Showing 60001 words to 63000 words out of 134378 words
ta hakimce ba tare da ta ce komai ba, hakan yasa Iyan Musa fara gaida ta cikin broken English nata, a daƙike matar ta amsa, nan Hamra ma ta gaida ta cike da girmamawa.
Yamutsa fuska tayi ta dubi Hamra da kai sannan ta mayar da kallonta ga Iyan Musa tare da faɗin "Wannan ce yarinyar da kika samo ɗin?"
Iyan Musa ta amsa mata da "Yes Ma." Kai ta jinjina sannan ta ƙara duban Hamra a karo na biyu, daga ƙarshe kuma ta murmusa tace "Ya yi kyau, daga gani tana da tsafta, Allah yasa tana jin turanci."
"Eh, tana ji."
"Ok" ta faɗa sannan ta ja bakinta tayi shiru, bayan wani lokaci kuma ta ce "Za ki iya tafiya Iya, Amaka!" Ta ƙwala ƙira, take wata baƙa ƴar duma-dumar arniya sanye da mini skirt ta bayyana tare da risinawa har ƙasa tace "I'm here Ma"
"Oh yea, take this Lady to your part and show her everywhere, she's new cook here."
"Ok Ma" Amaka ta amsa tare da kallon Hamra wacce tuni ta miƙe ta saɓa school bag nata a bay, nan suka bar wurin.
Madam ta dubi Iya tace "Is she a Muslim?" Ta faɗa tana son tabbatar da yanayin Hamra wacce ke sanye da mayafi
"Yes"
"Ok, we'll talk on call"
"Ok ma, than you" daga haka Iyan Musa ta wuce bayan wasu kaɗaɗe da Madam ta mika mata.
A can ɓangaren Hamra bin bayan Amaka tayi zuwa part ɗinsu na masu aiki inda tarar da ɗakuna birjik abun har ya so ba ta mamaki, ɗaki na uku Amaka ta shiga, Hamra ta bi bayanta, daga nan ta nuna mata ɗakin wanda ke ɗauke da Gado, wardrobe, mirror sai kuma ƙofar da ta tabbatarwa Hamra cewa toilet ne
"This is your Room, hope you know how to use water system"
Kai Hamra ta gyaɗa mata tare da ajiye jakarta, Amaka na shirin fita Hamra ta jefa mata tambayar "Ni da waye a ɗakin?" Cikin harshen turanci wanda yasa Amaka juyowa jin yadda Hamra ta faɗi maganar a gayance sai abun ya burgeta, normal English nata ya burge Amaka har ta saki wani murmushi tace "Ke kaɗai ne, amma turancin ki ya mun daɗi, muna tare za ki koya min ai?" Hamra murmusa tare da faɗin "E, zan koya miki" daga nan Amaka ta ce "Na gode" sannan ta juya za ta fita Hamra ta ajiye bag ɗinta ta bi bayanta.
