Showing 126001 words to 129000 words out of 134378 words

Chapter 43 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

75

_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER FOURTY*

Kwanci tashi, in ji hausawa, wai, asarar mai rai.
Haka dai su Hamra aka ci gaba da karatu, har ya rage saura wata guda bikin. Babu tsammani kuwa wata rana sun dawo daga lectures a gajiye Aunty Murjanatu na dama musu wani magani cikin cup, ƙarar wayar Hamra ya sa ta yi sauri ɗaukowa, ganin _Everbloom_ ɗin ta yasa ta yi saurin picking, a gajiye ta gaida shi ya amsa, bayan sun gaisa yace "Ina jiran ki ki Turo min address ɗin gidan da kike"
Idanuwa waje tace "Kai! Wai saƙo za ka aiko min?" Ta tambaya don son tabbatar da abun da kunnuwanta suka jiyo mata na surutun mutane da Hausa. Caraf kunnenta ya jiyo mata amsar tasa da ta saka ta daka tsalle
"Ga Ni nan a schoo ɗin ku, ga kuma yaro tare da Ni, please ki yi sauri zai rako Ni har gidan"
Ai ko amsa ba ta ba shi ba ta katse kiran tare da danna address ɗin via SMS, sai da ta tura tukun ta kira layinsa, shima bai ɗaga ba ganin saƙon sai kawai yayi wa saurayin da zai raka shi magana.

Can ba a daɗe ba sai ga kiran Ya Mubeen, lokacin Hamra ta baza wanka tana shafe jikinta da mayin da take ganin ba shi da ƙamshi cikin wanda suke amfani da su yanzu. Picking tayi ta kara a kunnenta.
"Ga Ni ƙofar gida mai blue gate."
Yana faɗin haka kuwa ya katse kiran. Turare kawai ta fesa sannan ta mulka lip gloss a lips ɗinta. Sa'adatu da ke haɗa tray ɗin abinci sai tsokalarta take.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauƙe da ganinsa, ai kuwa babu ɓata lokaci ta ƙarasa kusa da shi tana masa sallama. Amsa mata yayi, sannan ta gaishe shi, da ya amsa tsabar farin ciki maimakon ta ce masa ya shigo sai ta tsaya tana rufe fuska ganin yadda yake wani bin ta da kallo.
"Ke soulmate haka ake tarban baƙi? Tun daga uwa duniya na zo amma ba za ki tarbe Ni ba?"
Turo bakinta tayi ta fara magana a shagwaɓe "To ba kai ne kake kallona ba?"
Yadda ta yi sosai ya sosa masa ransa, babu ɓaga lokaci kuwa ya ci gaba da kallon nata yana faɗin
"To sai kuma ki bar Ni babu tarba?" Ya ƙarasa yana kokoyon muryarta. Ɗan tsalle tayi kaɗan tare da faɗin "Allah ba na so."
Saita kansa yayi yace "Oh yea, ki yi yadda ya kamata"
Bakinta gaba tace "Mu je ciki"

Tana gaba yana biye da ita har suka shiga gidan, part ɗin da ba a budewa sai in baƙi sun zo suka nufa, tas parlourn yake babu ƙura, sai ƙamshin room freshener da ke tashi sama-sama. Tsayawa tayi bakin ƙofa sai da ya shiga ciki tace "ina zuwa"
Da sauri taje ta kawo masa kayan sanyi, sannan ta koma ta ɗauko trayn da Sa'adatu ta haɗa. Lokacin da ta dawo ma har ya fara shan coconut juice ɗin da Aunt Murja tayi yana lumshe ido. Ciki ta shiga ta zauna a kujerar da ke facing nasa tana faɗin
"Wash"
Ƴar hararar wasa yayi mata yana faɗin "Kamar wacce ta yi wani aiki",
"Na yi mana, yanzu fa dawowana daga school",
Ba tare da ya mayar da hankalinsa kan zancen ba yace
"You look so breathtaking soulroot! Me kike ci ne a nan?"

