Showing 12001 words to 15000 words out of 134378 words
ba ki kai ki kula samarin ba ne ko me? Ina ce su ba abincin suke baki ba ma, don wani ya ba ki sai su saka ki gaba su jibga kamar jaka."
Ganin yadda Umma ta ɗau zafi yasa Hamra murmusawa tace "Don Allah Umma kada ki sa damuwata a ranki, Allah fa ba ya bacci, yana ganin duk abinda ke faruwa, in sha Allah ba zai taɓa ba su galaba a kaina ba." Numfashi Umma ta sauƙe tana faɗin "Haka ne wannan, amma fa ba zai yiwu ina gani ana Abunda bai dace ba kuma nayi shiru, tunda yanzu Hajara ta daina kula Ni ma saboda na faɗa mata gaskiya Inaga ƴan sanda zan kwaso musu daga ita har Sulen idan ya so a karɓa miki haƙƙinki da suke lanƙaye da shi wuyansu"
Idanuwa Hamra ta zare tace "Rufa min asiri Umma in ba so kike a min bugu ɗaya ba har lahira, ki bar su kawai, Ubangiji zai isar min."
Jikin umma sanyi yayi jin kalaman Hamra, hakan yasa tace "Hakane, Allah ya bi Miki haƙƙinki, sannan kuma ki ɗauke Ni kamar mahaifiyarki, duk wani abu da kike buƙata ki min magana in dai haifi ƙarfin halina ba zan samar miki kin ji?" Kai Hamra ta gyada, Umma tace "Kar ki kuskura dukan da suka Miki yasa ki yi wa Nassman wulaƙanci kinji, Kinga duk da Rahama ta aibata ki gabansa hakan bai sa ya janye soyayyarsa gare ki ba"
Da mamaki Hamra ke kallon Umma tana tunanin wa rai ya faɗa mata.
"Kina mamakin na sani ko? To ai Amira tana faɗa min komai da yake faruwa da ke, shi yasa ko kwana biyu kikayiba ki shigoban fiye damuwa ba tunda ina jin halin da kike ciki"
Ƙwallar da ta Zubo mata ta share tana ƙara godewa Allah da ya haɗa ta da Umma, matar da ba ta haɗa komai da ita ba ita ke tausaya mata, wacce ta zama kamar dolenta kuma ta ƙyamace ta, haka Allah yake yi dama. Murmusawa tayi tace "Amma Umma Inna ai ta ce ba zan yi aure ba tunda zan huta a gidan miji"
"Haka ta faɗa?" Kai Hamra ta gyaɗa, Amira tace "ƙwarai Umma, ranar da na biya ta gidan ma a kunnena naji ta faɗa, wai azaba sai dai ta kashe Hamra. To umma ki faɗawa Baban Rahamar mana, hala zai tsawatarwa Inna"
Murmushi kawai Umma tayi cikin ranta tana faɗin inama ace hakan ta faru, Ruwan da ta dundumawa Hamra ƙafa ta ɗauke ta watsa shi tsakar gida sannan tace "Amira ai da hakan za ta faru da sauƙi, ba ki ganin shine silar faruwar komai ne? Shi yake ɗaurewa Hajara gindi shi yasa take abinda ta ga dama."
"To Allah ya kyauta," Amira ta faɗa. Ƙoƙarin miƙewa Hamra ta fara Umma tace "Aa ya naga kin tashi kuma?"
Murmushi tayi tace "Zan wuce kada na ƙara wani laifin"
Umma tace "To Shikenan Hamra, Allah ya tsare, kar ki damu ko a ɓoye zan sa Amira take kai Miki abinci, rayuwa babu abinci ai ba so ake ka rayu ba."
Cikin sanyin murya Hamra tace "To Umma, na gode Allah ya saka da alkhairi " daga haka ta fito daga gidan ta koma gida. Cikin Sa'a kuwa ba ta ci karo da kowa ba, Baffa ya fice, Rahama kuma da uwarta suna ɗakinta, hakan yasa kai tsaye ta shige ɗakinsu ta zauna, da Azahar tayi ta ɗauko ɗumamenta ta ci sannan tayi sallah. Daga nan kuma aka ba ta aiken siyan wake. Da ta dawo ba ta tarar da abinci ba, hakan bai dameta ba tunda cikinta fal yake.
