Showing 69001 words to 72000 words out of 134378 words
ina za ta dosa tana mai tausaya wa rayuwarta.
*MUBEEN's POV*
Suna isa gida Nihla ta fice daga motar Ba tare da jira mahaifin nata ba kamar yadda suka saba, da kallo kawai ya bi ta tare da sauƙe gajeren numfashi. Shi kan shi abun da ya yi sai yanzu yake gagarumin da na sani, amma kuma idan ya duba wani ɓangaren sai ya ga ba shi da laifi, Kawai Dai yana ƙoƙarin kare abar ƙaunarsa daga mutane, amma kuma abu ɗaya da ya tsaya masa a rai shine, muguwar kamanni da yarinyar ke yi da ahalinsa musamman Ra'isa wacce in da za a jera su tare babu shakka za a yi tunanin jini ɗaya ne, sai dai kuma ai an ce kowa yana da mai kama da shi har mutane bakwai a duniya, to la'alla wannan ɗinma dai kamar waɗancan ɗin ne don iya saninsa ba su da wasu makusanta a nan Nigeria. Da haka ya rarrashi kansa tare da fitowa daga motar. A bakin entrance door suka ci karo da Ra'isa wacce ta fito don duba ko lafiya taga bai shigo ba Nihla kuma ta ƙi kulata.
Ɗauke da ayar tambaya kan fuskarta ta ƙaraso sai kuma yanayin nata ya sauya zuwa murna
"So akhy ashe tare kuke da Angel? But what's wrong with her Ina mata magana ta share?"
Kansa ya kawar tare da faɗin "Babu komai." Ya fara ƙoƙarin wucewa ta gefenta. This is uncommon to her, ba haka yanayinsa yake ba duk da cewa a yanzu ya sauya amma ai ba irin sauyawar da har yakan iya ratsa gefenta ya wuce ba as she knew Shi ɗin mutum ne mai ba wa nasa kulawa.
"Akhy" ta ƙira sunansa. Dakata wa yayi daga stepping ba tare da ya juyo ba. Ƙarasowa tayi har wurin da yake tare da fuskantarsa ta kuma riƙo hannayensa biyu yayin da idanuwanta da nasa suka haɗu
"Are You ok akhy?"
Murmushi ya ɗaura kan fuskarsa tare da faɗin "Yea, lafiya nake, kada ki wani damu, kawai dai gajiya ce."
Shirun dai shine mafitarta sanin cewa ba ya son takurawa Amma yanayinsa ya mugun sauyawa. Itama murmushin ta yafa tare da faɗin "alright. Allah ya sa hakan." Ba tare da ya amsa mata ba ya shige ciki hakan yasa ta bi bayansa tana riƙe baki.
Ko da ya shiga da ya tarar Ammiey ba ta parlour maimakon yayi wucewarsa ɗakinsa kamar yadda ya saba sai ya nufi bedroom ɗin Nihla, a daidai bakin ƙofar ya ci birki tare da sauƙe ajiyar zuciya, a hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar sai dai ga mamakinsa ƙofar a rufe, abun da bai taɓa gani ko ji ba, hakan yasa ya sha jinin jikinsa tare da faɗin "Subhanallah" a saman laɓɓansa.
Cikin sanyin murya ya ƙwalla sunanta ta yadda yasan za ta ji kuma ba zai janyo attention ɗin kowa gare su ba amma shiru ba ta amsa ba, kansa ya manna jikin ƙofar tare da ƙara furta "My Angel! My princess!" Shiru dai again, wannan dalili yasa ya ɗan yi knocking door ɗin sai dai a banza. Ƙara kara kunnensa ya yi jikin ƙofar tare da mayar da hankalinsa gabaɗaya kan jiyo motsinsa daga ciki sannan ya ɗauke numfashinsa gudun kar ya hana shi ji daidai. Kamar dai ya sani kuwa, gunjin kukan gudan jinin nasa ya jiyo wanda hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba.
Bakinsa ya saka jikin ƙofar tare da fatan Allah yasa ta jiyo shi sannan ya fara magana
"Angel! Please open the door and let your dad explain."
