Showing 3001 words to 6000 words out of 134378 words

Chapter 2 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

62

Daga haka ta fara takawa a hankali yayinda cikinta ke ƙugin neman agaji, a taƙaice dai, kwananniyar yunwarta tuni ta motsa, amma hakan bai sa ta tsaya ba ta nufi ƙofa, a hankali har ta isa gindin bishiya, bokitan wankin da aka riga aka saka ruwa ta fara tsoma kayan ciki sannan ta zuba garin omo ta fara wankewa.

Ikon Allah! Wannan uban kayan a hankali sai da ta wanke su, ta ɗauraye, tana shirin sanya kayan taji dundu a tsakiyar bayanata.
"Don ubanki duka omon kika ƙarar bayan kin san da sauran za mu yi wanka bayan kayan sun bushe?" Inna Hajara ta faɗa tana nuna ledar Omo ɗin da ke ƙasa.
"Shegiya ƴar baƙin ciki muguwa, tunda kika min asarar omo wallahi sai kin je kasuwa kin siyo waken suya an yi awarar kin fita da ita na samu wani kuɗin omon. Tsinanniya kawai, ki gama shanyar ki zo ki amshi kuɗin ki wuce kin ji?"

Runtse ido Zahrah tayi tare da sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya.
"Ba magana nake Miki ba? Ko ba kin kurmance ne?"
Da ƙyar ta iya furta "Na ji Inna." Yanayin yadda sautin ya fita kaɗai ya isa ya tausasa zuciyar kowanne dan Adam mai zuciya a ƙirjinsa ya kuma tausaya mata,banda Inna Hajara wacce ba ta da wani buri da ya wuce wulaƙantuwa da ɗaiɗaicewar Hamra, sai dai kuma Allah ba ya bacci, ba kuma ya yafe zaluncin azzalumi.

*Wannan kenan! Ban san yadda za ku amshi labarin ba, sai dai ba batun cika baki ba, ina da tabbacin cewa za ku so shi, so irin na gasken nan, sharhinku na da matuƙar muhimmanci, yanayin yadda naga kun amshi littafin kada ku manta shi zai sa na bar muku shi kyauta.*

# tumun_dare
# Diamond_bhatool

[15/05, 10:23 AM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER TWO: A life of labour*



Hamra na gama shanyar kayan ta kwashe bokitan ta ajiye su gindin randa, cike da ƙarfin hali ta ƙarasa zuwa ɗakin Inna Hajara, a bakin ƙofar ɗakin ta ɗan jingina da bango tare da leƙawa kaɗan tace "Inna na gama" daga haka ta ja gefe tare da ƙara lafewa jikin bangon tana sauƙe ajiyar zuciya yayinda idanuwanta ke lumshe.
Fitowa Inna Hajara tayi daga ɗakin ta tsaya tana ƙara ƙarewa Hamra kallo wacce ba ta ma san da wanzuwar Inna ba a lokacin.

Kyakkyawar yarinya ce ajin farko da ba za ta wuce shekaru goma sha huɗu ba, fatarta na da matsakaicin haske yayinda kamanninta ke yanayi da larabawa, tana da dogon hanci sai kuma kyawawan idanuwanta farare tas masu ɗauke da brown coloured iris, eyelashes nata zara-zara ne kamar dai ta shafa musu wani abun, girarta na da yalwar gashi sai kuma kwantacciyar sumar da ta mamaye upper aspect na goshinta. Tufafin da ke jikinta wata atamfa ce irin ta ƙauyawa da ake kira da _kandigirin_ wacce aka mata ɗinkin doguwar riga da ta tafi silif kamar alifun, duk da kasancewar kanta ɗaure yake da ɗan kwali amma hakan bai hana lallausa, doguwa kuma baƙar sumar kanta zubowa ba har zuwa tsakiyar bayanta.
_Tabarakallahu Rabbul- khaliqin_

Inna Hajara da ke duban Hamra yayin da ta faɗa tunani tana zayyana kyau irin na Hamra ɗin wanda ko maƙiyi da wuya ya hangi makusa a tare da ita. Yamutsa fuska Inna Hajara tayi tana faɗin "Shegiyar yarinyar kamar ita tayi kanta, duk sai na koje wannan kyan fuskar da take da shi" sai kuma ta saki ƙwafa wacce ta sanar da Hamra wanzuwar Inna Hajara kusa da ita, babu shiri ta buɗe idanuwanta tana sauƙesu ƙasa.

