Showing 114001 words to 117000 words out of 134378 words

Chapter 39 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

103

ne kuma sun ƙi barin parlour yasa ya fara tunanin abun yi. Me Barr zai yi ban da dariya? Sosai yake tsokalar ya Mubeen da idanuwansa wanda hakan ya hasala shi matuƙa, ganin yadda ƴanmatan ke ƙara himma ya sa ya ba su wuri ya koma kusa da Ya Ja'afar wanda ke wani zancen cikin ransa, hakan kuwa bai wuce yadda ya rasa wannan kyakkyawar kadara ba.
Da abun ya kai shi ƙarshe ma miƙewa yayi a fusace ya bar parlourn, hakan sosai ya ba wa Barr dariya.

Yammacin ranar iyalan Dadda suka fara dirowa tun daga kan Alhaji Isma'il, mahaifin Ya Ja'afar wanda yake wa ga Dad ɗin Hamra, Alhaji Salihu wanda ke bin Alhaji Isma'il, Dr. Umar ma ya iso, shi kuma ƙanin Dad ne, iya mutum uku ne ba su iso ba, wanda dukkansu matan aure ne, Hajiya Amina, tana aure a Kano, Hajiya Maryam tana aure a Katsina sai kuma autar Dadda, wacce Nurse in charge ce a wani ƙaramin asibiti, ita kuma tana aure ne a Hadejia.

Ganin dukkansu ma sun hallara yasa Dadda haɗo kansu dukka a parlournta, mamaki kowa yake na rashin sanin dalilin kiran da ta musu, amma da suka yi arba da Ammiy sannan suka ga kamannin matar ɗan'uwansu yasa kowa ke ayyana wani abun cikin ransu.

Bayan sun gaggaisa Dadda ta dubi yaran nata tace "na san dukkanku kowa da abun da yake tunani game da kiran da nayi muku, to ba dai komai ba ne sai zuwan Rahanatu yar Habiban Habu ɗan'uwanku, wanda sosai ta kyauta da ba ta jefar da mu ba tun da abun da ya haɗa yanzu babu. Kamata yayi ma a ce ku ɗin nan ku ke ziyarar, amma dai tun da ita ta zo alhamdulillah, Allah ya ba ta ladan ziyarar"
"Amin" suka amsa tare.
Duban su Ya Mubeen da ke zaune ƙasa tayi tace "Ga kuma yaran Rahanatun har da su aka zo, oh Ni Assha, wato dai da Habiba ma na raye da ɗiyarta Assha ai ta yi aure ko?"
Alhaji Isma'il ne ya murmusa yace "Dadda ai sa'ar su Ramla ce Hamra, Allah dai ya mata rahama."

"Amin" Dadda ta amsa cike da jimami sai kuma ta ƙara da faɗin "Yo su Ramla ai sun wuce a kira su da ƴanmata, yara kitiƙa-kitiƙa da in batun aure ake da yanzu su iyaye ne?"
Shiru dukkansu suka yi musamman Alhaji Isma'il da Alhaji Salihu waɗanda su ne iyayen Ramla da Sa'adatun kuma tun ba yau ba Dadda ke saka su gaba akan su aurar da su kada su yi kwantai, to su kuma yara sun ce karatu za su yi, takamaimai ma ba su da manema bare a yi auren. Maganar Dadda ce ta dawo da su daga duniyar tunani "Dole ku yi shiru mana tunda ba ku da zuciyar da za ku aurar da su, Allah dai ya kyauta." Tsumu suka yi dukkansu suna kallon kallo. Daga bisani Dadda tace