Tunda ta jiyo maganarsa kawai sai ta bar ɗakin ta nufi toilet tare da ci gaba da kukanta tana mai jin zafin abun da Abiey yayi a hakan ma ba ta da masaniya akan dakatar da Hamra da yayi daga aiki. Jin ta shiru da yayi ya ƙara ɗga hankalinsa. Da sauri ya juya ya nufi stairs kamar zai yi missing wani step ɗin. Bag ɗin da ke ɗauke da duka Spare keys na gidan ya ɗauko ba tare da samun sukunin duba wanne ba ne, sai da ya dire bag ɗin bakin ɗakik Nihla tukunna ya Zuge zip ɗin tare da juyesu ƙasa ji kake sun ba da wani sauti. Birkita su ya fara yana son duba wanne ne ma ɗaya na ɗakin sai dai gabaɗaya tashin hankali ya hana shi fahimtar hakan sai jujjiya su yake kamar mai gauraya abinci cikin kwano.
Fitowar Ammiey parlour ya yi daidai da ɗaukar wasu keys da yayi yana shirin miƙewa
"A'a, ashe kun dawo." Ta faɗa ta tunkaro wurin da yake tare da mamakin ko me yake da uban keys ɗin da ta gani zube
"Me kuma ya faru haka?" Ta tambaya bayan ta iso wurin
Bai ma ji me tace Ba shi kam burinsa kawai wannan ƙofa ta buɗe. Ja gefe Ammiey tayi ta tsaya tana zubawa sarautar Allah ido.
Wata ajiyar zuciya da ya sauƙe sai da Ammiey da ta jingina jikin kujera miƙewa. Murɗa handle ɗin yayi take ƙofar ta buɗe, yana shirin nausa kansa ciki Muryar Ammiey ta dakatar da shi
"Lafiya kuwa Azizy?"
Juyowa yayi tare da fuskantarta ba tare da ya saki handle ɗin ƙofar ba. Yadda yayi da fuska yasa Ammiey murmusawa ta ce "Shikenan" daga haka ta gyara tsayuwarta tana jiran ganin ikon Allah. Ciki ya shiga da sauri yana waigawa ta ko ina tare da kiran sunanta "Angel! Angel, where are you?" Ya waiga dama ya waiga hagu bai ganta ba, hakan yasa kai tsaye ya nufi toilet ba tare da tunanin ko da gaske can ɗin ta nufa ba, duk abun da yake Ammiey na kallonsa da yake bai rufe ƙofa ba.
Abun da Nihla ta manta shine, ba ta rufe ƙofar toilet ɗin ba, hakan ne ya ba wa CEO Mubeen damar shigewa kai tsaya, tsaye ya tarar da ita tana kallon ƙatoton madubin da ke manne a bayin idanuwanta har sun fara ja ga kuma hawayen da ke rige-rigen fitowa daga idanuwanta. Tsanar Hamra ce ta ɗarsu cikin ransa saboda ganin yarinyarsa a irin wannan yanayin wanda zai iya rantse wa bai taɓa ganinta cikin kwatankwacinsa ba. Ƙarasawa yayi tare da lifting nata up ba tare da ya ce komai ba, ita kuwa cilla ƙafafunta ta fara yi tana dukan ƙirjinsa
"Sauƙe ni Abie, I can't hold it anymore, ka sauƙe ni tunda ba ka son..."
"Shhhh" ya ɗaura yatsarsa kan lips ɗinta
"Abie is sorry, please don't punish him for doing nothing wrong." Shiru ta masa ba tare da ta ce komai ba yayin da ta dakatar da bugun da take kai mishi ta kuma bar cilla ƙafafun da take yi.
A kan bed ɗinta ya dire ta sannan ya fara aikin rarrashi amma kamar wa teddies ɗin da ke kan gadon yake yi wa. Dafe kansa yayi tare da furta "Ya Allah" sai kuma ya mayar da kallonsa gare ta.
Yana shirin yin magana Ammiey ta shigo tana faɗin "Yau kuma faɗa aka yi da Abie ɗin?"
Fuskarsa ya sake tare da faɗin "Gane min hanya Ammiey, yau Nihla da rigimarta dama ta tashi."
"Anya kuwa, yaki shalelena, zo ki faɗa min me yake faruwa me Abie yayi Miki kike kula?"
