Showing 39001 words to 42000 words out of 134378 words

Chapter 14 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

89

shi sun zo ɗaukar amarya, amma a madadin cewa zai ɗauketa ita ɗaya, za a haɗa da wasu manya ko mutum biyar ne sai su raka ta. Sosai Baffa ya ji daɗi don dama tunanin yadda za a kwashe da tsofaffin nan yake idan yace iya amarya za a ɗauka tunda dai an saba a al'adance akan tafi da Babanai ne idan ƴan kususu sun zo. Wannan ƙira ya matuƙar sanya shi jin relief, hakan ne yasa ya ɗauki excuse wurin mutanen da suke tare daga nan ya nufi gidan yana baza babbar riga.

Da yake duk dangin Baffan yawanci sun riga sun tafi sai tsiraru daga ciki ya rage, sai aka maye gurbin Babanai da Innoni sai kuma tsofaffi biyu waɗanda ke a matsayin kakanni ga Rahama cikon ta biyar ɗin kuma amaryace. A dai al'ada irin ta Hausa Fulani idan za a tafi da amarya takan yi kukan rabuwa, takan ji babu daɗi saboda sabo da iyaye, dalilin wannan tafiya da za ta yi ta dindindin za ta ji inama a bar ta tare da iyayenta. Amma wannan amarya ta zo da wani sabon salo, ashe tun kafin lokacin zuwa ɗaukarta take ta damun iyayenta akan a zo a kai ta, ita ta gaji da wannan gidan, yau dai itama za ta yi kwanan AC taji me ƴan gayu ke ji, this and that....Kuma a lokacin da su Inna Fatsum suka shigo ɗaki don fitowa da ita kallonsu tayi ta saki dariyar shaƙiyyanci tace "Ba dai wai sai kun riƙeni ba ko? Kun san fa Ni ba gurguwa ba ce?" Kasaƙe suka yi gaba ɗayansu suna Bin ta da kallon mamaki don su ko a tarihi ba su taɓa jin irin wannan abu ba, amma yau ga shi kan idonsu yake faruwa.

Shirun da Yaya Hamid yaji yasa ya ƙara kiran Baffa cike da ƙosawa don a dole yake tsayuwar sai duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yake. A fusace Baffa ya shiga a karo na biyu yasa aka fito da amaryar wacce ke gaba, Innoninta da kuma tsofaffin da ke matsayin kakanninta na biye da ita, tun da ta hango shi jingine jikin babbar motarsa ta fara sakin wani malalacin murmushi tare da hasaso irin rayuwar da za ta yi a gidan daula tare da kyakkyawan mijin nata. Suna ƙarasawa ta kalle shi fuska sake yayin da shi kuma tasa ke a cakume kamar an aiko masa da saƙon mutuwa, hakan kuma ya yii tasiri gare ta don ba ƙaramin kwarjini yayi mata ba.

*React and share Fisabilillah.*

[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:




_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER FOURTEEN: New home!*


*AZARE, BAUCHI STATE.*

Sati ɗaya da bikin Rahama Inna ta tisa Baffa da zancen zuwa gano Rahama, da Baffa ya hana sai tace ai za ta kai kayan Rahama ɗin ne, can dai Baffa yace in dai kai lefe ne ta kwantar da hankalinta zai ƙira Yaya Hamid ɗin yazo ya amsa ya kai mata. Babu yadda ta iya saboda samarwa kanta lafiya ta ja bakinta ta tsuke.
Can da yamma kuwa Yaya Hamid yazo ya kwashi lefen ya tafi da su don miƙawa amarya abunta.

*A MONTH AFTER*

Bayan wata guda, Su Hamra suka fara shirye-shiryen fara WAEC saboda dama ta yi registration sai dai ji take kamar in ta yi ma ba za ta ci ba, amma Ummie da humaira da kuma Yaya Hamid waɗanda suka kasance ƙarfin guiwarta na a tare da ita kowanne lokaci. Yadda suke encouraging nata yasa ta yadda cewa she can make it, cikin ikon Allah har suka fara suka gama tana ganin yawanci abubuwan da suka fito ma ta sassansu. Hakan ya mata daɗi matuƙa.

