Showing 129001 words to 132000 words out of 134378 words

Chapter 44 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

94

kama hannunta. Hannunsu sarƙafe da na juna suka nufi hanyar toilet, tun da ya buɗe ƙofar wani fitinannen ƙamshi ya bugi hancinsa. Ma sha Allah kawai ya furta a ransa don kuwa sosai hakan ya sa masa nishaɗi duba da cewa bai taɓa jin kwatankwacin wannan ƙamshin ba duk kuwa irin yadda yake mutum mai tsafta da son ƙamshi. Da taimakonsa ta gabatar da alwala sannan ta jira shi yayi tasa, bayan sun kammala suka fito. Praying mat da hijab, ya miƙa mata hijab ɗin sannan ya shimfiɗa musu sallayar, laffayar ya taya ta warewa sannan ta saka hijab ɗin.

 Sun gabatar da salla cikin nutsuwa da aminci, ya rufe musu da shafa'i da witri, sannan ya juyo ya dafa kanta yayi addu'a da ya dace ango yayi, kamar yadda addini ya tanadar, ya kuma sake cigaba da wasu addu'oin masu ratsa jiki da zuciya tsawon wani lokaci lokaci. Daga haka ya mata tambayoyi duk da yasan baida haufi a kanta ɓangaren addini sam. Amma dai yayi ɗin dan yana son yasan a zuwa yanzu wane mataki take a neman ilimin addini. Yaji daɗi sosai jin yadda ta amsa masa duk kuwa da cewa a kunyace take. Dan haka ya tabbatar mata zasu cigaba da karatu a gida, zai kuma sakata wasu online classes da yake yawan gani ana tallata su. Kanta a ƙasa tai masa godiya shi kuma ya ɗan ja hancinta kaɗan, ya ce, " Ni kike wa godiyar?”.

Murmushi tayi sai kuma a hankali ta ce, “Ka cancanci fiye da haka ma a gareni Yayana. Ka nuna min cewa kai ɗin jinina ne tun lokacin da na bayyana gare ku a ba zata, ka ƙwatar min ƴancina gurin waɗanda suka zalunce Ni, ka.."
 “Shiiiiii!!!” Ya Mubeen ya faɗa a hankali yana ɗaura yatsarsa akan lips ɗinta. Idannunta ta ɗago a hankali ta kallesa, shima kallon nata yake cikin wani irin kasalllalen yanayi. Yadda ta sake take kallon nasa kamar ba mai jin kunyarsa ba ya sa su shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa yayin da zukatansu ke ƙara narkewa. Ya Mubeen ne ya fara janye nasa idon a hankali, batare da yace komai ba ya yunƙura ya miƙe ita ma sai ta mike ɗin. Sallayar ya ninke, ya ajiye sannan ya zaunar da ita kan carpet ɗin da ke shimfiɗe, shi ma ya zauna. Sannan ya janyo ledar da ya ajiye tare da mayar da hankalinsa ga gasasshiyar kazar da ƙamshinta ya bugi hancinta. Bismillah ya mata bayan ya zuba guda biyu kan wani babban tray, Kanta a ƙasa tace ita ta ƙoshi, don ta ci abinci ɗazu amma fa kazar ta mugun yi mata, tashi yayi ya fita, babu jimawa ya dawo da cups guda biyu. Milk ɗin ya zuba a kofi ya miƙa mata. Kanta ta girgiza sai ya ɗan harareta. “Baki so nayi koyi da ma'aiki ne.?”.
A hankali ta ce, “Ina so mana”.

 “To bismillah”. Ya faɗa bayan ya sha madarar, itama ya saka mata kofin a baki. Hannunta ta ɗaura akan nashi tasha a haka. Bai kuma barta ba sai da ta shanye tass. Ganin haka yasa ya fara yagar kazar yana kaiwa bakinta, babu kunya kuma ta ci kamar ba ita tace A'a ba a farko, ƙara musu madarar yayi suka sha sannan ya haɗe komai waje guda ya fita da su. Babu wani jimawa ya dawo ɗakin. Ganin tana lullumshe idanu ya ce, “Barci?”. Kanta ta jinjina masa. Ya ce, “Okay, ki fara yin wanka ki cire wannan nauyin"
Ɗan harararsa tayi kafin ta miƙe, hijabinta ta mayar sannan ta nufi closet a kunyace ta janyo bathrobe, daga haka ta nufi toilet. A can ya cire kayan ta samu ta watsa ruwa sannan ta fito da hijabin kan bathrobe ɗin su kuma kayan ta bar su a wani sashe na bayin da ta fahimci kamar loundry ne, kasancewar kusan yanayin part ɗinsa na can irin wannan ne.