Sum sum sum Nihla ta fara jan jikinta akan gadon ta dawo ta gefen da Ammiey ke tsaye tana tura bakinta gaba. Murmushi kawai yayi cikin ransa yace "i can do anything for you Angel." Sai kuma ya fice a ɗakin ya wuce nasa don kimtsawa tunda solution ya zo.
Bayan fitarsa Ammiey ta dubi Nihla cike da kulawa tace "Me Abie ya yi wa shalelensa ne haka yau ake fushi da shi?" Marairaice fuska tayi tare da share ƙwallar da ta taho mata babu shiri
"Ni Ammiey ba ruwana da Abie."
Ido waje Ammiey tace "Abie ne fa Nihla? Oh yeah tell me! Me Abie yayi kike fushi da shi?"
"Ammiey kin ga, Ammiey Hamra tana da kirki, she's kind and nice, but Abie shouted at her Kamar Zai dukata hat Sai fa tayi kuka, ba ta da laifi Ammiey, nice Na je wurinta, amma Abiey make her cry, Ba ga mishi komai ba." Sai kuma ta fashe da kuka. Haɗa ta da jikinta Ammiey tayi tare da rungumeta kamar za ta shayar da ita, sai da ta yi kukanta tayi shiru tukun Ammiey ta raba jikinta da nata. Cike da kulawa tace
"Look Nihla, ban fahimce ki ba, who's Hamra da Abiey yayi mata tsawa?"
"She's my new friend, and she she she resembles...."
"Ammiey" Ra'isa ta shigo ciki "So you people are here? Wetin fishy is happening here? Eh?"
Ƙarasowa tayi ganin yadda Nihla ke jikik Ammiey. Da sauri ta kai hannunta jikin Nihla tana faɗin "What's wrong Angel?"
"Ƙyaleta haka nan Ra'isa, ba na son takura, now Baby, tashi ki watsa ruwa ko nasa Taqiyya ta watsa Malie?"
Kanta ta jijjiga, Ammiey tace "Good! Yanzu bari na kawo Miki abinci, yau Abie ba zai Ganki ba har sai ya ba wa Friend ɗinki haƙuri." Daga haka Ammiey ta miƙe Nihla luma ta nufi bayi, to Ammiey, this Nihla's friend ba ta yi tunanin babba b ce, and ita a tunaninta rashin ji tayi Mubeen ya ja mata kunne.
"Is she suck?"
"Who?"
"Baby" ta ba ta amsa kai tsaye, da kai ta mata alamar a'a, daga nan kuma ta ratsa gefen Ra'isa ta fice, baki Ra'isa ta riƙe tana faɗin "in ta yi wari dai za mu ji. " Daga haka ta fice zuwa nata ɗakin, dama abun da ya kawo ta kenan!
Ammiey na kawowa abinci ta jira fitowar Nihla, taimaka mata tayi ta sauya zuwa light expensive wears sannan tayi feeding nata a ɗakin, bayan ta gama ta fita da kwanukan, tana shirin dawowa taga ya yo hanyar ɗakin, sabkda alƙawarin da ta yi wa Nihla yasa ta jira ya iso sannan tace "I don't want to see you close to her, ka yi wa ƙawarta ihu, na ce mata ta yi haƙuri za ka ba wa ƙawarta haƙuri and ta haƙura, but I don't want you close to her at all!"
"Ammiey is..." Da hannunta ta dakatar da shi da faɗin "Ka ga i don't want to hear anything from you, ka tafi abun ka tunda ba ka iya tausasawa yara ma..."
"Ammiey is not.." shigewar Ammiey ciki da ya gani yasa ya dafe kansa tare da furta "Ammiey ba za ki san wace ce ƙawar tata ba, ba yadda kike tunani ba ne, and Abun da Nayi is the only solution, anyways, Bari Na sha iska. Daga haka ya shafa sajen da yayi lufuf akan fuskarsa tare da wucewa abun sa zuwa garden. Wasa-wasa tun da ya je ya kasa jinsa normal hasali ma tunanin wannan dirty girl ɗin yake yi yana tsaki shi ɗaya yayin da kuma wani lokacin yake jijjiga kansa. Abu guda da ya kasa mantawa sune kalamanta gare shi, kalaman da tunda ya zauna yake jin tamkar a lokacin take yin su. Toshe kunnuwansa yayi da yatsunsa tare da miƙewa yana shirin barin wurin. Kamar ana masa raɗa ya ƙara jiyo kalamanta cikin kunnuwansa. Runtse idanuwansa yayi yana ƙara hasaso lokacin da hakan ta faru, lokacin da ta zube gabansa tana roƙonsa
"Don Allah Sir, kar ka min haka wallahil-azim Ni ba muguwa ba ce, ban zo da komai ba sai don na nemi halalina, kar ka durƙushe samun mabuƙacin da ke ƙasanka na roƙe ka da Allah!"
