Showing 84001 words to 87000 words out of 134378 words
sauri ta dakata tare da juyawa tana tsurawa Nihla da ke tahowa wurinta da gudu. Bayan ta iso ta rungume ta tana farin ciki, ji tayi ina ma su kasance tare saboda yadda zuciyarta ke jin wani irin sukuni a kasancewarta da Nihla. Masallacin suka tafi tare suna ƴar hirar su wacce kusan duka Nihla na mata maganar Ammiey Ra'isa ne tana faɗin wai suna kama da ita. Shashantar da zancen tayi duk da cewa zuciyarta da farko ta fara hasaso mata abun da ba shi ne ba. A nan suka yi salla suka fito waje, wani wuri suka samu suka ci gaba da hirar su. Ba su yi tsammanin komai ba sai ga CEO a kansu yana bin su da kallon za ku sani. Hamra wacce ta fara lura da tsayuwarsa sosai ta tsorata tana zazzaro idanuwa.
"In...in...Ina yini" wani banzan kallo ya aiko mata tare da faɗin "Ke waye? Waye ke nace?" A zafafe. Jikinta na rawa tace "Ba muguwa ba ce ni....Na rantse maka, Ni ba muguwa..."
"Me na tambaye ki? Ke wacece? Don't let me repeat myself." Nihla ma wannan karon ta tsorata da yanayin Abie ɗinta, take ta ƙanƙame Hamra tare da cusa kanta a cikin Hamra tana jujjuya kan nata.
"Ni maa'aikaciya ce, ina share-share a nan!"
"Ƙarya kike!" Ya dakatar da ita a tsawace
"Ina shaidar ki?" Cikin ikon Allah ta fito da I.D card ɗinta jikinta na rawa ta zaro shi daga cikin rigarta da ta cusa. Karɓa yayi ya kalla tsawon wani lokaci sannan ya miƙa mata yana faɗin "Za ki bar aiki a nan...." Bai ƙarasa ba Hamra ta janye Nihla da ta ƙanƙameta gefe sai ga ta gaban CEO Mubeen durƙushe har tana taɓa ƙafafunsa da ke cikin cover shoe mai tsada da kuma kyau.
"Don Allah Sir, kar ka min haka wallahil-azim Ni ba muguwa ba ce, ban zo da komai ba sai don na nemi halalina, kar ka durƙushe samun mabuƙacin da ke ƙasanka na roƙe ka da Allah!"
Ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo tare da fashewa da kukan da ya fi na farko.
Abun mamaki mutane ne kusan goma maza da mata suka kewaye su tare da kallonsu, abun da ya ɓata kuma ba sa jin Yaren da take maganar da shi ko kaɗan.
Janye ƙafarsa CEO Mubeen yayi don ganin yadda ƙarfi da yaji yarinyar ke son saka zuciyarsa yin rauni ala dole sai dai bai kai ga matsawa ba yaji Nihla ta ƙanƙame shi tana kuka
"Abie....."
"You see?" Ya faɗa a kausashe yana nunawa Hamra Nihla da take kuka
"Ki faɗa min uban Meye kika mata har take kuka a kanki? Ki faɗa min me kika mata don ba haka Angel take ba." Ya ƙarasa cikin sanyin murya ba kamar yadda ya ɗauko zancen ba. Numfashi ya sauƙe ya dubi Hamra da ta yi shiru yace "Fine! Tunda ba za ki yi magana ba shike nan! Kin bar aiki a nan. Kuma in wani abu kika yi wa angel ki gaggauta ware shi, if not" ya ɗana mata hannunsa alamun za ki sani, ba tare da ya maida hankalinsa gare ta ba ya ɗaga Nihla a hannunsa tare da barin wurin duk irin yadda zuciyarsa ke lallashinsa akan abun da yayi, amma kuma ɗaga ɓari na zuciyar tasa ya fi ƙarfi shi yasa ya wuce abun sa hankali kwance.
