Showing 99001 words to 102000 words out of 134378 words

Chapter 34 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

87

tunanin zuciyata ya tabbata, Finally you're part of us, yau ɗin nan zan sanar da Uncle batun komai..."
Harara Ammiey ta dalla mata
"Kul na ji, kya jira mu gama settling komai itama ta murmure kafin nan."
Zumɓura baki Ra'isa ta yi tana faɗin "Ai shi ke nan, idan an gama da komai dai kowa ya huta, Ni fa Ammiey kin san me?"
Ammiey ta jijjiga kai
"I'm suspecting something oo, that brat, Baffa yake ko Uncle Sule, su ne waɗanda suka kashe Dad, babu shakka. Saboda haka in an yi booking ƙwararren lawyer komai zai zo ƙarshe, Ni kuma I'll in sha Allah assist him."

Shiru Ammiey ta yi tana nazarin kalaman Ra'isa daga bisani ta sauƙe numfashi tare da faɗin "Magrib ta ƙarato, ya kamata Kowa ya san ta yi, immediately after kuka yi salla, ku ƙaraso bedroom na, kun ji?"
Kai suka gyaɗa, Ammiey ta zame kan Hamra da ke kan cinyarta ta taimaka mata ta miƙe tsaye sannan tace "bari na wuce ko?" Da kai suka ba ta amsa, daga nan ta juya ta wuce bedroom nata, Ra'isa wacce ke riƙe da hannun Hamra ta dube ta tace "Here we go sister" Kai Hamra ta sauƙar ta fara takawa, shigowar Nihla yasa suka dakata
"Ammieys, mun dawo tare da Abie, in na yo salla kowa zan ba shi abun da na siyo masa."

"Hey Angel...." Kasa faɗan abun da yake shirin faɗa ya yi sakamakon ganin Hamra a cikin gidansu, wannan yarinyar da ta sa ƴarshi yin fushi kanta? Me take yi a nan? Ya tambayi kansa. A ɓangaren Hamra ita ma turus tayi gabanta na faɗuwa idanuwanta duk sun fito kamar an shaƙe ta. Da kallon mamaki Ra'isa ke bin su ganin yadda yanayinsu ya sauya lokaci guda.
"Ya dai Ukhty? Akhy? Ka san ta ne?" She asked furiously
Cikin rawar Murya Hamra tace "A'a...a...a"
"What the hell is she doing here?"

Mubeen ya faɗa yana bin Hamra da wani matsiyacin kallo.
A kiɗime Ra'isa tace "Akhy? Kana lafiya? Do you know her?"
"I said what the hell is she doing? Nan ɗin ma biyo mu kika yi? Ke wace ce?"
Ya faɗa yana zare mata ƙwala-ƙwalan idanuwansa da suka bayyana tsantsar ɓacin rai.
Kukan Nihla ne yasa ya ɗan sarara tare da dawo da attention ɗinsa kanta
"Abie, why don't you like her? Shi ke nan, I'm going with her because she's part of us..."
"Shhhh" ya faɗa da ƙarfi
"Shige ciki ki ba Ni waje, don't let me loose my temper on you!" Yanayin yadda ya yi maganar yasa Nihla rugawa ciki da mugun gudu, ganin ta tafi yasa ya aikawa Hamra da Ra'isa wani irin kallo.

Ra'isa wacce ke cikin ruɗanin wannan abu yasa ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa tace "Akhy, I'm sorry please, but Hamra is going nowhere, Ammiey ta san da zamanta and....."
A matuƙar fusace ya dakatar da ita yana faɗin "Did I ask you? Whether Ammiey is aware of her or not, dole ta bar gidan nan, munafika zo ki fice kafin na kira ƴan sanda"
Yana kai aya wani irin kuka ya suɓucewa Hamra, take ta fara ƙoƙarin raba hannunta da na Ra'isa don ta fice kamar yadda ya buƙata ɗin saboda yadda ta matuƙar tsorata da kalamansa, yadda taji Ra'isan ta riƙe mata hannun da ƙarfi yasa ta dube ta tare da jijjiga mata kai alamar ta sake ta babu komai.