Kamar mai yanke shawara da zuciya Inna Hajara tayi, shiru ta ɗan yi tana cizon ƙaramar yatsarta yayinda idanuwanta ke kan Hamra wacce nata ke ƙasa.
"Ga can guntun ɗumamen da Khadi ta ci, ba don halinki ba ki ɗauka ki ci, kina gamawa ki amso mudun waken suya." Cike da maɗaukakin mamaki Hamra ke kallon Inna tana tunanin anya kuwa Inna ce wannan yau ta ji tausayinta?, maganar Inna Hajara ce ta dawo da ita hayyacinta.
"Mayya kin wani tsare Ni da ido, to kurwata kur wallahi, shegiya dangin Mayu" ta faɗa tana kai mata hannu.
"Wuce ki samu kije ki dawo mu ɗaura tukunya."
Jiki na ɓari Hamra ta amshi kuɗin hannun Inna ta ƙarasa kitchen ɗinsu ta ɗauko ɗumamen wanda gabaɗaya Khadi ta gama jagwalgwala shi uwa uba ma rashin daɗin kallo da yake da shi, a bakin veranda ta zauna tare da aje kwanon gabanta tana ƙara kallon ɗumamen. Ya za ta yi? Godiya ga Allah da yasa wannan ɗin rabonta ne ma, "Bismillah" ta furta tare da kai hannunta cikin kwanon, kamar farko da ta kai baki ta fahimci cewa ɗumamen ya jiƙe amma haka ta zauna ta ciye tas saboda yunwar da ta addabeta ta kuma san ba lallai ta kuma samun wani abincin ba a yau.

Hamdala tayi wa mahaliccinta da ya ciyar da ita ba tare da wata dabara ko wayonta ba sannan ta kai kwanon wurin wanke-wanke. Randar da aka ware mata a gidan don shan ruwa ta nufa, sosai ta sha ruwan ta ƙoshi, sai a lokacin taji ƙarfin jikinta, hakan yasa kai tsaye ta ɗauko Hijabinta ta saka, ta ƙwama takalminta na danƙo da fita.

Ba a jima sosai ba Hamra ta dawo da awon waken suya, ita ta taimakawa Inna Hajara suka gama tsincewa, aka wanke ta nufi gidan Lantana mai markaɗe, bayan an markaɗa ta ɗauko ta kawo, abun ban mamaki bai wuce yadda yarinyar take aiki kamar wata mai shekaru da yawa ba, cike da ƙwarewa ta taya Inna Hajara suka yi komai har aka gama awarar.

Sallar Azahar Hamra tayi duk da cewa lokaci ya ƙure har wasu masallatan sun fara ƙiran la'sar, ganin hakan yasa ta daura la'asar ɗinta tukun ta fito jin ƙiran da Baffa Sule wanda bai jima da shigowa ba yake ƙwala mata.
"Na'am Baffa ga Ni" ta faɗa yayin da ta zo gabansa ta tsuguna
A zafafe yace "Ni ke kam Hamra kan kunnuwanki kike zama ne? Kina ji ina ƙolo amma kika yi banza da Ni saboda kin gama raina Ni ko?"
Kanta ƙasa tana wasa da yatsunta tace "Ka yi haƙuri Baffa, ina salla ne ban ji ka ba."
Cikin halin ko in kula da yanayin yadda ta ƙara ramewa yace "Maza ɗauko kofin silba ki je gidan Tamalin ki sayo min kunu, idan ba ta gama ba kar ki dawo sai an gama kin ji?"
"Amma Baffa za a soya awarar Inna fa, idan ba a gama ba zan dawo kar tayi fa..."

