Showing 111001 words to 114000 words out of 134378 words
umarnin shugaban ƴan sanda aka binciko su kuwa cikin kwana ɗaya kacal sannan aka haɗa da su ana binciken, su kam ba su ɓata lokaci ba suka amsa da cewa ogansu ne ya ba su kwangilar hakan kuma ma tare da shi suka aiwatar da aikin, in fact shi da hannunsa ya harbe su.
"Alhamdulillah" Ya Mubeen ya amsa yana faɗin, "akwai ƙamshin nasara akan abun da muka sa gaba, dubi fa cikin ƙanƙanin lokaci hujjoji sun taru saura a kai case ɗin court, amma Ni fa na fi so mayar da case ɗin Bauchi, a yi duk yadda za a yi kawai a mayar da mu can, ina ga zai fi ko?"
Barr ya gyaɗa kai yana na'am da zancen abokin nasa "Babu damuwa, yau ma za mu tafi kawai, shi kuma ɗan'iskan gobe za su taho da shi bayan sanar da iyalansa da za a yi."
"Ma sha Allah " Ya Mubeen ɗin ya faɗa a gajarce.
Kamar yadda kuwa Barr ya faɗa ya yi bakin iyawarsa wajen cike duk wata takarda da ake buƙata don mayar da su Bauchi, ai kuwa ƙorafi ya karɓu a bisa sharaɗin gobe polices za su damƙa shi a hannun police station na jaharsa. Saboda haka a ranar suka koma Bauchi.
Lokacin da wannan nasara da ke shirin samuwa ta isa kunnen Ammiey sosai ta yi farin ciki, daga nan kuma aka fara shirye-shiryen next step. A yanzu dai shi kaɗai ya rage, wato dangin mahaifin Hamra su san da wanzuwarta a ban ƙasa sannan kuma la'alla a ƙara samun wasu shaidun da za a yi amfani da su akan Baffa not because waɗanda suke hannu ba su kai ba.
Kamar yadda suka tsara Ranar Laraba gabaɗayansu suka yi wa Jahar Jigawa dirar mikiya, ba su wani sha wahala ba wurin gano gidansu Dad tun da dama sanannu ne, tun da suka isa babban gidan da aka sauyawa tsari ake dubansu, da yawa na mamakin me larabawa suke a Jigawa, Jigawa ma a gidan Gayu. Tun kafin su kai ga main house ɗin labari ya isa kunnen Dadda kakar Hamra wacce tun lokacin da aka ambaci Larabawa jikinta ke ba ta cewa makusantan matar Habu ne, yaronta mai tsananin nuna mata ƙauna da kulawa wanda miyagu suka mata yankan ƙauna da shi.
Wani kyakkyawan matashi ne dogo fari mai saje ya ƙaraso ganin baƙi, cike da girmamawa ya ƙarasa yana faɗin
"Sannunku da zuwa, maraba."
Fuska sake Ammiey ta amsa masa da "Yauwa sannu yaro"
Ɗan ƙaramin mamaki ne ya ziyarce shi jin yadda balarabiyar matar ta amsa masa cikin harshen Hausa wanda da za a kashe shi zai iya cewa ba ta taɓa sanin ko da kuwa ma'anar Hausa ba, balle kuma a zo gandun iya Hausar, cikin ƙanƙanin lokaci kuma ya bi matar da kallon sani yana tunanin ina ya san fuskar nan? Caraf ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da matar ƙanin mahaifinsa da ƴan fashi suka bi har gida suka kashe ta tare da mijinta lokaci guda.
A ɗan zabure ya dawo cikin hayyacinsa cikin rawar Murya yana gaida Ammiey tare da ɗan satar kallon ƴanmata biyu da ke tare da ita yana furta ma sha Allah cikin ransa. Amsawa Ammiey ta yi fuska sake tare da tambayarsa "Ko ta ina ake shiga ɓangaren dattijuwar.." ko me ta tuna tayi shiru tun da shekaru sun ɗan ja, ba ta san ko tana raye ba ko kuma Allah ya karɓi kayarsa ba.
Fuska sake yace "Wai Dadda" sai kuma ya washe baki tare da waigawa zai nuna, me ya tuna? Sai ya ce "Mu je na kai ku."