"Kuma biye da Ni ai ko?"
"Eh" suka faɗa a jumlace
"To madalla, nima dai kun gan Ni, ban san dalilin zuwan Rahanatun ba, amma tun da ga ta nan sai a yi magana, Rahanatu muna sauraronki."
"To Dadda"
Daga nan dai Ammiey ta buɗe baki ta bayyana Hamra a matsayin jikar gidan kuma ɗiyarsu, ta labarta musu yadda suka haɗu da ita, sannan tace
"Hausawa suka ce, waƙa a bakin mai ita, ta fi
daɗi, saboda haka Hamra, ki labarta musu yadda komai ya kasance a taƙaice."
Buɗe baki Hamra ta yi ta fara labarta musu komai. Sosai suka tausaya mata ainun, Hajiya Dadda sai face hanci take tana kuka tare da tsinewa su Baffa tana faɗin
"Tabbas, wannan jar fuskar ta Sule babu alheri, ashe dai baƙar zuciya gare shi, Allah ya saka mana cutar da mu da yayi."
Jiki sanyaye dukkansu suka amsa da "Amin"

Barr. Ya yi gyaran murya sannan ya ƙara da faɗin "Babban abun ma Hajiya ba wannan ba ne."
Jin maganar Barr ya sa Dadda mayar da gaba ɗaya hankalinta gare shi tana jiran jin me yafi irin wannan gallazawa da izayar rayuwa da jikarta ta rayu ciki.
Sai da Barr ya ƙara gyara murya sannan yace "Alhaji Abubakar Musa, da kuma matarsa Hibbatullah, an an cewa ƴan fashi ne da dare suka kashe su sannan suka gudu da Hamra ɗiyarsu, amma a iya sanina lokacin babu wanda ya san su waye waɗannan ƴan fashi kuma a lokacin ba a yi wani kyakkyawan bincike da zai bayyana su."
"Ƙwarai kuwa Ɗan nan" Dadda ta faɗa tana gyaɗa kai.
"To jama'a, shi dai wannan mutumin da ya ɗauki Hamra tare da wasu mutane su ne suka kashe Alhaji Abubakar da matarsa, saboda gudun kada a gano shi yasa ya tafi da yarinyar, ya kuma gallaza mata ne saboda kada ta yi doguwar rayuwa, duk wata kadara da suka mallaka shi ne yake riƙe da ita."

Take fuskarsu ta cika da zallar mamakin Sule, mutumin da Dad ya ɗaukaka kamar jininsa ne ya aikata haka? Tabbas sun ƙara yadda da cewa mutum ba abun yadda ba ne. Allah sarki Dadda, tun da Barr ya kai aya ta fashe da kukan ban tausayi, yaronta mafi soyuwa gare ta, yaron da kullum cikin faranta mata yake ba ya son ɓacin ranta, wasu mugaye suka mata yankan ƙauna da shi. Tabbas ba za ta taɓa yafewa wannan mutumin da masu mara masa baya ba. A ɓangaren su Alhaji Isma'il sosai abun ya tsaya musu a rai, suma kuma cikin rayukansu sun ƙudiri karɓawa waɗanda aka zalunta haƙƙoƙinsu, ko da kuwa shi ne Abu na ƙarshe da za su yi a rayuwarsu.

Tsit ɗakin yayi banda ajiyar zuciyar da Dadda ke sauƙewa. Barr da kansa ya kwantar musu da hankali ya kuma sanar da su a gaɓar da suke, ana san ran ma sati mai zuwa za a saurari ƙarar a High Court da ke jahar Bauchi. Lallai sun jinjina wa Ammiey bisa wannan aiki da ta jajirce a kai, wanda ita ta nuna musu hakan ba komai ba ne, ai an riga an zama ɗaya.
Babu wanda ya bar parlourn haka aka ci gaba da ƴan zantuka kowa na tofa irin yadda ya karanci rashin gaskiya a tattare da Sule, shi kuwa Barr yana naɗe jawabai.

Barr ne ya fara tashi bayan ya ɗauki excuse ɗin zai je gidan aminin mahaifinsa, wanda ya yi hakan ne don ya ƙara ba su dama su jajanta al'amarin a tsakaninsu. Bayan tafiyarsa Dadda ta dubi Hamra wacce kanta ke duƙe tace
"Matso kusa Aishatu, Matso kusa da Ni naji ɗuminki, Matso don Allah."
Ta faɗa cikin rawar Murya, take Hamra ta miƙe ta ƙarasa kusa da Dadda, hakan kuwa ya rage mata wani abun da take ji, don kusancinta da Hamra ya rage kaso da yawa na kewar ɗanta da take yi. Haka sauran jama'ar parlour n ke bin su da kallon tausayawa. A ɓangaren Yaya Ja'afar kuwa har da jimamin rasa wannan zankaɗeɗiyar budurwar a matsayin mata da yayi tun da jiya Ya Mubeen ya sanar da shi cewa matarsa ce.