Da yamma ta gama awarar ta fara suya, tana gamawa ta jera awarar a bokitinta sannan taje ta ɗan watsa ruwa tayi sallar maghrib ta fice talla. Yau ma kamar kullum Nassman ya zo wurinta suna hira tana sayar da awararta. Lura da yadda fuskarta ta kumbura yasa ya tabbatar an daketa, saboda ya riga ya san labarin Hamra a wurin Amira. Kallonta yayi cike da tausayawa yace "Hamra" juyowa tayi ta dubeshi tare da amsa kiran nasa.
"Na ga fuskarki ta kumbura, me ya same ki?" Kau da kanta gefe tayi tace "Babu komai fa, yau yinii nayi ina bacci" mamaki sosai ta ba shi ganin yadda take ƙoƙarin ɓoye masa damuwarta. Tausasa murya yayi yace "Ko za ki ɓoyewa kowa damuwarki, zuwa yanzu ya kamata ki fahimci cewa Ni ban cancanci hakan ba, Hamra ba da wasa nake sonki ba, ba kuma da yaudara na zo Miki ba, don Allah miye amfanin ɓoye min ɗin?"
Duk da cewa ba ta ji daɗin yadda yayi reacting ba amma zuciyarta ba ta ba ta goyon bayan sanar da shi ba saita fara ƙoƙarin kawar da zancen da ya mata da faɗin "Na yi tunanin yau fa ba za ka zo ba"
Murmusawa yayi ganin yadda ta dosa hakan yasa yace "Shikenan Hamra, amma bari na faɗa miki abinda ba ki sani ba, babu amfanin ɓoye damuwarki gareni saboda tuntuni na riga na san komai a tattare da ke, don haka Ni na gaji da wahalar da ke da ake yi, yau ba sai gobe ba zan yi wa Babana magana yazo ya nema min aurenki kowa ma ya huta!"
Ido waje take dubansa tana mai rausayar da kanta gefe ɗaya, tabbas da ya san cewa babu wanda zai ba shi aurenta da babu shakka ya rabu da ita, amma ba za ta hana shi ba,za ta bari ya gwada sa'arsa ko Allah zai sa a dace, itama tana fatan hakan, ta gaji da rayuwar duhu da jahilci da take yi a gidan Inna, amma duk da haka ta gode Allah tunda dai ta samu Abunda ta samu a baya, amma dai rashin karatunta shi yafi ɗaga mata hankali ainun!!
Wannan kenan, yau ma Nassman sai da ya jira ta sayar, ya raka ta har gida sannan ya ba ta ledar hannunsa.
Kai ta jijjiga tana faɗin "A'a ka bar shi kawai"
Da kallon me kike nufi ya bi ta yana faɗin
"Ba ki isa ba Hamra, dole ki karbi abun nan saboda kina da buƙatarsa, idan Ni ban miki ba waye kike tunanin zai Miki?" Maganarsa haka take amma dukan da aka mata jiya yasa ta ƙara jijjiga kai tace "Ni dai wallahi tsoro nake ji, ka ga yau ma dukan da Nasha Allah kawai ya sani,ka shafa min lafiya ka tafi da abunka."
A ɗan hasale wannan karen yace "Wallahi sai kin karɓa Hamra, su kashe ki in sun so, in sha Allah komai ya kusa zama tarihi don ko wata ba zan bari ki ƙara a gidan nan ba su kashe ki, zan ɗaukeki na kai ki gida na, na ba ki kulawa yadda ya kamata, na tarauraye ki kamar jaririya. Wallahi a daren nan zan yi wa Babana magana. Don haka karɓi abunki, sai ki kula lokacin da za ki ci, ungo nan!" Kalaman da ya faɗa sun yi tasiri ƙwarai a cikin ranta duk da cewa ta san abu ne mai matuƙar wahala hakan ta faru, hannu tasa ta amsa, tana faɗin "Na gode, Allah ya saka maka da alkhairi" fuska sake yace "Amin amaryar Nassman, ki wuce ciki ko?"
