Showing 54001 words to 57000 words out of 134378 words

Chapter 19 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

73

suka ci karo da Lantana, ko kallonta ba ta yi ba ta wuce, wanda hakan ba ƙaramin haushi ya ƙara mata ba. Ta sanar da Hajjaju ta koma ɗaki ta zauna. Bayan an raba Shāhiba, ɗaya daga cikin yaran gidan ta kawo mata rabonta. Bayan ta ci ta tattare ɗakin ta gyara tsaf, sannan ta dawo parlour ta shimfiɗa sallaya ta kwanta.

Tun ƙarfe shaɗaya Hajiya Lantana ta zo mata da batun girkin rana, dariya ma ta ba wa Hamra ganin yadda alo dole take son ƙuntata mata, tunawa da Inna tayi tace, "kamar yadda tayi nata lokacin kuma ya wuce, kema naki zai wuce!"

A ranar dai ba ƙaramar aikatuwa Hamra tayi ba, don ko cin dahuwar dare ba ta yi ba bacci ya kwashe ta. Tun daga wannan rana kuma ta fara girki, safe, rana, dare, duk ita ce, Malam kuwa duk dare sai ya zo mata, amma abun mamaki ba ya iya komai in yana tare da ita, wannan dalilin ya matuƙar ɗaure masa kai, ya kuma yi alwashin gano me ta masa hakan ke faruwa tunda a iya nata bangaren yake fuskantar haka.

Ɓangaren Yaran gida ta fara sabawa da wasu, babu laifi, wasu suna ba ta girma musamman ƴan ƙananan, amma masu wayon cikinsu, musamman yaran Larai da Lantana, rashin kunya suke zuba mata, tun tana daurewa tana haƙuri har suka kai ta bango daga nan kuma ta fara kwafɗarsu, tun ba a je ko ina ba iyayensu suka ce ba su san zance ba. In ta ƙara Dukansu za a hau a faɗo, musamman Lantana, Larai wasu lokutan ba ta cewa komai.

Ganin dai Hamra na rayuwa a cikin gidan ragas babu wata damuwa saboda ba ta bari kowa ya fahimci damuwar ko da kuwa tana da ita. wannan dalili yasa Lantana ƙoƙarin ɗinkewa da Larai don ganin ta cimma nufinta kan Hamra. Cikin lokaci ƙalilan Larai ta jona Lantana, nan fa suka kafa sabon dandalin tsiya a gidan, babu damar kuma a yi magana sai su ce ai sun fi yawa. Hajjaju dai kullum cikin ba wa Hamra haƙuri take, sannu a hankali kuma suka kawo wata Banzar magana wai wanke-wanke da sharar, wankan yara duka da da ba ta yi sun dawo hannunta, da ta nuna rashin yardarta sai suka ce ai sun fi ta yawa, in gadararta ma Hajjaju ne. Gaskiyar su, mijin ba ruwansa da sabgogin gida bare kuma a ce zai dasa dokar da za a bi, mata uku ne bayan ita, su biyu sun yi supporting babu yadda za a yi. Saboda haka wannan sabuwar doka tasu ta fara aiki.

Shikenan fa, Hamra ta zama boyi-boyi, ba ta da lokacin kanta, daga wannan aikin sai wannan, daga wannan sai wancan, salla kanta a gurguje take yi saboda ayyukan da suka mata yawa, lokacin cin abinci sai dai in ga gama girkin dare, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara zabgewa, ta Rame ta lalace kamar wata mabaraciya, kayayyakin sakawarta ma tuni sun mutu, haka dai gabaɗaya komai ya sauya babu tsammani, da farko ta ɗauki rayuwar gidan da sauƙi amma zuwa yanzu wahala ta zame mata. Sallar daren da take yi yanzu ba ta yi, gajiyar ayyuka yasa bacci ke kwashe ta da wuri duk da cewa Aminaye kan taimaka mata da wasu ayyukan.