Wayarsa ya ɗauko ya fice daga waje, Whatsapp group na family ya shiga yayi sallama, wasu tsiraru suka amsa, nan ya fara typing, ganin yana typing tsawon lokaci kuma babu abun da ya tura yasa marasa haƙuri daga cikinsu fara faɗin, wai me kake typing ne haka Jay? Me ya faru? Kowa dai da abun da yake faɗi musamman waɗanda ke gadi kuma a cikin gidan da dama can suna zaman jiran jin me yake faruwa a sashen Dadda sun kuma san cewa dai shi mazaunin can ne. Bayan ya gama typing a gurguje ya tura musu da cewa, Hamra ɗiyar Uncle Abubakar ce aka samu, amma dai ba zai ƙara da komai ba, duk mai son jin yadda abun ya kasance sai ya zo ya gane ma idanuwansa.

Take zance ya fara yawo, ƴanmata suka samar da iyayensu mata, hatta su Hajiya Amina duk zancen ya kai kunnensu, babu ƙaƙƙautawa suka fara dokawa babbansu Alhaji Isma'il ƙira don tabbatarwa, sai dai bai ɗaga ba tun da ya san maƙasudin ƙiran. Ganin yadda Dadda ta mamuƙe Hamra yasa suka haƙura suka watse, don sun san in suka yi magana Dadda cewa za ta yi baƙin ciki suke da kusancinta da jikarta.

Da daddare haka Dadda ke nan da nan da Hamra, Ra'isa ma ta ci albarkacin hakan, dalilin hakan ma yasa Dadda tace tare da su za ta kwana in sun tashi bacci, sosai Hamra ke jin daɗi ganin yadda kakarta ke nuna mata ƙauna, haka kuma irin tarin soyayyarta da ta hango cikin idanuwan baffaninta. Bayan sun ci abinci dare Ya Ja'afar ya wuce da Ya Mubeen zuwa ɗakinsa dake sashensu yana addu'ar Allah yasa kar su Ramla su lura cewa tare suke, don kuwa tsaf za ta ce za ta zo tun da kunya ba ta ishe ta ba, idan kuma yace zai hukunta ta mahaifiyarsu sai ta ga laifinsa tun da dama ita ta sangartar da ita.
Ammiey ma ɗaki aka kai ta, su kuma suka kwana tare da Dadda.

Washe gari da sassafe aka fara shigo da abinci kashi kashi daga sassan gidan. Tuni gida ya ɗau harama, Hamra da Ra'isa dai sai son Barka suke da mutanen gidan duk da ba kowa suka sani ba. Bayan sun karya ne aka fara zarya kowa na shigowa ya gaida Ammiry ya kuma ga Hamra, hatta iyayen su Ramla sun shigo, kuma sun nuna farin cikinsu bisa wannan abun farin ciki da ya faru tun da dai can da sun riga sun fidda rai, haka ƴaƴan Dadda ma da suka shigo gaida ta suka sakarwa Hamra fuska, Alhaji Isma'il kuwa har da faɗin ko zai haɗa ta da da ɗansa a yi ta gida, ita dai duk kunyarsu take ji haka kawai, shi kuwa Ya Mubeen sai da ya ƙware da ya ji zancen Alhaji Isma'il ɗin, hakan ya so ba wa Ammiey dariya ta kuma ƙara tabbatar da zarginta na cewa yaronta iya faɗa soyayyar Hamra dumu-dumu tare da fatan Allah ya sa kar ya nuna halinsa na burus, don da dukkan alamu in ya yi hakan to zai rasa Hamra ne na dindindin musamman da ta ga haularsu me ɗauke da zaratan samari.