Ɗan tura bakinta tayi tace "Me kuwa zan ci? Ni da karatu ma ya ramar da Ni?"
Sipping drink ɗin yayi sannan yace "Uhm, na ga wannan, To ya karatun? Hope ba wahala dai?"
"Hmm, to alhamdulillah za mu ce, amma wahala kam muna kwasanta, sai dai Allah ya sa mai amfani ce?"

"Amin, ko dai za a fasa karatun ne?"
Wata hararar ta wulla masa ba tare da ita kanta ta sani ba
"Yea" ya faɗa yana ɗage mata gira
"Ai wallahi sai na gama, ba ka san da yaya na fara gane karatun ba, sai da na fara enjoying za ka ce na bari?"
Yadda ta haƙiƙance tana maganar yasa yace
"Yi haƙuri Madam! Mayar da wuƙar taki, wasa nake"
Murmushi ne yayi escaping kan soft lips ɗin ta tace "Ya dai fi maka."
Ganin ya aje cup ɗin hannunsa yana kan tray ɗin tare da ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yasa ta ɗan dube shi irin kallon nan na me kake nufi?
Gira ya ɗage mata tare da faɗin
"Maam ya dai?"
"Me kake nufi?" Ta amsa masa da tambaya.


Ƴar hararar wasa ya mata yana faɗin
"Tambayarki fa nayi shine kike mayar min amsa da tambaya?"
"I'm sorry" ta ba shi amsa tana haɗa hannayenta biyu wuri guda.
Shiru yayi bai kuma cewa komai ba. Abinci tayi serving ɗinsa ta miƙa masa gabansa
"Ce miki nayi ina jin yunwa?"
A shagwaɓe tace "Ai na san kana ji, kuma fa wallahi sai ka ci, in ba haka ba na faɗawa Aunty Murjanatu."
Idonsa ya ɗan buɗe sannan yace "Sirrin mijin naki za ki fitar ko?"
Bakinta gaba tace "To ba dai ya ƙi cin abinci ba?"
"Hmm"
"Za ka ci ko?"
Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Kukan shagwaɓa ta saki wanda yasa shi ba shiri bin ta da kallo. Tsarguwa tayi da yadda idonsa ke yawo kanta tace "Ni ka daina kallona"
Murmusawa yayi yace "Ke ɗin ta waye ma tukun?"
Baki zumɓure tace "Kai mana"
"Ah, shi ne kuma za ki ce na daina kallonki?" Ba ta amsa masa ba sai ma bakinta da ta ƙara zumɓurawa.
"Ni dai kawai ka ci"
"To mutum ana masa dole ya ci ne?"
"Idan dai ba ka ci ba Ni ma tafiya zan"
"Ba mu yi maganar ba?"
Ta gyaɗa masa kai
"To je ki mu gani" miƙewa tayi kamar gaske ta nufi ƙofa, da sauri ya ce "Dawo mana Zuciyata"
Ba ta juyo ba sai ta tsaya cak, hakan ya ba shi damar faɗin
"Ki dawo, zan ci"
Fuskarta ɗauke da murmushi ta koma, nan ya fara ci. Tas ya cinye yayi hamdala, nan kuwa ta fara tsokanarsa wai yana so yana kai wa kasuwa, murmushi kawai ya mata yace
"Ba za ki cewa Auntyn naki mu gaisa ba ne?"
"To ba aiki take yi ba?"
"Huh " ya saki wani gauron numfashi tare da dafe kansa
"Wai kam Ni ke ba kya ji ne?"
"To me nayi?"
"Again? Ya Allah! Wallahi kina sa min ciwon kai, duk mutane su bi suyi ta faɗin ba ki da rigima, nan Ni kuma ba kya bari na na sake, Allah ya shirya min ke"
"Amin" ta amsa masa tare da faɗin
"Me yasa ba ka ce min za ka zo ba?"