Wasa-wasa duniyar haka taci gaba da zagayawa, rayuwar ta ci gaba da tafiya yayin da kwanakin mu ke raguwa, a lokacin da Hamra ta cika shekara guda a gidan ta gama lalacewa, wanda ya santa a da in ya ganta a hanya ba lallai ya gane ta ba, ashe wahalar gidan Inna kaɗan ce akan gidan bauta, e mana, bauta, bauta take wa yaran wasu. Su Lantana wannan sauyi yasa suka ci daɗi ita da Larai, nan fa suka mimmiƙe ƙafafuwa tunda babu ɗawainiyar kowa a kan su.

Tabbas wahala kan haifar da jinya babu ko shakka, a hankali in wahala na cin jikin mutum takan haifar masa da muguwar illa, haka ta kasance a ɓangaren Hamra, ɗaurawa da sauƙe tukunya ya haifar mata da matsanancin ciwon baya da kunkumi wanda a da can ba ta san su ba sai yanzu, ta tabbatarwa kanta cewa wannan ɗin ba komai ba ne face wahala, amma dai tana roƙon Allah ya kawo mata sauƙi cikin Rayuwarta.

Ana tsaka da wannan al'amari na ciwuwwuka da suka fara addabarta, wani babban al'amari ya faru wanda ya ƙara dagula rayuwar marainiyar Allah. Rashin samun lokacin kula da salla da kuma addu'o'in da ta sana ya sa magauta samun dama da nasarar fara yin ƙulli a kanta. Tana jin sauyi a tattare da ita amma ta gagara auna irinsa da kuma dalilinsa. Cikin abinda bai wuce watanni uku zuwa huɗu ba ta fara zama kamar mahaukaciya, dama already kayayyakinta duk sun mutu, kala ba su fi uku gareta ba wanda mai gidan yayi musu dukkansu. Damuwa da cunkushewar zuciya sun addabe ta, aikin abinci da take yi yanzu ya gagara, idan ta ɗaura sai abincin ya fara ƙauri an nemo ta, wasu lokutan kuma tayi shirme a girki, akwai ranar da za ta yi tuwo da rana, saboda rashin lafiyar gangar jikinta da ruhi yasa ba ta sani ba ta tuƙa Tuwon cikin miyar daren, ranar dai in gajarce muku babu wadda yaci abinci. Masifa da magana kam ta sha ta daga wurare daban-daban sai dai ita ba abun da ke gabanta kenan ba, in fact ba ta cikin hankalinta da har za ta saka batunsu a ranta.

Karo na farko, na biyu, na uku, ganin dai tabbas ba lafiya ba yasa Hajjaju sauƙe nauyin ayyukan wuyanta. Kowacce aka ba ta kasonta, duk da cewa Larai da Lantana ba su so hakan ba amma babu yadda za su yi tunda dai suma sun gaji da abubuwan Hamran, wata rana ko abinci ba sa ci don Abunda ta yi bai ciyuwa ga mai hankali sai dai yara su ci su kuma su zauna da yunwa. Wannan shi ne mafarin sauƙewa Hamra wahalar gida, ya kuma zama mabuɗin wata sabuwar ƙaddarar Rayuwarta, ƙaddarar da ta jefa ta cikin mummunar rayuwar da sai da ta Kamu da ciwon zuciya ita da kanta ba ta san da hakan ba.

A yau Litinin asussubahi ta zabura ta tashi, babu salla, babu wata ibada ta zura koɗaɗɗen Hijabinta, tana fitowa ta zari slippers ɗinta da shima ya ci ubansa, lokacin babu wanda ya fito hakan yasa daga nan ta nufi ƙofa gadan-gadan gadan-gadan, cikin ikon Allah ƙofar ta buɗe kuma ta buɗu, haka ta fara takawa cikin zauren gidan, ta daɗe tana krwayawa kafin daga bisani ta yunƙura ta nufi ƙofar waje, tana fita ta fara kalle-kalle kamar mahaukaciya, mahaukaciyar ce ma ba kama ba, har gari yayi haske tana tsaye tana kallon duk wani mahaluki da zai wuce tare da ƙara gane wurin, first time da ta fita kenan bayan shekaru kusan biyu, ita kanta tana mamakin me ya fito da ita? Ta yaya kuma ta fito ɗin?.

