Showing 36001 words to 39000 words out of 134378 words
kuma Hamidu zai zo ya ɗauki matarsa ya tafi da ita.
Suna wucewa Baffa ya shiga cikin gida fuskarsa washe kamar mai tallar toothpaste. Tun daga waje yake guɗa kamar wata mace, hakan ne ya jawo hankalin kowa ga fitowa don ganewa kansa Abunda ke faruwa, daga Hamra, Rahama, Inna har da Khadi babu wanda bai fito ba.
Ɗauke da mamaki Inna tace "Lafiya Malam?"
Juyi yayi yana rausayawa yace "Yau dai buri ya cika, Shalelen Baba?"
Rahama ta matso kusa da uban nata tace "Ga Ni Baba"
"Albishir!"
Ita da Inna suka haɗa baki suka ce "Goro"
"Yau dai na b da aurenki! Kin kusa zama amaryar muloniya! Kema za ki yi rayuwar hutu. Sati mai zuwa za a ɗaura auren."
Caraf Inna tace "Malam aure kuma? Da wa?"
"Ke kam Inna na ruwanki, ba ki ji ya ce mai kuɗi ba ne mijin, to ai ko ma waye Nikam na ji daɗi na. Ji nake kamar na jawo sati mai zuwan ma yayi." Rahama ta faɗa tana ɗagewa Hamra wacce ke tsaye tana kallon su ido.
"Ya dai Hamra? Aure zan yi dai, auren mai kuɗi."
Hamra dai ba ta ce komai ba, hakan yasa Inna faɗin "Duk baƙin cikin mai baƙin ciki sai dai ya mutu. Gobe da sassafe kuwa za mu fara shirye-shiryen biki."
Hannun Inna Baffa ya kama ya ja ta ɗaki. Nan ya faɗa mata komai game da auren, da yake dukkansu babu Gara, son zuciya ya rufe idanunsu ba ta ƙalubalanci abunda Mai gidan nata yake shirin yi ba. Ko dan, dama can duk jirgi ɗaya ne ya kwaso su.
*Wannan kenan!*
*A yi sharing don Allah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWELVE: Just the beginning.*
Mutanen da ba sa tashi da safe a safiyar Yau sammako suka yi don tun gari bai gama haske ba suka fito, kamar an sakawa Hamra hannu yau hayaniyarsu ita ta farkar da ita. Ta yi kusan mintuna biyar da tashi sai dai ba ta yi ƙoƙarin miƙewa ba, idanuwanta ta cilla ga ɓangaren Rahama, duk da cewa akwai duhu a ɗakin amma ba ta ga alamar mutum a kwance a wurin ba. Ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa. Tana fitowa bayi ta shiga bayan ta fito ta daura alwala tayi sallah. Bayan ta yi azkar ɗinta na safiya buɗe Alqur'anin ta don yin tilawa, cikin daddaɗar muryarta take rera karatun Alkur'ani, karatu mai sanyaya zuciyar mai saurara da kuma sanya nutsuwar zuci. Har gari ya gama wayewa ba ta samu damar fitowa ba saboda bayan tilawar da ta yi sai da ta gyara surar da Mu'allim ɗinsu yace su yi assignment ce ta hutu, a ranar da aka dawo a ranar zai karɓi haddarsa.
Misalin ƙarfe Bakwai da arba'in ta fito lokacin rana ta haska irin sosai ɗin nan, abun mamaki ba ta ji motsin kowa ba a wajen haka mashin ɗin Baffa ma ba ya nan. Taɓe baki tayi tana tambayar kanta ko ina suka je? Ganin babu mai ba ta amsa yasa ta taka zuwa kitchen, robar da ta gani rufe da murfin tukunya ta buɗe, ganin abincinta na karyawa ne, taliya da manja da kuma yaji, haka yasa kai tsaye ta ɗauka ta dawo ɗakinsu ta ajiye, ƙara fitowa tayi ta wanke hannunta sannan ta koma ta zauna tana mai furta Bismillah daga nan ta fara cin taliyar, hamdala tayi ga Ubangijin da ya ciyar da ita ba tare da wani wayo ko ƙarfinta ba sannan ta fito da robar, sai da ta sha ruwa tukun ta nufi wurin wanke-wanke, ƴan kwanukan da aka ɓata da safe ne kawai hakan yasa ta wanke su daga nan ta dawo ɗaki, ƙoƙarin fara rage kayan jikinta take don ta watsa ruwa ta jiyo surutun Khadi tana yi wa Innarta magana.
