Showing 6001 words to 9000 words out of 134378 words

Chapter 3 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

60

yau ita kam sai damubunta. A wurin babu wanda bai tausayawa mata ba ganin yadda take kuka, ga shi dai sun san yarinyar ba ta da matsala don babu wanda zai ce yau magana ma ta haɗa su da ita.

Jin Abunda Nassman ya faɗa yasa aka rage masifar da akewa Naja'atu yayinda wasu kuma suka riƙe Hamra suna lallashinta. Hakan yasa aka ɗan sarara wasu suka fara komawa mazauninsu. Nassman ne yace "Ku tambayeta awarar ta nawa ce sai a ba ta kuɗinta"
Ce musu tayi ba ta sani ba, "To ya za a yi kenan ƴanmata?"
"Innata dai ta ce ta dubu uku ce, amma na yi cikinkin dubu ɗaya da ɗari shida"
"Yauwa, to ai Kinga yanzu za a ba ki dubu da ɗari huɗu Kinga ya cika dubu ukun?"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana share hawayenta.
Nassman ne ya ciro dubu da ɗari biyar ya miƙa mata, hannu tasa ta karɓa, cikin kuɗaɗen dake hannunta ta ciri ɗari ta miƙa masa.
Murmushi ya mata yace "Bar shi kawai, ki riƙeta"
Kai ta jijjiga tana faɗin "a'a Mom ta ce min kada ina karɓan kuɗin mutane, ka karɓa zan wuce"
Ganin ba shi da niyyar karɓa yasa tace "To na gode, zan wuce, Amira na tafi, ki gaida Innarki"
"To Hamra sai gobe" murmushi Hamra ta saki tare da juyawa ta bar wurin har lokacin kuma Nassman na tsaye yana bin ta da kallo.

Tana komawa Inna ta Tare ta "ina kuɗin?"
Dubu uku da ɗari ɗaya ta miƙa mata sannan ta fara ƙoƙarin nufar butar da ta gani za ta yi alwala tayi sallar Isha'. Da kuɗi ya ƙaru Inna ki tambayeta mana ina ta samu sai ta ja ta wuce ɗakinta. Sai da Hamra tayi salla ta nufi ɗakinta ta kwanta kan matacciyar tabarmarta, kafin ka ce me bacci ya kwasheta abunka da jikin jinya. Can cikin dare zazzaɓi mai zafi ya rufke ta, rasa yadda za ta yi tayi ga shi kuma har cikin ƙashinta take jin ciwo. Haka dai daren nan ido biyu tayi shi, sai wuraren asubahi bacci ya kwasheta. Cikin baccinta taji sauƙar ruwa mai sanyi a jikinta, a zabure ta miƙe tana zazzare idanuwa.
"Maza fito ki samu ki ɗebo mana ruwa kinga anjima in suka ɗauke ba za a samu ruwa a famfon ba.

Fitowa tayi tayi salla kafin ta ɗauki botikin ɗibar ruwa ta fara jido, Allahn da ya taimake ta ma zazzaɓin da dare kawai yake nuƙurƙusarta, ba ita ta gama jidon ruwa ba sai da gari ya waye tarwal, can bayan ta koma ɗaki Inna ta ƙara zuwa tace ta fito ta hura wutar ɗumame. Babu musu ta hura ta ɗumama Tuwon, bayan ta sauƙe ta kashe icen tunawa da wata rana da ta sha duka akan ta bar ice babu komai kan murhu. Can Inna tazo ta raba ɗumamen, ta zubawa Baffa Sule, ta saka nata, ta sakawa Khadi nata da na anjima, sauran kari ɗayan da ya rage da miya ta nunawa Hamra wacce ke kwashe shara tace "Ungo wannan uwar Mayu." Daga haka tayi wucewarta ɗaki.
Bayan Hamra ta gama ta samu ta ci ɗumamen ta sha ruwa sannan ta fara kiciniyar haɗa kwanukan wanke-wanke. Tana haɗawa ta koma gefe ta zauna tana jiran su Inna su gama su fito da kwanukan tayi wanke-wanken.