"To algungumatu munafikatu, ashe dai? Ai kin san Malam ne gaba da kowa a gidan, Ni in ba ki soya awarar ba me zan Miki, nifa ba na son salon iskanci da munafurcin ki Hamra'u "
Kai kawai Hamra ta sunkuyar jin batun Inna Hajara tana kuma nanata irin halin Innar cikin ranta.
"Wuce ki ba Ni waje mai kama da mayu kawai"
Tun kafin Inna ta kai Aya Hamra ta nufi kwandon da ake ajiye kwanuka ta ɗauki kofin silver sannan ta dawo wurin Baffa.
"Baffa kuɗin zan wuce"
Fuska ya yamutsa sannan ya sa hannu cikin aljihunsa ya ɗauko ɗari ya ba ta
"Saura ki zauna" caraf Inna Hajara tace
"Ai kuwa za ta iya zan in dai Hamra'u ce, yarinya dai ga kyan fuska da jiki amma hali kam babu, jiya fa Malam yaron maƙociyar nan tamu Laure yace min ya ganta ta shiga ɗakin Usama na wajen Habbi da bokitin awara, ko me rai ya kai ta oho?"

Baffa Sule yace "Ai halin ƴar nan da uwarta zan iya ce Miki babu bambanci."
Inna Hajara ta riƙe haɓa tare da faɗin "Ni tsoro na ma ɗaya kar mu je ta kwaso mana abun kunya, gaskiya yarinyar nan Ni ta fara ba Ni tsoro."
"Ai kuwa zan koreta a gidana in dai wannan ɗabi'ar za ta yafawa kanta, dududu nawa Hamra take in banda lalacewa a ce tana bin ɗakuman samari, duk laifin iyayenta ne ai"
"Hmm Malam kenan" Inna Hajara ta faɗa tana gyara zamanta
"Nima dai da zan goya maka Baya a koreta amma me? Ka san idanun mutane kanmu suke akan yarinyar nan, duk yadda muke hidimtawa da ita ba sa gani, na san ba komai ke ruɗarsu ba sai kyanta "
"Aikin banza, Ni Inaga ma in Rahama ta dawo daga Galdimari haɗa su zan yi na aurar daga nan kuma na fara facalata da dukiya" ya idasa yana sakin wata shu'umar dariya.

"Amma dai Malam nawa ma Rahama take da za ka aurar da ita? Shekara sha biyar take fa, haba Malam, ita dai wannan ƙarfen ƙafan ita za mu cire, mu yada ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda"
"Maganarki dutse Hajara, amma kin riga kin san ba na so yarinyar nan taji wani daɗi a rayuwar nan, na fi buƙatar tayi rayuwar ƙaskanci da wulaƙanci, in so samu ne ma ya zamana daɗin da taji a da ya kasance jin daɗinta na ƙarshe a rayuwarta.
"Ai kuwa dai Malam, na rasa me yasa ba na son ƴar nan, ji nake kamar na kashe ta na huta." Malam yace
"Ki bar ta, wahala ita za ta kashe ta, ki ƙara akan ta da kin ji?"

*HAMRA*

Jin Inna ta ce kada ta daɗe kuma har ga Allah tana son shafawa kanta lafiya yasa ta fara zuba sauri, tana zuwa daidai kan kwanar layinsu taci karo da Atalanta, gabanta ne ya faɗi da tuna Abunda ya faru tsakaninsu a jiya, hakan yasa ta gota za ta wuce
"A'a Balarabiyar yarinya, ina za ki je haka?"
Ƙin amsa masa tayi ta gota za ta wuce caraf ya riƙo Hijabinta. Duk ƙoƙarinta na ganin ta ƙwace ta gagara. Dariyar shaƙiyyanci yayi yace
"Haba biyutipul, ki tsaya mu yi hira mana?"
Kanta ta kawar saboda yadda warin tabar da jikinsa ke fitarwa ya bushe ta, kamar za ta yi amai ta rufe bakinta.
Ta tsani taba, ta tsani mai shanta, ita haka take muffin za ta ji warinta sai ta yi amai.

