɗanɗana irin girkin nan, ta yi tunanin tunda Mom ɗinta ta rasu ba za ta ƙara cin kwatankwacinsa ba, but today, she's feeling at home ga ta kuma tana tasting favourite food ɗinta.

Wasa-wasa sosai ta ci wannan abinci, sai da ta yi hani'an ta dubi Ra'isa da ba ta ci ko rabin plate ba tana bin ta da kallo, girarta ta ɗage tana tambayarta ko lafiya. Numfashi Ra'isa ta sauƙe sannan tace "Babu komai fa, I'm just surprised on yadda kika ci abincin nan hankali kwance bayan kuma a nan Najeriya ba cimarsu ba ce, abincinmu ne na al'ada."

Tsabar yadda take jin ta cikin farin ciki ba ta san lokacin da ta ce "Na yi shekaru da yawa ban yi tasting girkin mom ba, i thought daga ranar da na rasa ta ba zan ƙara tozali da irin girkin ba, but today, ga shi gabana." Sai kuma ta yi shiru hawaye na bin fuskarta.
Ajiye spoon ɗin hannunta Ra'isa tayi ta Matso da kujerarta kusa da ta Hamra. Da hannunta ta share mara hawaye cike da kulawa tace "I'm sorry, ban son hawayenki ko kaɗan ban san dalili ba, it seems like there is sad memories a tattare da ke, feel free ki yi magana da Ammiey, she's nice and good, I'm sure za ta samar miki mafita."
Shiru tayi ta ƙara da "Now kin ƙoshi?"
Ta gyaɗa kai
"Ok, let's meet Ammiey."
Daga haka ta miƙa mata hannu, babu musu ta saka nata cikin na Ra'isa, ta ɗan sa ƙarfi tayi lifting ɗinta ta miƙe, tare suka fara takawa cikin sanyin jiki har suka isa parlourn, Ra'isa ta zaunar da Hamra gefen Ammiey ita kuma ta zauna a kujerar da ke kallonsu.

Cikin wata sassanyar murya mai cike da ɗumbun kulawa Ra'isa tace "Ammiey ga ɗiyarki, she really needs you, tana buƙatar kafaɗar da za ta kwanta a kai tayi kuka, tana buƙatar majingina da kuma majiɓanci, Please be her Mom, ki ɗauke ta kamar Ni, akwai abinda nake ji a tattare da Hamra, ina jin tamkar ita ɗin jinina ce, Ammiey ba ki kula da kamannin da nake yi da ita ba?"

Take hawaye suka fara zarya kan fuskarsu yayin da maganganun Ra'isa ke tasiri cikin ransu, hawayen da Hamra ta gani kan fuskar Ammiey yasa tayi saurin saka hannunta ta goge mata, itama Ammiey ta saka nata ta gogewa Hamra, Ra'isa da ke fuskantar su ta sauƙe numfashi tace tare da bin su da kallon sha'awa.

Riƙo hannun Hamra Ammiey ta yi tana murza tafin hannun nata Sannan tace "Tabbas Nima ina jin hakan a jiki, ina jin Hamra tamkar Hibbatullah! Sai dai kuma ban tabbatar ba duk da cewa sunanta ɗaya da ɗiyar ƴar'uwar tawa amma ita tuntuni ta rasu." Zirr sai ga hawaye, Hamra ta sa hannu ta goge mata lokaci guda kuma zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi da ƙarfi jin sunan mahaifiyarta a bakin Ammiey. Ko me ke shirin faruwa da ita? Anya kuwa ba su da wata alaƙa? Kai akwai.

Ammiey ta ƙira sunanta "Hamra"
Hamra ta ɗago ta dubi Ammiey sannan ta sunkuyar da kanta.
"Ban san ki ba, amma ina jin ki a jikina tun ranar da muka haɗu, ban taimaka miki don na cutar da ke ba, hasali ma yanzu ji nake zan iya bayar da rayuwata saboda taki, na ɗauke ki kamar Ra'isa da na haifa, kema ki ɗauke Ni kamar mahaifiyarki."

Cikin karyewar zuciya Hamra tace "Ina jin kwatankwacin yadda kike ji Ammiey, kin maye min gurbin Mom ɗina, na Kuma ba ki gurbinta cikin rayuwata."
Kuka ne ya ci ƙarfinta, Ammiey ta rungumo ta jikinta ta lallashe ta, bayan ta yi shiru Ammiey ta ce, "Ina ji a jikina you're part of me, please zan iya sanin tarihinki Hamra?" Kai Hamra ta jinjina sannan ta fara magana.

