Showing 57001 words to 60000 words out of 134378 words
kin ga dama ki nemi Abunda za ki biya, in kin ga dama ki tafi prison ba Ni da damuwa. Na san yanzu kin san wa kika aura, kin kuma san illar da Zaɓin TUMUN DARE da kika yi kaina ya haifar Miki, Sai an jima"
Daga haka ya saka ƙafa ya fara takawa cike da sassarfa tana ƙwala ƙiransa amma kamar bai ji ba. Hakan yasa ta dawo ta baje kan katifa tana sakin wani Marayan kuka, daga ƙarshe ta ɗauro alwala ta kai kukanta ga ubangijinta har dai bacci ɓarawo ya sace ta.
Ƙiraye ƙirayen sallar subh ya tayar da ita, bayan ta yi salla ba ta jira gari ya waye ba ta ɗauko takardarta ta fito don nunawa ƴan'uwanta, a tsakar gida ta tarar da su wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba. Ƙarasawa tayi ta gaida su, bayan an gama gaisuwa ta miƙo musu takarda,a tare suka furta "kema kin karɓa?"
"Kuma kun karɓa?" Ta amsa musu da tambaya akan tasu.
Wani irin tsallen murna suka daka yayin da farin ciki ya cika zukatansu suka rungume juna. Da yake har lokacin kuma yaran ba kowa ya tashi ba yasa suka fara shirye-shiryen da tsara yadda za su tafi ɗin, duk da cewa suna buƙatar tafiya amma kuma soyayyar yaransu ta tsaya musu a rai. Daga ƙarshe dai Hamra ce ta lallaɓa su da faɗin "Babu laifi a Tafiyarku ku bar yaran hannun ubansu, inaga wannan tafiyar ita za ta kasance maslaha garemu da kuma su, idan mun tafi a yanzu shine za mu samu damar neman hanyoyin da za mu kassara aika-aikar Malam, daga nan kun ga yaran za su dawo hannayenku." Shawarar da Hamra ta ba su ta yi matuƙar tasiri nan dai suka shiga wanka daga nan kuma suka shirya, dama tuntuni Hajjaju ta yi magana da Aminatu, ta sanar da ita komai da yake faruwa amma hakan bai sa ta ji daɗin tafiyar ba duk da cewa ita ce maslaha yayin da lokaci guda tsanar mahaifinta ta ɗarsu a zuciyarta amma yaya za ta yi?
A ranar da suka shirya don tafiya rant Alhaji Mamman Isawa ya zo don amsar kuɗinsa da ke wurin Hamra, abun ya zo musu a bazata sai dai ita Hamra dama ba ta cire tsammanin hakan a ranta ba hasali ma da tunanin take kwana ta kuma tashi ta san ko ba daɗe ko ba jima dole wannan ranar za ta zo, tare da Hajjaju suka koka al'amarin, duk da cewa Hajjaju ta tsaya kan cewa ba za ta tafi ba tare da Hamra ba amma daga ƙarshe Hamra ta yi convincing nata, nan dai ta musu sallama don bin Alhaji Mamman Isawa police station. Abu dai wasa wasa ya zama babba, don Alhaji Mamman cewa yayi ba zai yarda ba, miliyan goma ai ba wasa ba ce, daga ƙarshe aka musu sulhu kan cewa Hamra za ta ke biyan dubu ɗari-bibbiyu ko wanne wata na duniya har ta gama biyansa. Da haka ta koma gida zuciyarta cunkushe tana tunanin a ina za ta ke samun wannan kuɗin kowanne watan duniya, ta yi kukan ta yi kukan har ta gaji, tun daga yau ta fara ganin gurbin Hajjaju, daga ƙarshe dai ita ta rarrashi kanta ta kuma ƙarfafawa kanta guiwar neman aikin da za ta yi, amma a ina? Aiki ba zai yiwu ba dole sai da wurin aikin, Isawa ƙauye ne, babu wani wuri da za ta yi aikin da za ta tara waɗannan kuɗin. Hakan yasa ta fara tunanin ko ta koma Bauchi wurin Baffa? "A'ah" ta ba wa kanta amsa
"Ba zan koma ba, a da can ma da na zama dolensa ai bai yi min ba talkless of yanzu da ya riga ya gama rufe babina. To ina zan je?" Ta tambayi kanta.