Numfashi kawai Hamra ta sauƙe kana ta, zani ta ɗaura bayan ta rage kayan jikinta sannan ta saka hijabi a kai. Tana ƙoƙarin fitowa suka ci karo da Rahama. Ja baya kaɗan Hamra tayi saboda yadda kanta ya bugu da na Rahama ta ji zafi sosai, cakumo hijabin nata Rahama tayi cike da neman masifa tace "Ya ishe ki haka Hamra! Kawai don kin ji zan yi aure, auren ma zan auri wanda kike so shine kika ɗaga hankalinki? To uban me na Miki za ki faɗo kaina haka in kika ji min rauni fa?"
Da mamaki Hamra take bin Rahama da kallo, "Amma kamar dai ke kika buge Ni ko?"
"Tambayata ma kike? Ai na ga duk saboda an ce Miki zan auri Hamid ne yasa kike wani cin magani tun daren jiya."
Murmushi Hamra ta saki wanda ya ƙara ƙona ran Rahama "Lallai Rahama, idan kina tunanin kin kai na miki baƙin hali to wallahi ki daina, tun wuri ki daina don ba ki da wani abu da zan yi Miki baƙin hali a kai. Aure kuma da kike cewa za ki auri Ya Hamid sai aka yi yaya? Ko kin manta iyayenki sun ce ba za su aurar da Ni ba ne? Ya kamata zuwa yanzu ki kwantar da hankalinki don Ni na wuce yi Miki baƙin hali, neman ilimi na a yanzu shine abu mafi muhimmanci, matsa ki ba Ni waje."
Daga haka ta saka hannunta ta janye Rahama gefe ta fice zuciyarta na mata zafi. Wanka tayi ta dawo ta saka kaya sannan ɗauko wayarta, rasa me ma za ta yi tayi, can dai tayi scrolling apps nata, hannunta ne ya kai kan WPS office, da sauri ta fara duba littattafan da ƙawarta Maryam Umar ta tura mata. Karo na farko da ta fara karanta littafin Hausa a rayuwarta. Tana fara karanta littafin ta fara jin sanyi a ranta don sosai littafin ya ɗauki hankalinta. Tabbas a yau ta tabbatar da cewa kowa da irin ƙaddarar da Ubangiji ya rubuta masa, nata shafin kadan ne idan aka kwatanta da na wasu. Duk da cewa a labarin littafi ne amma tabbas rayuwar IMAAN ta matuƙar ba ta tausayi, lallai kuwa za ta ke bibiyar iron wadannan labaran ko ba komai za su ƙara mata ƙarfin guiwa. Book 1 ta gama karantawa ga shi kuma babu gwo, hakan yasa taji mazarin neman na biyun don jin yaya za ta kaya.
Ƙiran Maryam tayi ta tambayeta, nan ta ba ta amsa da cewa ai ba ta da shi itama, amma ta yi wa marubuciyar magana ta ce littafin na kuɗi ne, kuma ba ta fara na biyun ba, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar shiga group ɗin bayan ta biya kuɗin littafin. Tun daga wannan rana Hamra tame ji a ranta ta samu abokan ɗebe kewa, wato littattafa, salla kawai ke ɗaga ta daga karatun.
Washegari Saturday, ranar ta koma makaranta, yanayin yadda ƙwazonta da hukumar makarata ta duba yasa ta ba ta damar rubuta jarrabawar WAEC tana SS 1 ɗin saboda ganin yadda ta kere abokan karatun nata, sun kuma yi duba da shekarunta hakan yasa suka tuntuɓi majiɓancinta, Yaya Hamid da maganar. Sosai yayi farin ciki da hakan, da ya sanar da su Ummie sosai suma suka yi farin ciki, wannan dalilin ne ma yasa ummie ta ƙudiri aniyar dubo yarinyar Tata a yau da daddare tunda ta san dai yanzu zuwa yamma tana makaranta.