*React and share fisabilillah.*
[9/16, 10:46 AM] Diamond Bhatool:
*Tap the link below to follow my TIKTOK account.*


https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER FOURTY ONE*

Ganin ta nufi closet yasa shi ɗan ɗaga murya kaɗan yace "Oh yea, naza ki zo" kamar za ta ce a'a sai kuma ta ƙarasa wurin da yake ɗin a kunyace, ganin kamar kaya ne ajiye a gabansa kan gadon yasa ta kalle shi. Kai ya jinjina mata alamar ta ɗaga. Itama sai ta jinjina nata kan, a bisa tsautsayi tana ɗago na saman dake matsayin nata kawai rigar ta warware kanta. "Ya subahannallah" Hamra ta faɗa tana sakin rigar ƙasa ba tare da ta ankare ba sai kuma ta mayar da hannunta kan ƙirjinta sannan ta juya da sauri. Ganin yadda tayi yasa shi kauda kansa ya fuske kamar bai gani ba kafin ma ta juyo. Aiko sai ta wani sauke ajiyar zuciya, da sauri ta juyo tare cikuikuye rigar da pant ɗinta ya faɗo shima ta maida ciki ta ƙara cikuikuye wa. Miƙewa yayi abun sa batare da ya ce mata komai ba ya nufi closet ɗin ɗakin, bai wani jima ba ya dawo hannunsa da wasu kayan barcin don ya riga ya fahimci me take nufi. A saman gadon ya ajiye mata, sannan ya kwashe waɗancan ɗin ya mayar.

Haɓarta ya kamo sannan yasumbaci lips ɗinta. “Ga wasu kayan nan ki tashi ki canja ki kwanta ki huta goodnight”. Ya saki fuskar tata ya wuce yana ɗan murmushi. Sai da taji ya fice gaba ɗaya ya rufe mata ƙofar sannan ta wani sauƙe ajiyar zuciya mai nauyin gaske kai kace irin wadda ta kuɓuta daga hannun abun cutarwa. Kayan daya ajiye ɗin ta juya ta kalla a karo na farko, nan ma sai ta sake sauke ajiyar zuciya ganin su kam na mutunci ne. Amma waccan gantalalliyar riga ai ba'a magana, duk wanda ya saye ta ma ba ƙaramin ɗan iska Ba ne. Ta jima tana saƙe-saƙen a ranta kafin ta miƙe ta kwashi kayan ta nufi bay bayan ta kwashi wasu abubuwan daga kan mirror. Ƙara gyara jikinta tai sosai kamar yadda Aunty Murjanatu ta ce tayi, sannan ta saka riga da wandon na barci masu taushi though wandon iyakarsa guiwar ƙafarta ne, amma hakan ma dama-dama shi akan waccan rigar.. sosai ta saka ma jikin wasu turarurruka masu sirrin ƙamshi da Aunty daga nan ta buɗe ƙofar bayin ta fito..ganin ba ya nan ya sa ta kashe haske ta nemi wurin kwanciya.