Da "To" Ammiey ta amsa sannan ta bi bayansa, shi kuwa Ya Mubeen fuskar nan ya ƙara tamkewa ganin yadda saurayin ke bin ƴan ƙannen nasa da kallo, har ma gani yake kamar ya fi zubawa Hamra ido in dai ba wai sharrin gani ba.
Saurayin nan ne ya sada su da sashen Dadda mahaifiyar Dad wacce ke zaune a parlour tana lazimi kan sallayarta mai taushin gaske. Ganin mafi soyuwar Jikanta Ja'afar yasa ta saki fuska tana washe bakinta "A Jafaru kai ne? Dama can jira nake ka shigo ka ɗan nemo min goro don yau har wani zazzaɓi nake saboda rashin cinsa..." Shiru tayi ganin babu makamancin expression ɗin da ya saba nuna mata akan fuskarsa ga kuma wasu mutanen biye da shi. Ƙoƙarin tashi ta fara yi don ta tarbi baƙin Ammiey ta yi saurin faɗin "A'a Dadda, yi zaman ki, ba sai kin tashi ba ma."
Idanuwan Dadda ne suka firfito kamar wanda taga wani abun tsoro, take jikinta ya fara ɓari ta kuma ƙame wuri guda kamar status ta kasa motsawa, zama Ammiey ta yi a kan carpet ɗin da ke malale a parlourn, ganin haka ya sa su Hamra ma sulalewa ƙasa suka bi bayanta shi kuma Ya Mubeen har lokacin tsaye yake yana yi wa tsohuwar matar kallon ƙurilla tare da tunanin ko lafiyarta ƙalau kuwa.
Bayan tsawon wasu sakanni da za su kai daƙiƙu biyu Dadda ta zame ƙasa kan sallayarta, sai lokacin bakinta ya buɗe, abun da ta fara shi ne, nuna Ammiey da yatsa tana faɗin "Habibatu!" Cikin yanayi na firgici.
"Dama ba ki mutu ba? Ina yarona Habu? Ina yarona da jikata mai sunana? Ina..." Sai kuma maganar da take tayi miɗik sannan wani irin kukan ban tausayi ya kuɓuce mata.
Da sauri Ammiey ta ƙarasa kusa da ita tana shirin kai hannunta jikin Daddar ta dakatar da ita cikin shessheƙa "Don Allah Habiba ina kuka shiga ke da Habu?"
Ajiyar zuciya Hamra ta sauƙe ganin tsohuwar da kai tsaye za ta iya cewa ta manta ya kamanninta suke sai yanzu da tunaninta ya ƙara hasko mata ita.
Ganin yadda Dadda ke shirin rikice musu yasa saurayin da ta kira da Ja'afar saurin zuwa wurinta yana faɗin "Haba Dadda, ke kawai daga ganin mutane sai ki ce kin san su salon ciwonki ya tashi.."
Da sauri Dadda ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu, take kuma duk gunjin kukan nata ya katse
"Ungo wannan Jafaru!" Ta faɗa tana aika masa daƙuwa
"Baro ka ji ko ubanka mai sunan Alhaji bai isa ya ce min haka ba, ya za a yi ina ganin Habiba matar Habu ka ce min ban ganta ba? Yo idanuna an faɗa maka sun yi lalacewar da ba zan iya gane ahalin Habu ba? Ko dai hassada kake min ganin za su dawo...?"
Yadda Dadda ke shirin rikice masa yasa ya saki murmushi wanda iyakarsa daman fuskarsa, a yanzu babu abin da zai yi da ya wuce ya lallaɓa Dadda ta nutsu kada ciwon ta ya kuma tashi. Cikin sauƙe murya yace "Yi haƙuri Dadda, ki nutsu ki saurari baƙin ko kuma su tafi tun da ba za ki ji su ba..."
"Shhhh" ta ɗaura hannunta kan bakin Ja'afar tare da faɗin "Ya isa" cikin murya ƙasa-ƙasa.
"Na nustu ai, don Allah kar su tafi"
Fuska sake yace "To shi ke nan, yanzu dai ki saurare su." Daga haka Dadda ta gyaɗa kai tare da mayar da kallonta ga Ammiey tana faɗin"Matso kusa da Ni Habiba ki faɗa min inda Habu yake shi da Takwarata"
Rausayar da kai Ammiey ta yi cike da tausayawa tsohuwar ta matsa kusanta tana faɗin "Mun same ku lafiya Dadda?"