Tare da Humairah suka kai ziyarar. Tun daga shigarsu gidan suka fuskanci akwai sauyi sosai musamman yadda Rahama ta gaida Ummie cike da girmamawa sai wani sunkuyar da kai ƙasa take haka kuma Inna ma ta fito suka gaisa sai washe baki take and again, shima Baffa yau har da shi a gaisuwar, mutumin da duk zuwan Ummie gidan bai taɓa ko da gigin kallon yadda take ba saboda girman kai irin nasa sai yau kuma zai zo gaisuwa har da sakin fuska?. Da suka tashi tafiya dukka baffa, Inna da Rahama babu wanda bai musu sai da safe ba, ita dai Hamra dama ta san kwanan zancen Shiyasa take binsu da ido kawai. Hijabi Hamra ta sanya don taka musu, bayan sun fito Humaira da sauyin da ta gani yake ta nuƙurƙusarta ta dubi Hamra tace "Sister, mutanenki sun sauya haka ashe?"
"Hmm" kawai Hamra tace tunawa da cewa sun raba ta da Abunda take muradi da kuma ƙauna, sai dai ta yi mamakin tambayar Humairahn, kamar ya? Ko ta manta cewa gidan sirikansu ne yanzu?. Babu mai ba ta wannan amsar hakan yasa ta ja bakinta ta ɗinke tana shirin sauya akalar hirar sai dai tambayar da ummie ta aiko mata yasa ta dakata
"Kin yi shiru Hamra, da gaske dai akwai Abunda ke damunki ko?"
Kanta ta kawar gefe tana faɗin "Kai Ummie, me kika gani? Babu komai fa, kin san yanzu karatu ya sako Ni gaba tunda shekara ɗaya kawai nayi a senior school zan zana SSCE, akwai abubuwan da ban iya ba har yanzu, kin ga dole na dage."
Ba don Ummie ta yarda ba tace "Allah sarki Daughter, kada ki damu, U can make it! Na yarda dake tunda ga shi su kansu malaman sun buƙaci da ki rubuta jarrabawar a yanzu."
"To Allah yasa" wannan lokacin both Ummie da Humaira ne suka amsa duk da cewa har lokacin hankalin Humairah na ga wayarta da take dannawa. Sallama ta musu bayan sun iso wurin da suka yi packing motarsu, Ummie ta miƙa mata ledar hannunta, da hannu biyu ta amsa tayi wa Ummie godiya daga nan ta musu mu kwana lafiya tana faɗin "Sister ki gaida Yaya!" Daga haka ta juya ta fara takawa, taku uku ta jiyo Muryar Humaira na faɗin "Ai kun fi kusa da shi, kamar ba ɗazu kuka gama soyewarku ba."
Ba ta tanka mata ba kawai ta ci gaba da tafiyar ta duk da cewa ta ga buƙatar tankawar don a yanzu ta tabbatar da cewa su Ummie ba su san da batun auren Yaya Hamid ba. "Anya kuwa Rahama da gaske take Yaya Hamid za ta aura?" Ta tambayi kanta. Da sauri ta fara jijjiga kanta tana faɗin "Nooo, that's impossible, Hamra Ni ce matar Yaya, babu wata bayan Ni."
"But kin dai ji ai me Inna ta faɗa, may be Ummien ma lafiyarki tazo dubawa saboda tunanin ko kin shiga wani yanayi da jin zancen auren Yayan."
Wani ɓari na zuciyarta ta faɗa mata, cike da gamsuwa ta jinjina kai "Ƙwarai kuwa, hakan ne ma, Ni dai yanzu na haƙura da soyayya, da farko Nassman, and now Yaya Hamid, I all lost them! Miye ma amfanin soyayyar?"
"Babu " ɗaya ɓarin ya ba ta amsa. Tana tafe tana zancen zuci ba ta ankara ba sai ji tayi ta yi karo da mutum.