Sau kusan uku Inna na wanke ƙafafunta ta shafa mai ita da Khadi su tafi gidan Rahama, sai dai abun mamaki sai su tarar da gidan a rufe, tun tana shiru har dai ta tunkari Baffa da maganar amma ga mamakinta shima ba shi da masaniya da hakan. Kwantar mata da hankali yayi yace bari na ƙira mijin nata naji ko dai sun tafi yawon shaƙatawa ne. A lokacin ya ƙira numbern Yaya Hamid, ga mamakinsa mumbern switched off, ya ƙara ya kuma amma dai amsar ɗaya ake ba shi, sai a lokacin Inna ta dub shi idanuwanta fal da tsoro "Amma Malam ba ka tunanin akwai matsala kuwa? Nifa kawai na yi shiru ne tun lokacin bikin nata ban yi magana ba saboda ka ce yaron wannan Hajiyar ce da take son ƴar can amma yadda aka yi bikin ya ɗaure min kai."
Kai Baffa ya jinjina yace "Eee ban ƙi maganarki ba Hajara, amma dai Nima sai yanzu na fahimci hakan. Yanzu dai yadda za a yi ki kwantar da hankalinki, Ni ina tunanin sun bar Najeriya ne, kin ga yaron yana da kuɗi sosai."

"To Shikenan Malam, amma fa ka duba wannan al'amarin da kyau, wallahi Ni hankalina ba a kwance yake ba kwata-kwata." Cikin sigar Lallami Baffa yace "Ki yi haƙuri Hajara, Rahama na lafiya ƙalau tana jin daɗinta, kin san fa an ce Alamar shiru lafiya ne."
Kamar Inna za ta yi kuka tace "Nidai Malam ka taimaka ka ƙara dubawa."
Kwantarwa Inna da hankali Baffa yayi da faɗin "Gone Na in Allah ya kai mu zan je gidan su shi yaron, sai muji daga majiya mai tushe."
"Eh to zai fi, amma ka san gidan Hajiyar ne ko sai Hamra'u ta maka rakiya?"
Shiru Baffa yayi can yace "E, goben ta raka Ni."
Inna ba ta ƙara cewa komai ba sai ma tagumin da ta rafka, Baffa na ganinta ya kau da kansa gefe, tabbas da a ce ta san irin tashin hankalin da shi yake ciki ma ba za ta ce komai ba kan batun, don kuwa nasa tashin hankalin ya linka nata, sai dai dole shi zai cinye nasa tunda shi ne babba.

*Washegari*

Kamar yadda Baffa ya faɗa, da batun Rahama Inna ta kwana ta tashi Shiyasa tunda gari ya waye ta fito waje, ganin Hamra na shara yasa ta saki fuska ta kira sunanta. Cike da maɗaukakin mamaki Hamra ta tsaya da sharar ba tare da ta amsa ba, sai da Inna ta ƙira ta a karo na biyu tukun ta tabbatarwa kanta cewa Innar ce ke kiranta. Ƙarasawa tayi kusa da Inna tace "Ga Ni Inna"
Fuska sake kamar ba Inna ba tace "A'a yau har kin fara sharar?" Sakaka Hamra tayi tana bin Inna da kallo cikin ranta tana faɗin anya kuwa lafiyar Inna?

Rashin ba da amsar da Hamra tayi sam bai damu Inna ba, going straight to her point tace "Ni Hamra za ki iya gane gidan Hajiyarki?" Kamar ba ta fahimta ba tace "Inna wace Hajiya kuma?" Sarai ta gane ta amma tunda ta fahimci yau Innar da mutunci ta tashi yasa itama tace sai ta ɗan wana ta. Dafe kai Inna tayi sannan tace "Oh Ni takwarar tsohuwa, ina nufin Mamar yaron nan da ya auri Rahama, Hamidu dai wan Humaira masu kuɗin nan da suka yi jinyar ki kina asibiti."
Dariya ce ta kusa ƙwacewa Hamra da kyar ta danne duk da cewa bayanin Innar ya mugun ba ta dariya.
"Ni fa Inna har yanzu ban gane wa kike nufi ba, ai Yaya Hamid kam bai yi aure ba Inna..."