Bayan fitarsu haka Ramlat da Sa'adatu har ma da sauran ƴanmatan da b su kai su ba suka shigo sai nan da nan suke da Hamra, ita dai Sa'adatu ta fi mayar da hankalinta kan Ra'isa da ta gano cewa ƙanwar crush ɗin nata ne, idan ta samu gindin zama wurinta a nata tunanin mallakar Ya Mubeen zai zo mata ne da ɗan sauƙi, cikin ƙanƙanin lokaci suka saki jiki da su, sabo ya fara shiga tsakaninsu, a nan ne ma suke tambayar numbern wayar Hamra, da ta ba su cikin gaggawa da zaƙuwa suka tura family group tare da faɗin a yi adding ɗin ta, ita ce ɗiyar Uncle Abubakar da aka samu. Babu ɓata lokaci admin a'a group ɗin ya saka ta, sannan kuma wasu daga cikin dangi suka fara jera mata ƙira sai dai wayar a can cikin ɗakin Dadda ta bar ta su kuma suna parlour.

Wuraren ƙarfe sha ɗaya sai ga Momyn Katsina da Ummin Kano sun diro gidan tare da ƴaƴansu, can bayan Azahar Autar Dadda Maimuna ta iso daga Hadejia bayan tashinta daga morning duty ɗinta.
Sosai gida ya cika kamar ana aure, Dadda da kanta take ba su labarin yadda komai ya kasance wani wurin kam har da ƙari take, sun matuƙar tausayawa Hamra irin rayuwar da ta yi cikin rashin sani, da a ce sun san tana raye ai da babu abun da zai sa ta rayu da miyagun mutane masu son zuciya haka. Sai dai abun ya musu sauƙi da suka ji cewa Ammiey da ɗanta suna gab da gamawa da mutanen nan. A lokacin da Dadda ta labarta musu auren Hamra da Malam kuwa babu wnada bai koka ba cikinsu, tabbas labarin ya taɓa zuciyarsu fiye da zato kasancewar ba su taɓa jin makamancin hakan ba. Amma a yanzu suna fatan Hamra ta yi rayuwar farin ciki da walwala don ba kowa zai iya jure tarin kalubale da damuwar da ta jura ba.

Kwana ɗaya suka ƙara, daga nan suka fara shirye-shiryen tafiya amma Dadda ta ce ba ta san zance ba, ai nan ɗin ma gida ne, sai da Dr. Umar ya lallaɓa ta da faɗin akwai sauran hujjojin da za su koma su samar in ba haka ba ba za a hukunta mutumin da ya cutar da iyalinta ba, da haka ya ci nasarar shawo kanta ta amince amma ta buƙaci a bar mata ɗiyar Habu ta zauna tare da ita, duk da Dr. Bai so hakan ba amma hakan ne kaɗai maslaha sai ya ba wa Ammiey haƙuri tare da roƙonta da ta bar Hamra, Ammiey ta nuna ba komai, wanda hakan ya ƙara mata ƙima a idon Dadda. A lokacin da Ya Mubeen ya ji cewa ba tare za su wuce da Hamra ba sai yaji babu daɗi, wani sashi na zuciyarsa na jin in ya barta a nan ita kaɗai tabbas za a iya samun matsala, abun da yake ta gudu zai iya faruwa, Gara kawai shima ya zauna a nan ɗin, ko ba komai zai san ta yi da masu farmaki, Ammiry da ta gani dalilin ƙin tafiyarsa sai ta ƙi amincewa tace da shi tare za su tafi, ta yi hakan ne kuma ba don komai ba sai don tana so ya bayyana abun da ke ransa kafin lokaci ya ƙure masa. Ba yadda ya iya haka ya bi su Ammiey suka tafi ba don ransa ya so ba, amma sai da ya tabbatar ya kashe wa Hamra warning kan kada ta kuskura ta sake da Maza duk da cewa ƴan'uwanta ne, itama murmusawa kawai tayi tana fatan abun da zuciyarya ke raya mata game da Yayan nata ya tabbata, daga haka ta musu sallama suka wuce, ita da Ra'isa kuwa har da ɗan kukansu.