"Ina so nayi surprising naki"
"Congrats!" Ta faɗa tare da tafa hannayenta "Ka yi nasara, na ji daɗin zuwan naka kuwa"
"Ma sha Allah!Magana za mu yi fa"
"To ranka ya daɗe, ina jin ka"
Hararar wasa ya cilla mata tare da faɗin
"Ammieynki ce ta takura wai sai na ji me da me za a buƙata tun da bikin ya ƙarato"
A kunyace tace "To ai da Ra'isa ka tambaya, Ni ban san me ake yi a biki ba?"
"Hm, shi ke nan! Yanzu dai na yi tafiyar banza ke nan?"
"A'a" ta ba shi amsa a gajarce, gira ya ɗaga mata tare da faɗin "To ya ne?"
Tace "ba ka gan Ni ba? Ba ka yi farin ciki da hakan ba?'
"A'a gimbiya, Ni ban ce ba. Ina ga ma yau Ni kam zan wuce can Jigawa, gobe kuma na bi Flight na wuce. Kin san Ammieyna ba ta son nesa da Ni" ya ƙarashe cikin sigar zolaya. Kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa.

Haka dai suka ɗan tattauna kan yadda komai zai kasance, though ita Hamra abun bai wani ma dame ta, ita dai burin ta shi ne kawai a ɗaura aure ba sai an wani ja abun ba. Suna tsaka da hirar Aunty Murjanatu ta zo suka gaisa da Ya Mubeen. Mutumin da zai tafi ne kafin Magrib har aka fara kiraye-kirayen sallar bai tafi ba saboda yadda hira ta yi daɗi, kiran sallar ne ma ya ankarar da shi, hakan yasa ya buƙaci zuwa masallaci da ya dawo kuma sa yi sallama, tare da Yaron Aunty Murjanatu suka je masallacin, suna dawowa kuma ya ajiye wa Aunty Murjanatu kuɗi bayan fakar idon Hamra da yayi, har bakin mota ta raka shi sannan ta masa sallama tare da addu'ar Allah ya kiyaye. Daga nan ya wuce ita kuma ta dawo.

Sa'adatu ce ta nuna mata kuɗin da Ya Mubeen ɗin ya ajiye tana tambayarta ko wa ita ya ajiye wa? Kai tsaye tace na Aunty Murjanatu ne. Sosai ta nuna farin cikinta kuwa tana ƙara yabawa da Alkhairi irin na Ya Mubeen tare da musu addu'ar zama me ɗaurewa har mutuwa ta raba.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya, sai da ya rage saura sati biyu biki tukun suka ɗauki maternal leave a makaranta, daga nan suka wuce Jigawa don fara wasu shirye-shiryen.
Ta kowanne fanni kuwa shirin ake yi babu kama ƙafar yaro, su Ammiey duka sun dawo Gombe saboda a nan za a yi hidimar, haka su Ummie duk suna nan. Itama Ummie da Ra'isa duka sun sha nasu gyaran jikin sai dai a ce ma sha Allah.

Tun ranar Laraba aka fara didima, duk da cewa ita Hamra nata bikin babu wata bidi'a kamar na sauran, dinner kawai ta amince itama ya Mubeen ya ce yana so ne, ita kuma ta zaɓi tree planting campaign, ranar juma'a kuwa suka je ita da Ya Mubeen ɗin tare da wasu friends ɗin ta da suka mata halaccin zuwa suka dasa bishiyoyi a wata makarantar gwamnati da suke buƙatar hakan tare da addu'ar Allah ya ba su lada ya kuma albarkaci auren nasu.

Ranar Asabar aka ɗaura aurarrakin, biyu a nan Gombe biyu kuma a Jigawa, wanda sai rarraba mutane aka yi tun da abun duk ya haɗa wannan da wannan ne. Daren ranar kuma aka yi dinner ɗin bikin, Sa'adatu, da kuma Humaira ranar aka miƙa su gidajensu, ita kuma Hamra da Raisa sai washe gari suka bi Flight tare da su Ammiey, da kuma mutum goma a ɓangaren kowa suka wuce can Lagos bayan nasihar da Hamra da kuma Ra'isa suka sha daga dangin mahaifansu maza, haka dai suka wuce airport suna sharar ƙwalla yayin da kanunsu ke ƙasa kamar tsoffin munafukai, suna cikin wani irin yanayi ne da ba su iya fasaltawa ba, amma duk da haka, daɗi suke ji ta wani ɓarin tun da duk a cikin gida guda suke, sashe kawai aka sauya musu, Hamra na part ɗin Ya Mubeen na ainihi da ke cikin gidansu wanda yanzu ya sha gyara kamar ba shi ba, ita kuma Ra'isa nata part ɗin bai kai na Hamra ba, amma shi ma a gidan yake kuma ba a ma taɓa amfani da su ba. Mammah ce ta damƙa amanar Hamra a hannun Ammiey sannan Ammiry ta karɓa, ita kam Ra'isa wannan lokacin babu wanda ma ya bi ta kanta. Nasiha sosai Ammiey ta yi musu sannan ta raka kowaccensu nata sashen, ta baro su suna kuka, (Ni Ko nace don ma dai cikin gidanku ne aka kawo ku).