Kanta ta jinjina tare da furta "Akwai mafita" a bayyane.
"Zan tafi wata babbar Jaha, Kano? Abuja? Lagos? Cikinsu zan tafi, akwai masu kuɗi a wuraren nan, akwai kuma masana'antu da wuraren aiki amma kuma ai ban san kowa ba." Ta tsaya tana tunanin mafita daga ƙarshe ta fara bubbuɗe jakarta, kamar wasa sai ga ƙaramar wayarta da Malam ya saya mata lokacin yana neman ta wacce ta ma manta da ita tun tuni. Wata ajiyar zuciya ta sauƙe tare da saurin danna switch ɗin wayar sai dai ba ta kawo ba ba kuma tayi mamakin rashin kawowar Tata ba, shekaru nawa ta ɗauka a kashe? Ta yi farin cikin ganin wayar sosai don ji tayi kamar ta gama biyan kuɗin da ake binta, daga nan ta ci gaba da birkita kayayyakin nata, wani abu ne ya faɗo wanda ke naɗe cikin farar A4 paper, hannunta ta kai don duba menene, a hankali ta ware takardar, Abunda ya bayyana mata yasa ta murmusa tare da faɗin "Alhamdulillah! With this certificate, I can easily get employed!" Nan ta kai WAEC scratch card ɗin bakinta ta sumace shi.
Tabbas Allah ba ya bacci, kuma yana sane da kowanne bawa, taimako da jin ƙansa ga bayinsa ba mai ƙarewa ba ne, da farko Hamra ta sare ga samun ingantacciyar rayuwa amma sai ga shi kwatsam ƙwarin guiwa ya zo mata. Nan take ta fara shirya abubuwan da za ta ɗauka, da yake kayayyakinta duk sun ji jiki, jin jikin ma kuma irin na sosai yasa ta ɗebi masu ɗan dama damar ta saka cikin school bag ɗinta sannan ta saka abubuwanta masu amfani tana zubar da ƙwallar tausayawa kanta, rayuwar da ba ta taɓa tunaninta ba ko da a mafarki ga shi ita ke bibiyarta. Wanka tayi daga nan ta fito tana shafa mai.
Sallama aka ƙwala yaran da ke wasa a tsakar gida suka amsa lokacin da ta gama shafa man ta fito don ganin waye. Wata tsohuwa ce haka amma ba can ba ta ci adonta irin na tsofi ga lallenta da ya sha taki yayi baƙi siɗik, gaida ta Hamra tayi a girmame, nan tsohuwar ta bi Hamra da kallo, hakan yasa Hamra ɗagowa ta dube ta cikin sanyin murya tace "Sai dai ban waye ki ba."
Dariya ƴar tsohuwar tayi tace "Ko za mu iya zama?"
Hamra tace "Laa yi haƙuri fa, kin ga ashe ko wurin zama ban baki ba, ki shigo mana." Ta gama fadar hakan ta juya matar ta biyo bayanta.
Sake gaisawa suka yi a mutunce, sannan tsohuwa ta gyara zama ta mayar da hankalinta ga Hamra alamar akwai saƙo mai muhimmanci sa take son sanar da ita
"Da farko dai sunana Iyan Musa, yau ne karo na farko da na zo gidan nan duk da cewa ina yawan shigowa garin ɗibar ma'aikata"
Hamra ta maimaaita kalmar "ma'aikata" cikin ranta a zahiri kuma ta saki fuska tace "Lale, na ji kince ma'aikata, ma'aikata kamar yaya?"