Hali a jikin rai, in ji hausawa, a hasale Inna tace "Ungo nan!" Ta mika mata daƙuwa "Don ubanki yaron nan da ya kaɗe ki mijin Rahama, in Bai yi aure ba ubanki Rahamar ta aura." Rufe bakinta Hamratsyi da tafin hannunta don ba ƙaramar dariya Inna yau ke ba ta ba.
"Kin min shiru Shegiya, to ba sakinta yayi ba naga sai wata fara'a kike, za ki raka malam gidansu yaron ne."
Kai tsaye Hamra tace "Ni ban san gidan ba Inna."
Duka Inna ta kawo wa Hamra, da sauri ta zame tana faɗin "Me nayi kuma Inna?"
"Uwaki, Shegiya nace uwarki kika yi, na dai faɗa Miki dai"
Cikin halin ko in kula Hamra tace "Nidai na faɗa ban san gidan ba, yauwah" daga haka ta ci gaba da shararta. Takaici koma da ashirin ya cika Inna ga babu halin magana, so take ta bugi Hamra amma tunda nema take wurinta ai dole ta lallaɓa ta.

Can wuraren goma sha ɗaya na safe, Baffa ya shirya cikin shaddar da Yaya Hamid ya ɗinka masa lokacin bikin Rahama, ya ƙwama hula ya fito Inna na biye da shi, daidai ƙofar ɗakin Hamra Inna ta leƙa shi kuma ya wuce wurin da yake ajiye babur ɗinsa.
"Hamra'u, ki yi wa Allah ki zo ki raka Baffanku gidan Hajiyar nan"
"Hajara! Hajara!" Inna ta Jiyo Baffa na ƙwala mata kira, ƙara leƙawa ɗakin tayi tana faɗin "Kinga ya fito ma."
"Ina zuwa Mallam, na je kiranta ne."
"Yi maza ki fito, sauri." Tana ƙarasawa ya cire wayar da ke kare a kunnensa ya raɗa mata "Ga shi nan ya kira ma." Wata wawuyar ajiyar zuciya Inna ta saki sannan tayi Tsim tana jiran jin me za a ce.
"To, to to, na gane, wallahi har mun shiga damuwa ne na rashin tarar da ita da muka yi, ka ga Innarta nan tun yaudhe take tusa Ni gaba sai na binciko, yanzu haka gidan iyayen naka na nufa sai kuma ga kiranka."
"To madalla, Allah ya tsare ku, sai kun dawo ɗin, yauwa, a gaida Rahama."

Daga haka Baffa ya gimtse wayar ya juyo tana fuskantar Inna bakinsa washe kamar an masa albishir da aljanna yace "Kin ga ikon Allah Hajara, dama na faɗa Miki ai shiru alamar lafiya ne.."
Katse shi Inna tayi da faɗin "Ba wani dogon bayani ba Mallam, ina Rahamar take?"
Murmushi Baffa yayi yana faɗin "Kwantar da hankalinki mana Hajara, ke da kika aurar da ƴar ki ga mai kuɗi, ai ba sa Najeriya ma, yanzu haka wayar da muka yi yace suna Dubai, kin ga lambar ba irin ta ƙasar nan ba ce, Kinga har da alamar Tarawa (+) a jiki."
Washe baki Inna tayi lokaci kuga kuma ta saki guɗa tana rangaji tace "Haba, ai ba wasa, ɗiyata a Dubai dai da ake faɗi, wayyo daɗi kashe takwarar tsohuwa, na rantse Malam yanzu kam tunda mun san yadda take muma lokaci ya yi da za mu ji daɗin rayuwar nan."
Da hannu ya mata alamar ta kwantar da hankalinta yana faɗin "Kin ga dama na riga na gama shirye-shiryen komai, wannan al'amari da kika ɓullo da shi yasa naji jikina babu ƙwari, Shiyasa ma nace sai komai ya daidaita mun san yadda take tukun mu tashi ɗin."

