Showing 30001 words to 33000 words out of 134378 words

Chapter 11 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

65

°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER TEN: Unexpected proposal.*

*Dedicated to Sister Sa'adatu Abdullahi, your support and dedication lift me up to the next level. I really appreciate.*

Numbernta da ainihin sim nasa ne ya bata ya dannawa ƙira kamar cikin ransa yana addu'ar Allah yasa tayi picking, cikin Sa'a kuwa sallamarta cikin daddaɗar muryarta ta doki dodon kunnensa. Ajiyar zuciya ya sauƙe har tana iya jiyowa. Asa sallamar yayi cikin muryarsa da ta gama sanyi. Bayan sun gaisa ne ya fahimci kamar ba ta gane shi ba, ya tambayeta "Ba ki gane Ni ba ko?"
"Uhm, ban gane ba" ta amsa masa kai tsaye.
"Yayanki ne" baki ta rufe tana zare ido kamar tana gabansa.
"Ya Salam! Wallahi ban ɗau Muryar ba sai da ka faɗa, kayi haƙuri yaya, ina yini?"
Ƴar ƙaramar dariya yayi yace "Ai mun riga mun gaisa, kina lafiya ko?"
Tace "Uhm, lafiya ƙalau Yayana, kai fa?"
Yace "Nima haka."
Shiru suka yi na wani lokaci can ya katse shirun da faɗin
"Har na kwanta fa, sai dai na kasa bacci."
"Allah sarki Yaya na, ai ga Ni zan taya ka hira ko?"

Murmushi mai sauti yayi yace "Yauwa sweet Sister, Amma dai Allah yasa ban takura Miki ba."
"Takurawa kuma Yaya?" Ta faɗa da alamar tambaya.
"Yhup! Ina nufin ko kina jin bacci ne?"
Da sauri tace "A'a Yaya, Nifa babu abinda nake ji, Nima a kwance nake Baccin ya ƙi zuwa."
Cikin ransa yace "Ko tunani kike yi ne?" Bai sani ba ashe ya furta hakan saman laɓɓansa.
"Tunani....Uhm Yaya, tunani ya hana Ni bacci" ta faɗa tana gyara kwanciyarsa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana fatan a ce tunanin da yake fama da shi irinsa take. Jin ya yi shiru yasa ta ƙira sunansa a sanyaye, kamar wanda aka zabura yace "Sweet sis."
"Ya ka yi shiru?"
"Uhm, kika ce kema tunani ne ya hana ki bacci."
"Uhm" sai kuma tayi shiru
"Tunanin me kike?"
Rashin wayo yasa tace "Yaya ina yawan tunaninka,yadda kake kulawa da Ni, ina jin daɗi sosai, kana da kirki."
"Are you sure kina tunani na?"
"Eh mana Yaya, da gaske nake."
"Then...Shikenan dai, Alhamdulillah. Yanzu ki ba Ni labari."
"Labari kuma Yaya? To wanne iri kake so?"
Can ƙasan maƙoshi yace "Na soyayya."

Miƙewa tayi daga kwancen da take ta zauna tana zaro ido waje kamar tana gabansa sai kuma ta rufe fuskarta da ɗaya hannunta.
"Are there?"
A saman laɓɓanta tace "Uhm." Sai kuma tayi shiru.
"Hamraaa" ya ƙira sunanta yana mai jan ƙarshen sunan, ji tayi kamar duk duniya babu wani mahaluki da ya iya furta wannan sunan har ba ta san lokacin da smile Yayi escaping kan lips nata ba.
"Ba ki iya labarin soyayya ba?"
Rasa me za ta ce tayi kawai sai tace "Uhm Yaya"
"Is ok, ni bari na ba ki labari, wane iri kike so?"
Hamra tace "Irin wadda kace na maka za ka min, ka ga sai na koya nake maka."
"Ok... Bari na ba ki labarin soyayyar Yaya Sadauki da Zahrah cikin littafin A BABBAN GIDA wanda Diamond Bhatool ta rubuta."
Baki buɗe tace "Laa, Yaya kaima ka san Diamond Bhatool?"
"Eh mana, na santa, ai Ummie ta san Ummarta."
"Ayya, a wayar wata a wurin markaɗe na taɓa jin ana karanta littafin ta, kaima karantawa kayi?"
"A'a fa, ita ta tura min da kanta da yake muna gaisawa."
"Watara za ka ba Ni ita mu gaisa ko? Ina so za mu yi magana da ita, amma kafin nan ka fara ba Ni labarin."
Haka dai ya fara ba ta labarin kafin su farga 2:30am, a hakan ma basu gama ba, ganin yadda lokaci yaja yasa yace ta bari gobe zai ƙarasa mata. Daga nan suka yi sallama.