A taƙaice dai wannan itace rayuwar da Hamra take yi a gidan Inna Hajara, kullum cikin ƙyara da tsangwama take, aikin wahala kowanne ita ake ba wa ba tare da an duba shekarunta ba, wahalar ba ta ƙary mata ba sai da Rahama ta dawo, nan cin kashin da ake mata ya linku, kowa na ƙara kumari banda Hamra da take rayuwar ƙunnci da azaba.

*Mun kammala overview, in sha Allah gobe za mu tsunduma cikin labarin TUMUN DARE, kowa ya shirya*


[17/05, 2:50 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:



_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THREE: Journey of life*



Kwanaki sun ja, watanni sun tafi har tsawon shekara guda, A halin yanzu dai girki, da wasu ɗawainiyar gidan sun dawo kan Hamra while kuma Rahama da ke gaba da Hamra koyaushe jibge take, ita ci kawai ta iya da shegiyar mugunta, ba dama taga Hamra sai ta mata Abunda ranta ba zai ji daɗi ba, amma a hakan still ganin Hamra suke matsayin wacce suka taimaka ba ma wacce take taimakonsu ba. A halin da ake ciki yanzu Hamra ta saba da wasu mutane a unguwar, ciki har da Amira da Kuma ummarta, wanda suna matuƙar taimaka mata duk da suma ba wani hali ne da su ba, idan an kawo wa Amira kuncen kaya Ummarta za ta ware a kai wa Hamra wacce tsawon shekaru biyu kenan babu wanda ya taɓa ba ta ko da ƙyalle ne a gidan amma in ta samu an iya kwashewa. A wannan shekarar ne kuma girma ya fara kama Hamra, masoya ta ko ina zuwa suke, cikin unguwar nan har faɗa ake akanta sai dai ita duk ba ta da lokacinsu ma, in short ita ba ta ma san soyayya ba, yadda ake kururuwar sonta yasa Inna da ƴarta Rahama shiga tashin hankali, tsoron Inna ɗaya kar Hamra ta auri mai kuɗi taji daɗin rayuwa, hakan yasa suka fara ɓullowa da wasu sabbin salo don har ga Allah sun tsani Hamra, ba sa son ci gabanta kai ba sa mata ko da fatan jin daɗi a rayuwar nan. In da a ce za su iya ƙwace kyan da Allah yayi mata ma, to babu shakka da sun daɗe da aikata hakan gani suke wannan kyan nata kaɗai zai iya sanyawa ta samu hutu da jin daɗi nan gaba shi yasa koyaushe suke ƙara jibga mata ayyuka ko ma yaya ne dai, ba za ta ke samun lokacin samari ba.

Ita dai Hamra ta rasa gano dalilin wannan baƙar ƙiyayya da suke nuna mata, a yanzu ta yi hankali kuma ta san ina ne yake mata ciwo, ta san mai sonta da kuma maƙiyinta, hakan yasa itama ba ta biyewa masu zuwa mata da soyayya don ta shafawa kanta lafiya, mutum ɗaya da take ɗan kulawa shine Nassman, shi kaɗai ne take gani a matsayin mai ƙaunarta da gaskiya tunda koyaushe shi cikin bibiyar rayuwarta yake kuma duk wani abu na cutarwa da ya gani zai tunkareta yakan yi ƙoƙarin kawar da shi.

Wannan dalilin yasa Hamra aminta da shi ba tare da sanin kowa ba, ta yi imani cewa ba lallai ta samu wand zai so ta ya ƙaunace ta kamarsa ba tunda bai ƙyamaceta a yanayin da wasu ke ƙyamatarta. Yana ƙoƙarin kyautata mata da samar mata da wasu abubuwa na rayuwa, lokaci bayan lokaci yakan ɗauki kuɗi ya ba ta don magance wasu matsalolinta, musamman a yanzu da girma ya cimma mata, kuɗij ba ƙaramin amfani suke mata ba, in da a ce babu shi la'alla ƙananun buƙatu dai na ɗiya mace wacce girma yazo mata da sun fi ƙarfinta.
An sha kai masa zantuka marasa kyau saboda ya rabu da ita, amma hakan bai yi tasiri ba, to me yasa za ta ƙi shi? Babu dalili.