*Wace ce Hamra?*

Alhaji Abubakar Musa babban ɗan kasuwa ne da ke kasuwancin kayan ƙawa a tsakanin kasarsa ta Najeriya da kuma Misra (Egypt), yana tafiya da wasu abubuwa da muke da su ya sayar a can sannan ya saro wasu kayayyakin ƙawa irin nasu ya kawo nan, Asalin Alhaji Abubakar ɗan garin Azare ne amma kuma ba mazaunan nan ba ne shi da iyayensa, Jahar Jigawa nan ne matsuguninsu. Iyayensa na da tarin dukiya sai dai shi bai dogara da tasu na, hasali ma neman nasa ya sa a gaba, hakan ya sa ya fara wannan kasuwanci saboda shine burinsa, a fannin boko da wayewa Alhaji Abubakar yana da kwalin digiri a likitanci wanda yayi bisa umarnin mahaifinsa.

Cikin amincewar Ubangiji Allah ya bunƙasa nemansa, ganin hakan yasa dangi suka masa caaa akan rashin aurensa har wasu na jifansa da miyagun maganganu, wasu na cewa dama in an ga saurayi mai kuɗi y kamata a bincike shi, wasu na faɗin anya ba satar yara yake ba, wasu su ce ai ɗan yankan kai ne.

Bai taɓ damuwa da maganganunsu ba amma a hakan ya zaɓi yayi auren saboda iyayensa sun buƙci hakan, babu ɓata lokaci ya baza don neman abokiyar rayuwa sai dai yawanci matan kuɗinsa suke so ba wai shi ba, watarana ya kai ziyara Azare ya haɗu da ɗiyar abokin mahaifinsa ya kuma ji ta masa, kasancewarta mace mai tarbiyya da kuma kamun kai, bai baro Azare ba sai da ya sanar da mahaifin Murjanatu, sosai ya nuna farin cikinsa ya kuma tabbatar masa da cewa kafin ya isa Jigawa ma za su yi magana d iyayensa.
Hakan ce ta faru kuwa, sosai iyayensa suka yi farin ciki da hakan, babu jimawa aka sanya ranar biki don mahaifin Murjanatu Ahlussuna ne, ya kuma ce ba za a ja abun da nisa ba tunda itama ta amince da Alhaji Abubakar ɗin.

Cikin watanni biyu aka yi auren Murjanatu da Alhaji Abubakar, aka kawo ta Jigawa, Murjanatu ta samu karɓuwa a wurin danginsa da ke nan Jigawa sosai sai dai bayan shekaru uku da aure da suka ga ba ta taɓa ko da ɓatan wata ba suka fara maganganu, nan Jigawa da Azare kowa magana yake tunda dama danginsa sun so ƴar gida ya aura kuma da yawa kuɗin nasa suke hange. Nan fa suka fito mata da halaye iri-iri, yau wannan taje da ƴarta budurwa su ci mutuncinta suna mata shaguɓe, wasu suna mata albishir na da cewa ƴarsu zai aura.


*React and Share Lillah*



[8/27, 7:27 AM] Diamond Bhatool (Fatisah):



_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY*

Duk abun da ke faruwa Alhaji Abubakar bai sani ba, don ko kaɗan Murjanatu ba ta taɓa nuna masa hakan ba duk da cewa abun na damunta, babu tsammani ta samu juna biyu, kar ka so ganin murna wurin Alhaji Abubakar da ita kanta, ba su sanar da kowa ba, haka kuma ƴan'uwansa daga Azare ba su daina zuwa gidan ba suna takura mata idan ya tafi Egypt ba. A lokacin da suka fuskanci tana da ciki sai suka fara takalar ta da faɗa ganin in magana ne da zagi suka mata ba ta taɓa tanka musu ko ta kalle su, amma in sun taɓa jikinta ai dole ne ta kare kanta, a haka sai su illata ta.

Tun sau ɗaya da hakan ta faru sai ta rufe sashenta ma ta daina fitowa gabaɗaya, har dai ta daina jin motsinsu alamar sun gaji sun bar gidan. Ba su fi sari da tafiya ba ƴanmata biyar suka dira gidan sai dai dawowar Alhaji ysa suka ji haushi ganin ba su cimma burinsu ba. Abun da ba su sani ba shi ne, Ubangiji yana tare da ita, a lokacin da cikinta ya kai haihuwa ta fara naƙuda tun a gida sai dai kuma babu wanda za su je asibiti tare da shi tunda mijinta ba ya nan, haka dai abu kamar wasa sai naƙuda take amma babu ci gaba har dai ƙarfinta ya ƙare, cikin ikon Allah sai ga ƙanwar Alhaji Abubakar, Habiba ta zo gidan, yanayin da ta tarar da matar ɗan'uwanta yasa ta fita da sauri ta tsayar da mai adaidaita sahu, ta dawo da ƙyar ta taimaka mata suka fito, asibiti ta kai ta daga nan ta dawo gida ta sanar da iyayenta. Kafin ka ce me suka taho asibitin tare.