"Ke bar wannan gaisuwar haka ki ba Ni amsoshi na" ta faɗa tana katse Ammiey wanda hakan har sai da ya so ba wa Ya Mubeen dariya kasancewar bai saba ganin rikitattun tsofi irin waɗannan ba, kallonsa ya mayar ga Ja'afar sai dai ga mamakinsa gaba ɗaya hankalinsa na ga Hamra, take Zuciyar Ya Mubeen ta doka da wani irin sauti, wani irin baƙin ciki da tuƙuƙi ne suka mamaye rayuwarsa, take tsayuwar wurin ta so gundurarsa ganin yadda Ja'afar ɗin ya kafe ta da ido, cikin zafin nama ya ƙarasa kusa da shi sannan ya dafa shoulders ɗinsa, da sauri Ja'afar ya ɗago tare da duban Ya Mubeen, gira Ya Mubeen ya ɗage masa tare da miƙa masa, hannu, hannunsa kuwa shi ma Ja'afar ya saka kamar yadda Ya Mubeen ɗin ya buƙata, sai kuma ya sa ƙarfinsa kaɗan ya ɗago shi suka fice daga parlourn, duk wannan drama da ake, Ammiey na hankalce da su.
Ajiyar zuciya Ammiey ta saki tana faɗin "Rayhana ce Dadda, ba Hibbatullah ba!"
Ƙanƙance Idanuwa Dadda tayi tana bin ta da wani kallo da ke nuna son gano wani abun, tsawon dakika ɗaya kuma fashe da kuka tare da faɗowa jikin Ammiey tana faɗin "Rahanatu dai yar Habiba, babu shakka ke ce" sai kuma ta janye jikinta tana bin Ammiey da wani irin kallo
"Ashe dai kuna nan? Ku shi ke nan daga mutuwar ƴar'uwarku sai ku yanke zumunci? Allah dai ya hane mu da yanke zumunci."
Cikin sigar lallashi Ammiey ta ce
"A yi haƙuri Dadda, ba wai haka kawai ne muka nesance ku ba, Nima da ɗin mun koma can Ethiopia da zama, yaron can ne ya sa takura muka dawo, sai dai a yi haƙuri da muka dawo ɗin ba mu neme ku ba"
"To, to. To ai shi ke nan, amma dai ba ki kyauta ba, uhm shi ke nan dai, yau ɗin kam kin kyauta da kika ziyarce mu, Allah dai ya tona asirin ashararrun nan da suka kashe Habiba da Habu"
Da "Amin" Ammiey ta amsa sannan wani ɗan shiru ya gitta tsakaninsu. Dadda ce ta dubi Hamra da Ra'isa da kansu ke sunkuye tace
"Oh Ni Assha, wato dai har yanzu akwai bagidadan yara? Yo bagidadai mana tun da ba su iya gaisuwa ba."
Kunya ce ta kama su jin yadda tsohuwa ke neman laƙa musu abu bayan dai ita ce ba ta nutsu ba ma bare su samu damar gaida ta. Tunaninsu ya katse ne lokacin da Ammiey ta ce
"Jira kuke tace ku gaida ta ne Ra'isa?"
"Yo bari na gaida su mana Rahanatu, ai kin san ƴaƴan yanzu sai addu'a, haka nan su Ramla da Sa'adatu ke, duk jikokin da nake da su ma zan iya ce miki iya yaron nan Jafaru ne ke gaishe Ni, yo shi kaɗai ya gaji tarbiyya, yaron mai sunan malamin nan da aka kashe ne, Allah sarki."
"Ina yini" suka gaishe ta baki haɗe
"Lafiya ƙalau yaran nan, ko ku fa? Wallahi bari ku ji" ta ɗan kwantar da murya "Kun ga, kul kuka ɗebi ɗabi'un su Ramla na rashin ɗa'a, da zarar kun ga baƙo ko kun je baƙunta ku buɗe baki ku yi gaisuwa, albarkacin haka sai a dube matsayin mutanen kirki, amma in kuka gumshe baki ai za a yi tunanin marasa ɗa'a ne tifika (typical. Take son faɗi, amma babu damar wani ya ce ba haka ake faɗi ba sai ta hau shi da faɗa wai yana nuna mata iyakarta akan Yaren Yahudu da tun kafin a haifi iyayensu take ji.)