Kuka Ra'isa ta fashe da shi tare da rungume Hamra tana faɗin "you're going nowhere Ukhty, Ammiey ba za ta bari ki ƙara guje mata ba" jikinsu ta raba daga nan ta riƙe hannunta ta ja ta za su yi sashen da bedroom ɗin Ammiey yake "Mu je mu sanar da ita komai..."
Tsawa Mubeen ya daka musu wanda babu shiri suka saki juna jikinsu na karkarwa, ba tare da wani tunani ba ya janyo hannun Hamra da mugun ƙarfi yana shirin fitar da ita, babu tsammani kawai yaji tas! A kan fuskarsa. Ba kowa ba ne sai Ammiey wacce fuskarta ke lulluɓe da mayafin ɓacin rai. Cikin ruɗu da kuma mamaki da suka mamaye shi lokaci guda ya tsaya ƙyam kamar wani soja, take komai na jikinsa ya daina aiki na wani ɗan lokacin, ƙwaƙwalwarsa ta tsaya da nata aikin na wucin gadi.

"Lallai Mubeen! A yau ka nuna min cikakkiyar mummunar ɗabi'arka da ban taɓa tsammanin kana da ita ba sai yau! Hakan ya nuna ba za ka iya riƙe wani nawa ba bayan raina, ka kyauta!" Ammiey ta faɗa a fusace, ba ta jira amsar da zai ba ta ba ta riƙo hannun Hamra da ke zubar da ƙwalla har zuwa wannan lokaci. Janta tayi suka yi bedroom nata, Ra'isa ma ta bi bayansu ya rage sai iya shi da ke cikin shock har zuwa lokacin. Ko da ya dawo saiti, abu ɗaya ne ya tsaya mishi a rai, mari? Ammiey da kanta ne wai yau ta mare shi? Abun da ba ta taɓa yi masa ba tun yana ƙarami? To akan me me ta mare shi?" Ya tambayi kansa "A kan wannan munafukar yarinyar da har yau zuciyarsa ta gagara amincewa da ita a matsayin mutumiyar kirki? A kanta wai yau Ammiey ta ɗauki hannunta mai daraja ta mari fuskarsa. Lallai yau kuwa ko me yarinyar nan tayi wa ahalinsa dole ya lalata shi, dole ne ta ɗanɗana azabar da ba ta taɓa jin ko da ƙamahinta ba, za ta san yau ta taɓo shi." Cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya ya shige cikin parlour kai tsaye ya haye bene, idanuwaensa har rufewa suke saboda yadda ransa ya matuƙar ɓaci.

A can ɓangaren Ammiey ashe shigar Nihla wurinta ta tafi, gama wankanta kenan tana shirin ɗauro alwala, alwalar kenan da ba ta yi ba ta fito bayan bayanan da ta kurɓa daga Angel, hakan ya matuƙar ɓata ranta sosai shi yasa tana isa wurin ta ajiye masa tafi akan kyakkyawar fuskarsa.

Lallashin Hamra Ammiey ta yi da ƙyar ma ta yi shiru, bayan ta yi shiru Ammiey ta sa Ra'isa ta ɗauko musu kaya, a toilet ɗin Ammiey suka yi wanka suka yi sallar Magrib su duka. Sai a lokacin Nihla ta hango ƙatuwar ledar da tayo musu siyayya zube a ƙasa. Ganin kowa ya daina fushi yasa ta rarrafa ta ɗauko ta fara fitarwa da komai ɗaya bayan ɗaya sannan ta ba wa kowa, na Abie ɗin ta kuma ta zumɓura baki ta tura su gefe har sai da ta so ba wa Ammiey dariya. Tabbas jini ya fi ruwa, yau ta tabbatar da hakan da ta tuna da yadda Nihla ta ƙi bin bayan mahaifin nata.

A nan suka zauna suka sha hirarsu har suka yi sallar isha, daga nan suka yi dinner, Ammiey ya sallami kowa zuwa nasa ɗakin sannan itama ta wuce nata. Bayan sun koma ɗakinsu ba su yi bacci ba, Ra'isa na ƙara tayar da labaran da Hamra ta ba su, wasu wurin ta tsinewa su Inna, idan ta yi wani abun har dariya take ba wa Hamra ganin yadda ta haƙiƙance.