Suna zuwa aka sanar da su cewa Murjanatu ba za ta iya haihuwa ba, ga Form ɗin izini nan an cike saura saka hannun mijinta za a shiga a mata CS, Ɗan'uwan Mijinta Kabir shi yayi signing a maimakon ƙaninsa, take aka shiga da ita ɗakin aiki.

Bayan wasu awanni aka cire yaron da wahala ma ta kashe shi tun a ciki ashe, aka kawowa danginta gawarsa, sai lokacin aka kira Abubakar aka sanar da shi, bai wani tayar da hankalinsa ba lokacin da ya ji cewa Murjanatu na cikin ƙoshin lafiya, washe gari ya diro Jigawa. Bayan sati da haihuwar Murjanatu itama Allah ya ɗauki abarsa, tun daga wannan lokaci Alhaji Abubakar ya sauya zuwa mutum maras magana, ya kuma rage dawowa Najeriya tunda yanzu bai da iyali. Ko shekara ba a yi ba ya fara samun masu son sa daga dangi sai dai kuma sam shi ba shi da wannan ra'ayi, ko da Umma mahaifiyarsa ta sanar da shi cewa yayi a'a, ba ya buƙata, itama ba ta takura shi ba ta masa uzurin har lokacin yana makokin marigayiya Murjanatu ne.

Shekara guda bayan rasuwar Murjanatu Abubakar ya haɗu da wata balarabiya a ƙasar Ethiopia mazauniyar Egypt, ya Sha wahala sosai kafin Hibbatullah ta amince da shi duk da irin tarin ƙalubalen da za su fuskanta in an zo batun aurensu, don mahaifiyarta wacce ita ɗin haifaffiyar Egypt ɗin ne, ta ƙi irin wannan haɗin saboda illar da ya yi wa rayuwarta.

Cikin ƙanƙanin lokaci Hibbatullah da Abubakar suka saba da juna, nan shi kuma ya matsa mata akan zai tura magabatansa don su magantu da nata, amma me? Sai ta nuna rashin amincewarta daga farko don sosai take shakkar mahaifiyarta Ammah. Bayan lallashin da yayi mata dai ta amince amma ta buƙaci lokaci don yin shawara da tilon ƴar'uwarta Naja'at wacce ke aure a Nigeria.

Takanas Hibbatullah ta taka har Najeriya wurin ƴar'uwarta, bayan shawararin da ta da kuma goyon baya, ta yanke hukuncin fuskantar ko wanne irin ƙalubale da zai fuskanci alaƙarta da Abubakar daga wannan lokaci zuwa auren su. Ganin yadda suka nace kan su mallaki junansu ya sa Mahaifiyar Hibbatullah sare wa daga ƙin ta ga wannan haɗi. Cikin ƙanƙanin lokaci alaƙarsu ta ƙara ƙarfi, hakan ya sa babu ɓata lokaci mahaifiyar Hibbatullah ta sanar da Abubakar kan ya turo da magabatansa kawai a musu aure, ta kuma sanar da shi can Ethiopia ɗin wajen dangin mahaifinta za su je, ba a ɗau tsawon lokaci ba komai ya ƙullu, aka ɗaura auren Hibbatullah da mijinta Abubakar wanda a ranar ya taho da ita ƙasarsa Najeriya.

A ranar da aka kai ta washe gari danginsa suka fara tururuwar zuwa ganin balarabiyar amarya wacce da yawa mugun baƙin ciki da hassada ke ɗawainiya da su, sai dai duk ƙoƙarinsu na gano aibun Hibbatullah ɗin ba su ci nasara ba, don ko ɗaya ba su samu ba, hakan ya sa suka fara tunanin ta ya za su raba wannan alaƙa da ta musu shigar sauri.

Hibbatullah mace ce mai haƙuri, kamun kai, hangen nesa uwa uba kuma iya zama da mutanen da ke kusa da ita, hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka sabo ya ƙullu tsakaninta da dangin Abubakar wanda yanzu dukiyarsa ke ƙara bunƙasa kamar ana zuba mata taki. Rashin samun wadataccen lokaci da ya tsinci kansa ciki ya sa ya ɗauki matarsa suka koma can Egypt da zama, shekara ɗaya da aurensu Allah ya azurta su da samun ɗiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login