 Har bacci ya ɗauke ta bai dawo ba, sai can ya shigo ɗakin yana sauƙe ajiyar zuciya. Gadon ya nufa bayan ya haaka da wayarsa. Sai da ya haye tukun ya kashe wayar tasa ya kwanta. mayataccen ƙamshin turarenta ne ya bugi hancinsa, take kuwa kasalar jiki da ta zuciya ta dabaibaiye shi. Cikin sakanni komai na jikinsa ya canja. Wanda suke a sume domin gajiya duk suka farfaɗo. Idanunsa kam sun kasa buɗuwa, a hankali ya miƙa hannunsa gare ta tare da janyo ta kusa da shi. Ai kuwa babu shiri ta buɗe idanuwanta. Kasantuwar dim light yasa ya ga hakan, da sauri yace "ya dai?"
 Maimakon bashi amsa sai ta ɗago idanunta da suka tara ƙwalla ciki ta kallesa. Kauda nasa yayi, sai dai ina zuciyarsa tabbatar masa take bazata bashi haɗin kai ba, haka ma gangar jikinsa gaba ɗaya. Kuma har ga Allah yanayin da ha kasance a cikin yanayi ne da yake ji ba zai iya jira ba. Ƙara Jawota yayi jikinsa ya rungume ta tsam ko zai ɗan samu sassauci, amma ina komai ma sake yin tashin gauron zabi yayi cikin ƴan sakkani, farashin ya sauya daga ainahin farashinsa. Da ƙyar ya iya furta mata "Ki yi baccinki" a cikin kunnena. Kamar mai shirin yin kuka ta ce, “Bana jin bacci”.


 Murmushin gefen baki ya ɗan saki, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan. Sake matsowa yayi kusa da ita sosai, ya ƙara matsota ya saka a cikin jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya, hannunsa na shafa gadon bayanta ya furta, “Yau gadin gida zamuyi ke nan?”.
 Ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a kai ka kwanta kayi bacci”.
 “Ke kuma fa?”.
Shiru tayi taƙi yin magana.
Dariya sosai ke cin Ya Mubeen yana dannewa don yadda ya wani yi laƙwas sai ya ba ka dariya. “Anya wannan amaryan rowara ba ta yi yawa ba?”.

 Baki ta ɗan tura kaɗan, sai kuma ta ɗan ɗaga ido ta kallesa, shima kallon nata yayi, amma tai ƙoƙarin janye nata dan bazata iya kallon juyayyun idanunsa ba. Ƙin bata damar cire idanun nata yayi, ya sarƙesu da nata dake cike da rauni da fargaba. Rau-rau suka cika da hawaye, maimakon ya tausaya mata ya barta sai ma ya sake narke nashi dake cike da salon shauƙi da buƙata. “Miyasa bazaki iya cigaba da kallon idona ba Rouhy? Babu abin da zai same ki a cikinsu sai natsuwa.”
 Cikin raɗa, da muryarta mai rawa ta ce, “Ina jin tsoro”.
 "Why? Zaki ji tsoro Rouhy?, Mubeen ne fa ne fa, wannan yayan naki da ya kore ki a Companynsa. Ni ba ƙarfe bane mai dukan farin ciki ko ruguzashi. Ni ruwa ne, mai goge tsoro, in shayar da kwanciyar hankali musamman a duniyarki”.
 A hankali hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta samu damar lumshe idanun tare da kife fuskarta a ƙirjinsa. 
 

Gefen fuskarta ya sumbata kaɗan, cike da raɗa ya furta, “Kar kiji komai, zan saurari bugun zuciyarki har sai ta tsaya cikin nutsuwa. Zan jira fitar sautin kalamanki har su bayyana a cikin kunnuwana." Numfashi ta sauke mai ɗan nauyi, sai kuma ta buɗe idanunta kaɗan tana kallonsa yanzu, cikin ido. Idonta yana ɗauke da yanayin nuna tausayawa a gareshi da kuma ɓoyayyar fargaba. Shi ko kallonta yake kamar yana karanta rubutu a cikin idanun nata. Murmushi ya mata ita ma sai ta maida masa murtani a karo na farko. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa saboda murmushin nata ya shige shi,Ƙoƙarin janye jikinta tayi, sai ya hanata yin hakan ta hanyar sake rungumeta da kyau. “Ina kike ƙoƙarin guduwa? Bayan naji wani abu mai sanyi yana ratsani, kamar numfashinki. Rungumarki ce kuma tamkar addu’ar da ta yi karo da cikar amsar da nake nema. Ina so ki cigaba da zama a haka a kirjina, ba dan yau kawai ba, sai dan in cigaba da tuna cewa kece sassanyan lambun da zuciyata take so ta huta daga yau har zuwa ƙarshen rayuwata.. Na miki alƙawarin in sha Allah, za ki cigaba da kasancewa anan. A duk lokacin da duniya ta rikice, zan ajiyeki a wannan mafakar ta jikina babu mai damunki."