Cikin yanayin farin ciki Inna tace "Lokaci ya yi da za mu sha romo, yanzu dai zuwa yaushe ne tarewar kuma a ina ne za mu zauna ɗin?"
Baffa yace "Mu je ɗaka" tare da nuna mata ɗakin da hannunsa. Babu musu suka nufi ɗakin Inna suka zauna kan tabarmar da ke shimfiɗe tsakar ɗakin.
Cike da zaƙuwa Inna tace "Yauwah Malam, duk na ƙagu naji amsar wallahi, a ina ne gidan kuma yaushe za mu tafi?"
Fuska sake Baffa yace "Gobe-goben nan za mu tashi, ba za mu tafi da komai ba sabkda na saka gidan ma a kasuwa, abun da ya rage kawai ki fara shirin shiga rayuwar daula."
Guɗa Inna ta yi tare da faɗin "Daɗi kashe takwarar tsohuwa, amma Malam wai har da shegiyar nan za mu tafi?" Ta faɗa lokaci guda yanayin fuskarta na sauyawa, shima Baffa hakan ne ta kasance a nasa ɓangaren, cikin kakkausar murya yace "Da ita za mu tafi mana, Kinga ko Mai gadin gidan namu ne yace yana so shikenan sai a ɗaura Kinga buri ya cika kenan, dole dai kinga tana ƙarƙashin ikonmu har zuwa lokacin, in muka yi niyya ma sai mu ba shi kuɗaɗe mu sa shi ya azabtar da ita, har ciwon zuciya ya kamata ta bunga murus har lahira, kin ga haƙarmu ta cimma ruwa."

Fuska sake Inna tace "Kai Malam, kai fa ƙarshe ne, yanzu dai bari na samu na rabar da kayana Tunda ba su da amfani."
Dakatar da ita baffa yayi da faɗin"Ki bar su ciki kawai ba sai kin bayar ba, kayan da ba wasu na kuzo mu gani ba ne, ita dai wannan yarinyar ta tafi da nata, don kuwa bayan ciyarwa ba zan kya tufatar da ita ba tunda ta ƙi fidda talaka kamar yadda nace."
"Tsinanniya ba" Inna ta ƙara da nata zagin daga haka ta fita ta sanar da Hamra ta haɗa dukka kayanta gobe z asu bar gidan. Murna fal cikin ranta tace "To Inna" tunaninta za ta bar gidan ne baki ɗaya. Murnarta ta katse ne da maganar Inna "Shegiya ki ma daina murna wallahi, ba za mu ɗauki ma'aikata a gidan ba, duk ke za kike yi tunda dai ba za ki fitar da miji ba." Daga haka Inna ta juya ta bar Hamra da karatun wasikar jaki yayinda mamakin Inna ya mamaye ruhinta, kalmar da tafi tsaya mata a rai ma ba ta wuce "kin ki fitar da miji ba".
"Wai na ƙi fitar da miji?" Ta tambayi kanta.
"Sau biyu ina kawowa ana kai tallansu gaba, sai kuma yanzu da na ajiye zancen za su dame Ni, lallai kuwa, wannan Hamra da kuke gani ba ta da ba ce, wayayya ce wacce ta kammala secondary school ta kuma je islamiyya." Daga tayi ƙwafa ta fara haɗa trolley nata.

************************************

*02:57pm*
*Isawa*
*Bauchi State.*

Gida ne mai ɗauke da baƙar ƙofa, ginin gidan ginin block wanda ba a shafe shi da siminti ba, siririn lungu ne daga ƙofar gidan zai sada ka da wata ƙofar mai launin ja wacce za ta sada ka da wani zaure, cikin zauren akwai wata ƙofa ta ɓangaren kudu wacce ke nuna alamun ɗaki ne ciki sai kuma wata ƙofar ta ɓangaren Arewa wacce za ta sada ka da ainihin cikin gidan.
Ɗakuna ne guda bakwai jere kamar gidan haya sai kuma bayi guda ɗaya ta can ƙarshen gidan, ta can gefe kuma ɗan ƙaramin ɗakin girki ne wanda aka kafa wasu manya-manyan duwatsu guda uku kashi biyu waɗanda za su iya ɗaukar tukunya lamba 30 da kuma 10.

