Showing 120001 words to 123000 words out of 134378 words
suka yi mai isarsu tukun suka saki juna, Ammiey ta dube su da ɗimbun mamaki tare da faɗin
"Dama can kun taɓa haɗuwa ne?"
Ummie ta jinjina kai tare da labarta musu komai kamar yadda ya faru shekarun da suka gabata. Sosai suka jinjinawa ƙudirar Ubangiji, lallai rashin sani ya fi dare duhu, amma tabbas sun lura da kamannin da Hamra ke yi da wasu da suka sani amma dalilin ganin tare da Baffanta ɗan'uwan mahaifinta take yasa suka kau da duk wani tunani da suke na alaƙanta Hamra da wasu.
Sun yi farin ciki sosai, musamman Ya Hamid da har yanzu bai yi aure ba, gani yake damarsa Ubangiji ya kawo a wannan lokacin ba tare da wani tunani ba. Cikin ran Ummie ma addu'a take Allah ya sa dai Hamra ba ta da wani tsayayyen, don ta san ɗanta har yanzu yana son Hamrar. Ganin la'asar na ƙara yi yasa Ya Mubeen miƙewa tare da miƙawa Ya Hamid hannu, wnada gaba ɗaya hankalinsa ke kan Hamra, "Za mu wuce, ban san ko za mu je tare ba?"
Cike da son rashin barin Hamra yace "Tare Da ita za ku tafi?"
A ba zata Ya Mubeen yace "Who?"
Ya Hamid ya yi pointing Hamra da yatsa yana faɗin "Hamra" sosai hakan ya daki ransa amma sai dai abun ka da Ya Mubeen namijin duniya sai ya kawar tare da yafa murmushi kan fuskarsa ya gyaɗa masa kai. Babu shiri ya miƙe yana faɗin za mu je, Ummie da ta karanci wani abu a tare da guys ɗin guda biyu ta yi saurin faɗin "A'a Hamid, daga zuwa sai ku wani fice? Su je kawai, ku ku zauna tukun, ko ba ku yi kewar Ammieyn taku ba ce?"
Ajiyar zuciya Ammiey ta sauke tana faɗin "Rabu da su Maryam, idan suna so su je mana, in sun dawo ba sai mu yi hirar ba."
Ummie tayi saurin faɗin "Rabu da su kawai Ammieyn Yara, koma ku zauna, Hamra ki je maza, ganin yadda fuskar Humaira ta nuna rashin jin dadin haka yasa Ammiey faɗin "Bi su Humaira, kai kuwa ka ci girma tun da na ga Ummie yau girman take son ba ka. Ba komai ya nuna a fuskarsa amma cikin ransa bai ji daɗi ba musamman yadda yaga fuskar ya Mubeen da ya kasance ɗan'uwa kuma amininsa sauyawa, tabbas akwai wata alaƙar tsakaninsu.
Da haka suka fice suka bar Ya Hamid yana ayyana wasu abubuwan cikin ransa. A nan ne ma Ammiey ta labarta musu komai game da Hamra wanda hakan ba ƙaramin kaɗar da su yayi ba, musamman Ya Hamid da yake ganin kamar a yanzu Hamra ta masa nisa, duba da irin gudunmawar da ɗan'uwsnsa ya bayar a rayuwarta. Jiki sanyaye ya jajantawa Ammieyn wacce s yanzu ita ma ta fahimci abun da ke damun ya Hamid ɗin tun da Ummie ta faɗa mata dalilin rabuwar su ɗin.
Wurare daban-daban suka je wanda hakan ba ƙaramin faranta ransu yayi ba, musamman love birds ɗin da zuciyarsu ke bugawa kusan lokaci guda. Hotuna da videos sosai suka yi wanda yawanci Ra'isa ke musu, wasu kam ma ba su san ta yi musu ba. Ba su suka dawo ba sai da duhun Magrib ya fara, hakan yasa suka nufi gida cike da farin ciki bayan sun yi wa mutanen gidan tsaraba, Ya Mubeen tare suka fice da Ya Hamid zuwa masallaci yayin da su kuma suka shiga suka yi sallah, suna idarwa suka dawo parlour tare da buɗe ledar tsarabar, Ammiey da Ummie ne suka shigo hakan yasa suka sauƙa ƙasa suka ba su wuri su zauna, nan Ra'isa ta miƙawa kowa nasa, cikin farin ciki kuwa suka karɓa suna saka musu albarka wanda hakan ba kaɗan ya sanya su farin ciki ba.