Fuskarta ta rufe da hannayenta tana shigewa gidan da gudu jin ya kira ta da amarya.
*Wannan kenan!*
*TUMUN DARE fans ina kuke? Nace ina kuke? To ku matso yau ku min sharhi, me kuke tunanin zai faru? A ganinku za a yi auren Nassman da Hamra ko kuwa dai su Inna ba za su bari ba kamar yadda suka yi alƙawari, ya kuke tunanin rayuwar Hamra za ta kasance nan gaba?*
*Kada ku manta littafin TUMUN DARE gajeren labari ne kuma kyauta, amma Inaga zan ƙara 2pages akai daga nan kuma ya zama na kuɗi tunda na ga alamar ba za kuke appreciating ɗina ba, in sha Allah littafin zai zama na kuɗi, masu karantawa suna ƙin reacting Shikenan, na gode, wasu za su saya kuma su min comment tunda ku kun ƙi. Thanks*
# Tumun_dare
# Diamond_bhatool
[22/05, 9:55 AM] Diamond Bhatool 🦋.:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER FIVE: Sealed fate , new path*
Yana barin ƙofar gidan kai tsaye gidansu ya wuce, sanin cewa Babansa ya yi bacci yasa ya nufi ɓamgaren mahaifiyarsa wacce ya tarar da ƴan ƙannensa suna zaune suna hira. Sallama ya doka yana faɗin "A'a yau Mama hirar da su Jidda ake ne?" Cikin sakin fuska ta amsa masa sallamar tana faɗin "To yaxa a yi ne ubana, kai kam ai yanzu ba na samun lokacin da za mu yi hira da kai, daga ka dawo daga wurin aiki za ka saɓs wanka ka fice, anya ma ba hira kake zuwa ba?"
Kansa ya sosa yana bin ƙannensa mata biyu Jidda da ƙanwarta Salma da kallo, Gira ya ɗage ganin suna kallonsa suna dariya.
"Ya dai ƴanmata? Kun wani tsareni da ido sai dariya kuke min, nace lafiya?" Ƙunshe baki ƙaramar tayi jin dariyar da ta ciyo ta.
Mamah ce ta dube Nassman ta koma kan Jidda da Salma tana faɗin
"Ku anya lafiyarku kuwa? Kai Nasir ya suke maka dariya? Ke Salma meye hakan?"
Shima dai kallonsu Salman kawai yake yana jiran ji daga gare su. Sai da suka yi mai isarsu tukun suka tsaya. Gira ya ɗage musu, Salma ta dubi Jidda tace "Adda?" Sai suka rufe bakinsu da hannayensu. Mamah da takaici ya ishe ta tace "Ba na son iskanci fa Salma, uban me ya faru kun samu gaba kuna dariya kamar wasu mahaukata?" Dakatar da dariyar suka yi, Salma tace "Mamah babu komai fa, ba ga dai Yaya Nas ɗin ba? Ya faɗa Miki ina yake zuwa da daddare ba ya zama a yi hira kamar da" tana faɗin haka ta ƙara ƙunshe baki tana dariya, dukan da ya kai mata yasa ta miƙe a guje ta wuce bedroom ɗinsu.
Jidda ma miƙewa tayi ta bi bayan ƙanwarta don su zanta. Sai da yaga sun wuce ya gyara zamansa kusa da mamah yace "Mamana Ni na isa na ɓoye Miki wani abu da ya shafe Ni? Ki share yarankin nan duk sai na koya musu hankalin."
Murmusawa Mamah tayi tace "Ina jin ka Nasir, ko dai ka yi budurwa ne ban sani ba?" Kansa ya fara sosawayana faɗin "Innalillahi, Mamah kar dai Salma ta riga Ni faɗa Miki?"
Dariya tayi irin ta manya sannan tace "Ya za a yi Salma ta faɗa min kuma? Ai kawai na fuskanceka ne kwana biyu, ba ka irin daɗewar da kake yi da a waje, dole akwai wanda yake koroka gida da wuri." Murmusawa yayi yana sunkuyar da kansa ƙasa yace "Dama maganar nake so mu yi da ke Mamah kafin na samu Baba"
Fuska sake ta dafa kansa tace "Ma sha Allahu,haka ake so ai, darajar ɗa namiji ai sai da mata, faɗa min wacce mai sa'ar ce wannan?"