"Wato dariya ma nake ba ki ko?"
"Tuba nake ƴar'uwa, amma ai abun da ya wuce ya wuce, tunda dai daga ƙarshe na haɗu da dangin Mom, kuma na san Ammiey za ta sada Ni da dangin Dad ma."
"Uhm haka ne, amma wallahi dole a ƙwatar miki ƴancinki, kin ga yanzu dai sai kin ƙara murmurewa tun da haka Ammiey ta ce, amma tafiyar ka tare za mu yi, dole ko sau ɗaya ne nima naga shegiyar Innar nan.."
"Ukhty har da zagi? Ki bar ta da abun da tayi ma, Allah ba zai bar ta haka ba."
"Ƙwarai kuwa" in ji Ra'isa "Allah ba zai bar ta ba, shima tsinannen Malam ɗin nan ko? Hmm, ji nake kamar na haɗa tawagar sojoji muje mu ci ubansa. Mugu mai son zuciya." Ta idasa taba cije lips ɗin ta

"Wai dama haka kike da faɗa Ukhty?"
Hararar wasa ta Banka wa Hamra tana faɗin
"Wasa ma kike, wallahi na tsani azzalumi, shi yasa na tashi da burin zama lawyer."
"Hmm, to Allah ya taimaka yasa ki rage zafin rai."
"Amiin fa" ta amsa mata a taƙaice. Shiru suka yi gaba ɗayansu har bacci ya kwashe su.

*Washe gari*

Bayan sun yi sallar subh suka koma bacci, ba su suka tashi ba sai wajajen ƙarfe goma na safe, nan ma sai da Ammiey ta zo ta tayar da su. Bayan sun yi breakfast suka yi wanka, pictures suka yi snapping da wayar Ra'isa daga nan suka koma parlour wurin Ammiey wacce ke tasbihi hannunta riƙe da counter, dandalin hira suka buɗe abun su, Hamra sosai ta saki jiki yau kam saboda yanayin da ta tsinci kanta ciki na farin ciki wanda ke ƙoƙarin shafe mata baƙin labarinta na baya.

*CEO MUBEEN*

Da ƙyar daren ranar ya runtsa sakamakon wani irin azababben ciwon kai da ya tasar masa sanadiyyar wannan fitinanniyar yarinyar da bai san wace ce ita ba kuma bai san mene ne ƙudirinta a kansa da kuma ahalinsa ba. A haka bacci ɓarawo ya sace shi, da ƙyar ma ya iya tashi ya yi sallar subh a gida don har lokacin kansa kamar an ɗaura masa dutse yake jinsa. A kan praying mat ma bacci ya ƙara ƙwashe shi. Siririn Hasken ranar da ya hasko ta wurin da curtains ba su gama lulluɓewa ba ne ya tayar da shi. Babu laifi bacci ya rage masa ciwon kan da yake ji, ko da idanuwansa suka sauƙa kan agogon bangon da ke manne a ɗakin sai ya zaro idanuwansa waje, da sauri ya miƙe ya shiga bayi, cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin wata Black suit da ta amshi jikinsa. Bayan ya fesa turarensa mai daddaɗan ƙamshi ya zari jakarsa ya aza kan kafaɗarsa da sauri ya janyo wayarsa yana ficewa daga ɗakin.

Kai tsaye ɗakin Ammiey ya fara nufa duk da cewa ya san ba lallai ta amsa gaisuwarsa ba, amma dai zuwan dole ne a gare shi, ko ba komai yana so ya samu lokaci don ya fahimtar da Ammiey wace ce yarinyar da ta mare shi a kanta. Minti biyu ya yi tsaye bakin ƙofar yana shawari da zuciyarsa a kan ya shiga ko akasin hakan, daga ƙarshe dai ya saddaƙar tare da ƙwanƙwasawa sai kuma ya murɗa ya shiga kansa ƙasa kamar wani munafuki.

