Showing 72001 words to 75000 words out of 134378 words
tsoro tare da saitawa, nan ta arta a guje don tseratar da ranta da kuma mutuncinta tunda ba ta san su waye mutanen ba, ba kuma ta san ƙudirinsu ba, ba ta cire tsammanin ko masu kashe rayuka ne. Ganin ta arta da gudu yasa suma suka fara gudun don ganin sun cin mata, Allah Sarki Hamra, Allah ne kawai bai sa zuciyarta tsayawa ba a lokacin don kuwa matuƙar tsorata ta tsorata wanda mutane da yawa da su ne babu abun da zai hana heart ɗinsu tayi failing musamman waɗanda dama can suna da raunin zuciyar.
Gudu take sosai amma yunear jikinta ba ta yi tasiri wurin dakatar da ita ba, ganin sun kusa cin mata yasa ta yasar da trolley ɗinta don ceton ranta. Tana cikin gudu kwatsam hasken wata mota ya dalle mata idanuwanta ta yadda ba damar ta ci gaba da gudun saboda ba ta ganin komai sai shi. Wannan yasa ta ci birki tare da saddaƙarwa kanta ita kam ta gama yawo a duniyar Rahmanu, Shikenan ta tabbata dai mutuwar wulaƙanci za ta yi a hannun ƙasƙantattu.
*React and share fisabilillah.*
Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY SIX: opportunity escaped.*
*El-Mubeen's mansion, Victoria Island , Lagos State.*
Bayan CEO Mubeen ya daidaita parking Nihla ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar fita sai dai ya riga ta yi locking. Kallonta ta mayar ga mahaifin nata tana zumɓura baki, cike da shagwaɓa ta kira sunansa "Abieee" tare da jan ƙarshen sunan, shima dai fuska haɗe yace "Ba dai kin raina Ni ba Angel? Mu je ciki, i'll make sure that I teach you a lesson."
"Abie" ta ƙara kiran sunansa sanin ba za su wanye ƙalau ba in ba ta nemi sulhu ba. Cikin halin ko in kula da ya arawa kansa yace "out of my car!"
"Abieee" ta ƙara faɗa sai ga hawaye na zubowa daga idanuwanta, ba tare da ya ankare ba rauninsa ya bayyana, hannunsa ya miƙa mata alamar ta sanya nata cikin nasa, babu ɓata lokaci ta yi hakan. Shafa hannun nata yayi yace "Ba dai kin fara musu da Abie ba?" Kanta ta jijjiga tana faɗin "Ka yi haƙuri Abie, ba na ƙarawa, don Allah."
Fuskar mahaifiyarta kawai yake gani a irin yanayin da tayi magana, lokaci guda ya fara tunano irin moments ɗinsu shi da Marigayiyar matarsa wacce ya bayar da zuciyarsa gare ta, duk da cewa mutuwa ta musu yankan ƙauna amma har ila yau tana cikin ransa kuma ya gagara samun macen da za ta iya maye masa gurbinta.
Nana Khadijah! His only love, ɗiyar uncle ɗinsa ne wan mahaifinsa, kyakkyawa kuma wayayyar mace wacce ta san ƙima da darajar mutane, macen da san haƙƙin aure kuma take ƙoƙarin sauƙe su, macen da take daraja dangin mijinta ta kuma kasance wacce ake ƙira da macen ƙwarai. A tsarin da ya yi wa rayuwarsa, zai rayu da ita ne har numfashinsa na ƙarshe don shi ko a tunani bai raɓa kawo cewa ita za ta tafi ta bar shi ba. Sai dai kuma, kana naka ne, ubangiji na nasa, a lokacin da ta sauya rayuwarsa ya zama mutum kamar kowa, lokacin da take shirin ƙarawa rayuwarsu farin ciki ta rasa Tata rayuwar, sanadiyyar haihuwar Nihla, idan ya duba irin rashin da ya yi sai ya ga kamar shi kaɗai ne ubangiji ya jarraba amma da ya kalli fuskar yarinyarsu Nihla sai ya ji sauƙi da raɗaɗin rashin ta wanda ya gagara koɗewa tsawon shekaru goma sha biyu ya ragu. Tabbas yana so da ƙaunar Nihla fiye da komai idan ka cire Annabinmu, mahaifiyarsa...to ita ce gaba kuma, ita kaɗai ce ke tuna masa da matarsa, sanadiyyarta ko yaushe yana cikin yi mata addu'ar rahama da gafarar ubangiji tare da roƙon Allah ya haɗa su a gidan Aljanna.