Ko da su Ya Mubeen suka dawo suma zama suka yi aka ci gaba da hirar tare da su, sallar Isha ce kawai ta daga su a wurin, bayan sun dawo kuma suka yi dinner. Ammiey da Ummie ne suka fara musu sallama don akwai masu private zantuttukan da za su yi, Ya Mubeen da Ya Hamid ma suka wuce ya rage iya su uku, Hamra, Humaira da kuma Ra'isa. Su kam ba su tashi ba ci gaba da hirar su suka yi, Cikin ba zata Humaira tace "Yanzu kam Hamra kin manta da Yayana, Allah ya sa dai babu wanda ya maye gurbinsa s zuciyarki."
"Kamar ya kenan?" Ra'isa ta faɗa a ba zata itama
"Yadda dai kika ji, ai Ra'isa..."
Nan ta labarta mata komai daga haduwarsu da Hamra, soyayyar Hamra da Ya Hamid da kuma dalilin rabuwar su na hana aurensu da Baffa ya yi, zuwa barin su Azare da zama duk ta faɗa mata.
Fuska na nuna tsantsar mamaki Ra'isa tace "Ikon Allah, amma dai Allah da iko yake, lallai kuwa Ya Hamid ya zo a gaɓar da ba zan iya cewa kai tsaye ya rasa Hamra ba amma kuma ina tunanin ba lallai ya same ta ba"
Ra'isa ta faɗa zuciyarta na wani irin bugawa tun da taji batun soyayyar Ya Hamid ga Hamra.
Jinjina kai Humaira tayi tare da duban Hamra sannan ta sauya akalar kallonta zuwa ga Ra'isa wacce itama wani zancen take a yanzu cikin ranta.
"Ku min dalla-dalla mana sisters"
Ajiyar zuciya Ra'isa ta sauƙe tana faɗin "Hmm, abun bai min ba sam, Hamra da Akhy soyayya suke?" Cike da mamaki Humaira tace "You mean Ya Mubeen?"
Ta jinjina mata kai
"Ƙwarai kuwa Humaira, Yaya yana matuƙar son Ukhty, so irin wanda zan iya ce miki ko Ne-ha bai yi wa irinsa ba, ke ba ki yi mamakin ganin yadda ya sauya ba?"
Cike da tabbatarwa Humaira ta gyaɗa kai tana faɗin "ƙwarai kuwa, ki ce dai Yayana ya yi kwantai"
Ta faɗa tana duban Hamra wacce a yanzu jikinta ya gana yin sanyi.
Murmusawa Ra'isa tayi tace "Ke shima Akhy ɗin da bai tabbata ba, still akwai Ya Ja'afar a layi, Cousin bro ɗin ta ne a Jigawa, da Daddynss da Dad ɗin ta uwa ɗaya uba ɗaya suke, kuma kin san me?"
Humaira ta jijjiga kai tana mamakin wannan badaƙala tare da tunanin ta ya za a wanye sumul a ciki.
Sai da Ra'isa ta gyara zama kafin ta ce "Ƙwarai kuwa, shi Ya Ja'afar ya bayyana soyayyarsa don har an sani a can Jigawa, Akhy da Ya Hamid ne yanzu a ruwa, shi yasa nake so tun Yanzu Ammiey ta magantu, don wallahi in dai don ta Akhy ne, hmm, ba zai taɓa magana ba ko da kuwa zai rasa ta ne."
Ta ƙarasa cikin murya mai matuƙar sanyi wacce ke nuna zallar tausayawarta ga ɗan'uwan nata.
Ajiyar zuciya Humaira ta sauke lokaci guda kuma tace "To yanzu ina mafita? Ke Hamra ya kike? Wa kika zaɓa cikinsu? Tukunna ma kin yi istikhara ne?"
A sanuaye Hamra ta ce "Na yi"
"To wa kike jin zuciyarki ta fi aminta da shi?"