Tun da Ammiey ta fice babu wadda ya ƙara waiwayar kowacce, ganin har Isha ta yi Yaya Mubeen ɗin bai shigo ba yasa ta gyara curtains ɗin ɗakij sannan ta kunna haske, daga nan ta wuce bayi ta yi alwala ta gabatar da salla. Bayan ta idar kuma ta dawo parlourn da ya gaji da haɗuwa ta zauna tana karanta wasiƙar jaki, duk da cewa kuwa fargaba ce fal tattare da ita musamman in ta tuna da irin lectures ɗin da Aunty Murjanatu tayi ta ɗirka musu, haka ka yadda taji ƙawayen Sa'adatu na ta ɓarin baki. A ba zata ƙamshin turarensa ya bugi hancinta, saurin rufe fuskarta tayi da mayafi ba tare da ya lura da ita ba kasancewar bayanta yake kallo.

Sallamarsa ce ta bugi kunnenta, sai dai yadda take jin wata fargaba yasa ba ta amsa ba, hakan yasa ya ƙaraso inda take ɗin ya ɗaura hannunsa kan kafaɗarta, kamar zai ce wani abu ko me ya tuna sai ya fice da sauri, can sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da leda, a yadda ya bar ta anan ya sameta. Ya ɗan bi ta da kallo kafin ya ajiye ledar a gefe ya cigaba da takawa a hankali zuwa yadda take. Ba tare da ya ce uffan ba ya kama laffayar da aka lulluɓe ta da shi ya yaye, ɗagowa tayi ta ta kalle shi kaɗan sai ta maida kan nata ƙasa, Kasancewar akwai yalwar haske yasa ya sanyawa hannunsa da ke haɗe da nata ido sai kuma ya saki guntun murmushi.

Duƙowa yayi ya kama hannun nata ya miƙar da ita tsaye, ita dai Hamada ta ma ƙi yarda ta kalle shi saboda wata irin kunyarsa da ta dira mata lokaci guda da a baya ba ta ji kamarta a tattare da shi ba. Da wata irin murya mai taushin gaske da komawa can cikin maƙoshi ya ce, “Habibty kalle ni mana”.
 Kanta ta girgiza masa alamar a'a. Ƙara sauƙe muryar tasa ƙasa sosai yayi sannan yace, “Why?”.
 Da ƙyar ta iya motsa lips ɗinta, batare da sautin muryar tata ta fita da kyau ba ta ce, “Ba komai”.
Bakinsa ya taɓe tare da jinjina kansa still yana bin ta da kallo, Don gani yake kamar an sauya masa ita, ashe ganinta da yayi jiya kaɗan ne duba da yau?. A hankali ya furta, “Okay, tun da ba za ki kalle ni na, ko na mayar da ke part ɗin Ammiey ne?”.
  
Ai bai ma rufe bakinsa ba ta wani ɗago ta kalle shi. Da ƙyar ya iya gimtse dariyar da ta taho masa, tsoronsa sosai ya hango a cikin ƙwayar idanunta ga yadda ta wani ƙara yin sanyi fiye da da.
“Zaki je kenan?”. Ya faɗa yana riƙo haɓarta dan ƙoƙarin ƙara duƙar da kanta da take. A mamakinsa sai ta girgiza masa kai, idannunta a lumshe. Kafin yayi magana ta cigaba da faɗin, “Akwai baƙi ai a part ɗin Ammiey,"