Tun daga wannan ranar kullum suna manne a waya, idan ba ya gari kuwa yini suke tare har Ummie ta fuskanci hakan, Ranar kawai ta tsare ta da tambayar da wa take waya haka? Nan Humairah ta tsomo baki tace "wallahi kam ki tambayeta ummie, duk dare in na farka sai naji tana kashe murya."
Harararta Hamra tayi tare da kai mata dukan wasa tana faɗin "Wallahi Ummien kice Humaira ta daina min sharri."
"Wallahi Ummie ba sharri na mata ba, kullum sai ta yi waya da dare, har na yi bacci na farka shan ruwa."
Wannan karen shiru Hamra tayi jin an rafko ta. Kallonta Ummie tayi tace "Ina jin ki Hamra, faɗa min da waye kike raba dare kina waya?" Ba ta iya ƙarya ba, kasancewar ƙaryar ba halinta ba ne. Kanta ƙasa tace "Ummie Yaya Hamid ne fa." Ta faɗa tana tura baki gaba.
"Wanne Hamid ɗin?" Ummie ta tambaya yayinda Hamra ta zaro ido tana kwashewa da dariya, daƙuwar da ummie ta miƙa mata yasa ta rufe bakinta da hannunta.
"Tashi ki ba Ni wuri, shashasha kawai!"
"Kai Ummien Hamra, na yi shiru to."
"Da ya fi Miki" kallonta ta mayar kan Hamra tace "Da gaske. Ne kullum kuna raba dare kina waya?" Wiƙi-wiƙi da Ido Hamra tayi ta mayar da kallonta ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta.
"Ina jin ki" kai ta gyaɗa ba tare da ta kalli Ummien ba.

Numfashi Ummie ta sauƙe lokaci guda tana hamdala cikin ranta, a zahiri kuma ta haɗe fuska tace "Shi ne ko sau ɗaya ba za ki faɗa min ba?"
"Ki yi haƙuri Ummie"
"Shikenan na yi haƙuri, amma dai Abunda kika yi kar ki kuma kwatantawa. A matsayi na na mahaifiyarki, ya kamata ki zama open da Ni, kina faɗa min abubuwan da suka shafe ki, at least ko da shawara zan ke taimaka Miki musamman irin wannan issues ɗin, kin ga dai Abdul-Hamid ɗana ne, amma ban ji daɗi ba da kika ɓoye min, kamata yayi kafin ki fara faɗa min, idan son ki yace ma yana yi ba zan hana ba, amma a matsayina na mahaifiyarki ya kamata na sani. Shima zan masa faɗa kar ki ƙara irin haka kin ji."
"In sha Allah ba zan ƙara ba Ummie, na gode."
"Yauwa yarinyar kirki, na ji daɗi ƙwarai,na jima ina fata da hasashen hakan, na gode Allah da ya tsara hakan. Ya ce Miki yana son ki ne?"
A kunyace tace "Eh"

"Ma sha Allah, na ji daɗi, Allah ya tabbatar da alkhairi, kin ga yanzu idan na mayar da ke can wurin su Inna in sun yadda su bar min ke ki dawo nan da zama gabaɗaya, In sun ƙi sai a ɓullo da zancen aurenku da Abdul, Kinga sai ki ci gaba da karatunki." Ba ta ce komai ba ita dai sai wasa take da yatsunta. Humaira wacce ke ƙunsheda baki da hannu ta cire hannun nata tana dariya sai kuma ta juyo wurin Hamra tace "Ina yini Aunty Hamra, sai da ke babbar Yaya" ta faɗa cikin sigar tsokala.