Buɗe idanuwansa yayi da lokaci guda suka sauya launi zuwa ja kaɗan, daga haka ya fice a garden ɗin ya koma cikin gidan, Ra'isa ce ya tarar a parlour ita kadai tana kallon wani Korean series Film, Zama yayi ba tare da ya ce komai ba, duk da cewa ta san ba lafiya ba ganin ɗan'uwan nata a wannan yanayi amma ba za ta ce masa komai ba, in ya faɗa fine, in Kuma ya ɓoye in ta yi tsami dai za a ji. Ganin bai fahimtar komai yasa ya ɗuko wayarsa daga aljihinsa yana dannawa.
Har lokacin sallar magrib yana parlourn shi kaɗai, bayan ya dawo daga mosque, yana zaune a bedroom nasa yana aikin nasa na kallon hotunan Marigayiyar matarsa wanda a yanzu da wuya ka gan shi yana hakan sai in yana cikin damuwa. Haka nan shi kaɗai yake suruce-surucensa sa'i-sa'i yayinda wasu lokutan sai yayi murmushi, wasu lokutan kuma ya ɓata fuska kamar wani ƙaramin yaro. Sallar Isha ce ta fito da shi yana shirin shigowa cikin gidan yaci karo da su za su fita. Ammiey, Ra'isa, sai kuma Nihla wacce take tsakiyansu ko wannensu na riƙe da hannayenta. Tsayawa yayi da zimmar ya tambaye su sai dai gargaɗin da Ammiey ta masa yasa ya sosa kansa tare da wucewa. Driver ne ya fita da su, ba su tsaya ko ina ba sai Jabi lake mall, ƴar siyayya suka yi wacce ba ta ɗauke su tsawon lokaci ba sannan suka ƙarasa Silverbird cinema da ke jikik Jabi lake mall. Ko tsakiyar sabon Film ɗin da ake kalla ba su kai ba saboda dalilin tafiyar ainihi don wartdakewar Nihla ne, ganin hakan yasa suka tafi da misalin ƙarfe tara na dare.
*Hamra*
Ta yi tafiya sosai daga ƙarshe ta yanke shawarar tsayar da mai adaidaita. Rashin sanin inda za ta je yasa ta lumshe idanuwanta da suka cika da ƙwalla take ƙwallar da ta matse ta zubo. Tambayar ta inda za ta je yayi,kawai tace da shi su je kawai, a daidai wani wuri da take da tabbacin makarantar gwamnati ne tace ya tsaya, bayan ta sallame shi ta nufi wurin hankalinta tashe saboda ba ta san wane irin abu za ta tarar ba, addu'arta dai Allah ya kare ta d kariyarsa ya kuma yi mata tsari da wulaƙantacciyar mutuwa. Cikin makarantar ta nufa ganin hankalin mai gadi ba ya kanta yasa ta shige da sauri. Ajujuwan da ke can baya ta zagaya ta shiga cikin ɗaya ta ajiye trolleynta ba tare da ta sauƙe jakarta ba, a dai yanzu kam ba ta da wani buri da ya wuce samun makwanci, safiyar gobe kuma ta nufi Isawa, can in ta mutu akwai masu yi mata salla, nan kwa in ta mutu hala sai dai a take gawarta ma.
Taimakon da ta samu daga Ubangijinta akwai banɗakai da kuma ruwa a kusa, hakan yasa sallolinta ba su kuɓuce mata ba, ta kuma faɗawa ubangiji damuwoyinta tare da roƙarsa da ya samar mata sauƙi cikin rayuwar. Daga nan ta fara rera Alqur'ani a hankali cikin abun da ta haddace a kanta. Bayan ta yi sallar Isha ne cikinta ya fara ƙugin yunwa, har ga Allah ita ta manta ma da wani abinci don damuwar da ke kanta ta wuce batun ciki.