*********************************

Rahmah ce da Inna Hajara zaune kan tabarma suna shan iska sai kuma Khadi wacce ke wasa ƙasa. Can gefe guda kuma Hamra ce zaune ta miƙe ƙafarta saboda ƙunar da tayi a tuƙa tuwo ta sha iska. Duk da cewa akwai rata tsakaninsu amma neman magana irin na Rahama yasa ta miƙe daga kwancen da take ta kalli Hamra tana wani yamutsa fuska tace
"Ke Hamra dalla can ki rufe mana wannan gyambon naki duk sai kin bi kin sa cutukan jikinki sun bi iska sun shafe mu?"
Cike da ƙosawa da gajiyawa da irin Abunda Rahama ke mata tace
"Wai ke Yaya Rahama ina ruwanki da ciwona? So kike mutum ya ruɓe ne? Ina ce dai duk a tuƙa muku Abunda za ku ci a ji ciwon." Cikin ranta kuma tana tsoron kada taje su duka ta amma dole ta ɗauki shawarar Umman Amira, la'alla sanadiyyar haka ta samu sassauci.

Zaune Inna Hajara ta miƙe tana duban Hamra da mamaki kan fuskarta
"E lallai Hamra'u, kice kin samu mai goya Miki baya? To ko uban waye ya tsaya Miki ba zan juri iya shege da rasar kunya ba, wai ma uban wa ya tsaya Miki?"
Kafin Inna ta rufe baki Rahama ta isa wurin da Hamra ke zaune, tana zuwa ta saka ƙafarta mai uban datti da kaushi akan ciwon Hamra tana murzawa cike da mugunta, wani irin ihun azaba Hamra ta saki tana ture Rahama gefe amma ta gagara. Ihu ta cilla tana yarfe hannunta saboda zafin da ya shige ta har tsakiyar ƙwaƙwalwarta. Ƙwafa Rahama tayi sannan tace:
"Don ubanki shegiya ina Ni za ki yi wa iya shege, wallahi a gidan nan kashi ma ya fi ki daraja, banza mai kyan tsiya kamar mayya"

"Yauwa ƙara mata shegiya" Inna ta faɗa tana nuna Hamra da yatsa
"Wato kan ki ya fara wayewa ko? To don ubanki komai yadda kika girma hakan ba zai hana na ci ubanki a gidan nan ba."
"Inna ki bar Ni da ita" Rahama ta faɗa tana huci
"Idan dai ina gidan nan wallahi sai ta bi umarnina, shegiya dan kin samu an taimaka Miki shine yanzu za ki fara yi wa mutane tsaurin ido, wato don kin ga Nassman yana tare Maki faɗa a waje ko?"
Dafe da ƙirji Inna tace "Nassma kuma? Waye Nassma?"
Dariya Rahama tayi tana faɗin
"Wallahi Inna ke kam ƴar ƙauye ce, Nassman fa ba Nassma ba"
Basar da Rahama tayi tace "Yo Ni ina ruwana, ai ba sunan Allah bane da in na faɗa ba daidai ba za a gyara min. Shi waye Nassman ɗin?"

Abu na gurmi, nan da nan Rahama ta cire ƙafarta kan ciwon Hamra ta koma mazauninta kusa da Inna.
"Inna wallahi wani saurayi ne, ɗan gidan Alhajin Gagidiba ne, kuma dai yadda naji an ce son Hamra yaje wai har kuɗi yake ba ta, Inna in ba ki tashi tsaye ba wallahi Hamra tsaf wani mai kuɗin zai ce yana sonta, ki ga fa Inna, yanzu ma ake son ta bare ta ƙara girma "
Jinjina kai Inna tayi tana ƙara jaddada maganar Rahama cikin ranta. Hakan ya yi wa Rahama daɗi shi yasa ta yi murmushi ta ci gaba da magana
"Kina dai gani Inna Ni ce gaba da Hamra, kuma Ni ce ƴar gida amma Hamra ta fi Ni masoya, Ni fa Inna iya Sa'adu ne ma ya taɓa cewa yana so na." Ta Idasa tana zumɓura baki gaba.