Shirun da Nihla ta ga mahaifinta ya yi yasa ta ji babu daɗi, duk da cewa ba ta san mahaifiyarta ba, amma yadda mahaifinta ke nunawa yasa ta san cewa mamarta na da muhimmanci gare shi, sau tari idan ta tambaye shi a makamantan lokutan da yake faɗawa duniyar tunani idan yana kallonta, yakan amsa mata da cewa "Ina tuna Mahaifiyarki ne!"
Sajensa ta shafa tare da ƙoƙarin samar da eye contact tsakaninsu. "Abie" ya ɗago a ɗan firgice "I'm sorry, ba zan ƙara ba." Tana faɗar haka ta ɗauke hannunta daga sajenshi ta kama kunnuwanta biyu tana jansu"Ba zan ƙara ba, na tuba."
"Kamar dai mahaifiyarta" ya faɗa cikin ransa a zahiri kuma ya yi murmushi yace "Is ok, Amma idan kika ƙara babu ruwana da ke." Kafin ya rufe baki tace "ba ma zan ƙara ba, ubana mai share min kukana"
Ƴar ƙaramar dariya yayi don shi kullum cikin sabon mamaki take sanya shi.
"Yauwa Abie, na gode, Ina son ka, a kan ka tsaf zan iya kashe ɓera.."
"You said?"
Dariya tayi ta maimaita masa "A kanka tsaf zan iya kashe ɓera..."
Shima dariyar ya yi tare da jan kuncinta yace "Let's get in, Ammiey Kar ta gaji da jira ta shiga damuwa.." ba ta ƙarasa jin mai zai ce ba ta ɓalle murfin motar ta fita tare da shigewa da gudu, ko da ya fito ya ga har ta kusa shiga ciki sai ya harɗe hannayensa a ƙirji ya bi ta da kallo yana murmusawa, ganin ta shige yasa ya bi bayanta.
Kamar yadda suka yi tsammanin kuwa, Ammiey ce sai Ra'isa a katafaren parlourn suna kallon news wanda lokacin kuma hankulansu ya bar wurin kallon ya koma ga Nihla da ke jikin Ammiey tana mata shagwaɓa.
Ƙarasawa yayi wurinsu ya zauna gefen Ammiey tare da kwantar da kansa jikinta kamar wani ƙaramin yaro, can ƙasan maƙoshi yace "Barka da gida Ammiey."
Fuska sake Ammiey ta saki Nihla ta mayar da hankalinta ga yaronta "Kun dawo lafiya?"
"Alhamdulillah Ammiey."
"Ma sha Allah, sai ka yi wanka za ka ci abinci ko kuwa?" Yamutsa fuska ya yi yana faɗin "Bari dai na fara wankan."
"Ok, Babu damuwa."
Jim ya yi shiru yasa Ra'isa da ke danna laptop ɗinta ta mayar da hankalinta ga yayan nata tace "Masā'ul khair akhy."
Kamar ba zai amsa ba can yace "Masā'ul ward, kaifa yaumuki?"
"Bikhair...."
"Māsha Allah." Daga haka kuma bai ƙara cewa komai na. Ƙwalla kiran maa'aikaciyar gidan Ammiey tayi sau ɗaya "Taqiyya!"
"Na'am Sayyidaty" ta amsa daga madafar abinci tare da ƙarasowa parlourn, kanta ƙasa ta miƙa gaisuwarta cikin harshen Hausa ga CEO Mubeen kasancewar ta san bai fiye son yin larabci ba kamar mahaifiyarsa. Amsa mata yayi daga nan ya miƙe ya bar wurin, ganin haka yasa Taqiyya kiran Nihla don watsa mata ruwa...kamar dai yadda take ɗawainiya da ita.