Shiru ta yi can tace "Ya Mubeen, Humaira, gani nake kamar ba zan same shi ba."
Cike da kulawa Humaira ta dafa ta tana faɗin "Kar ki ɗaga hankalinki, in sha Allah komai zai yi daidai, Ni nan, zan sadaukar da komai ganin kun mallaki juna."
"Ta ya kenan?" Both Hamra da Ra'isa suka faɗa
Murmushi tayi irin na ƙarfafa guiwar nan kafin tace "Ba wata wahala fa, amma dai ina son tabbatar muku cewa within a week, komai zai daidaita."
"Allah ya sa" Ra'isa ta faɗa tana mamakin ta ya hakan zai kasance.
Ƙiran wayar Ya Ja'afar yasa Ra'isa faɗin "Kin ga ɗan halak, Ya Ja'afar ɗin ne"
Murmusawa Humaira tayi tace "Ki ɗaga mana Hamra, da kun gama gaisawa ki haɗa Ni da shi. If possible ma ki ban numbernsa, in sha Allah komai zai daidaita."
Kamar yadda Humaira ta faɗa suna gama gaisawa Hamra tace "Yau ina tare da sisters dina, amma ɗayar ba ka santa ba, ta ce tana son gaisawa da kai."
Ba tare da ya kawo komai cikin ransa ba yace "To babu damuwa Babe, ba ta."
Miƙawa Humaira wayar tayi wacce ke famar sakin murmushi ita kuma ta yi hanyar bedroom ɗin su.
Sosai Humaira ta gaisa da Ya Ja'afar, bayan sun gaisa ta fara sako masa hurarraki daban-daban ta ƙi ba shi ko da damar faɗin ta ba wa Hamra, ta kanainaye shi da hira, har Ra'isa ta gaji da jira tace da ita itama ta yi ciki.
Wasa-wasa har kusan 10pm Humaira na parlour suna hira da Ya Ja'afar, sai da ta tabbatar ta ɗana tarkonta tukun ta ce mishi bacci take ji, nan suka yi sallama tana sakin wani irin murmushi wanda ke nuna cin nasararta kai tsaye, daga nan ta ɗauki numbersa a wayar ta saka a nata sannan ta yi dialling. Bayan ya ɗaga tace yayi saving numbernta, hakan kuwa aka yi daga nan ta wuce bedroom, lokacin su Ra'isa kam sun yi nisa cikin baccinsu, hakan yasa ta ajiye waypyin nasu kan mirror, daga nan ta sauya kaya zuwa na bacci, itama ta haye bed tna addu'ar bacci.
Washe gari da safe Hamra da Ra'isa suka saka tsare Humaira da tsokalar daga gaisuwa shi ke nan sai a fake da hira.
Murmushi kawai tayi tare da faɗin
"Kawai fa gaisawa muka yi da Yayan nawa ko ƙanina zan ce?"
"Can miki dai, ƴar shegen son girma" Ra'isa ta faɗa tana jifan Humaira da harara
"Harare Ni da kyau, tun da na girmi mutum dai dole ya mutunta Ni, aha"
Parlour suka ƙarasa suna ɗan faɗansu wanda Hamra dai iyakarta murmushi ne.
Abincin da ke jere a dining suka buɗe, Humaira dai tace babu wanda za ta ci, don Allah su taya ta tayi kafin su Ammiey su fito.
Hakan kuwa aka yi suka shiga kitchen su ukun suka yi nasu girkin, lokacin har su Ammiey sun karya, gaishesu suka yi cike da girmamawa. Ammiey ta dubi Hamra tace
"Ki haɗa a tray ki kaiwa su Hamid ɗin sama"
Kamar za ta yi yaya haka tace "To" sannan ta dubi su Ra'isa da ke mata dariya ganin yadda tayi kici-kicin da fuska kamar za ta yi kuka
"Please ku ɗan taimaka min"
Humaira tace "Ni dai babu inda za Ni tunda Ni ma dai baƙuwar ce" daga haka ta wuce abun ta.