"Ya isa ki shiru, ai kuwa ke ce ɗiyar asali ɗiyar masu gida,babu yadda za a yi ƴar cikon gida ta fi ki farin jini, ki kwantar da hankalinki bari Jamilan Ɗanlarai ta dawo daga garinsu, za mu je a san abun yi."
"Yauwa Innata, Ni wannan kyan nata ma shi yafi ɗaga min hankali, Inaga ma saboda ita ne fa yasa ba a zuwa wurin nawa."
"Nima na lura da hakan fa, amma ki kwantar da hankalinki wannan kyan sai mun lalata shi, Hamra dai da jin daɗi a duniyar nan sai dai Hajara ba ta numfashi. Ke kuwa miji ma sai mai Naira, a gidan Naira za ki yi aure, muma mu ci albarkacin ki, ita kuwa a tsiya za ta ƙare."
"Yauwa Innata" Rahama ta faɗa tana kwantawa kan cinyar Inna.

Duk abun da suke faɗi Hamra na jiyo su sai dai ba ta da ikon tankawa, amma sam hakan bai yi tasiri a zuciyarta ba, hasali ma ba ta damu da maganar ba, abu ɗaya da ta sani shine Allah ba ya barci kuna zai ci gaba da kasancewa a tare da ita. Ganin ba ta da wani abu da za ta yi yasa ta miƙe za ta shiga ɗaki Rahama ta dakatar da ita
"Ba na ce Miki iya dare ne lokacin da za ki na shiga ɗakin ba?" Cike da ɗacin rai ta juyo tana kallon Rahama kamar za ta ce wani abu kuma kawai ta juyo ta zauna a wurin da take.

Yau ma cikin ikon Allah ta fita tallan awara Nassman yazo, bayan sun gaisa ya nemi wuri gefenta ya zauna suna hira tana sayar da awarar, babu tsammani ta ji an ɗuma mata dundu, da sauri ta juyo tana ganin waye, Rahama ce wacce ke huci kamar mayunwaciyar zakanya.
"Shegiya yau ma sai da kika nemo shi ko?" Ba ta iya ba ta amsa ba sai ma juyawa da tayi kamar ba ta san da wanzuwar Rahama ba tunda ba yau ta fara mata wannan iskancin ba. Nassman ne ya miƙe a fusace yake kallon Rahama yace
"Ke uban waye ya sa ki dake ta?"
Dariyar rainin wayo tayi tace "Kai kuma a su wa? Ina ruwanka tunda ba kai na taɓa ba?" A hasale yace "Da ruwana tunda sonta nake, Kinga kuwa dole na shiga."
Baki buɗe take kallonsa har ya idasa faɗin abun da zai ce
"Amma ka ba Ni kunya Nassman!" Katseta yayi da faɗin
"Kinga Malama, ba na son jin komai daga gareki.."
"A'a Nassman dole kaji komai kuwa daga gare Ni, saboda Ni kaɗai ce za ka ji komai daga wurinta. Namiji har namiji, saurayi har saurayi, ga shi dai baka rasa komai ba kuma ba a ganin talauci a tattare da kai, amma ka rasa wa za ka so sai maras asali? Anya ka kyautawa kanka da iyayenka..."
Tsawa ya daka mata yace "Ya isa haka, ki ɓace ki ba Ni guri!"

Yanayin da yayi magana ya mugun tsoratar da ita amma ta dake tace "wallahi sai na faɗa maka ko ba ka so, in ma za ka nemi mace mai asali da tushe ka nema,idan kyawunta ne yake ruɗarka tun wuri ka san inda je maka ƙaiƙayi." Tana gama faɗar haka ta ja ta bar wajen ranta fes don ganin kamar kalamanta sun yi tasiri a zucitar Nassman tare da fatan Allah yasa ya dawo yace ita yake so.

Tafiyar Rahama yasa masu bawa idanuwansu abinci gusawa daga wurin, kowa na tunanin Abunda ta faɗa, babu shakka ta san asalin Hamra kuma watakila ma gaskiya ta faɗa tunda a gidansu Hamra take. Wasu kuma na faɗin yo Allah na tuba dama in mace ta fiye kyau in ka binciko za ka ga ba ta da asali.