 Hawaye ne suka gangaro mata a hankali, tsigar jikinta na ƙara tashi ga kuma yadda yake shafa tattausar sumar kanta. Muryarta can ƙasa sosai ta ce, “Kafin wata rana ina kallonka ne a matsayin maras tausayi, daga baya ka zama garkuwata, amma a yanzu kam, zan iya kiranka kai tsaye da rayuwata, idan har babu kai, to babu ni”.
      
 
Ajiyar zuciya ta sake sauƙewa, fargabarta da tsoro na sake daidaituwa a cikin gangar jikinta. Ɗagowa tai a hankali ta zuba masa ido, shima kallon nata yake a cikin ɗan hasken ɗakin mara ƙarfi. Lips ta motsa a hankali zatai magana ya ɗaura yatsarsa a kansu yana wani lumshe mata idanun da buɗewa. “Ba sai kince komai ba. Idanunki suna gaya min abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba ma. Na ga fargaba da kuma tsoro, amma a lulluɓe da su kuma, ƙauna da sha’awa ce mai tsarki.”
 Idanu ta zaro sosai. Ya kashe mata ido ɗaya. "Kwarai kuwa Rouhy, ki sa a ranki cewa zan kula da ke, zan baki garkuwa daga ɓangaren ko wanne abun hari da ya tunkaro ki cikin ba ci ko kuma ido biyu.”

 Idanuwanta ta lumshe tare da sakin murmushi, dan yadda bakinsa ya buɗe yake zuba zance sai take jin shauƙin hakan. Shima murmushin yake, sai kuma ya kai yatsarsa a saman idanunta yayi kamar yana sosawa, hakan ya sata ta ɗan lumshe ta sake buɗewa a cikin nashi. Shima lumshe nasan yayi ya sake buɗewa a cikin nata. “Idanunki sunyi shiru, amma tawa zuciyar nata amsa dukkan abinda suke son isarwa. Bari mu kalli juna har duniya ta manta da lokaci. Saboda ni da ke mun ishi juna a wannan ƙyaƙyƙyawan dare har zuwa sassanyar safiya. Kice kin amince ni kuma zan baki tabbaci”. Cikin kasalliyar murya ta ce, “Na amince" tana ɗan sumbatar lips ɗinsa, sai kuma tai yunƙurin ƙwace jikinta zata juya dan kunya. Sai kawai ya riƙota da saura ya ɗaura tausasan lips ɗinsa akan nata.
 
Alhamdulillah kamar yanda yayi fata ba tayi musu ba, sai ma ajiyar zuciya da take sauƙewa a jajjere. Sannu a hankali ta miƙa wuya tare da sake shigewa jikinsa harma da maida murtani, hakan sai ya ƙara masa ƙaimi da armashi, gaba ɗaya yaji duniyar tai wani irin zama shirun da su kaɗai yake zaton sun rage rayayyu cikinta.
Sannu a hankali salon wasan ya fara canjawa, jikin Hamraya fara rawa, tsoronta na dawowa fresh a zuciya. Ƙoƙarin janye jikinta take amma babu dama, bakin da za ta nemi afuwa da shi ma ya rufe Mata shi rda nashi ba damar magana. Dai-dai yana gama ɓalle illahirin botiran rigarta ya finciketa yay wurgi da ita, Hamada kam ta gama tsorata dan Alaramma Mubeen kam ya fara zuwa inda ake masa rowa ta sake ƙoƙarin fincike jikinta ya sake nuna mata ina ai ta riga ta shiga tarko. A dai-dai gaɓar ya gama rabasu da garkuwarsu daga ita har shi, ALLAH ya ba wa Hamra sa'ar fincike lips ɗinta da jikinta tana ƙoƙarin matsawa ya riƙota, ta fashe masa da kuka. Cikin murya mai nuna zallar roƙo da. magiya ta ce, “Wlhy bazan iya ba! Ka tausaya min, ba yau ba”
       