Allah Sarki Hamra, a gurin da ya bar ta a nan ta ci gaba da kukant ba tare da ta tashi ba, su kuwa mutanen take suka bar wurin duk da cewa ba abun da suka fahimta dangane da abun da ya farun. Tabbas yau tana cikin tashin hankali, wannan shi ake kira da ga ci ga kwanan yunwa. Tana farin cikin aikin da ta samu kuma lokaci guda ta rasa shi, wai shin wace irin ƙaddara ne wannan take bibiyar rayuwarta? Anya kuma akwai yiyuwar ci gaba da rayuwarta? Damuwarta ɗaya ce, ba wai neman wani aikin ba, a ina za ta zauna? Ina za ta samu muhalli? Ko ba ta da hankali ba za ta yi kwanan titi ba musamman yadda ta ji ana cewa ana yanka mutane a Lagos ne kamar dabbobi a kuma wuce a bar su a wurin, babu shakka a yanzu in mutuwa za ta zo gare ta, da gudu za ta rungume ta don ta fi buƙatar mutuwar akan rayuwar, sai dai me? Ba mutuwar wulaƙanci take yi wa kanta fata ba! Meye amfanin irin mutuwar da za a bar ka a titi ba tare da salla ba, ba tare da wani ya ma yi tunanin ko da yi maka addu'a ba ne? To waye ma ya san kai Musulmi ne?
Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin ran tana mai yanke shawarar barin Lagos da gaggawa, gara ta koma Isawa, basussukan da ake bin ta kuma tun da Allah ya gani ba ta halin biya a yi mata hukuncin da ya kamata, idan ma kisa ne ita a shirye take. Malam kuma ya sha Allah ya isa cikin ranta ya fi cikin babbar mota saboda silarsa ne komai ma ya faru da ita, ga shi ya saka ta ga al'amarin da ya fi ƙarfin kanta da rayuwarta.
Tana zaune wurin ba ta jima ba taji tsayuwar mutum a kanta,
"Excuse me!" Ya faɗa tare da tsugunnawa kusan ta
Da ido ta bi shi don a halin da take ciki ba ta son ko da furta harafin A ne, shiru ta fi buƙata ko ta samu damar samarwa kanta mafita. Takarda ya miƙa mata, kamr wata maras hankali ta zuba masa idanuwa tare da amsa. Riƙe takardar tayi na tare da ta yi ƙoƙarin fara karanta ta ba don babu shakka ta san ra Meye. Hawayenta ne ya ɗisa kan fefar hakan yasa ta janye fefar a hannunta guda ta kuma share hawayen da hannu ɗaya. Ƙoƙarin miƙewa tsaye ta fara saboda zaman ba shi da wani amfani gara ta tattara komatsanta tasan yadda dare yayi mata. Riƙe hannunta taji an yi an damƙa mata envelope, ba shiri ta ƙanƙame tare da mayar da kallonta ga hannun nata. Muryar mutumin ce ta doki kunnuwanta cikin harshen turanci
"Wannan shi ne ladan aikin da kika yi, mun gode sosai, ki yi haƙuri, CEO ya ce a sallame ki ba ya da buƙatarki a nan." Daga haka kuma ya ja ya tafi.
Karo na farko da Hamra ta ji zuciyarta ta bushe, ta fuskanci ƙalubale iri iri, ta shiga tashin hankali iri iri amma babu kamar wannan, ba ta taɓa jin haushi da kuma tsanar mutum ba irin CEO Mubeen! Ya cutar da feeling ɗinta, ya Kuma ruguza mata gobenta, wannan dalili yasa tayi fatan ko sau ɗaya ita ma ubangiji ya ba ta dama akansa, wallahi zafinsa da taji ko Na Malam da su Baffa iyakaci saboda su dama can ba su ba ta dama ba, amma shi sai da ta samu ya daƙile mata ita a lokacin da ta fi buƙatuwa. A sanyaye ta duba envelope ɗin da ya kasance mai nauyi ta kau da kanta gefe, tabbas da a ce tana da wani kuɗin bayan wannan babu abinda zai sa ta karɓa, amma a rashi za tayi amfani da shi uwa uba kuma dama can haƙƙinta ne.