Tare da Ra'isa suka kai breakfast ɗin su Ya Mubeen daga nan suka dawo, tatar da Humaira suka yi tana waya ciki ciki kamar ba ta so a ji ta. Ai kuwa Ra'isa tace "Ukhty duba min matar nan, ko dai ko dai?" Ta faɗa sounding so rude.
Dariya Hamra tayi tana faɗin "A hada mu mu gaisa da Yayan namu mana" ai kuwa tana jin haka sai ta jefo mata harara ta ci gaba da wayarta. Cike da tsokala Ra'isa tace "Uhm, in ta yi tsami dai za mu ji"
"Haka ne" Hamra ta faɗa tana faɗawa toilet.
Yammacin Ranar Ammiey ke sanar da su zuwa Jigawa, tafiyar kuma iya su uku ne tun da su Humaira ba ranar tafiyarsu. Sosai suka yi farin ciki sannan suka fara haɗa kaya, ita dai Hamra tsoro ma take kada a ce suna zuwa a yi zancen aurenta da Yaya Ja'afar, hakan ne ma ya rage mata karkashin son tafiyar, uwar rawar kai Humaira kam sosai taji daɗi, tana ganin lokacin cikar plan ɗin ta ya yi.
Sallah da sati ɗaya, ranar Laraba kenan, suka wuce, da yake ma tafiyar jirgi ce cikin ƙankanin lokaci suka kai, ai kuwa Ya Ja'afar ne ya zo ya wuce da su. Suna isa kuwa suka samu tarba mai kyau daga Dadda. Da yamma kuwa suka wuce cikin gida suka yi gaisuwa, abun da ya ɗaure ma Hamra da Ra'isa kunne bai wuce yadda Ya Ja'afar ke ta nan da nan da Humaira ba, sai suke ga ma kamar bai ga Hamra ba. Amma ba su da ta cewa tun da dai bai fito fili ya ce yana son Humairar ba.
Cikin wannan hutu nasu abubuwa da yawa sun faru, na farko dai dama an faɗa, don dai yanzu kam sun tabbatarwa kansu cewa Humaira da Ya Ja'afar are in love, sannan ita da kanta ta riga ta faɗa musu hakan, to, ba a ce komai ba, hakan ma wata nasara ce ga Hamra da ke hangowa kanta na ganin ta mallaki Y Mujeen ɗin ta, sannan a ɓangaren Ra'isa ma kullum cikin waya take da Ya Hamid, kasa shiru Hamra ta yi har sai da ta tanka. Ita dai Ra'isa murmusawa kawai take don ita ta san me yake faruwa. Ko da Humaira da Hamra suka keɓe su biyu lokacin Ra'isa kuma na waya, nan Humaira ta sanar da ita yadda ta tsara, dama ta yi hakan ne kawai saboda taga kowa ya mallaki wanda yake so.
Nan ta ba ta labarin yadda Ra'isa ke son Ya Hamid ɗin tun suna yara, don ko irin zuwa suka yi ba ta zuwa wurin kowa sai shi, da ɗin shima yana son ta amma daga baya kuma sai duka su biyun suka watsar tun da dama ji da kansu ya fi su ƙarfi. Ganin yadda take so al'amarin ya tafi yadda ya kamata kawai yasa ta yi wa yayan nata magana kan cewa already Ya Mubeen yana soyayya da Hamra kuma ita ma Hamrar a yanzu tana son sa, ya kamata ya duba irim wahalar da Hamra ta sha a rayuwa ya bar t da wanda ta tsara rayuwarta da shi a yanzu, ya manta cewa ya so ta kawai. Hakan kuwa aka yi, washe gari da maganar kuma shi ne suka zo Jigawa, ta ƙira shi a wata bayan sun gaisa ta kawo masa zancen Ra'isa wanda da yawa dai rayuwarsu ta baya da irin kulawar da ya ba ta da ne, ko me? Daga nan ta bar shi da tarin wasiƙun jaki. Ai kuwa ba a jima ba sai gashi yanzu kullum a ɗinke suke a waya da alamar ma dai lobayya suke yi.