"Ya kike rufe hanci biyutipul?"
Ya faɗa yana tsarets da jajayen idanuwansa
"Babu, ka sakeni Inna ta ce kar na daɗe"
"Ina za ki je?" Ya tambayeta
"Kunu zan sayo a gidan Tamalin"
Washe baki yayi yana faɗin "To mu je in raka ki mana"
Da sauri ta fara jijjiga masa kai
"Ba kya so naje ne?"
Kai ta gyaɗa masa
"To Shikenan biyutipul, sai kin dawo, i lobiyu"
Ba tare da ta ji me yake faɗi ba jin ya sake Hijabinta da sauri ta fara tafiya, shi kuwa da kallon mamaki yake bin ta ganin yadda take sauri, dariya yayi yace
"Wannan yarinyar ba dai kyau ba, aradun Allah ko kashe wani aka ce nayi za a ba Ni ita zan kashe, kai da gudu ma"


Tana isa ƙofar gidan Tamalin ta ci karo da Hamida ɗiyar maƙotansu ce kuma ƙawar Rahama. Saurin janye idanunta tayi daga na Hamidan sanin cewa ba ta mata da wasa cikin rashin Sa'a kuma ashe Hamida ta ganta.
Da sauri Hamida ta ƙaraso tare da jan Hijabin Hamra.
"Ke mayyatu!"
Da sauri Hamra ta juyo cike da tsoro
"Rahama ta dawo daga Galdimari?"
"A'a"
"Shegiya to ban wuri, iya tambayar da zan Miki kenan"
Har harɗewa take saboda ta shige cikin gidan Tamalin, ana zuba mata aka ba ta canjinta, daga nan ta taho gida kai tsaye gudun kada ta yi wani laifin, tana shiga ta ci karo da Inna tana yanka awara kan tray.
Dakatawa da abunda take tayi tana riƙe Haɓa tare da mayar da dubanta ga Hamra.
"Ke Yanzu Hamra'u sai Yanzu za ki dawo? Tun ɗazu aka aike ki shine kika wuce yawon gallafirinki?"
Cikin sassanyar muryarta tace "Inna wallahi ban tsaya ko ina ba, Allah ma yana gani"

Taɓe baki Inna tayi tace "Oh Ni takwarar tsohuwa, ke Hamra'u har za ki nuna min sanin Allah ne? To bari ki ji abunda ba ki sani ba ga gidanmu nan ga masallaci, don haka kul kika ƙara faɗa min haka don na fi ki saninsa, in ba haka ba kuwa sai na ci ubanki, shegiya mai kama da mayu"
Shiru Hamra'u tayi ta nufi ɗakin Inna ta kai wa Baffa Sule kunun, tana fitowa ta kamawa Inna Hajara suyar awara, cikin ƙanƙanin lokaci suka gama, a cikin ashonen awara aka juye mata sannan aka yanka mata albasa, sannan Inna ta miƙo mata robar yaji.

Tana karɓa ta tsaya cak, tambayar Inna take son yi amma babu damar hakan gudun kada tayi laifi. Ganinta tsaye yasa Inna faɗin
"Ke me kike nufi ne? Ba za ki fita da awarar ba ne sai ta yi sanyi?"
"Eh a'a, Inna dama na ga maghrib ta yi shi yasa nace in Na yi salla sai na fita da ita."
"E lallai Hamra'u, kin fara raina Ni, yaushe na fara wasa da ke? Ce Miki aka yi ke kaɗaice mai salla a duniyar? To don ubanki yau ko azumi ne ba za ki yi ba sai kin futa da awarar na, maza ɗauki."
Bokitin awarar ta ɗauka babu musu sannan ta juya za ta fita
"Ta ₦3000 ce, ko biyar ce ta ɓata sai kin biya Ni, kuma banda bashi, kar ki dawo min da kwashe, kuɗina kawai nake so."
"To Inna"

Kai tsaye dabar shamuwa ta nufa saboda nan ne samari da ƴanmatan unguwar ke taruwa daga lokacin magriba, wani lokacin ba sa tashi sai dare ta fara. Tun da ta kai dabar idanuwan samarin da ke zaune wanda mafiya yawansu ƴan sholi ne ya dawo kanta ga shi da zuwanta suka fara magana ƙasa-ƙasa wanda ta tabbatar kanta suke maganar. Abunda ta fi tsana kenan! Kallo, sosai kallon nasu ya haifar mata da tsoronsu, kanta ta mayar ƙasa ta ci gaba da takawa, harɗewa ƙafarta ta fara yi saboda tsoro, da kyar dai ta iya ƙarasawa kusan sauran masu talla tana musu sallama tare da ajiye bokitinta a gabanta.