Tare suka zaga ko'ina na gidan Amaka na yi wa Hamra bayanin komai cikin harshen turanci yayin da Hamra ke responding from time to time, kitchen shine wuri na ƙarshe da suka shiga, Amaka ta nunawa Hamra komai kama daga kayan aiki da yadda za ta yi amfani da wasun da ta nuna rashin sani a kansu, ta nuna mata komai tukunna suka koma sashensu na masu aiki, nan Hamra ta wuce ɗakinta haka Amaka ma ta wuce nasu saboda a ƙa'idar gidan gejin mutanen da za a iya haɗawa a ɗaki guda uku ne, idan ya kai uku sai dai wadda suka zo a basu wani ɗakik tunda dama sashen ma'aikatan kansa wata duniyar ce. Kayanta ta fara fitarwa daga jakar tare da bin su da kallo saboda yadda suka koɗe suka yi haske, ta daɗe tana kallon kaya daga bisani ta sauƙe ajiyar zuciya tare da jera su cikin wardrobe ta can sama, bayan ta gama ta ciro muhimman abubuwanta ta saka ƙasan kayanta. Daga nan ta miƙe ta nufi bayi. Wanka tayi irin wanda ta jima ba ta yi irinsa ba saboda rashin samun wadataccen ruwa a baya, tana gamawa ta ɗauro alwala ta fito. Ba ta sauya kaya ba saboda wanda ta taho da su ba yawa gare su ba kuma wannan ɗin duk ya fi sauran daɗin gani, hakan yasa kai tsaya ta sanya Hijabinta, sai a lokacin ta tuna da ta bar sallayarta a gida, langwaɓar da kanta gefe tayi sannan ta janyo wani milk color ɗankwalnta ta shimfiɗa tare da gabatar da sallar walaha. (Salatul duha)
*Sallar walaha*
_Sallar Dhuha ita ce Bahaushe ke ce mata "Walha. Sallar Walha sunnace mai karfi wadda aka kwadaitar akan kowane musulmi ya raya wannan Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon Allah ﷺ da bin Umarnin da kuma dacewa da falala da lada mai yawa._
● ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
_Yana cewa:- "Sallar Walha sunnace ta Manzon Allah ﷺ mai karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar da Sahabbansa akan aikita ta"._
_Allah yana cewa:_
ﻭَﺍﻟﻀُّﺤَﻰ
_Allah yana rantsuwa da Hantsi ko Walha idan Allah yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna girmama wannan abu da matsayinsa awajan Allah"._
_Hadisan Manzon Allah ﷺ masu yawa sunzo masu bayyana falalar sallar Walha, ga kaɗ an daga cikinsu;-
1- Yazo acikin Hadisil Qudsy, Allah mai girma da Buwaya yana cewa:- {Ɗan Adam, kayi min Raka'o'i guda huɗu a farkon yini, zai isar maka wannan yinin zuwa karshensa}_
ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ( 475 )
_Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi sallar Walha raka'a huɗu a farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da taimakonsa na musamman._
ﺍﻟﻄﻴﺒﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ :
_Yana cewa; "An isar maka al'amuranta da shagulgulanka da baka kariya da kiyaye ka daga abin ƙi bayan sallarka ta Walaha har zuwa karshen yini,......"._
ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻷﺣﻮﺫﻱ : 2/478
_2- Manzon Allah ﷺ yana cewa; (Jikin mutum akwai gaɓoɓi guda 360, kuma an ɗaura masa yin sadaka akan kowace gaɓa) sai Sahabbai suka ce masa:_
_"Wa zai iya sauƙe wannan nauyi ya Manzon Allah ??" sai Yace;_
_(Goge majina ko kakin da aka yi a masallaci, ko ɗauke wani abin cutarwa daga kan hanya, idan kuma mutum bai samu dama ba, to yayi sallah raka'a guda biyu na Walaha ya isar masa)_
ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ , ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ
_3- Manzon Allah ﷺ yana cewa;_
(Babu mai kiyaye Sallar Walha sai bayin Allah masu yawan komawa zuwa ga Allah, sallar Walaha sallace ta bayin Allah masu yawan komawa zuwa ga Allah)_
ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ .
*Mafi ƙaranci ko yawanta*
_Mafi karancin Sallar Walaha raka'a biyu, amma bata da adadi wajan yawanta ko nawa ka iya ne, amma wasu Malaman sun tafi akan mafi yawanta shine raka'a Takwas kamar yanda Manzon Allah ﷺ bai wuce raka'a takwas ba kamar yanda Hadisin Ummu-hany R.A ta ruwaito._
*Lokacin sallar walaha*
_Lokacin Sallar Wa5lha yana farawa ne daga fitowar rana, ta ɗan daga kaɗan kamar bayan fitowar rana da minti 30 zuwa 45am har zuwa gab da zawalin rana daga tsakiya da ƴan mintina biyar._
ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( /14 306 ))
_Wato kamar; "Daga karfe 7am zuwa 11:45am._
_mafi falala da alkhairin lokacin yin Sallar Walha, shine lokacin da rana ta fara zafi sosai, lokacin da mutane sukafi shagaltuwa da ayyukansa na yau da kullum, kai kuma sai ka shagaltu da gani da Ubangijinka, gab da zawalin rana._
ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ( 6/148 )
ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
_Yana cewa; "Abinda yafi muhimmanci shine idan mutum yana da damar yinta a lokacin mafi falala to yayi amma idan baya da dama to ya yi ta a farkon yininsa, amma yinta lokacin da rana tafara zafi sosai yafi"._
_Daga Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tace; Manzon Allah ﷺ yayi Sallar wallaha, sannan yace;_
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ , ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ , ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
_"ALLAHUMMA_GHFIR LI, WA TUB ALAYYA, INNAKA ANTAT TAUWABUR_RAHIM" har sai da ya fadi hakan sau 100._
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻷﺩﺏ ﺍﻟﻤﻔﺮﺩ
ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 619 .
● ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
_Yana cewa: "Sallar walha idan lokacinta ya wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci kayyadadde"._
● ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
_Yana cewa: "Sallatul Ishraki wato Sallar hantsi itace sallar walha afarkon lokacinta, kuma sunnace ta kowace rana"._
_Allah ka bamu ikon kiyaye wannan sunnah mai girma.🤲_
*Dawowa cikin labari*
Tana idarwa ta yi ƴan addu'ointa tare da roƙar Ubangiji da ya haɗa ta da alkhairin wannan aiki ya kuma kare ta daga sharrin dake cikinsa, sannan ta kawo sauran buƙatunta ga Ubangiji yayin da take zubar da ƙwalla tana mai ƙasƙantar da kanta ga ubangiji, ta daɗe tana addu'oin daga bisani ta tashi tare da naɗe kwalinta da ta shimfiɗa, kamar a fuzge ta hango mutum tsaye bakin ƙofa, cike da mamaki ta mayar da kallonta wurin, "Amaka?" Ta faɗa cikin sigar tambaya. Murmushi Amaka ta saki tare da ƙarasowa wurin da Hamra ke tsaye tana murmusawa.
"Sorry Amra" ta faɗa tare da haɗa hannayenta biyu, "Na shigo without notice, kin ɗauki hankalina ne da bautarki, na ga kina ta yi amma ba ki san na zo ba."
Itama murmushin ta mayar mata bayan jin yadda ta nuna kuslurenta,a nutse tace "Babu komai, ina salla ban san kin zo ba, akwai wani aiki da zan taya ki ne?"
Fuska sake Amaka tace "No, Babu komai fa, kawai dai na zo duba ki ne na tarar kina abun nan na Muslims, ko me yasa hankalinku ke tafiya ga bautarku in kuna yi bayan ba kwa ganin wadda kuke wa bauta?"
Murmushi Hamra tayi lokaci guda kuma ta ji daɗin tambayar ta Amaka yayinda cikin ranta take fatan Amaka ta shiga daga cikin hasken addinin Allah. Bayani ta mata dalla-dalla har sai da Amaka ta fahimta, sosai jikinta yayi sanyi lokaci guda kuma taji ƙaunar addinin musulunci sai dai kuma ba ta isa ta fara gugin converting zuwa Islam ba saboda ba ita ke iko da kanta ba, amma dai ta sa a ranta cewa watarana sai ta shiga cikin Muslims itama, daga nan wani ɗan sabi da yarda ya shiga tsakanin Amaka da Hamra, suna gama zantawa Hamra ta tambaye ta babu aiki ne? Fuska sake Amaka tace "Ai an riga an gama, sai dinner kuma." Wannan dalilin yasa Hamra ba wa Amaka wuri keɓaɓɓe a ɗakin ta zauna suna zantawa, a nan ne Amaka ke sanar da ita cewa ita ɗin ma marainiya ce, a wurin step mom nata take, ita ce ma ta Turo ta aikin kuma kuɗin ma ita ke karɓewa in lokacin salary ya yi. Ƙarin experience, kenan dai kar ka ga mutum cikin fara'a ka yi tunanin ba shi da damuwa, kowanne bawa akwai yadda Ubangiji ke jarabtarsa, yayin da jarabawar wani ta kere ta wani, sai dai kuma, jajirtacce ne kaɗai zai iya ɓoye damuwarsa daga kan fuskarsa, ya ɓoye ta daga jin mutane yayin da zai kai kukansa ga mai sharewa kowa hawaye, wato Ubangiji.