Duka Hamra ta kai mata tare da shagwaɓe murya tace "Ummie kin ganta ko?"
Haɗe fuska Ummie tayi tace "Ba na son shashanci fa Humaira, ki shiga taitayinki."
"To Hajjaju Ummie, yi haƙuri babbar Yaya, kaina bisa wuya, tuna nake kar ki sa babban Yaya yayi fushi ya daina siya min powder." Tana gama faɗin haka ta ruga bedroom a guje.

A ranar da Yaya Hamid ya ƙira Ummie ta tsare shi da batun. Cike da kunya ya amsa mata, ta yi musu fatan alkhairi sannan ta masa faɗa kan kiran dare da yake wa ɗiyarta, nan ya ba ta haƙuri. Bayan kwana biyu ya dawo daga Kaduna, sosai ya yi musu tsaraba musamman sarauniyar tasa. Washegari kuwa ya kai Hamra Ummul Qura Science Academy, Bayan an gama mata komai yace amma sai zuwa next week za ta fara zuwa, dama yadda ya tsara SS 1 za ta shiga, SS 2 tayi paper saboda shekarunta sun girmi haka, yanzu kamata yayi ace ta gama secondary school tunda ga Humaira ma ta gama admission kawai take jira kuma dai a girme Humaira ba za ta fi Hamra ba.

Sati mai zuwa kuwa ta fara zuwa school, sosai take fahimtar abinda ake tunda can dama tana da gold foundation a karatun na baya. Haka ɓangaren evening session ma wanda ake higher Islamic studies tana ba da himma. Cikar satinta biyu a gidan Ummie, ummie ta shirya mayar da ita ga su Inna. Kuka sosai Hamra tayi da ta ji wannan batu amma ya za tayi, tunda ummie ta rarrasheta haka Yaya Hamid ma yace zai ke zuwa sai hankalinta ya ɗan kwanta kaɗan, Da yamma aka haɗa mata kayayyakinta, uniform ɗinta da school bag ɗinta. Da yamma suka shirya dukkansu idanuwan Hamra da Humairah sun yi ja saboda kukan da suka sha na rabuwa a kuma keear juna da za su yi. Yaya Hamid sai da ya biya ta wani shopping mall, Dama can ya sanar da su su hada masa kaya, yana zuwa amsa yayi kawai yayi payment suka wuce.

Tunda suka karyo layin Dabar kifi gabanta ke faɗuwa har suka ƙarado unguwarsu. A bakin layinsu suka yi parking, Ummie ce ta ɗaga wayarta jin tana neman agaji tace "Ok mu har mun iso, to ka hanzarta, bari mu shiga." Almajirai dake ta zirya ganin babbar mota ta ƴan gayu a layin a tunaninsu ko sadaka aka zo bayarwa. Ɗaya daga cikinsu Ummie ta ƙira da sauri dukkansu suka zo gabanta suka tsugunna.
"Murmushi tayi tace sannunku ƴan matasa"
"Ina wuni Hajiya" suka faɗa cikin haɗin baki.
"Lafiya lau, mutum biyu kaɗai nake so, za su shiga min da kaya cikin layin nan. Wannan kuma" ta miƙo musu bunch na kuɗi tace "Ku raba, banda faɗa"
Godiya suka fara yayinda mutum biyun cikin suka ƙaraso, Yaya Hamid ya buɗe Boot ɗin motar suka ɗauki kayan ciki." Gaba Yaran suka yi su khma su Ummie na biye da su har suka iso daidai ƙofar gidan Inna.

Numfashi Hamra ta sauƙe yayinda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, gani take kamar in ta dawo ba lallai ta ƙara ganinsu ba. Fahimtar hakan da Ummie tayi ta kama Hannun Hamra tace "Calm down daughter, Babu abunda zai ƙara faruwa, remember, yhu're soon to be my in law, za ki dawo kusa da ni gabaɗaya, Musa da Abdul har abada. Numfashi ta sauƙe tace "To Ummie".
Shirun da tayi yayi daidai da fitowar yaran da suka kai kaya ciki. Kuɗi Ummie ta ba su dubu 3 tace su raba,nan suka fara godiya, daga haka suka nufi cikin gidan Inna bakinsu ɗauke da sallama.