Sarai Ammiey da ke kwance kan gadonta ta ga shigowarsa amma ta make kamar ba ta gan shi ba saboda yadda take mugun jin haushinsa, fahimtar hakan da ya yi yasa ya kau da kansa gefe, a sukwane ya ƙarasa kusa da ita sannan ya fara ƙoƙarin dasa guiwoyinsa a gabanta. Ɗago idanuwanta tayi gare shi sannan tace "Babu buƙata, fice min a ɗaki."
Idanuwansa ya ƙwalalo waje yana mamakin sauyawar mahaifiyar tasa take kuma ya ji wani iri kan hakan.
"Ana āsif Ammiey, ba zan maimaita b..."
"Na ce ka bar min ɗaki tun da ban isa da kai ba."
Kamar zai yi kuka haɗe hannayensa biyu yana faɗin "Don Allah Ammiey, ki yi haƙuri."

Ganin ya ƙi fita yasa ta juya masa baya, hakan ya sa ya tabbatarwa kansa cewa ba ƙaramin abu ba ne wannan ɗin. Cikin Wata murya mai nuna zallar rauninsa yace
"Idan har kafaɗar da zan kai kukana gareta ta rushe, shin ina zan kai kukana? Ba Ni da wata ko wani a duniyar nan da zan yi tutiya da shi bayan ki, don Allah AMMIEY ki min afuwa ki yafe min, ba ki tunanin in na fita da fushinki wata musiba ta sauƙa a kaina?" Shiru ya yi yana addu'ar Allah yasa ta ji tausayinsa ta haƙura.

Babu shakka kalamansa sun yi tasiri cikin ranta sai dai kuma tana so ta nuna masa kurakuransa akan abun da ya so aikatawa ne. Jin ta ƙi juyowa yasa yace
"Shi ke nan Ammiey tun da ba za ki yafe min ba, zan fita aiki, na san ba lallai na dawo ba tunda kina fushi da Ni, la'alla ma wani hatsarin ya faru da Ni..."
Juyowa tayi ba shiri amma fuskarta haɗe, ko iya wannan ya faranta ransa ya san ta haƙura amma sai ya ƙaraso kusa da ita ya tsugunna tare da ɗaura kansa akan ƙafafunta.

"I'm sorry Ammiey, ki yafe wa autanki don Allah, ba zan ƙara ba." Ya riƙe kunnuwansa biyu yana zazzaro idanuwansa waje.
Miƙewa Ammiey ta yi ta zauna tana aika masa wani kallo mai kama da gargaɗi.
"Ki yi haƙuri Ammiey."
Gyaran murya tayi sannan tace
"Ka san irin munin abun da ka aikata kuwa Ibny? Ka san irin yadda ka ɓata raina jiya har ka sa hannuna ya kai fuskarka? Ban taɓa tunanin kana da wata muguwar ɗabi'a ba sai jiya, hakan ya sa naji kamar ba za ka iya riƙe Ra'isa ba bayan raina..."

Ɗan guntun hawayen da ya zubo masa ya goge tare da tsayar da Ammiey da maganganun da take yi masu karya masa zuciya sannan yace
"Don Allah ki bar faɗin haka Ammiey, ko kina raye Ni mai kula da Ra'isa ne, ba ma ita ba, hatta waɗanda ban sani ba, tabbas na ƙona miki rai, amma don Allah ki yafe min Mommah"
Ta so murmusawa jin ya kira ta da Mommah, amma ta make tace "Ba zan iya fushi da kai ba, na riga na yafe maka kuma ina maka addu'ar shiriya amma dai, tabbas da buƙatar ka sauya ɗabi'unka."
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya sunkuyar da kansa yace "Ina godiya Ammiey, in sha Allah zan sauya."
"Allah ya amince"
Ya amsa mata da "Amin"

"Za ka iya tafiya kar na makarar da kai, amma dai ka kiyaye."
"Na gode Ammiey" ya faɗa tare da matsawa kusa da ita ya ba ta side hug sannan ya sumbaci goshinta. Daga nan ya miƙe yana faɗin
"Bye Mommah"
Yana shirin ficewa ta tsayar da shi
"Ka dawo da wuri, da yamma za ka fita da su su yi shopping."
"Su?" Ya maimaita yana faɗin "to Ammiey"
Wani kallo ta aika masa daga nan ya fice yana sakin murmushi.

*React and share fisabilillah.*

[9/1, 9:08 PM] Diamond Bhatool:

_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY TWO*

Ajiyar zuciya kawai Ammiey ta sauƙe tana yi wa ɗan nata addu'ar shiriya.