"Ke wace irin mahaukaciya ce? Ba Kya gani ne?"
Firgit ta dawo hayyacinta tana ƙarewa mai maganar kallo, wani ɗan maƙotansu ne wanda da ke son Rahama, sai dai rashin mutuncin da yaga Rahamar na yi wa Hamra yasa shima ya yafa wa kansa ya bi sahu.
"Kai da kake gani me ya hana ka matsawa gefe ka ba wa makaho wuri?"
Cikin maganganunsa na rashin ɗa'a yace "Shegiyar ga ki da kyau amma babu damar a ɗauke ki, matsa min kan hanya." Sanin cewa ba hankali gare shi ba yasa tayi sauri ta matsa gefe, cikin sassarfa ta samu ta ƙarasa gida.
Shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dangin Inna da Baffa sun cika gidan duk da cewa a makare suka san da al'amarin bikin, amma duk da haka sun taho ƙwansu da ƙwarƙwatarsu sun cike gidan, a ranar farko Hamra sai kayanta ta haɗa ta wuce gidan Umma saboda babu wurin kwana a gidan, in akwai ma me za ta zauna tayi bayan babu wanda ta sani a cikinsu? Dangin Baffa? Suma babu wanda ta sani a tsawon rayuwarta duk da cewa Baffan ya kasance ɗan'uwan mahaifinta, abun da ma ya ɗaure mata kai bai fiye yadda suke ta tambayar su Inna ko ita wace ce? Sai dai amsar da Innar ke ba su yasa kanta ƙara ƙullewa, wai tsintarta suka yi, to amma ita a iya tsawon rayuwarta ai Baffa ƙanin Dad ɗinta ne, to me yasa suke yi wa ƴan uwa ƙarya? Cikin ranta tace "Ina buƙatar sani, da alama akwai wani abu da ban sani ba."
Ranar talata Dije suka kafa a layin suka fito suna takawa gabaɗayansu har da su Inna kamar wasu masu ciwo a ƙwaƙwalensu. Ita kam Hamra lokacin dawowarta daga makaranta da ta biyo ta ƙofar gidan Inna taga me suke sai ta taɓe baki ta saki murmushin takaici tare da yi musu addu'ar shiriya, daga nan ta wuce gidan Umma abunta.
Ranar Laraba dangin ango suka zo don saka amarya a lalle, sai dai kaf cikin waɗanda suka zo ɗin babu wani wanda alamar maiƙo ta bayyana jikinsa, duk wasu ya ku bayi ne suka zo, hakan ya tayar da ɗan ƙaramin rikici tsakanin dangin Inna da Baffa sakamakon yadda Innar ke ɗaɗɗaga musu kafaɗa wai ƴarta za ta auri millionaire tunda da can an riga an yi wa Rahamar miji, ɗiyar ƴar'uwar Innar Baffan. Nan dai aka yi ta ɗauki ba daɗi abu dai sai ya lalace, wasu dangin Baffa kam ma kayansu suka tarkata suka wuce abunsu don ba za su iya jurar takaici ba. Bayan tafiyarsu aka ci gaba da hidimar biki kamar dai yadda aka fara lafiya, biki ya yi biki tabbas, tukunyar abinci kawai ake sauƙewa ana ƙara ɗaurawa sai kace gasar cin abinci aka zo yi, sai dai ka hango mata curi guda sun saka tire suna ta ɗura abinci.
Ranar Alhamis ƙawayen Rahama suka zo don cin caccanga (tsagwaya) tare da ba ta shawarwari, juma'a juma'a kamar yadda aka sanya ita ce ranar da za a ɗaura auren Rahama amma har zuwa yau Alhamis ɗin ƙwandala ba ta haɗa ta da mijin ba, a taƙaice dai duk wani abu da aka saya baffa ke fitarwa daga aljihunsa, a ganinsa tunda an ɗauke masa kayan ɗaki ai an rage mai wuyar, a bar ma batun rashin bayar da kuɗi, hasali ko zuwa suyi magana bai taɓa ba, yau kam haƙurinta ya kai maƙura hakan yasa ta saka Hijabinta ita da ƙawarta Hamida suka je har wurin da Baffa ke kanikanci, sallama suka masa ya ɗago yana bin Rahama da kallon mamaki.