Nassman ne ya dubi Hamra da kanta ke sunkuye kamar mai kuka, ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara jin ƙaunarta na ratsa kowanne sashe na zuciyarsa, ji yake kamar ma ƙara masa sonta ake cikin zuciyarsa, mazauninsa ya koma sannan ya kira sunanta.
"Hamra" ba tare da ta ɗago ta amsa da "Na'am"
Yanayin yadda ta amsa ɗin ne yasa jikinsa yin sanyi, tausayi da kuma ƙaunarta suka mamaye zuciyarsa.
"Kin ga, kalle Ni"
Ba tare da ta kalle shi ɗin ba tace "Ina jin ka, kai ma yau za ka rabu da Ni ko?" Kansa ya fara jijjigawa as if tana kallonsa "Ba haka bane Hamra"

Ba ta san lokacin da ta ɗago ta kalle shi ba jin kalamansa,dariyar takaici tayi tace "Kaima yau za ka rabu da Ni, ka ji ba Ni da asali, kamar yadda ta faɗa ka nemi ɗiyar mutunci irinta"
Kalaman Hamra sosai suka bugi zuciyarsa, kamar zai yi kuka yace "Haba Hamra, kin san dai ba zan guje ki ba, da gaske son ki nake, wallahi ko yau gidanku suka ce na fito zan fito tunda dai ina da sana'ar da zan riƙe ki alhamdulillah, kuma Kinga Ni ba mutumin banza ba ne."
Numfashi ta sauke tana tsare shi da ido alamar jiran me zai faɗi take. Fahimtar hakan yasa ya langwaɓar da kansa yace
"To Ni me zan ce Miki ki yadda da Ni, in sha Allahu zan turo iyayena a nema min izinin aurenki, idan ya so ko zuwa yaushe ne ma, ai an san da zamana ko?"

Ba ta ce masa komai ba sai mayar da dubanta da tayi ga wani saurayi da yazo siyan awara, bayan ta sallame shi ta juyo tace "Idan na sayar za ka raka Ni chemist don Allah?"
"Ba ki da lafiya ne?" Ya ba ta amsa da tambaya. Kai ta gyaɗa masa, hakan yasa ya ɗan rikice kaɗan.
"Me ya same ki? Shine kuma kika fito talla bayan ba ki da lafiya?"
Numfashi ta sauƙe cikin ranta tana faɗin "da ina da wannan damar da na more" a zahiri kuma tace "Ka manta tun yaushe nake sayar da awara ne? To ai kullum ka ga ina fitowa ka ka taɓa ganin na yi fashi?" Kai ya jijjiga, murmusawa tayi tace "to ka gani. Kawai ka min addu'a Allah ya ba Ni lafiya."
"Shikenan Hamra, addu'a ai kullum ina yi miki, Allah da za a bar Ni a gidanku ma Ni tun yanzu zan tura a nema min aurenki, ai za ki zauna ko?"
Numfashi Hamra ta sauƙe tace "Aure kuka, shekarata 15 ne kaɗai, na yi ƙarama da yin aure."
"Amma ai za ki iya zama tunda tsab na san za ki ɗauki ciki." Ba tare da ta san ina ya dosa ba tace
"Ka dai ƙara min lokaci ba yanzu ba."
Murmusawa yayi yace "Babu komai, Allah ya kai mu lokacin, amma Biyuti wannan ƴar'uwar taki tana da taɓin hankali ne?"
"Taɓin hankali kuma? Me ka gani?"
"Kawai dai na tambaya ne" ya ba ta amsa.
Dariyar da iyakacinta saman laɓɓa tayi tace "Lafiya ƙalau take."

Yanayin yadda tayi maganar yasa ya fahimci ba ta son zancen hakan yasa ya sauya akalar zancen da tambaya.
"Biyuti ba ki faɗa min me yake damunki ba fa"
"Ba fa wani abu ba ne, ƙunar da nayi ne take zafi sosai shine nake son na sayi maganin rage raɗaɗin zafin, yauwa kuma ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login