Tabbas an samu banbanci a yau, tarba mai kyau aka musu bayan sun zauna an gaisa can aka kira Ummie a waya, ɗagawa tayi tana faɗin "Are You there? Ok ka shigo kawai." Sai kuma ta dubi Inna tace "Za a shigo"
"To to ba komai" ta faɗa cikin rawar murya. Ganin ɗan sanda yasa Inna faɗin "Innahu min sulemanu"
Murmushi kan fuskar ummie tace "Kada ki damu, tare muke da shi."
"To to"
Ummie tace "Mai gidan fa?"
"Ai ba ya nan, sai dai Rahama ta ƙira layinsa. Rahama Rahama "
"Na'am Inna ga Ni"
"Yi maza ki ƙira layin Babanki, kice ana nemansa a gida."
"To Inna" nan ta ƙira Baffa ta sanar da shi. Can ba a jima sai ga shi ya turo mashin ɗinsa ya faka. Fuska haɗe ya ƙarasa tunda ya fahimci su waye yayinda kuma farin ciki ya mamaye ransa ganin kamar sun maido masa da Hamra ne saboda haka zai bar rayuwar talauci yanzu kam.

Ƙarasawa yayi, bayan an gaisa Ummin tace, "To kamar dai yadda kuka ganmu dai tare muke da Hamra, ta dawo kamar yadda muka yi alƙawari, sai dai wannan dawowar cike take da sharruɗa masu tsauri, za a karanta muku sharruɗam idan har kun ga ba za ku iya bi ba kada ku damu ku sanar da mu, Ni nan zan iya ɗaukar Hamra na riƙe ta idan kuna ganin kamar nauyi ce a gareku." Da sauri Baffa yace "La ai Hajiya ba za a kuma maimaita abunda aka yi ba, In Allah ya so za ma mu iya kiyayewa, dama can sharrin shaiɗan ne." Ya faɗa tare da marairaice fuska. Murmusawa Police ɗin yayi yace "Kamr yadda Hajiya ta faɗa, sharruɗan ci gaba da zaman yarinyar nan Hamra a tare da ku sun haɗa da, samar mata rayuwa mai inganci, ba ta kulawa ta musamman, ciyar da ita, shayar da ita, tufatar da ita, sanya ta farin ciki da walwala kowanne lokaci, sauƙe duk wani nauyi nata da ke kanku, tallar da take yi a soke shi, Aikin da kuke bata kamar jaka, shima mun yi bincike a kai, matuƙar za ku ci gaba da yin hakan babu shakka zamu karɓe ta daga hannunku bayan horo mai tsanani da za a ba ku, ko da sau daya kuka suka ta baƙin ciki, saƙo ya Riske mu, ku tabbatar kashinku zai hura wuta ranar. Sannan kuma ko da sau ɗaya kuka bar ta da yunwa, za ku fuskanci hukunci kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar...."

Haka dai ya jero musu sharruɗa masu yawan gaske da tsauri wanda su kansu sun san ba iya kiyayewa za su yi ba sai dai da yake sun riga sun shirya wa abun suka amince. Takardar sa hannu aka ba su su biyun kowa ya saka hannu sannan police ya ba su copy ɗaya, ummie copy ɗaya, shima ya ɗauki copy ɗaya. Daga haka ya musu sallama yana fatan Allah ya ba su ikon kiyaye sharruɗan. Ba a jima ba su Ummie ma suka wuce, ummie har sai da ta zubar da ƙwalla, Hamra da Humaira kuwa ssosai suke kuka kamar ransu zai fita, da ƙyar aka ɓamɓare Humaira daga jikin Hamra, Yaya Hamid ya mata sallama yace mata sai sun yi waya. Ta tabbatar kuma tana zuwa school. Daga haka suka wuce zuciyoyinsu gabaɗaya babu daɗi.

Bayan tafiyarsu Hamra ta shiga da kayanta ɗaki, daga nan babu wanda ya ce mata ci kanki har dare yayi, abinci dai da aka gama an saka mata, ita kuwa ta karɓa taci. Bayan ta yi salla ta ɗauko littafanta na makaranta tana duddubawa. Rahama wacce gulma ke cinta ta dubi Hamra tace "Makaranta kike zuwa ne Hamra naga littafi gabanki?"
"Eh" Hamra ta ba ta amsa kai tsaye. Bakinta ta ja ta gimtse duk da dai da ta so faɗan magana ne amma da ta tuna sharruɗan da aka gindaya musu tuni ta tsuke bakinta. Bayan ta gama karatu tana shirin kwantawa saboda gobe da makaranta wayarta ta fara vibration. Ita fa har ta manta ma da tana da waya, da sauri ta miƙe ta njfi jakarta ta ɗauko wayar tare da duba mai kiran. "My Yaya" ta gani a rubuce hakan yasa ta ɗaga wayar da sauri tare da karawa a kunnenta. Ita dai Rahama sosai gulma ke cinta sai dai babu damar hakan.