Dariya yayi yace "Mamah nine dai mai Sa'a da na samo ta."
Cike da maɗaukakin mamaki ta kalle shi tana faɗin "Allah Nasir?, ƴar gidan waye wannan kuwa?" An taɓo masa wurin da yake masa ƙaiƙayi, marairaice murya yayi kamar wani Maraya yace "Mama ba fa ƴar kowa ba ce, hasali ma tausayinta ne ya saka na fara son ta, don Allah Mamah ki goya min baya mu ceto rayuwarta, wallahi ina son ta."
"Toooo, babbar magana,har da roƙo haka Nasir, ya isa haka, faɗa min dai ƴar ina ce, in sha Allah in ba ta fi ƙarfinka ba zan yi iyakar iyawata naga ka mallaketa."
Nan Nasir ya kwashe duk abinda ya sani game da Hamra ya faɗawa Mamah. Sosai jikinta yayi sanyi ta kuma tausayawa Hamra tun kafin ta ganta. Kallon yadda ya wani marairaice tayi kamar za ta yi dariya tace "Allah sarki, su Nasir an kamu,kada ka damu in sha Allah kamar ka same ta, meye ma sunanta?"
"Hamra" yafaɗa a tausashe.
"Ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairi yana zaɓi mafi alkhairi "
"Amin" ya amsawa Mama.
Gyara zamanta tayi tace "Yanzu dai ka ga Babanka ya riga ya yi bacci, gobe kuma zai wuce Gagidiba, ban san ko zai wuce kwana biyar ba, idan ya dawo in sha Allah zan masa maganar sai a je a nema maka izinin aurenta ko?"
Kansa ya sunkuyar ƙasa yana faɗin "To Mamah, Allah ya ƙara girma. In sha Allah kafin Baba ya dawo ɗin zan sa ta zo ta gaishe ki, in kika ganta na san ba za ki bari na rasa mace irinta ba."
Jinjina kai mamah tayi tace "Lallai Nasir, to Shikenan, sai ta zo ɗin"
Murmusawa yayi yana ƙoƙarin miƙewa, Mamah ta dakatar dashi faɗin, "Au, hirar kenan Nasir?" Kansa ya sosa yana faɗin "A'a Mama zan ɗan zaga bayi ne"
Dariya tayi tace "To Shikenan, tunda ka faɗi saƙonƙa kam babu matsala, mu kwana lafiya." Ko kunya bai ji ba duk da ta gano shi ya saka kai ya fice yana faɗin "Sai da safe Mamah."
*HAMRA*
Tana shiga ta kai wa Inna kuɗinta,daga nan tayi sallar Isha', tana idarwa ta fito a hankali ta ɗauko ledar da Nassman ya bata ta lallaɓa ta ajiye ta a ƙasan jakar kayanta, daga nan ta kaɗe shimfiɗarta ta zube kwance.
Lumshe idanuwanta tayi sannan ta karanto addu'ar bacci a bakinta daga nan ta kwanta ta ɓangaren dama. Awarta kusan uku a kwance amma bacci ya ƙi ɗaukarta, tunani ne fal a ranta, banda kewar iyayenta babu abinda take, tunaninsu take har tana iya gano fuskar Mom da Dad ɗinta suna murmusa mata. She wasted those hours thinking about them, remembering the moments they shared together, the love care and support the showed her. Hawaye ne kawai ke zubowa daga idanuwanta da suke lumshe. Ganin dai baccin ba ɗaukarta zai yi ba yasa ta miƙe zaune.