*Alal haƙiƙanin gaskiya matuƙar ba za a yi sharing da reacting ba, zan ajiye alƙalamina a channel, Zan kuma sayar da ƙarshen labarin ne.*
*Share and react fisabilillah!*
*Diamond Bhatool 🦋✍️*
Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY SEVEN: Depressed*
Cikin raunin zuciya Hamra ta nufi masallaci tare da ɗauko trolleynta ta goya school bag ɗinta, Allah Allah take ta bar wannan wurin da aka cutar da zuciyarta, fuska haɗe ta fito tare da jan trolleyn tana tafiya hawaye na zubowa daga idanuwanta. Tafiya sosai tayi saboda rashin sanin ina za ta dosa tana mai tausaya wa rayuwarta.
*MUBEEN's POV*
Suna isa gida Nihla ta fice daga motar Ba tare da jira mahaifin nata ba kamar yadda suka saba, da kallo kawai ya bi ta tare da sauƙe gajeren numfashi. Shi kan shi abun da ya yi sai yanzu yake gagarumin da na sani, amma kuma idan ya duba wani ɓangaren sai ya ga ba shi da laifi, Kawai Dai yana ƙoƙarin kare abar ƙaunarsa daga mutane, amma kuma abu ɗaya da ya tsaya masa a rai shine, muguwar kamanni da yarinyar ke yi da ahalinsa musamman Ra'isa wacce in da za a jera su tare babu shakka za a yi tunanin jini ɗaya ne, sai dai kuma ai an ce kowa yana da mai kama da shi har mutane bakwai a duniya, to la'alla wannan ɗinma dai kamar waɗancan ɗin ne don iya saninsa ba su da wasu makusanta a nan Nigeria. Da haka ya rarrashi kansa tare da fitowa daga motar. A bakin entrance door suka ci karo da Ra'isa wacce ta fito don duba ko lafiya taga bai shigo ba Nihla kuma ta ƙi kulata.
Ɗauke da ayar tambaya kan fuskarta ta ƙaraso sai kuma yanayin nata ya sauya zuwa murna
"So akhy ashe tare kuke da Angel? But what's wrong with her Ina mata magana ta share?"
Kansa ya kawar tare da faɗin "Babu komai." Ya fara ƙoƙarin wucewa ta gefenta. This is uncommon to her, ba haka yanayinsa yake ba duk da cewa a yanzu ya sauya amma ai ba irin sauyawar da har yakan iya ratsa gefenta ya wuce ba as she knew Shi ɗin mutum ne mai ba wa nasa kulawa.
"Akhy" ta ƙira sunansa. Dakata wa yayi daga stepping ba tare da ya juyo ba. Ƙarasowa tayi har wurin da yake tare da fuskantarsa ta kuma riƙo hannayensa biyu yayin da idanuwanta da nasa suka haɗu
"Are You ok akhy?"
Murmushi ya ɗaura kan fuskarsa tare da faɗin "Yea, lafiya nake, kada ki wani damu, kawai dai gajiya ce."
Shirun dai shine mafitarta sanin cewa ba ya son takurawa Amma yanayinsa ya mugun sauyawa. Itama murmushin ta yafa tare da faɗin "alright. Allah ya sa hakan." Ba tare da ya amsa mata ba ya shige ciki hakan yasa ta bi bayansa tana riƙe baki.
Ko da ya shiga da ya tarar Ammiey ba ta parlour maimakon yayi wucewarsa ɗakinsa kamar yadda ya saba sai ya nufi bedroom ɗin Nihla, a daidai bakin ƙofar ya ci birki tare da sauƙe ajiyar zuciya, a hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar sai dai ga mamakinsa ƙofar a rufe, abun da bai taɓa gani ko ji ba, hakan yasa ya sha jinin jikinsa tare da faɗin "Subhanallah" a saman laɓɓansa.