Bayan sun bar wurin Ammiey ta murmusa. A tare suka fito kamar haɗin baki, Dining kai tsaye ya nufa, Ammiey ta yi wa Ra'isa alama ta hanyar taɓa ta, bayan ta Yi serving ɗinsu kuma ta dawo ta ci gaba da abinda take. Har suka gama ci babu wanda ya ce uffan sai hamdala, daga nan suka dawo cikin family ana surutu wanda duk Nihla ce da Ra'isa ke jan ragamar hirar sai kuma Ammiey da ke tsoma bi lokaci bayan lokaci. Kamar wanda aka tsikara Nihla ta duni Ra'isa tace "Ammiey Ra'isa..."
Ɗago kanta tayi tare da ɗage mata gira
Mayar da kallonta ta yi ga Ammiey ta ƙira sunanta itama "Ammiey"
"Ina jin ki Nihla"
"Dama can ashe ba iya Ammiey Ra'isa ce kika haifa ba ashe su biyu ne????"
Jujjuya maganar Ammiey ta fara jin wani batu da Nihla ta zo musu da shi.
Jin Ammiey ta yi shiru yasa tace "Ammiey Ra'isa ashe ku ƴan biyu ne?"
Shi kansa CEO Mubeen bin ƴar tashi yake da kallo yana jiran yaji ko daga ina ta samo wannan bahagon labarin nata maras makama.
"Waye ya faɗa Miki Nihla?" Ammiey ta tambaya har lokacin fuskarta ɗauke da mamaki.
Amsa ta ba su da faɗin "Ɗazu na ga ɗayar ai, mai kama da Ammiey Ra'isa."
Gaban CEO Mubeen ne ya buga don kuwa lokaci guda ya gano wa take nufi, tabbas shima da a ce Ra'isa ce gaba da shi da zai iya faɗin kwatankwacin abinda Nihla ta faɗa sai dai shi aka fara haifa ya kuma san adadin ƴaƴan da Ammiey ta haifa har zuwa rasuwar Daddysa. Shiru ya yi yana jujjuya abun cikin ransa tare da dakon amsar da Ammiey za ta bayar. Jin Ammiey ta yi shiru yasa Ra'isa kiran Nihla ta dawo kusa da ita tare da kunna mata cartoon a system ɗinta, wannan ne dalilin shashantar da zancen saboda can dama ba shi da wata mahanga ko direction.
*Washe gari*
Bayan Hamra ta yi sallar asubahi ta yi maza ta yi azkar da ƴan addu'o'inta tare da neman sa'ar ubangiji wurin samun wannan aiki da take nema. Bayan gari ya waye kuma ta nufi cikin ma'aikatar sai dai ba ta samu dama ba saboda an sanar da ita cewa committee na masu ɗaukar aiki suna gab da fitowa da sanarwa ta ɗan jira.
Tun daga wannan rana ta mayar da masallacin kamar ɗakinta, a nan take bacci amma kuma sosai ta samu damar samar da kusanci tsakaninta da mahaliccinta, sayan abinci ne kawai ke fitar da ita daga masallacin. Tsawon kwanaki huɗu tana zaune a El-Mubeen Luxuries ba ta ƙara haɗuwa da CEO Mubeen ba, haka zalika Nihla, yarinyar da taji tana ƙauna lokaci guda har take jinta tamkar jininta. A rana ta biyar Nihla ta biyo ta ma'aikatar bayan ta sa driver ya kawo ta direct daga school wai ita a motar Abie ɗinta za ta koma gida. Tunda suka haɗu suke surutu sai dai yau cikin Sa'a ta hango CEO Mubeen tahowa, tana ganin haka ta yi wa Nihla sallama ta koma masauƙinta. Bayan su Nihla sun tafi, tun a mota ta fara damun Abie ɗinta akan ya ɗauko musu Ammiey Hamra ta dawo gidansu da zama, sai dai banza ya mata ba tare da ya ce komai ba.