A cikin zaman gidansu mahaifinta da ta yi ta fahimci ba ƙaramin so ake wa mahaifinta ba, don kuwa wannan soyayyar da suke masa babu shakka ita ce ta shafe ta itama ta samu nata kason. Da yammacin ranar da su Ammiey suka tafi, Ya Ja'afar ya buƙaci Dadda da ta bar Hamra su fita tare da su Ramla ta ga gari, ba don ta so ba haka ta amince tunda Jafaru ne ya buƙaci hakan, ai kuwa sosai Hamra ta shirya cikin abayar da ta amsheta sai ta ƙara fitowa a ainihinta na balarabiya. Sun ɗan zaga kuwa kamar yadda ya faɗa, sun kuma sha hotuna kamar me duk da cewa ita Hamra wasu hotunan ma ba ta san an yi su ba. Magriba lilis suka dawo gida.

Kwanaki uku Hamra ta yi Wanda cikinsu ta yi sabo da danginta, ba ta fuskanci tsangwama ko tsana wurin kowa ba, hatta matan yayun mahaifinta ma sun nuna mata so, sabo ne ya shiga tsakaninta da Ya Ja'afar wanda duk hakan yana yi ne don ya samar da kusanci tsakaninsu, tabbas ya tabbatarwa kansa cewa son Hamra yake, ko da ya gano cewa Hamra ba matar Ya Mubeen ba ce tsam ya gano cewa dole shi ma son ta yake, kuma magana ta gaskiya shi ma ba zai iya bar masa ita ba, dama ai an ce mace allura ce cikin ruwa, mai rabo kan ɗauka, don haka kowa tasa ta fisshe shi.

Ranar Lahadi da Yamma su Hamra suka wuce Bauchi kasancewar za a fara zaman wannan Shari'a ne ranar Litinin, su Dadda, Alhaji Isma'il da Alhaji Salihu, Dr. Ma da kuma wasu daga cikin samari da ƴanmatan family suka sauƙa a Bauchi. Thank God Gidan babba ne, an samarwa kowa wurin da zai zauna ɗin. Su Hajjaju ma duka sun zo, haka nan kowa ya hallara kowa yana addu'ar Allah ya sa a samu nasara a wannan ƙara da za a yi, wacce ta Malam ita za a saurara gobe, next week Kuma ta Baffa.

Ranar Litinin tun da garin Allah ya waye Hamra ke jin zuciyarta wani irin, amma in ta tuna cewa Allah na tare da su sai ta yi hamdala ta ci gaba da ambatonsa tana ƙara roƙonsa kan ya ba su Sa'a. Da wuri kowannensu ya shirya, bayan kowa ya shirya motocin su suka fice daga gidan Ammiy zuwa High Court Bauchi of justice da ke Bauchi.



*React and share fisabilillah*
*Diamond Bhatool 🦋*
*#FATISAHWRITES*
[9/13, 5:32 PM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*


https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY SEVEN: Justice and Redemption II*

*High Court of Justice, Bauchi, Bauchi State*

Cike kotun take maƙil da jama'a kasancewar yau ranar Litinin ce, akwai ƙararraki kusan uku da za a saurara a yau ɗin, ɗaya daga cikin kuma akan kisan kai ne da wasu matasa suka yi na wani ɓarawo da ya yi sata a unguwarsu, sai kuma ƙarar Malam Yusha'u da za a saurara matsayin ta biyu, sai ta ukun da ba za a ce komai a kai ba.

Yadda mutane ke kai kawo da sanyin safiya cikin kotun zai tabbatar maka da cewa ƙarar ta shafi wani babban mutum mai babbar haula. Misalin ƙarfe tara na safe danƙareriyar motar da motocin ƴansanda suka saka a tsakiya ta Kunno Kai, hakan yasa kowa ya fara shiga ciki ganin alƙali ya iso, cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya shiga ya samu wuri ya zauna, wasu kuma suka tsaya a can baya saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login