"Eh ma'aikata" ta faɗa bakinta washe "Kin gan Ni nan, sana'a ta kenan, ina ɗiban yara haka ƴan mata ina samar musu da aiki a can Lagos ko a gidan masu kuɗi ko kuma a wasu wuraren sayar da abinci."
Aniyar zuciyar Hamra ta saki nan take tana ƙara godewa Allah.
"Amma kuma Baba ta yaya kike wannan aiki mai wahala."
Wani iri tayi da fuskarta lokaci guda sannan tace
"Yo abun ai mai sauƙi ne, kin gan Ni nan, na iya Yaren yahudu don tun ina budurwa nake can Lagos ɗin, to kin ga kuwa komai da sauƙi zai zo tunda za a iya ganawa da su ko?"
"Haka ne" Hamra ta ba ta amsa daga haka ta ja bakinta tayi shiru.
Iyan Musa tace "To dama yau da yamma za mu bi babbar motar Lodi ne zuwa Lagos ɗin kawai sai na haɗu da wata maƙockyarmu shine take ce min ai nan ma akwai yara mata, ban san ko za su je aikin ba." Jim Hamra tayi tana dhawara da zuciyarta, tabbas wannan dama ce gare ta da take tsammanin sauƙi daga Ubangijinta idan ta bi ta, to amma itama a gidan wasu za ta yi aiki kenan in ta bi wannan matar? Tana shirin ba wa tsohuwar amsa da a'a babu sai kuma zuciyarsa tace "Kina tunanin za ki ƙara samun wata damar ne Hamra? You better accept it now because opportunity comes at once, kada ki bari ta kuɓuce Miki, idan ma aikin ne ba ki so a gidan wasu you're with your scratch card, za ki iya cire result ɗinki na WAEC, at least kina da wani certificate da za ki iya neman wani aikin da shi ko ba haka ba?"
Maganar da zuciyarta ta faɗa mata ta tsaya tana nanatawa lokaci.guda yayin da ta kuma yi na'am da ita. Hakan yasa bayan kwashe tsawon lokaci tana tunani ta ba ta amsa da
"Babu komai iya, amma fa babu ƴanmata a nan, sai dai Ni, idan kina tunanin zan iya sai na biyo ki mu je, don ina da buƙatar aikin nima."
Girman idonta tsohuwar ta rage tare da faɗin "Ban gane ba, dama wai ke ɗin ba budurwa ba ce ko me?"
Murmushi kawai Hamra ta yi ba tare da ta ba ta amsa ba. Iyan Musa tace "To madalla, yanzu dai ki haɗa ƴan kayayyakinki, da an yi azahar za mu tafi can AZARE, a can za mu sami motar mutumin da yake min wannan mutuncin da dare kuma lodimsa ya cika sai mu wuce."
Nan Hamra ta yi wa Iyan Musa godiya, daga nan ta mata sallama ta wuce, tana fita Hamra tayi sujudus-shukr (sujjadar godiya) tare da yi wa Ubangiji kirari lokaci guda tana ji kamar an yaye mata kowanne irin ƙunci da yayi wa zuciyarta dabaibayi a baya.
Tsabar farin ciki yau ita tayi wa ƴaƴan Malam girki bayan ta sanar da Aminatu cewa za ta wuce itama. Sai da ta ci abincin rana Iyan Musa ta zo, saboda haka Hamra ta fito don su wuce, take suka wuce tare da ƴanmatan garin wanda za su kai goma zuwa bakin titi, cikin Sa'a suka samu motar da za ta je AZARE, nan Iya ta biya musu kudin suka ɗuru ciki, basu wani daɗe ba suka iso Azare, tinda suka shigo hankalin Hamra ya bar jikinta, tunaninta yayi ƙaura daga zuciyarta. Take ta fara tuna irin moments ɗinta a zamanta cikin garin, ta wajen FUHSA TH suka biyo take zuciyarta ta fara tunawa da kwanciyarta a wurin dalilin kaɗarta da Yaya Hamid yayi, mutum mafi daraja da ƙima a rayuwarta wanda ya inganta rayuwar Tata a zamanta da shi, tabbas ba za ta taɓa mancewa da alkhairinsa da kuma ahalinsa gareta ba. Sun cancanci ƙauna daga gareta maras yankewa, a daidai trailer park aka sauƙe su, bayan kowa ya sauƙa ƴan ƙauyen sai kalle-kalle suke yayinda Hamra ta samu wuri ta zauna tana ta tunane-tunane, ji take kamar ta kutsa cikin gari tayi ziyara, to wa za ta ziyarta? Umma ko Ummie? Duk ciki a yanzu ba ta buƙatar ɗaurawa kowa nauyinta saboda haka ta fi buƙatar ta inganta rayuwarta a yanzu tunda tana da ƙarfin yin hakan, fatanta dai Ubangiji ya taimaka mata.