"Ya dai Amarya?" Baffa ya tambaya yana tsare su da ido. Kamar Rahama za ta yi kuka tace "Baffa wurinka na zo fa." Ajiye ƙarfen hannunsa yayi ya matso zuwa wurin da suke yana faɗin "Lafiya dai Shalele?"
Bakinta gaba tace "Baffa wai shi angon nan ba ka ce mai kuɗi ba ne yaron Hajiyar Hamra?" Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
"To in haka ne meye dalilinsa na ƙin zuwa ko sau ɗaya wuri na? Ko dai ba ya son auren ne?"
Shiru Baffa yayi a take alamun rashin gaskiya suka bayyana kan fuskarsa, ƙasumbarsa ya shafa yana rarraba zance yace "A'a e a'a, haba Shalele don kawai ba ki ga miji ba sai ki damu? Ba ki ga abun a ƙurarren lokaci yazo ba babu tsammani? Anya kina son shiga cikin daular nan?"
Da sauri tace "e mana Baffa, amma ai ko sau ɗaya ya kamata yazo, ka ga fa har yau ko lefe ba su kawo ba, Ni da nake jira azo a jibge min akwatuna har yanzu ko baƙar leda ban gani ba."
Numfashi ya sauke sannan yace "Haba Shalele, idan kika yi haƙuri ko bai kawo ba idan ya tafi da ke ai dole zai siya Miki, Kika san ko wata ƙasar ya tafi Shiyasa ba a kawo ba?" Ido waje tace "Don Allah dai Baffa?" Gani ya samo hanyar da zai shawo kanta yasa ya gyaɗa kai yana faɗin "ƙwarai Shalele, don haka ki kwantar da hankalinki, kayan ɗaki ma shi zai Miki ya faɗa min."
Lokaci guda farin ciki ya mamaye fuskarta, cikin wani irin yanayi mai kama da fariya tace "Haba! Ni ɗin ce fa, Rahama Shalelen Baffa, to Hamida kin dai ji da kunnenki,in Mun je kya musu bayani Susan cewa Ni yanzu matar babban mutum ne." Cike da ƙarfafawa Baffa yace "ƙwarai kuwa, yanzu dai ku koma gida kin san ba a so amarya ta fita yawo." Babu gardama tace "To" daga nan suka koma gida. Ba su daɗe da komawa ba aka kawo lefen Rahama, akwati biyar ne, kayayyakin babu laifi dai amma kayayyakin ba wasu na ku zo mu gani ba ne, hasali ma dai ba masu tsada ba ne.
Wannan abu ya ƙara hasala Rahama amma ga dangin Inna sai murna ake yarinya ta yi goshi, kaya masu tsada, akwati ɗai-ɗai har biyar? Ai yarinya kam ta samu miji mai kuɗi. Hajiya Inna tuni kanta ya gama huruwa sai wani buɗe hannu take in tana tafiya wai ƴarta za ta auri mai hannu da shuni. Duk wannan abu da ake yi Hamra ba ta da masaniya, hasali ma sau ɗaya take shiga kullum ta gaida Inna idan ta dawo daga makaranta, ganin baƙi da kuma mutane yasa ba ta tozarta ta a bainannasi.
Washegari aka ɗaura auren Hamid da kuma Rahama akan sadaki ₦150K kamar yadda aka sharɗanta mafi ƙarancin sadaki a garin, kuɗin kuma ya kasance lakadan ba ajalan ba, Baffa ne ya amshi kuɗin bayan an ɗaura aure tuni aka fara shigowa da Abinciccika ana rabawa ƴan ɗaurin auren.
Da yamma can sai ga Yaya Hamid ya faka motarsa a bakin layin sannan ya ƙira wayar Baffa wanda lokacin ke tare da wasu manyan abokansa a rumfar da aka kafa a ƙofar gidan. Yana ɗagawa ya sanar da