Ƙasa-ƙasa da muryatasa ya ƙara yi kamarai raɗa ya ce, “Idan na barki mutuwa zanyi Rouhyl”.
“Wlhy nima mutuwa zanyi Akhy”.
 “Na shiga uku, da gaske ka zama kurma da makahon da kai alƙawarin komawa? Kafa min alƙawarin barina na har abada”
“Akhy!”
Taa sake buɗe baki za ta yi magana ƙarfin kukanta na ƙaruwa ya ce, “Shiiiii!!!” ya sake maida lips ɗinsa akan nata. Yayinda yake wani kalar bata saƙonsa mai nauyi da karya garkuwar jiki, cikin gushewar tunani ya sake himmatuwar isa inda ya daɗe a cikin mafarki da hasashen zuciya kawai. Nan ya ɗau harama sai dai ga mamakinsa sai ya ga abun da sam bai taɓa tunani ba duba da cewa ta taɓa yin aure. Zuciyarsa ce ta kawar masa da wannan tunanin na cewa may be idanuwansa ne. Hakan ya sa kai ya tsaye ya......

Sai da ya gama samun nutsuwa sannan ya ja gefe yana sauƙe ajiyar zuciya tare da nanata wasu tarin tambayoyi game da kasancewar Hamrar a yadda ya same ta. Ko da ya dawo da dubansa gareta sai ya ga kamar ba ta motsi. A matuƙar firgice ya fara kiran sunanta but babu amsa, hakan ya sa yayi saurin kunna haske jin wani kuzari ya zo masa. "Subhanallah!" Kawai ya furta daga haka yi saurin ɗaukar wayarsa. To wa zai kira? Ganin babu ga kuma yanayin da take ciki yasa ya yi saurin ɗaga ta kwacakom ya wuce toilet da ita.

Zafin ruwan haɗi da azaba su suka tayar da ita daga duniyar da ta tafi. Ajiyar zuciya ta saki tana ƙara sakin wani irin kuka mai tsuma rai. Lallashinta ya fara yana faɗin ta yi haƙuri zai dena in ta zauna cikin ruwan. Sau uku yana sauya mata ruwa tukun ya tambaye ta yayi mata wankan tsarki? Tace masa a'a.
Ba ya son ƙara takurata shi yasa ma yayi nasa ya fice yayin da idanuwanta ke rufe tun lokacin da ta ga a yanayin da yake. Yana gamawa yayi saurin fitowa tare da sanya wasu light riga da wando, sannan ya koma ciki yana tambayarta ko ta gama.
A fusace tace "Ina ruwanka, ka tafi abun ka, kuma ka kawo min kaya, saura ka shigo."
Murmusawa yayi jin yadda ta wani yi maganar a zafafe cikin ba da umarni. A zuciyarsa yace "She deserve to be."

Sai kuma ya ƙarasa tare da janye bedsheet ɗin da ke shimfiɗe, tare da kayayyakin nasu da ke baje, sauya wani yayi duk da cewa bai wani shimfiɗu da kyau ba amma ya yi ƙoƙari.
Kamar ba ta san cewa dare ba ne ta kwaɗa kiransa. Da sauri ya ƙarasa bayin. Ganin ya ƙara shigowa yasa ta saki kuka tana faɗin "To cewa na yi ka shigo?"
"Sorry" ya faɗa yana ja da baya, jikinsa kuwa har wani rawa yake. Daga wurin yaji ta ce "Ya kawo mata kaya. Hakan yasa ya ɗauko kayan da ta fara cewa ba za ta saka ba, ya miƙa mata. Babu yadda za ta yi haka ta saka ta fito a daddafe tana cije lips ɗin ta. Cike da tausayawa ya ɗagata cak, duk irin mutsuniyar da take kuwa bai sa shi sauƙeta ba sai kan bed ɗin, daga haka ya kwashe bedsheet ɗin da ke zube ya wuce da su loundry. Bai tsaya ba ya dawo ya haye gadon. Sa sauri ta ja gefe, murmusawa yayi sannan ya janyota jikinsa.

Duk yadda ta so kwacewa kuwa bai sa ya rabu da ita ba, sai ma maganar da ya fara rada mata a kunne. Shiri tayi tayi lamo jin yadda yake saka mata albarka tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login