Batun Ya Ja'afar kuma tun ranar da suka gaisa da Humaira ta ja shi da surutu, washe gari da ta kira shi da layinta, ta sanar da shi cewa nata ne, to daga nan kullum sai ta ƙira shi da safe, da rama da dare kuma daidai lokacin da ya ƙira Hamra ranar, kulawar da take ba shi yasa ya ji yana neman mantawa da Hamra, daga ƙarshe mai sai ya gano cewa Ba son Hamra yake ba, kawai dai soyayya ce irin ta jini ɗaya, wannan dalilin yasa kai tsaye ya sanar da Humaira ƙudirinsa a kanta, ta kuwa ji daɗin hakan don ita ma a lokacin ta tabbatar cewa ta kamu, sai dai ƙin nuna amincewarta tayi ta kawo masa batun Hamra. Sai da yace zai ba wa Hamra haƙuri tukun ta tabbatar cewa e, sonta yake, don haka sai ta ce babu komai.
Shi dai bai yi wa Hamra magana ba amma kuma ta ci gaba da kwasar romon soyayya wurin sabuwar tauraruwar tasa wato Humaira, ranar Alhamis ya karɓi wayarta yana kallon pictures ya ci karo da pictures ɗin da suka yi a salla, nan ya ci karo da na Hamra da ya Mubeen. Wata ajiyar zuciya ya sauƙe cikin ransa yana ƙara ganin yadda suka mugun dace da juna ita da Ya Mubeen ɗin, godiya ya yi wa Allah da ya kawo Humaira cikin rayuwarsa don kuwa silarta yaji ba ya son shiga tsakanin masoya biyun duk da cewa a da ya ƙudiri aniyar mallakar Hamra ɗin duk rintsi duk wahala. Amma da shigowarta ta haskaka masa abun da ya shige masa duhu har ma ya fahimci cewa ba son Hamrar yake ba. Duk abun da yake kuma Humaira na lura da shi, sai dai ba ta nuna hakan ba ta ba shi dama ne kawai na yankewa kansa hukunci mai ɓillewa.
Ai kuwa ya yanke ɗin, don a ranar ya samu Daddynsa da batun fasa auren Hamra, duk da Daddy ya kaɗu amma ya buƙaci dalili, nan kuwa ya sanar da shi cewa akwai wanda Hamrar take so, da ya bukaci sanin waye bai ɓoye masa ba.
Daddy ya ji babu daɗi amma da labarin cewa akwai wacce yake so a yanzu sai yaji daɗi tare da tambayarsa wace ce, bai kuwa ɓoye ba ya sanar da shi. Cikin nuna jin dadi yayi ta saka musu albarka .
Satinsu guda suka fara shirye-shiryen dawo
wa Lagos, sai dai kuma dawowar iya Ra'isa da Humaira ne, don kuwa Daddy ya ce ta zauna zai nema mata school ta ɗaura karatunta tun da ba aure za ta yi ba yanzu. Hakan ne ma yasa ta ɗan ji sanyi a ranta. Ranar da za su tafi kuwa har da kukanta, duk da su ma sun ji babu daɗi amma fa sai da suka tsokane ta, nan dai Hamra da Ya Ja'afar da suka musu rakiya shi ma sai tsokalar Tata yake. Sai da suka isa suka ƙira, sosai Hamra ta matuƙar ji daɗin isarsu kuwa.
Ko da Ya Mubeen yaji cewa ba da ita aka dawo ba ji yayi kamar yayi hauka don gani yake kamar abun da Ammiey ta faɗa zai iya faruwa, ai kuwa idan aka ce za a aurawa Babe ɗin da wannan Ja'afar guntun tabbas ba zai bari ba. Kamar zai yi kuka ya ja ya kirata, nan ya rufe ta da fadan da ba ta san dalilinsa ba. Ita kam ma dariya ta ba shi don ta harbo jirginsa, cike da son kular da shi kuwa tace ai Daddy me yace ta zauna su daidaita kansu ita da Ya Ja'afar.
Tsabar ɓacin ran da ya ziyarce shi bai san lokacin da yayi cilli da wayarsa ba. Ai kuwa abun da bai sani ba Ammiey na kallonsa, don ta zo wucewa bedroom ɗin su Ra'isa ta hango shi. Ajiyar zuciya kawai tayi ta saki wani gauron numfashi sannan ta wuce.
*React and share fisabilillah.*
[9/15, 7:29 AM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_