A hankali ta zaro wayarta da ke ciki aljihun jakarta da ke maƙale bayanta, wani shago da ke opposite da wurin ta tsallaka titi ta nufa, a mutunce suka gaisa da saurayin da ke ciki sannan ta dube shi tace "Yayana don Allah ɗan saka min wayar nan a caji ko za ta kawo don kusan shekaru biyu tana kashe."
"Ok Babu damuwa" daga haka ya amshi wayar ya saka mata, cikin ikon Allah kuwa ta kawo, nan ya faɗa mata, a wurin tace "Don Allah ko za ka iya siyanta ka ba Ni kuɗin ina da uzuri mai muhimmanci Kuma ban san inda ake sayarwa ba"
Ba tare da ya musa ba yace "Babu komai, nawa za ki sayar min?"
"Ko nawa ka saya na sayar"
"To ma sha Allah, ana sayar da sabbin su dubu goma sha huɗu zuwa sha biyar yanzu, na ga kuma takin ma kamar sabuwa ce."
Da kai ta masa alama da "E"
Yace "To yanzu dai tunda ba a kwali take ba zan siya dubu goma sha biyu tunda naga kamar a buƙace kike da kuɗin"
Da sauri tace "babu komai, na sayar maka, na gode, ka cire min SIM ɗina sai ka ba Ni."
Take ya ƙirga dubu sha biyu ya miƙo mata da kuma SiM ɗinfa da ya naɗe mata cikin wata paper. Godiya ta masa sannan ta dawo wurin zamanta.
Tana zaune ko me ta tuna? Ta miƙe ta fara takawa, tafiya mai ɗan tsayi tayi kan titin sannan ta tsaya a wani Café da ke kusa ta miƙa scratch card ɗinta aka cire mata WAEC result ɗinta, NECO kuma ta bari watarana in da rabo ta fitar, result nata so ma sha Allah, hakan yasa ta biya su dubu ɗaya daga nan suka saka mata a envelope suka bata, tana amsa ta kama hanya ta koma can ɗin tare da adana takardar cikin jakarta. Wuraren Isha' motar da za su bi ta gama lodin taburmai, nan aka tura su cikin motar suka hau kan tabarman, daga nan suka bar garn AZARE don tafiya zuwa Lagos.
*Allah ya tare hanya Hamra.*
*React and share Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY THREE: The Escape*
*This is Lagos!*
Alhamdulillah, sun isa Lagos lafiya, bayan sun sauƙa daga babbar motar Iyan Musa ta sama musu abun hawa dukkansu duk da cewa dai sun matsu amma a haka suka ƙarasa wata ƙaramar unguwa wacce ba ta cika manyan gidaje da kuma masana'antu ba. Daidai wani matsakaicin gida wanda ke yanayi da na haya suka sauƙa sannan Iyan Musa ta biya kuɗin, daga nan ta ja su suka shiga. Ɗakuna biyu ne a ciki irin dai ɗakunan haya da muke da su a arewacin Najeriya, nan ta nuna musu ɗaji tace kowa ya huta, another day kowacce za ta haɗa ta da wurin da ya dace tayi aiki, cike da farin ciki ƴan matan suka wuce nasu ɗakin hakan yasa Hamra joining nasu. Abunka da duk sun gaji ko abinci ba su nema ba wasu bacci ya ɗauke su banda Hamra wacce haƙƙin mutanen da ke wuyanta ya hanata sukuni, fatan ta dai Ubangiji ya yassare mata yasa wannan tafiya ta zama silar farin ciki a gareta.