Ra'isa dai kamar za ta dara ganin yadda Dadda ta haƙiƙance tana zubar zance kamar an saka ta, ita mamaki ma take yadda tsohuwar ke a rikice sashe guda na zuciyarta kuma na dasa mata ƙaunar tsohuwar don ba ƙaramin nishaɗi take ba ta ba.
Ƙara buɗe bakin Dadda tayi tare da faɗin "Mun dai ji ko?"
"E" suka hada baki
"To ma sha Allahu, ke kuma Rahanatu kina musu faɗa kar ki zama kamar Hajara da ba ta kwaɓar yaranta, kin ga Sa'adatun nan in dai ba gani tayi raina ya ɓaci ba to fa ba za ta gaida Ni ba. Kin dai ji ko?"
Ammiey ma ta ba ta amsa da "to"
Dadda ta dubi Hamra da Ra'isa sai kuma ta mayar da kallonta ga Ammiey tare da faɗin
"To shi kuma ɗan Balaraben yaron naki baƙin hali ne da shi da ba zai gaida Ni ba ya fice? Allah yasa dai kar ya koya wa yaron nan Jafaru rashin gaisuwa don na ga ya ja shi sun fita."
Dariya Ammiey ta ƙunshe, Hamra da Ra'isa kam wannan karon kasa riƙe tasu suka yi sai da suka dara suna masu haɗa kansu da guiwa.
"Allah dai ya kyauta" Dada ta faɗa tana kyaɓe baki
"Kin ga Ni Ko ruwa ban kawo muku ba tsabar ruɗu, ku yi haƙuri fa, amma Ƴanmata ku fa zan aika ku ɗauko don ba na son Laraba ta zo ta tsaya min nan in na yi baƙi, ungo nan" ta faɗa tana nuna fridge ɗin da ke parlourn tace "Ki duba samansa akwai farantin silba irin na da sai ki zubo muku ruwa ko? Ko dai ba ku san farantin silbar ba? Ta faɗa tana bin su da kallo ganin babu wanda ya miƙe, saurin kaɗa kai Hamra ta yi tare da miƙewa tsaye ta nufi ɗebk musu ruwa. Da ta kawo Ammiey ce ta fara sha, sai su ma suka buɗe jarka ɗaya suka sha.
Bayan Ammiey ta sha ruwa, Dadda ba ta ba ta ƙofar magana ba ta ce "Kin ga ruwan nan ko Rahanatu?" Ammiey ta gyaɗa mata kai
"Wallahi Rahanatu in na ce miki iya Ibrahim ne ke kawo min kar ki musa, gaba ɗaya tun da Habu ya mutu shi ke nan sai abubuwa suka tsaya, komai fa sai na roƙa suke ba Ni...."
"Dadda!" Muryar Ja'afar ta katse ta, fuska ta kwaɓe ganin yadda ya haɗa fuska tace "Yo ƙarya na yi ne za ka zo ka sa Ni gaba? Laaa! Ka dawo da shi kenan"
Sakin fuska ya Mubeen da ya shigo bayan Ja'afar yayi sannan yace "ina yini Hajiya"
Ta amsa masa da "Lafiya ƙalau Balarabe, kai kam ka san darajar manya, ko dai Jafaru ne ya koya maka gaisuwa da kuka fita?"
Ya gyaɗa mata kai
"Ai la shakka, Rahanatu kin ga abun da na faɗa miki ai, Jafaru dai kam ba dai hankali ba"
Ammiey ta amsa mata da "haka ne"
"Amma da Balarabe yau ka burge Ni, Matso ciki, kai ku fitar mun a parlour tun da sai da na roƙe ku kuka gaida Ni, Matso nan ka zauna kusa da Ni "
Hamra da Ra'isa ne suka miƙe sunƙui sunƙui suka yi baya don ba wa Ya Mubeen wuri kusa da Dadda, bayan ya zauna ta dube shi sannan ta ce
"Ka san me yasa na mutunta ka kuwa?"