Alhamdulillah, cikin Sa'a da ikon mai duka, Hamra ta fito sallar azahar ta ga takarda nanne jikin wani notice board da ke kusa da masallaci na cewar Ranar Litinin za a yi tantancewa don ɗibar sabbin ma'aikata, a wurin ta yi sujjada ta godewa Allah, dama fargabarta ba ta wuce rashin kuɗi ba, gaba ɗaya kuɗaɗen da ke wurinta sun ƙare ta ma rasa yadda za ta yi ta dai miƙa komai ga Ubangiji,ga shi kuwa ya isar mata. Ranar Litinin kuwa ta fitar da WAEC result ɗinta ta shirya, ƙarfe bakwai ta fita tare da tambaye wasu mutane venue ɗin da za a yi interview ɗin wanda ta riga ta haddace a jikin takardar sanarwa. Tabbas ta sha mamaki kam, ashe sashen da take admin block ne, ba komai ba ne daga EL-MUBEEN'S LUXURIES... Don kuwa wurin da aka kaita har sai da ta ji tsoron neman aiki a wannan wuri don gani take kamar ya fi ƙarfinta. Tabbas El-Mubeen Luxuries ba ƙaramin Company ba ne da ya yi fice a fannoni da dama da suka shafi ci gaban zamani sai dai sun fi fice a ɓangaren samar da kayayyakin more rayuwa da zamani ya zo da su, motoci da sauran machines da ke sauƙaƙawa mutane aiki. Akwai sashe na musamman da suke zane, zanen motoci waɗanda ba a taɓa ƙera irinsu ba, waɗannan zane da suke yi kuma ba kara zube ake yi ba, sai an tsara yadda wannan mota za ta kasance tun daga kan injinta da kuma wata siffa ta musamman da wasu motocin ba su da su. A cikin El-Mubeen Luxuries akwai sashen da suke yin takalma na ƙasaita da kuma gama gari, akwai sashen da ake kaya...in nace kaya ina nufin English wears. Daga haka ya isa ku yarda cewa El-Mubeen is luxurious industry.
Bayan kowa ya bayar da takardunsa, sakamakon wadatattun ma'aikata a take aka dudduba, aka kuma zaɓi kowa a ɓangaren da ya cancanta, alhamdulillah, Hamra ma ta samu a ɓangaren share-share da goge goge amma a sashen admin block. Bayan orientation da aka musu ne ma ta fahimci cewa aikin ba wani yawa ne da shi ba amma kuma akwai kyakkyawan payment. Murna sosai Hamra ta yi tare da yi wa Ubangiji godiya, addu'o'i masu kyau kam Yaya Hamid da Ummie sun sha ta, daga nan kuma ta koma masallaci kamar yadda ya zama masauƙinta. Washe gari Hamra ta fara aiki, tsawon sati gana aiki amma kuma ba ta taɓa haɗuwaa da CEO Mubeen ba, hasali ma takan share shashensa ne wanda yake da ɗan girma kaɗan kafin zuwansa ta kuma jera komai tsaf-tsaf.
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya mata har tsawon wata guda har ranar kuma ba ta ƙara ganin Nihla ba, hakan kuma ya sa ta ji babu daɗi don kuwa yarinyar ta mugun shiga ranta ne fiye da tunaninta. A yau bayan ta kammala ayyukan ta tana shirin komawa masallacin ta jiyo Muryar Nihla na ƙwala mata ƙira, da sauri ta dakata tare da juyawa tana tsurawa Nihla da ke tahowa wurinta da gudu. Bayan ta iso ta rungume ta tana farin ciki, ji tayi ina ma su kasance tare saboda yadda zuciyarta ke jin wani irin sukuni a kasancewarta da Nihla. Masallacin suka tafi tare suna ƴar hirar su wacce kusan duka Nihla na mata maganar Ammiey Ra'isa ne tana faɗin wai suna kama da ita. Shashantar da zancen tayi duk da cewa zuciyarta da farko ta fara hasaso mata abun da ba shi ne ba. A nan suka yi salla suka fito waje, wani wuri suka samu suka ci gaba da hirar su. Ba su yi tsammanin komai ba sai ga CEO a kansu yana bin su da kallon za ku sani. Hamra wacce ta fara lura da tsayuwarsa sosai ta tsorata tana zazzaro idanuwa.