Sun dade tare da Amaka har lokacin zuhr yayi Hamra tace za ta yi salla, Amaka ta mata sallama duk da cewa ta so ta kalli sallar don ba ƙaramin burgeta take yi ba. Can sashen masu gida ta nufa sannan ta je dining ta tsaya tana jiran fitowar masu gidan don serving ɗinsu abincin rana, wannan kaɗai shine aikinta, ta daɗe tsaye can dai Madam Chioma ta fito, Mr. Nwaku mijinta ya fito, can sai ga wata ƴar budurwar yarinya wacce ba za ta wuce sa'ar su Hamra ba ta fito, Joy, family's happiness, biye da ita kuma wani zarton matashi ne fari mai ƙirar samudawa, Emanuel kenan!. Nan Amaka tayi serving ɗinsu tana mai taka-tsan-tsan, tana gamawa ta nemi izini wurin Madam don ta wuce, da kai Madam ta mata alama, har ta kusa barin arean da suke Madam ta ƙira sunanta, cike da girmamawa ta dawo tare da sunkuyar da kanta ƙasa
"Ki ƙira min sabuwar ƴar aikin nan!" Ta faɗa cikeda gadara cikin harshen turanci
Ido ƙasa Amaka ta ba ta amsa da "Ok ma" tare da wucewa, sai data ɗauki nasu abincin ta wuce da shi sashensu, bayan ta sanar da sauran ma'aikatan ta wuce ɗakin Hamra, ko da ta isar da Hamra saƙon Madam a tare suka je wurin Madam ɗin zuciyarta na ɗar ɗar.
Ba ta gama rikicewa ba sai da suka haɗa ido da joy ta aiko mata da wani killer smile, ai babu shiri ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da risinawa ta gaida su ɗaya bayan ɗaya. Daga Mr Nwaku, Joy, zuwa Emanuel duk kallonsu ya koma ga Madam ne don ta musu bayanin wace wannan kuma miye aikinta. Sai da ta gama shan ƙamshinta tukun ta yamutsa fuska tace "She's just perfect" sannan ta dubi Hamra tace "Hope Amaka did orientation for you?"
"Yes Ma" ta ba ta amsa kai tsaye
"Is good, you can go, I'll call you later"
"Ok Ma'am" ta faɗa tare da juyawa har tana shirin faɗuwa saboda kallon da dukkansu ke mata.
Bayan wucewar ta Madam Chioma ta dubi familynta tace
"She's my new worker, za ta ke kula da sashe na da na Emanuel, I think that's all"
Ajiyar zuciya Emanuel ya sauƙe jin cewa he's part of the maids boss Sannan ya lashe lips nasa, baki Joy kuma turo sannan ta miƙe ta haye sama ba ka iya banbance yanayin fuskarta. Murmushi Madam tayi sannan ta wuce nata bedroom ɗin hannunta maƙale da na mijinta, ganin an bar Emanuel shi ɗaya yasa ya murmusa sannan ya miƙe shima.
A ranar da daddare Hamra na bacci taji ƙarar waya a ɗakin nata, a matuƙar tsorace ta tashi tana duba ta ina ne ƙarar ke fitowa, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da furta "Landline here?, then who's calling me at this time?"
Tunawa da ita ɗin ma'aikaciyar gidan ce yasa ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta, Muryar Madam ɗinta ne ta doki dodon kunnenta directing her to meet her at their apartment. Ajiyar zuciya Hamra ta saki sannan ta nufi sashen Madam ɗin tana mai jin zuciyarta na bugawa da sauri da sauri daga ƙarshe dai ta kai part ɗin, kamar wata munafuka ta nufi ƙofar har lokacin buhun zuciyarta bai daidaita ba.