Ganin yadda gari ya waye, mutane ke famar wucewa yasa Hamra saka ƙafa ba tare da ta san yadda za ta je ba, within some minutes ta isa kasuwa, ganin yadda ake ɗure wake a buhu yasa ta ƙarasa kusan mutanen, kamar wata mai lafiya haka suka gaisa. Bayan sun gaisa ta buƙaci ganin mamallakin waken, take wani mutumi da ba zai wuce 37-38yeasr ba ya bayyana kansa matsayin mai kayan. Murmushi ta saki tace "Ko zan iya magana da kai?"
"A babu damuwa." Tace "Mu ɗan ja gefe mana"
Ba musu mai waken ya ja gefe ta bi bayansa. Sunanta ta faɗa masa shima ya faɗa mata nasa matsayin Alhaji Bubari, nan dai ta yi ƴar magana kaɗan, within few minutes mutumin ya murmusa tare da faɗin "Babu komai, bari a ƙarasa ɗure shi a buhu sai ki samo ƴan dako su ɗiba."
"To na gode, bari na nemo su kafin nan" ta faɗa tare da murmusawa sai kuma ta miƙe ta bar wurin. Bayan wani lokaci ta dawo tare da wasu maza bakwai kowanensu na tura emty kurar ruwa.

Suna ƙarasawa ta musu alama da yatsa, take suka fara loda wannan buhuhunan waken a buhu, tas suka ɗebe, nan ta yi wa Alhaji Bubari sallama ta wuce suna biye da ita, abun mamaki sai ga ta ta dawo unguwarsu, daidai ƙofar gidan Malam ɗin, ita da kanta ta nuna musu tunda za su ajiye a zauren sannan tace "Na gode fa"
Abun mamaki mutanen ba su buƙaci Hakkinsu ba suka wuce abunsu, ita kuma ta dubi buhuhunan waken da za su kai buhu 30 sannan ta saki wata irin killer smile, daga nan ta shige cikin gida, babu wanda ya san ta fita, haka dawowarta ma ta kasance babu wanda ya sani. Saɗaf saɗaf ta ƙetare yaran da ke ta bushasharsu tsakar gidan tare da shigewa ɓangarenta, tana buɗe ƙofar ta shiga, cikin ɗaki ta ƙarasa tare da zubewa kan bed kamar wata maras lafiya, ko dan, maras Lafiyar ce sakamakon wani mahaukacin ciwon kai da ya ziyarce ta lokaci guda, tuni duniyar ta fara juya mata. Nan dai wani azababben bacci ya ɗauketa.

Ba ita ta tashi ba sai wuraren azahar, nan ɗin ma saboda tayar da ita da Hajjaju tayi ne, da ƙyar ta miƙe Hajjaju na aika mata sannu a jejjere. Da ƙyar ta wuce toilet, tana shiga taji ciwon kan ya yi sauƙi kamar dai an fige shi daga jikinta, ruwa ta watso tare da yin alwala ta fito, sallaya ta shimfiɗa ta hau, sai dai me? Tunda tayi kabbara ta gagara karanta komai sai ƙaura da tayi tare da lulawa i zuwa duniyar tunani, abinda ta aikata da safe ne ya dawo cikin kwanyarta, tun daga tashinta, fitarta zuwa dawowarta da uban tulin wake, ko me za ta yi da shi? Waye ya aike ta?, haka ta rinƙa jefawa kanta tambayoyi iri-iri wanda ba ta da mai ba ta amsar su, tana cikin tsayen ne jiri ya kwashe ta, nan ta faɗi ƙasa sumamiya. Shigowar Yusuf da ya kawo mata abincin rana ya tarar da ita yashe yasa ya fara kiran sunanta don sanar da ita ya kawo abincin sai dai shiru. Hakan ne yasa ya tafi abunsa amma abun na cikin ransa duk da cewa ba wani hankali ne ya wadace shi ba.