Ta fito kenan tana bin katanga har ta iso bakin gate, tana shirin ficewa sai ga wani ɗan Dattijo wanda da gani shi ke kula da makarantar, tsayar da ita yayi cikin harshen turanci, abun ka da mutum mai shegen tsoro sai ta tsaya. Bayan ya ƙaraso ya tambaye ta ko me take yi a nan? Sai ta ba shi amsa da cewa "Ni baƙuwa ce, mafaka nake nema zuwa safiya zan wuce garin mu?"
"Nan fa makaranta ne, ina laifin ki tafi hotel ba nan ba, kin san kuwa nan ɗin babu wani tsaro? Magana ta gaskiya Ni ina shawartarki da ki nemi hotel zai fi miko tsaro don Ni nan da kike gani wasu lokutan ana hara ta idan an zo satar wasu kayayyaki da gwamnati ta ba wa makarantar." Ya faɗa mata yana gyara zaman hularsa irin ta mutanen Igbo. Juya maganarsa take cikin ranta, kenan she's not safe there?
A hankali ta fara magana cikin sanyin jiki "Na kwana ɗaya ne zan tsaya, da sassafe Zan tafi." Dattijon yace "Na dai faɗa Miki, idan ba haka ba duk abun da ya faru da ke Ni ba Ni da matsala." Numfashi ta sauƙe sai taji kamar ta faɗi ƙasa ta ɗaura hannunta ka ta rausa kuka, amma dai a yanzu ba shi ne mafita ba, hakan yasa ta juya ciki kanta na mugun sarawa har wata juwa take ji kamar za ta faɗi.
Cikin iko da kariyar ubangiji ta ƙarasa ajin da shirginta suke, tattara su tayi ta goya jakarta tare da janyo trolleynta ta saɓa jakarta a baya. Ko sallama ba ta yi wa mai gadin ba ta fice tare da tsayawa daidai ƙaton signboard da ke gaban makarantar mai ɗauke da sunanta _"LEA model Primary school, Asokoro"._
Ta furta da ƙarfi tare da zama kan ɗan dakalin da ya riƙe signboard ɗin, ba tare da ta ankare ba ta faɗa duniyar tunani sai da ta share kusan awa guda zaune a wurin, farkawarta daga duniyar da ta saba da ita ta faru ne sanadiyyar hayaniyar da ta jiyo, hakan yasa ta fara cilla idanuwanta kowanne gefe don gano daga ina ne kuma me yake faruwa?
Without her knowing ashe wasu samari ne suka biyo ta wurin suna dube-dube da alamar dai akwai abun da ya kawo su yankin saboda unguwar gabaɗa ba ta ƙananan mutane ba ne bare a samu irin waɗannan lalatattun matasa, tsoro ne ya mamaye ruhi da ƙalbinta, haka yasa ta fara ƙoƙarin samarwa kanta maɓoya a wurin, jakarta wacce dama ke bayanta ta gyarawa zama lokacin bayan lokaci tana waigawa tare da fatan Allah yasa kada su ganta don kuwa dole a yanzu ta bar wurin, idan ma hotel ɗin ne ta kama da safe ta bar wannan gari maras gata da tsaro gare ta da mutuncinta. Trolleynta da ta ja ne ba tare da ta sani ba ta bugi jikin dakalin da ta tashi kai, nan ya ɗan ba da wani sauti wanda bai ciki ƙara ba, cije lips ɗinta tayi kamar ɓarauniya ta fara ƙoƙarin barin wajen sai dai me? Tana fara stepping waɗannan samarin suka lura da ita, ɗayansu ya ba da shawarar bin ta, babu ɓata lokaci suka ɗauki shawarar tasa tare da bin bayanta a hankali suma kamar yadda take tafiya.
Titi ta nausa bayan barin wurin, ganinta kan titin da babu kowa sai hasken kan titin yasa ta fara sauri tana haɗawa da gudu gudu, kamar an ce ta juya kwatsam ta ci karo da samarin da ke biye da ita wanda in ba mistake tayi ba don su ta gudu daga jikin LEA model Primary school. Wannan dalilin yasa zuciyarta shiga wani matsanancin