Ya jijjiga mata kai
"Yo ka min magana mana, sai ka ce wani ƙadangare?"
Dariya sosai ta ba shi har sai da ya murmusa tukun yace "A'a"
Dadda tace "To madalla, wallahi ina so a Kira Ni da Hajiya, amma ka ga karankatakaf ƴaƴan gidan nan da jikoki hassada suke min da sunan bayan tun kafin a haife su Alhaji ya biya mana muka je"
"Gaskiya ba su kyauta ba Hajiya, amma dai ki yi haƙuri." Ya tsinci kansa da faɗa mata. Jij hakan sai Dadda ta rausayar da kai tace "To ya zan yi? Ai dole na yi haƙuri Balarabe, Allah dai yasa ba tafiya za ku yi ba kun dawo kenan?"
Idanuwansa ya zaro waje sai kuma yace "E to, ba yau za mu tafi ba, kina son zamanmu ne?"
Ta gyaɗa kai tana faɗin "E mana, larabawa a gidana ai abun alfahari ne. Bari Jafaru ya kira min Ubansa a sanar da su ko?"
Ya Mubeen ya gyaɗa mata kai.. Ja'afar dai kallonta kawai yake yana jin daɗin yanayin da take ciki yanzu duk da cewa bankaɗen da ba a tambaye ta ba take musu. Mamaki ne kuma ya mamaye shi ta wani ɓarin ganin yadda Mubeen ya sake da Dadda har yake tambayar kansa dama yana murmushi ne?
Ƙarasawa yayi wurin Dadda ya miƙa mata wayarsa da ke ringing. Karɓa tayi tare da faɗin
"Sa min a amsa ƙuwwa"
Ya saka hannunsa ya danna speaker sannan ya miƙa mata wanda ya yi daidai da ɗaga wayar da aka yi.
Bayan sun gaisa ta ce "Dakata haka mai Isma'il, baƙi ne nayi masu muhimmanci, don haka ko me kake yi, yanzu ka ƙira ƴan'uwanka ku hallara don tarbarsu" a ɓangaren can aka ce "To Dadda, za a yi yadda kika ce"
Ta washe baki tana faɗin "Yauwa ko kai fa, su huɗu ne, uwa da kuma ƴaƴa uku.."
Caraf Ya Mubeen yace "Mu huɗu ne, ɗayan ya shiga gari ne"
"Ooo to ka ji Balarabe ya ce su huɗu ne yaran, don Allah ka haɗa ƴan'uwanka duk ka sanar da su"
"To Dadda" ya ba ta amsa.
"Zo Jafaru ka kashe kiran nan haka tun da saƙo ya isa."
*React and share fisabilillah*
*Diamond Bhatool 🦋*
*FATISAHWRITES*
[9/9, 7:18 PM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER THIRTY SIX: Justice and Redemption*
Ƴar hira ce ta ɓarke tsakanin Dadda da kuma Ammiey jefi-jefi kuma Daddan na tsimi Ya Ja'afar da Ya Mubeen da kuma su Hamra wacce har lokacin tunanin Dadda ƴaƴan Ammiey ne.
Suna zaune sai ga matan gidan suna shigowa ɗaya bayan ɗaya suna gaisawa da Ammiey bayan zancen zuwan Larabawan ya riske su, Nihla kuwa tuni ta bi yara sun fice da sashen Dadda.
Girki mai rai da lafiya aka fara shigo musu da shi daga sassa mabanbanta na gidan, sosai suka ci gaba ɗayansu lokacin Barr ma ya dawo daga wurin da ya je.
Bayan sallar Azahar jikokin Dadda ma suka fara zaryar zuwa musamman da suka ji an ce har da haɗaɗɗen guy suka zo, don su maƙasudin zuwansu bai wuce don ganin guy ɗin ba.
Su Hajiya Ramla da Sa'adatu iyayen rawar kai tuni suka fara ƙoƙarin shige masa ba tare da tunanin komai ba don har ga Allah ya riga ya sace zukatansu. A ɓangaren Ya Mubeen sosai yake jin kamar ya make su Sa'a da ke shige masa sai dai babu halin hakan tun da shi yazo wurin da suke, ganin abun nasu ba na ƙare ba