Haka ya ke barin wasan da suke yi ya riƙa zagayawa lokaci zuwa lokaci amma sai ya ganta a kwance, daga ƙarahe dai ya buɗe samirar da aka zuba abincin ya ga ba ta ci ba. Nan ya je ya sanar da Hajjaju cewa Baba Hamra ta mutu. A firgice ta biyo bayansa suka nufi ɗakin nata, amma ga mamakinta sai ta tarar da Hamra zaune kan sallaya alamar ta idar da salla ne.





*Diamond Bhatool 🦋✍️*
*React and share Fisabilillah.*


[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER TWENTY TWO: Secret revealed*


"Bari ki ji na faɗa Miki." Shiru ya ƙara yi yayin da zuciyar Hamra ta shiga ruɗani da kuma tsoron jin me zai faɗa, tunda ya fahimci hakan ya saki murmushin mugunta ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya sannan ya ci gaba
"Duk wannan basussukan da kika ciyo ba wa kowa kika ciyo wa ba sai Ni! Ni nan" ya nuna kansa cike da izza da taƙama, kallonsa take tana maimaita Abunda ya faɗa don ta fahimta da kyau yayin da kowacce gaɓa ta jikinta ke ɓari, sai da ƙwaƙwalwarta ta ta gama comprehending komai tukun ta miƙe tsaye har lokacin kuma jikinta ɓari yake yi ta nuna shi da yatsa. Cikin rawar murya tace "Kkkkai? Kaine? Kaine ka..." Ba ta gama fitar da tambayar ba ya dakatar da ita yana murmushin da ya saba na mugunta
"Koma ki zauna mana Hamra, so kike ki tambayar Ni Ni ne?" Kai ta gyaɗa masa saboda rashin sanin makama
"Kwarai kuwa, nine, bari na tabbatar Miki. Dama ai na faɗa Miki ke ce Sa'a ta shiyasa ma na aure ki, ko ba haka ba ne?"
Kamar mahaukaciya ta gyaɗa masa kai
"Yauwa ƴar gari, na kuma san kina son sanin ko Ni waye ko?" Kai ta ƙara gyaɗa masa nan yayi shu'umar dariyarsa ya ƙara gyara zamansa bakin katifa.

"Sunana Yusha'u kamar yadda kika sani, Ni haifaffen ƙaramar hukumar Fatigi ne da ke jahar Kwara, mahaifi na Malam Isa, ya kasance mazaunin can, ba shi da wani aiki da ya wuce duba, tsibbu da kuma aiki irin na bokanci, a duban da yayi ya gano cewa a nan Isawa arziƙinmu yake, hakan yasa ya yi wa ƴan'uwansa Magana kan hakan, daga nan suka yi hijira su duka suka dawo Isawa. A ranar da suka iso ba su samu tarba mai kyau ba sai da suka gama cinikin gidan da za su zauna, bayan sun gama suka aje shirgunansu suka nufi fadar mai martaba sarkin Isawa. Nan Babana Malam Isa, tsohon limamin masallaci ya fara bayanin dalilin zuwansu tare da sanar da shi cewa shi ɗin babban malamin addini ne, a can garinsu ma shine limami, take kuwa ƴan uwansa suka goya masa bayan hakan, in taƙaice Miki zance dai aka ɗaura shin kan limancin masallacin da ke hannunsa. Kaf cikin yaran mahaifina babu wanda aka samu jituwa da fahimta tsakaninsu kamar Ni nan, hakan yasa da mahaifina yaga na kawo ƙarfina ya fara ɗaura ni kan wasu abubuwan, tuni na tumbatsa har na wuce shi a wasu fannonin, ana cikin haka kuma Allah ya ɗauke rayuwarsa, bayan an gama makoki da komai aka fara watsewa, nan aka buƙaci wanda zai maye gurbin mahaifina, daga nan nan kuma komai ya sauya don ɗan'uwan mahaifina ya buƙaci wannan matsayi sai dai Ni nan na fi shi buƙatar hakan saboda na duba na kuma gano cewa ina da arziƙi ciki."