Cikin sanyin murya ya ƙwalla sunanta ta yadda yasan za ta ji kuma ba zai janyo attention ɗin kowa gare su ba amma shiru ba ta amsa ba, kansa ya manna jikin ƙofar tare da ƙara furta "My Angel! My princess!" Shiru dai again, wannan dalili yasa ya ɗan yi knocking door ɗin sai dai a banza. Ƙara kara kunnensa ya yi jikin ƙofar tare da mayar da hankalinsa gabaɗaya kan jiyo motsinsa daga ciki sannan ya ɗauke numfashinsa gudun kar ya hana shi ji daidai. Kamar dai ya sani kuwa, gunjin kukan gudan jinin nasa ya jiyo wanda hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba.
Bakinsa ya saka jikin ƙofar tare da fatan Allah yasa ta jiyo shi sannan ya fara magana
"Angel! Please open the door and let your dad explain."
Tunda ta jiyo maganarsa kawai sai ta bar ɗakin ta nufi toilet tare da ci gaba da kukanta tana mai jin zafin abun da Abiey yayi a hakan ma ba ta da masaniya akan dakatar da Hamra da yayi daga aiki. Jin ta shiru da yayi ya ƙara ɗga hankalinsa. Da sauri ya juya ya nufi stairs kamar zai yi missing wani step ɗin. Bag ɗin da ke ɗauke da duka Spare keys na gidan ya ɗauko ba tare da samun sukunin duba wanne ba ne, sai da ya dire bag ɗin bakin ɗakik Nihla tukunna ya Zuge zip ɗin tare da juyesu ƙasa ji kake sun ba da wani sauti. Birkita su ya fara yana son duba wanne ne ma ɗaya na ɗakin sai dai gabaɗaya tashin hankali ya hana shi fahimtar hakan sai jujjiya su yake kamar mai gauraya abinci cikin kwano.
Fitowar Ammiey parlour ya yi daidai da ɗaukar wasu keys da yayi yana shirin miƙewa
"A'a, ashe kun dawo." Ta faɗa ta tunkaro wurin da yake tare da mamakin ko me yake da uban keys ɗin da ta gani zube
"Me kuma ya faru haka?" Ta tambaya bayan ta iso wurin
Bai ma ji me tace Ba shi kam burinsa kawai wannan ƙofa ta buɗe. Ja gefe Ammiey tayi ta tsaya tana zubawa sarautar Allah ido.
Wata ajiyar zuciya da ya sauƙe sai da Ammiey da ta jingina jikin kujera miƙewa. Murɗa handle ɗin yayi take ƙofar ta buɗe, yana shirin nausa kansa ciki Muryar Ammiey ta dakatar da shi
"Lafiya kuwa Azizy?"
Juyowa yayi tare da fuskantarta ba tare da ya saki handle ɗin ƙofar ba. Yadda yayi da fuska yasa Ammiey murmusawa ta ce "Shikenan" daga haka ta gyara tsayuwarta tana jiran ganin ikon Allah. Ciki ya shiga da sauri yana waigawa ta ko ina tare da kiran sunanta "Angel! Angel, where are you?" Ya waiga dama ya waiga hagu bai ganta ba, hakan yasa kai tsaye ya nufi toilet ba tare da tunanin ko da gaske can ɗin ta nufa ba, duk abun da yake Ammiey na kallonsa da yake bai rufe ƙofa ba.
Abun da Nihla ta manta shine, ba ta rufe ƙofar toilet ɗin ba, hakan ne ya ba wa CEO Mubeen damar shigewa kai tsaya, tsaye ya tarar da ita tana kallon ƙatoton madubin da ke manne a bayin idanuwanta har sun fara ja ga kuma hawayen da ke rige-rigen fitowa daga idanuwanta. Tsanar Hamra ce ta ɗarsu cikin ransa saboda ganin yarinyarsa a irin wannan yanayin wanda zai iya rantse wa bai taɓa ganinta cikin kwatankwacinsa ba. Ƙarasawa yayi tare da lifting nata up ba tare da ya ce komai ba, ita kuwa cilla ƙafafunta ta fara yi tana dukan ƙirjinsa
"Sauƙe ni Abie, I can't hold it anymore, ka sauƙe ni tunda ba ka son..."