Yara ne bi-ni in bi ka ke ta kai kawo a tsakar gidan wasun su duƙu-duƙu kai ka ce ba a gaban mata suke ba, wasa wasu daga cikinsu suke yayin da wasu kuma ke cala ihu, masu iyaye a gidan kuma suna nane gefen iyayensu. Abincin ranar da aka gama bai samu sauƙa ba, sboda irin yawan da yake da shi yasa Lantana, turakin gidan wacce keda girki yau ta fara zubawa cikin tirarruka irin na silba, sai da ta zuba cikin trays kusan bakwai tukun ta iya sauƙe tukunya lamba 30 ɗin. Yara na ganin abinci a take suka zo suka kewaye ta kamar kututturen kashi ya faɗi ƙudaje sun taru.
Matar ce ta dubi yaran cike da masifa tace "Wai Nikam don Allah ku ba Ni waje, ga can tire guda bakwai, kai Mahrazu, ka ɗauka muku ɗaya kai da sa'anninka, Salihu kaima a cikin waɗanda na kai can ka ɗauka muku ɗaya, Hafsatu kema ki ɗauka muku ɗaya, Maryam kema ɗaya naku ne, sai ki kai wa su Ashir da Baffa ki kai musu gefe" kallon yaran da ke gabanta tayi tace "Baffa ku bi Yaya Maryam ta ba ku naku."

Sai da yaran suka matsa tukun ta samu sukunin ci gaba da rabon abincin cikin silbobi masu murafe sannan ta zuba a wani ƙatoton tire, daga nan ta zubawa tukunyar ruwa ta ɗauki abincin da ta zuba a tray ɗin ta nufi baranda da shi, kai tsaye a tsakiyar wasu mata biyu da suka zauna akan tabarma ta ajiye kana itama ta samu wuri ta zauna. Babu ɓata lokaci suka fara ci.

_Gidan Mallam Yusha'u kenan, limamin masallacin unguwar wanda yake da tarin mata ɗai-ɗai har uku da kuma yaran da za su kai ashirin da ƴan ɗori. Malam Yusha'u mutum ne da mutane ke matuƙar shakka saboda kwarjinin da yake da shi, kai ko da kuwa irin yaran da suka gagari iyayensu idan aka sada su da shi akan samu sauyi, mata da dama suka zo wurinsa neman addu'a Musamman masu matsala irin ta kishiya, sukan biya shi kuɗaɗe sannan su ba shi aikin da suke so a yi masa._

_Wani abun mamaki shine, duk irin yawan ƴaƴa da Allah ya azurta Malam Yusha'u da shi kullum cikin neman matar da za ta cike masa gurbin ta huɗu yake, a koyaushe zancen sa kenan a wannan lokacin, "Matar da za ta dace da Ni nake nema, nan babu jimawa za ku ji an ɗaura aurena da shallelliyar budurwa." Tun matansa ba sa damuwa har suka fara saka abun a ransu, musamman saboda wannan zancen na malam yasa suka haɗe kansu tun kafin zuwan amaryar da yake ta ƙulafuci duk da cewa babu zaman lafiya a tsakaninsu ko kaɗan, kullum cikin faɗa suke, don ma mijin nasu jajirtacce ne Shiyasa, amma da kullum sai an fitar da sanarwar kisa a gidan in ba a ci Sa'a ba. Ko meye dalilin da yasa suke shakkar mijin nasu.?_


***********************************************

*A GURGUJE*

Kamar yadda aka sanar da Hamra washegari da sassafe su Inna suka tashi, wanka dukkansu suka yi including Hamra wacce ta gama tsaftace gida. Suna karyawa aka kira wayar Baffa, bayan ya gama wayar yace "Sai a yi Himma, ga driver nan ya zo ɗaukarmu."
Inna kamar za ta yi yaya saboda murna, ture plate ɗin abincin da ke gabanta tayi ta ɗaga Khadi tsaye suka nufi ɗakin Inna.
"Kai Inna, ina za mu je kike ja na?"
"Ƴar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login