"A ranar da ya fitar da ƙaunarsa ga matsayin babu tsammani Nima na nuna nawa so ga matsayin, duk da cewa Ni ne ya kamata na gaji mahaifina amma wasu sun fi goyon bayan shi ya maye wannan gurbi, hakan ba ƙaramin fusata Ni yayi ba, ina da baƙar zuciya dama can sun sani amma suka mance da hakan suka goyi bayansa, sosai na fusata na kuma ƙudiri aniyar yaƙi da duk wani wanda zai kasance shamaki tsakani na da limancin, na yi niyyar kawar da uban kowa don samun cikar burina.
Hakan dai ta kasance, bari na taƙaice miki maganar, Ni da kaina da kuma siddabaruna na hallaka baffana da ƙannensa biyu da suka goyi bayansa na kuma kulle bakin kowa daga magana kan mutuwarsu, har ila yau da nake Miki maganar babu wanda ya ƙara furta uffan a kai."

Duniyar mamaki da tsoro Hamra da ke sauraron Malam ta shiga yayin da ta yi tsit kamar ruwa ya cinye ta. Murmushinsa yayi wanda ya kasance al'adarsa sannan ya ce
"Ya naga kin nutsu? Ko har kin tsorata ne?"
Zazzare idanuwa Hamra tayi ba tare da ta iya cewa uffan ba. Wata dariyar ya kuma yi sannan yace
"Tukunna ma dai, ki godewa Allah ina ɗan tausayinki da na gasa Miki aya zazzafa a tafin hannayenki, amma ke kin san me da me na Miki?"
Kai ta jijjiga bai kuma jira ne za ta ce ba ya ci gaba da magana
"Na daɗe ina duba akanki Inaga tun kina hannun Iyayenki"
"Iyayena?" Ta maimaita kalmar cike da maɗaukakin mamaki
Kai ya gyada yana faɗin "Ƙwarai kuwa, iyayenki, Alhaji Imaduddeen Muhammad da mahaifiyarki Hibbatullah Humaid."
A wannan karon mamaki ne ya cika Hamra banda tsoro, tuni taji son sanin yadda za ta sami wasu nata ta wurin Malam ɗin. Murmushi yayi yace "Zan faɗa Miki amma dai sai na sanar da ke illar da na Miki ta yadda ko nan gaba in kin rabauta za ki ke tuna cewa kin yi jarrabawa zazzafa."

"Kin gan ki? A lokacin da na fara sam ba na samun ganin ainihin inda zan same ki, hakan yasa na share wasu lokuta ina duba amma dai shiru, ba Ni da niyyar cutar da ke a da, amma Abunda jakin uban riƙonki, Malam Suke ɓarawo kuma maciyin dukiyar marainiya ya min shi ya fusata Ni, in da ba don haka ba, da zan yi amfani da ke ne kaɗai ta Wasu hanyoyin don bunƙasa dukiyata da arziƙina ba wai na sa ki cikin tashin hankali ba. Ke amincewar ki ma ba don son ranki ba ne, aikina ne ya ci ki, biyo NI da kika yi nan ma dai dukka aikina ne, za ki iya tuna randa na kawo ki?" Bai jira Amsarta ba ya ɗaura da
"To tun ranar na kafa ki kamar yadda na kafa sauran Matana, Hajjaju, Lantana da Larai. Ke bari ki ji, babu wanda ya san da ku a duniyar nan, hatta yaran da na haifa babu wanda ya san da su don na kawar da baki da ganin mutane daga gareku, ba ki taɓa tunanin me yasa babu wanda ya taɓa zuwa gidan nan ba tunda kike?"

"To dai duk aikina ne, babu wanda ya taɓa shiga ko fita daga nan sai ranar da na karya abun da kai na, wacce kwaɗayi ya kawota inuwata kuma Kinga ta tafi, haka kuma za ku bar gidan, za ku bar min yarana har zuwa randa Nima zan mutu, daga nan komai zai Karye ku samu damar iya tona sirrikana, amma dai a yanzu ko kun yi ba za ku yi nasara ba."
"Sannan batun basussukan da kika ciyo min Nagode, don yanzu maganar da nake Miki na buɗe kamfanin ledodi da jakakkuna. In

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login