Wuraren 3:30pm motar su ta shigo gidan, yana daidaita parking Nihla ta fice da sauri saboda har lokacin tana fushi da shi, murmushin gefen baki yayi tare da faɗin "Mu headache." Daga haka shima ya fito, ko da ya iso parlour ganin babu kowa kamar ko yaushe ya sa ya lumshe idanuwansa. Ko ɗakinsa bai wuce ba ya samu ya lallaɓa ya yi hanyar bedroom ɗin Ammiey, kamar wani maras gaskiya ya saka kansa ya leƙa ganin ƙofar a buɗe.
"La ilaha illallah!" Nihla ta faɗa tana tafa hannu
Tsorata ya ɗan yi har da yin ɗan tsallensa.
"Ammiey ga Abie yana leƙowa bedroom ɗinki"

Kansa ya jijjiga daga baka ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa Ammiey ta yi wacce a lokacin da idar da sallar la'asar ɗinta.
Zama ya yi akan carpet ɗin da ke shimfiɗe a ɗakin sannan yace
"Sannu da gida Ammiey" langwaɓar da kansa yayi yana jiran response ɗinta sai dai ba ta kula shi ba, hakan ya san ya ɗan kwantar da murya ya ƙira sunan Ammiey. Dariya Nihla ta kwashe da ita ganin yadda Abie ɗinta ya koma kamar baby. Bakinta ta rufe da hannayenta ganin dariyar ta ƙi tsayawa yasa ta fice da gudu.

"Ammiey" ya ƙara ƙiranta, sai a wannan karon ne ta ɗago ta kalle shi, da ido ta masa alamar sauraro.
"I'm sorry Ammiey, ki taimako ɗan autanki ki yafe masa." Harara ta cilla masa shi kuma ya saki dariya.
"Har yanzu ba ki haƙura ba Ammiey? Ya kamata ki fahimce Ni ba wai na yi hakan ba ne don na ɓata ki ba, hasali ma ina so na kawar da duk wani abu da zai cutar da ku ne a matsayina na wanda haƙƙin hakan ke rataye a wuyansa."
"Hakki ka ce Mubeen? Ka kuma ce abun cutarwa?"

Jikinsa ya tare wuri guda gudun kar yaje yayi ɓaranɓarama.
"Ina jin ka? Me ka gani dai zai cutar da mu?"
Fuska yamutse yace "That brat, I mean wannan yarinyar da zan fitar da ita, Ammiey ba ki san wace ce ba, ina da tabbacin macuciya ce ita ɗin saboda ita ce same girl da kwanaki Angel je kuka akan na kore ta a Company, Ammiey she's..." Hannunta ta ɗaga tana mai dakatar da shi
"Ya isa Mubeen, falyaqul Khairan?" Ya ƙarasa mata da "Au liyasmud"
Ta harare shi sannan tace To me yasa ba ka yin shirun?"
"Haba Ammiey, do you expect me to keep quiet? So ma kike na naɗe hannu ina ganin abun da zai cutar da ku?"
Ammiey ta amsa masa da "Ka dai rinƙa yin tunani kafin ka yi abu, kada ka bari tsanarka ta ɗarsu a zuciyar Hamra."

Fuska ya haɗe sannan yace "Haba Ammiey, please don't trust that girl, ina da tabbacin tana da wata mummunar manufa a kanmu ne, in ba haka ba me yasa zan ganta a Company? Da ta ga ba ta samu karɓuwa ba sai ta dawo gida?"
Wani murmushi da ke nuna har yau ba ka da wayo Ammiey ta saki kafin ta ƙira sunansa a sanyaye.
"Ibny" amsa mata yayi da "Na'am"
"Manzon Allah" suka ƙarasa" Sallallahu alaihi Wasallama" ɗin a tare sannan ya ja bakinsa ya yi shiru
AMMIEY ta ci gaba da faɗin "ya hane mu da yin zato, saboda shi zato ƙaryar zance ne. Wannan zaton da ka yi wa Hamra ka sani, laifi ka aikata ko da hakan take, bare kuma ba gaskiya ka faɗa ba, ka san waye Hamra kuwa a gare Ni?"

Jikinsa ne ya yi sanyi da tunatarwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login