Another day, Iyan Musa ta saka su gaba dukkansu suka yi wanka don ta lura mutanen ƙauyen nan sam ba su don wanka. Bayan kowa ya yi wanka ta dube su tace "Haba ko ku fa?"
Washe baki suka yi suna dariya
Iyan Musa tace "Yauwa, yanzu dai ina so kowaccen ku ta buɗe kunnuwanta ta saurare Ni, aiki kuka zo ba wai hauka ba, kuma kun ga, nan ba ƙajye ba ne, wanka ya da tsafta dole ku koya in ba haka ba duk wacce aka kore ta daga wurin aikinta saboda rashin tsafta ko kallonta ba zan yi ba, ta san ta yaya za ta koma gida, yauwah kuna ji?" Suka gyaɗa mata kai, washe bakinta tayi ta ci gaba da musu bayani daga ƙarshe ta tsoratar da su da faɗin Duk wanda yayi ba daidai ba a nan kashe shi ake a kashe banza. Daga ƙarshe da taga sun fahimci komai tace "Kuma turanci, yanzu dai dole ku koyi Turanci saboda a nan da shi ake magana, ku buɗe ƙwaƙwalenku ku koya, wannan shi ne zai saka ku samu aiki mai tsoka, kun ji ko?"
"E mun ji"
"Yauwah ƴan albarka, yanzu dai ke A'isha, tunda kin iya turanci, za mu je na kai ki wani guda da za su biya ki da kyau idan kin musu Abunda ya dace, ku kuma, tare za mu ke fita restaurant ɗin da nake aiki, a hankali idan kuka fara koyan turanci sai na sama muku gidaje kamar dai yadda na samar wa A'isha, kun gane?"
Miƙewa Hamra tayi bisa umarnin Iyan Musa, daga nan suka fice daga gidan da suke suka hau abun hawa, tafiya mai nisa suka yi kamar za su bar gari tukun suka isa gidan da Hamra za ta yi aiki. Tabbas duniya tana yadda take, don kuwa Hamra buɗe baki tayi tana bin fantamem gidan da kallo kamar idanuwanta za su cire, sosai hakan kuma ya ba wa Iyan Musa dariya tace "Aiki kuwa bai ishe ki ba, sai ma mun shiga."
Ai kuwa dai hakan ta kasance, gida ne iya gida, tun da suka shiga taga uban girman gidan da ba ta iya iyakance shi ta yiwa Ubangiji tasbihi cikin ranta, daga nan suka nufi ƙofar shiga gidan, wani abu Iyan Musa ta danna,babu ɓata lokaci wata mata ta fito wacce itama dai da gani ƴar aiki ce, sosai suka gaisa da Iyan Musa alamun dai sun daɗe da sanin juna daga nan tace bari ta yi wa Madam ɗinta magana.
Shiru sun daɗe a tsaye can sai ga Matar ta dawo tare da faɗin su biyo ta. Babu ɓata lokaci suka bi ta suka shiga ciki fantamemen parlourn sannan dukkansu suka zauna a kan carpet ɗin da ke shimfiɗe a Parlourn. Sun shafe ya kai mintuna bakwai tukun suka jiyo takun takalmi daga matakalar beni, hakan ya ɗauki hankulansu har suka mayar da kallonsu ga staircase ɗin, wata mata ce da ba za ta wuce 35years ba sai dai hutu da jin daɗi zai iya sa ka sanya ta cikin jerin ƴan 20's ba. Sanye take cikin rigar bacci guntuwa zuwa guiwa yayinda Kitson kanta ya Zubo ta bayanta har yana taɓa ababen zamanta, fuskarta yamutse ta ƙaraso cikin parlourn ta samu kujera