A hankali ta fito waje ta ɗaura alwala ta fara nafilfilu, tana roƙon Ubangiji da ya kawo wa rayuwarta mafita, a haka dai har bacci ya ci ƙarfinta ta yashe kwance kan tabarmarta, ko hijiabin jikinta ba ta cire ba. Ƙiran asubar fari shi ya tayar da ita daga bacci mai daɗi da ya ɗauke ta, haka kawai take jinta cikin farin ciki maras misaltuwa duk da cewa tana so ta ƙara tariyo mafarkin nata a rayuwar farke amma hakan ta gagara, da haka ta miƙe ta fito tsakar gidan, babu kowa babu motsin komai sai tsuntsayen da ke kan bishiyar yandi sai kuma ganyen da ya zubo ƙasa. Numfashi Hamra ta sauƙe daga nan ta nufi bayi ta ɗauro alwala. Tana yin salla ta kama aikace-aikacen da ta san nata ne, sai da ta gama komai tukun ta ɗebo ruwan wanka, tana yin wanka ta sauya zuwa wata orange and sky blue coloured atamfarta wacce ta gama koɗewa ta yi haske sosai. Cikin kayayyakin da kwanaki Nassman ya ba ta ta dauko Vaseline ta mulka, ta shafa powder, tas ta fito kamar jinin Arab yayinda fuskarta ke bayyana tsantsar farin cikin da take ciki duk da cewa ita kanta da za a sa mata wuƙa ba ta san dalilin wannan farin ciki ba.
Can wuraren ƙarfe takwas suka fito suka gama baza ikonsu, Rahama ta kwaso kayan wankinta ta zubowa Hamra su kan shimfiɗarta tace "Ki wanke min su ba Ni da kayan sakawa."
Ba tare da nuna kin jin haushin Abunda tayi mata ba Hamra tace "Da wane sabulu zan Miki to?"
"Ki tambayi Inna" tana faɗin haka ta bar Hamra da kayan wankin a gabanta. Kamar ta rausa ihu tace "Shegen nuna isa kamar su kaɗai ne suka mallaki gida, mtsss" da haka ta miƙe ta kwashe kayan ta fita da su waje. A wurin tambayar Inna sabulun ma sai da taga ta karɓi bugu kamar jaka tukun aka ba ta kuɗin Omo ta sayo ta wanke. A hakan ma ba ta tsira ba da Rahama ta dawo daga bidirinta sai faɗa take wai kayan ba su wanku ba. Cikin jin haushi Hamra ba ta san ta ce
"Idan ba ki godewa Allah ba Shikenan, ana Miki kamar ba a yi, mtsss" taras ashe a kunnen Rahama ta faɗi ai kuwa a harzuƙe ta yo kan Hamra, Hamrah na ganinta tayi sauri ta miƙe a guje, wurin ƙoƙarin cafko Hamra Rahama ta sule ƙasa ji kake Timm, kamar faɗuwar ƙato.
Ihun da ta cilla ne yasa Hamra waiwayowa tana dubanta ido waje, dariya ce ta suɓuce mata, ganin har lokacin Rahama ba ta miƙe ba yasa Hamra aika mata gwalo, a kan idon Inna hakan ta faru wacce ta shigo duba Rahama jin irin ihun da take. Rahama da Inna ta gani yashe yasa ta buɗe baki tare da riƙe baki.
"Lafiyarki kuwa Rahama?" Ba ta juyo ta kalli Inna ba saboda ita kaɗai ta san zafin da take ji sai dai Muryar Inna da taji yasa ta ƙara tale baki tana ihu. Da sauri Inna ta ƙaraso tare da tsugunnawa kusa da Rahama ta kamo hannayenta. Fizgesu tayi da hannun Innata ci gaba da kuka ita dai Hamra tana ganin ikon Allah, ga abun dariya amma babu damar hakan don yanzu sai Inna ta laƙaba mata sharri ta kuma buge ta.
Kamar Inna ta san me Hamra ke tunani ta juyo wurinta tace "Ke Hamra'u me ya sami Rahama ?"
Ajiyar zuciya ta sauƙe ashe dai Inna ba ta ga gwalon da tayi wa Hamra ba. Fuska ta marairaice tace "Wallahi Inna ban sani ba, Nima ihunta na jiyo daga waje shine na shigo na gani amma ta ƙi kula Ni."
Yunƙurin tashi Rahama tayi a matuƙar fusace sai dai tana shirin miƙewa