Kiraye-kirayen sallar maghrib yasa ta fara tunanin ta ina za ta fara, zamanta ta ci gaba da yi ganin ana sayan awarar sai dai duk wanda zai saya sai ya faɗa mata maganar da ta gagara fahimtarta saboda ƙarancin shekaru irin nata. Har duhu ya shiga ba ta samu damar yin sallar ba, ba kuma ta ga ɗaya daga cikin ƴan yan da ke gefenta wata ta tashi da nufin yi ba ko kuma ta magantu da rashin yin sallar, haka zalika samarin da ke zaune suna zantukansu babu wanda ya tashi. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana ƙara tausayawa kanta a irin rayuwar da ta tsinci kanta babu tsammani.

Cikin ƴan mata da ke zaune ta kalli Amira ƴan gidan Sailuba taga ita ma ba ta da damuwa da hakan, numfashi ta sauƙe sannan ta miƙe ta thnkareta kasancewar akwai mutum biyu tsakaninsu.
"Amira" ɗagowa Amira tayi tana duban Hamra wacce magana ba ta taɓa haɗa su da kowa a wurin ba tsawon sati biyu da ta fara talla a wurin, cike da maɗaukakin mamaki Amira tace "Hamra" tana sakin murmushi. Murmushin da tayi shi ya ba wa Hamra ƙarfin guiwar faɗin abunda ya kawo ta.
"Don Allah Amira bari na kawo miki botikin awarata ina so nayi salla ne"
"Salla?" Amira ta maimaita tana bin Hamra da ta ɗaga mata kai da kallon mamaki
"To, in kin dawo Nima zan je nayi"
"To" daga haka Hamra ta juya ta nufi famfon da ke kudu da dabar shamuwa. Alwala tayi sannan ta dawo, ɗankwalin kanta ta cire ta shimfiɗa sannan tayi sallarta yayin da samari da ƴanmatan ke binta da kallon mamaki.

Tana sallamewa ta karɓawa Amira itama taje tayi sallar ta dawo. Har Isha' tayi da sauran awarar ba ta ƙare ba, ga shi jikinta tsami yake mata saboda irin bugun da ta sha yau amma kuma babu damar tafiya sai ta sayar cas.
Nassman, ɗaya daga cikin samarin da ke zaune sun saka wata ƴar matashiyar budurwa tsakiya shi da wani suna hira ne ya hango Hamra. Gabansa ne ya faɗi ganin yarinyar duk da cewa it's not the first time da ya fara ganinta amma kyanta yana ba shi tsoro matuƙa.

Abokinsa ne ya lura da hakan yace "Ya dai Nassman? Ka ga ƴar biyutipul gel shine ka tsare ta da ido?"
Haushi ne ya kama budurwar da ke tsakiyar su tace "wannan wane irin cin fuska ne Sabe, ka fa san cewa ina kishinka amma kake kiran wata biyutipul a gaba na, wallahi sai na ɓarar da awarar da take sayarwa yadda daga yau ba za ta ƙara gigin kawowa ba bare ta ɓata min rai." Tana faɗan haka ta miƙe a hasale ta nufi wurin Zaman Hamra yayinda both Nassman da Sabe ke mata magana kan ta tsaya amma ba ta waiwye su ba.

Tana isa gaban masu tallar ta zari bokitin Hamra ta, saboda tsantsar mamaki da kallo kawai Hamra ta bi Naja'atu, ganin da gaske cutar da ita za ta yi yaɗata miƙeda sauri ta kai hannu za ta karɓi bokitinta sai dai mai faruwa ta faru, tuni Naja'atu ta kira bokitin awarar cikin da ta rage ta zabe ƙasa gabaɗaya, ba ta tsaya haka ba sai da ta tumurmushe awarar da ƙafarta sannan ta cilla bahon gefe, a matuƙar fusace tace "Gobe ma ki kawo, sai na zubar da kayan tallarki, mai kama da mayu kawai"

Hamra kam tuni ta yi sumar tsaye, gani take kamar mafarki take, ta ya za a zubar da awarar Inna Hajara? Hayaiyar mutanen wurin da ke tashi yasa ta dawo hayyacinta, rufe Naja'atu suka yi da masifa kamar za su daketa, hakan ya yi daidai da isowar su Nassman,
"Kun ga ya isa haka, ku sake ta kun ji"
Sai a lokacin Hamra taji wani Marayan kuka ya kufce mata tunawa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login