"In...in...Ina yini" wani banzan kallo ya aiko mata tare da faɗin "Ke waye? Waye ke nace?" A zafafe. Jikinta na rawa tace "Ba muguwa ba ce ni....Na rantse maka, Ni ba muguwa..."
"Me na tambaye ki? Ke wacece? Don't let me repeat myself." Nihla ma wannan karon ta tsorata da yanayin Abie ɗinta, take ta ƙanƙame Hamra tare da cusa kanta a cikin Hamra tana jujjuya kan nata.
"Ni maa'aikaciya ce, ina share-share a nan!"
"Ƙarya kike!" Ya dakatar da ita a tsawace
"Ina shaidar ki?" Cikin ikon Allah ta fito da I.D card ɗinta jikinta na rawa ta zaro shi daga cikin rigarta da ta cusa. Karɓa yayi ya kalla tsawon wani lokaci sannan ya miƙa mata yana faɗin "Za ki bar aiki a nan...." Bai ƙarasa ba Hamra ta janye Nihla da ta ƙanƙameta gefe sai ga ta gaban CEO Mubeen durƙushe har tana taɓa ƙafafunsa da ke cikin cover shoe mai tsada da kuma kyau.
"Don Allah Sir, kar ka min haka wallahil-azim Ni ba muguwa ba ce, ban zo da komai ba sai don na nemi halalina, kar ka durƙushe samun mabuƙacin da ke ƙasanka na roƙe ka da Allah!"
Ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo tare da fashewa da kukan da ya fi na farko.
Abun mamaki mutane ne kusan goma maza da mata suka kewaye su tare da kallonsu, abun da ya ɓata kuma ba sa jin Yaren da take maganar da shi ko kaɗan.
Janye ƙafarsa CEO Mubeen yayi don ganin yadda ƙarfi da yaji yarinyar ke son saka zuciyarsa yin rauni ala dole sai dai bai kai ga matsawa ba yaji Nihla ta ƙanƙame shi tana kuka
"Abie....."
"You see?" Ya faɗa a kausashe yana nunawa Hamra Nihla da take kuka
"Ki faɗa min uban Meye kika mata har take kuka a kanki? Ki faɗa min me kika mata don ba haka Angel take ba." Ya ƙarasa cikin sanyin murya ba kamar yadda ya ɗauko zancen ba. Numfashi ya sauƙe ya dubi Hamra da ta yi shiru yace "Fine! Tunda ba za ki yi magana ba shike nan! Kin bar aiki a nan. Kuma in wani abu kika yi wa angel ki gaggauta ware shi, if not" ya ɗana mata hannunsa alamun za ki sani, ba tare da ya maida hankalinsa gare ta ba ya ɗaga Nihla a hannunsa tare da barin wurin duk irin yadda zuciyarsa ke lallashinsa akan abun da yayi, amma kuma ɗaga ɓari na zuciyar tasa ya fi ƙarfi shi yasa ya wuce abun sa hankali kwance.
Allah Sarki Hamra, a gurin da ya bar ta a nan ta ci gaba da kukant ba tare da ta tashi ba, su kuwa mutanen take suka bar wurin duk da cewa ba abun da suka fahimta dangane da abun da ya farun. Tabbas yau tana cikin tashin hankali, wannan shi ake kira da ga ci ga kwanan yunwa. Tana farin cikin aikin da ta samu kuma lokaci guda ta rasa shi, wai shin wace irin ƙaddara ne wannan take bibiyar rayuwarta? Anya kuma akwai yiyuwar ci gaba da rayuwarta? Damuwarta ɗaya ce, ba wai neman wani aikin ba, a ina za ta zauna? Ina za ta samu muhalli? Ko ba ta da hankali ba za ta yi kwanan titi ba musamman yadda ta ji ana cewa ana yanka mutane a Lagos ne kamar dabbobi a kuma wuce a bar su a wurin, babu shakka a yanzu in mutuwa za ta zo gare ta, da gudu za ta rungume ta don ta fi buƙatar mutuwar akan rayuwar, sai dai me? Ba mutuwar wulaƙanci take yi wa kanta fata ba! Meye amfanin irin mutuwar da za a bar ka a titi ba tare da salla ba, ba tare da wani ya ma