Awanni sosai Hamra ta shafe da Yaya Hamid suna waya wacce yawanci yana sanar mata irin yadda yake matsananciyar kewarta kamar shekara guda suka yi ba sa tare, itama dai hakan zagewa tayi tana masa shagwaɓa, haka dai suka sha hirarsu suka more. Har suka gama Rahama kunnenta kan Hamra. Mtsowa Musa da ita tayi tace "Hamra waya kika siya?" Hamra tace "E"
"Mu gani don Allah." Miƙa mata wayar Hamra tayi, Rahama ta kunna torch light ɗin wayarta ƴar ƙaramar Tecno mai madannai. haska wayar tayi tana kallo, har cover ta cire saboda ta ga wace iri ce, ai kuwa ganin zanen apple yasa ta xari idanuwanta waje tace "Aifo kika siya Hamra?" Ƴar ƙaramar dariya Hamra tayi tace "E iPhone ake cewa Rahama ba Aifo ba."

Shiru Rahama tayi can tace "Hala a can aka saya Miki?"
"Eh"
"Ta yi kyau, nima Kinga wacce Inna tasa Baffa ya saya min." Kallonta Hamra tayi tace "Ma sha Allahu, ta yi kyau." Daga haka Hamra ta nufi shimfiɗarta ta kwanta.
Ganin ta kwnata yasa Rahama saurin ficewa ta nufi ɗakim Inna, ko sallama bata yi ba ta kutsa.
Baffa yace "Lafiya Rahama?"
Ƙasa-ƙasa tayi da muryata tace "Inna, Baffa, wallahi an saka Hamra a makaranta, har waya haifin ko haifo ake ce mata, irin wacce ake hoto da ita ɗin nan mai Apple a bayanta ɗinnan? Wallahi Inna har ita aka saya mata."
Murmusawa Baffa yayi yace "Haba Rahama, shine kika tada hankalinki? To ki kwantar da hankalinki Rahamatun Baba, kwanan nan za mu tashi a wannan gidan da kike gani, za mu koma gidan mai matukar kyau, kin ga makaranta kuwa? Jarrabawa kawai zan siya Miki ki tafi jami'a kai tsaye. Daga nan har mota zan saya Miki."
"Da gaske Baba?" She asked with eagerness

Cike da tabbatarwa Inna da Baba suka haɗa baki suka ce “Ƙwarai kuwa, ƙwarai da gaske." Inna ta ƙara da "Don haka kar ma ki nuna mata komai, ki ja bakinki kiyi shiru kawai, za ki ga yadda komai zai kasance. Idan kuma kika yi kuskuren yi mata wani abu, daga mu har ke za a tafi da mu gidan yari, Shikenan wannan rayuwarsa muka tsara ta ruguje, don haka ki kiyaye kin ji?"
"To Inna, zan kiyaye. Na kusa zama ƴar masu kuɗi ashe. Bari naje na kwanta."

Daga haka ta fice itama taje ta kwanta. Washegari da sassafe Hamra ta tashi daga bacci, bayan ta yi salla tayi wanka ta zauna tana shirya duba Physics ɗinta da za su yi test yau, ganin har rana ta fara ƙyallowa babu wanda ya tashi hakan yasa tayi haramar saka uniform ɗinta, tsafa da sandal ɗinta ta saka ta goya jakarta ta goyo sannan ta danna numbers, trolleynta ya buɗe, cikin kuɗaɗen da Yaya Hamid da Ummie suka bata ta zaro 1K ta fito. Ƙofar ɗakin Inna ta ƙwanƙwasa don ta musu sallama, amma tsawon mintuna uku ba su buɗe ba, hakan yasa ta fice kawai, bakin titi ta tafi ta tari abun hawa ta wuce school.

*Ku yi manage da wannan, gobe da safe zan muku wani.*

*React and share Fisabilillah.*

[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:

_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login