"Shhhh" ya ɗaura yatsarsa kan lips ɗinta
"Abie is sorry, please don't punish him for doing nothing wrong." Shiru ta masa ba tare da ta ce komai ba yayin da ta dakatar da bugun da take kai mishi ta kuma bar cilla ƙafafun da take yi.
A kan bed ɗinta ya dire ta sannan ya fara aikin rarrashi amma kamar wa teddies ɗin da ke kan gadon yake yi wa. Dafe kansa yayi tare da furta "Ya Allah" sai kuma ya mayar da kallonsa gare ta.
Yana shirin yin magana Ammiey ta shigo tana faɗin "Yau kuma faɗa aka yi da Abie ɗin?"
Fuskarsa ya sake tare da faɗin "Gane min hanya Ammiey, yau Nihla da rigimarta dama ta tashi."
"Anya kuwa, yaki shalelena, zo ki faɗa min me yake faruwa me Abie yayi Miki kike kula?"
Sum sum sum Nihla ta fara jan jikinta akan gadon ta dawo ta gefen da Ammiey ke tsaye tana tura bakinta gaba. Murmushi kawai yayi cikin ransa yace "i can do anything for you Angel." Sai kuma ya fice a ɗakin ya wuce nasa don kimtsawa tunda solution ya zo.
Bayan fitarsa Ammiey ta dubi Nihla cike da kulawa tace "Me Abie ya yi wa shalelensa ne haka yau ake fushi da shi?" Marairaice fuska tayi tare da share ƙwallar da ta taho mata babu shiri
"Ni Ammiey ba ruwana da Abie."
Ido waje Ammiey tace "Abie ne fa Nihla? Oh yeah tell me! Me Abie yayi kike fushi da shi?"
"Ammiey kin ga, Ammiey Hamra tana da kirki, she's kind and nice, but Abie shouted at her Kamar Zai dukata har Sai da tayi kuka, ba ta da laifi Ammiey, nice Na je wurinta, amma Abiey make her cry, Ba ta mishi komai ba." Sai kuma ta fashe da kuka. Haɗa ta da jikinta Ammiey tayi tare da rungumeta kamar za ta shayar da ita, sai da ta yi kukanta tayi shiru tukun Ammiey ta raba jikinta da nata. Cike da kulawa tace
"Look Nihla, ban fahimce ki ba, who's Hamra da Abiey yayi mata tsawa?"
"She's my new friend, and she she she resembles...."
"Ammiey" Ra'isa ta shigo ciki "So you people are here? Wetin fishy is happening here? Eh?"
Ƙarasowa tayi ganin yadda Nihla ke jikik Ammiey. Da sauri ta kai hannunta jikin Nihla tana faɗin "What's wrong Angel?"
"Ƙyaleta haka nan Ra'isa, ba na son takura, now Baby, tashi ki watsa ruwa ko nasa Taqiyya ta watsa Malie?"
Kanta ta jijjiga, Ammiey tace "Good! Yanzu bari na kawo Miki abinci, yau Abie ba zai Ganki ba har sai ya ba wa Friend ɗinki haƙuri." Daga haka Ammiey ta miƙe Nihla luma ta nufi bayi, to Ammiey, this Nihla's friend ba ta yi tunanin babba b ce, and ita a tunaninta rashin ji tayi Mubeen ya ja mata kunne.
"Is she sick?"
"Who?"
"Baby" ta ba ta amsa kai tsaye, da kai ta mata alamar a'a, daga nan kuma ta ratsa gefen Ra'isa ta fice, baki Ra'isa ta riƙe tana faɗin "in ta yi wari dai za mu ji. " Daga haka ta fice zuwa nata ɗakin, dama abun da ya kawo ta kenan!
Ammiey na kawowa abinci ta jira fitowar Nihla, taimaka mata tayi ta sauya zuwa light expensive wears sannan tayi feeding nata a ɗakin, bayan ta gama ta fita da kwanukan, tana shirin dawowa taga