Furucinta sosai ya ba shi dariya duk da bai dara ba, amma a zuciyarsa sai yace (Childish) a fili kuma yace, “Okay! Ni kuma fa ina zan kwana?”.
Idannunta ta buɗe ta nuna masa stairs. Kallon wajen yayi shima sannan ya ce “To ina godiya, yanzu dai mu je ki taya ni yin salla, sai na raka ki part ɗin Ammiey”.
 Kallonsa ta ɗanyi, ganin yana son maidata wata ƙaramar yarinya. Wai ya manta ba wa ashirin baya? 20+, tana da ilimin addini da na zamani, tana karance-karance sosai duk da cewa ma ta yi aure a baya, amma hakan ba yana nufin wai ta ga komai a zahiri na ne kuma ma tun da ta koma gida Aunty Murjanatu, komai buɗe musu shi take da sunan nasiha sai kuma abun da ta manta ne kawai ba ta faɗa musu dangane da rayuwar aure.


“Miye kuma na tunanin?”. Ya Mubeen ya raɗa mata cikin kunnenta. Ajiyar zuciya ta sauƙe a hankali. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya kama hannunta. Sai ta ƙi motsawa. Dawowa yayi ya tsaya a gabanta tare da faɗin “ko dai goya ki zan yi?”. Kai ta girgiza. “Ɗauka?”, shiru tayi dan saƙe-saƙenta yadda za ta yi ne ya bar ta ta sauƙe sauran gajiyarta. Ganin ta ƙi magana yasa yace “Uhm?” tare da sa hannu ya zare babbar rigarsa tare da hular dama duk sun ishe shi musamman ma da ba sabawa yayi da su ba, gabanta ya dawo bayan ya ajiye su jikin hannun kujera, cak ya ɗagata daga kan kujerar, saurin kallonsa ta yi don abun ya zo mata ne a ba zata. Ido ɗaya ya kashe mata, babu shiri ta kife fuskarta a ƙirjinsa tare da saka hannunta a kafaɗarsa ta dafe cikin ranta tana mamakin Yayan nata da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin zai yi hakan ba, don ko idan ana hirar yadda ake yi a daren aure Ita kam ba ta kawowa cikin ranta Yayanta zai yi hakan.

Murmushi yayi kawai ya fara takawa a nutse kai kace ba mutum ya ɗauka ba. Haka ya dinga taka steps ɗin cike da ƙasaita har upstairs. Kai tsaye ɗakin da ke matsayin nata ya kaita, duk da shi a ransa ya gama sakawa babu batun raba ɗaki, don kuwa yadda yake jin sa a yanzu shi kansa yana mamaki, bai taɓa tsammanin zai so wata macen ba tun bayan rasuwar matarsa. ƙamshin da ya bugi hancinsa ne ya sanya wata kasala ta ziyarce shi. Shi kansa ɗakin ya yi masa kyau, ya kuma yaba da ƙoƙarin familyn nata. Saman gado ya dire ta kai tsaye, batare da yace komai ba ya juya ya fita sai dai bao wani daɗe ba sai gashi ya dawo da ledar da ya bari a parlourn ƙasa tare da babbar rigarsa da kuma hularsa.

  Kusa da ita ya zauna, ya kamo ya haɗe da nasa wuri guda, take wani irin sanyi ya ziyarci duka su biyun. “Barka da zuwa duniyata Rouhy. Gidanki da kuma mijinki maraba da shigowarki, Yadda UBANGIJI ya nuna mana wannan rana, ina roƙonsa ya sa mu ci gaba da kasancewa tare a nan duniya kai har aljanna ma. Aishatul-Hamra, ki ɗauka ke ce Muhammad El-mubeen, idan babu ke, kenan dai shima babu shi har abada.”
 Hawayen da suka zubo mata ne suka sauƙa kan hannunsa, zuba wa ruwan hawayen ido yayi sai kuma murmusa tare da matsota jikinsa ya rungume. Bayanta ya shiga shafawa alamar lallashi. Kafin ya ɗagota ya share mata hawayen da handkerchief ɗin da ya zarodaga aljihunsa yana faɗin “Is ok, kuka kuma ya ƙare haka Matar Mubeen, muje mu yi alwala domin nuna godiyarmu ga ubangijin da ya cika mana burinmu."
 Kanta kawai ta jinjina masa tana sauƙe ajiyar zuciya. Da kansa ya miƙar da ita, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login