A Parlourn ta ci karo da Madam, kanta ƙasa ta gaida ta sai dai saɓanin ɗazu wannan karon Madam fuskarta sake take, a lokacin Hamra ta fara saƙawa da warwara tare da fatan Allah yasa komai ya tafi daidai. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ta saki jin cewa Madam ɗin na faɗa mata cewa za ta kula ne da part ɗinta da na Emanuel don ba abinda tayi tsammanin ji daga gareta ba kenan, abu mafi daɗi shine Madam ta ce ta burgeta, gobe ta shirya za su je siyayya don ba za ta zauna da waɗannan tsofaffin kayayyakin nata ba a matsayin mai kula da sashenta da na Heartbeat ɗinta. Daga nan ta sallami HTap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY THREE: The Escape*
*This is Lagos!*
Alhamdulillah, sun isa Lagos lafiya, bayan sun sauƙa daga babbar motar Iyan Musa ta sama musu abun hawa dukkansu duk da cewa dai sun matsu amma a haka suka ƙarasa wata ƙaramar unguwa wacce ba ta cika manyan gidaje da kuma masana'antu ba. Daidai wani matsakaicin gida wanda ke yanayi da na haya suka sauƙa sannan Iyan Musa ta biya kuɗin, daga nan ta ja su suka shiga. Ɗakuna biyu ne a ciki irin dai ɗakunan haya da muke da su a arewacin Najeriya, nan ta nuna musu ɗaji tace kowa ya huta, another day kowacce za ta haɗa ta da wurin da ya dace tayi aiki, cike da farin ciki ƴan matan suka wuce nasu ɗakin hakan yasa Hamra joining nasu. Abunka da duk sun gaji ko abinci ba su nema ba wasu bacci ya ɗauke su banda Hamra wacce haƙƙin mutanen da ke wuyanta ya hanata sukuni, fatan ta dai Ubangiji ya yassare mata yasa wannan tafiya ta zama silar farin ciki a gareta.
Another day, Iyan Musa ta saka su gaba dukkansu suka yi wanka don ta lura mutanen ƙauyen nan sam ba su don wanka. Bayan kowa ya yi wanka ta dube su tace "Haba ko ku fa?"
Washe baki suka yi suna dariya
Iyan Musa tace "Yauwa, yanzu dai ina so kowaccen ku ta buɗe kunnuwanta ta saurare Ni, aiki kuka zo ba wai hauka ba, kuma kun ga, nan ba ƙajye ba ne, wanka ya da tsafta dole ku koya in ba haka ba duk wacce aka kore ta daga wurin aikinta saboda rashin tsafta ko kallonta ba zan yi ba, ta san ta yaya za ta koma gida, yauwah kuna ji?" Suka gyaɗa mata kai, washe bakinta tayi ta ci gaba da musu bayani daga ƙarshe ta tsoratar da su da faɗin Duk wanda yayi ba daidai ba a nan kashe shi ake a kashe banza. Daga ƙarshe da taga sun fahimci komai tace "Kuma turanci, yanzu dai dole ku koyi Turanci saboda a nan da shi ake magana, ku buɗe ƙwaƙwalenku ku koya, wannan shi ne zai saka ku samu aiki mai tsoka, kun ji ko?"
"E mun ji"
"Yauwah ƴan albarka, yanzu dai ke A'isha, tunda kin iya turanci, za mu je na kai ki wani guda da za su biya ki da kyau idan kin musu Abunda ya dace, ku kuma, tare za mu ke fita restaurant ɗin da nake aiki, a hankali idan kuka fara koyan turanci sai na sama muku gidaje kamar dai yadda na samar wa A'isha, kun gane?"
Miƙewa Hamra tayi bisa umarnin Iyan Musa, daga nan suka fice daga gidan da suke suka hau abun hawa, tafiya mai nisa suka yi kamar za su bar gari tukun suka isa gidan da Hamra za ta yi aiki. Tabbas duniya tana yadda take, don kuwa Hamra buɗe baki tayi tana bin fantamem gidan da kallo kamar idanuwanta za su cire, sosai hakan kuma ya ba wa Iyan Musa dariya tace "Aiki kuwa bai ishe ki ba, sai ma mun shiga."
Ai kuwa dai hakan ta kasance, gida ne